Showing 30001 words to 33000 words out of 58385 words
Chapter 11 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt
uwana bane?
Maryam tayi mata tambayar cikin mamaki kafin taci gaba da cewa mama dan Allah ki fad'a min illar hakan naga kin rud'e ko zai iya cutar danine?"
Tayi mata tambayar tana mai wani irin kafeta da ido, take haj. Sailuba ta dawo hayyacin ta tace "ba haka bane baby kinsan in mace da namiji suka keb'e to na ukun su shed'an ne shiyasa kikaga ina kaffa kaffa dake"
Cikin k'osawa da zancen tace "babu ma abinda zai faru insha Allah mama, kuma ni ban tab'a shiga d'akin ba sai yau" boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tace "to kar ki k'ara"
"Naji tafad'a tana shigewa d'akin ta domin harga Allah zancen ya gara gundurar ta.
Itama haj. Sailuba tana shiga d'akin ta ko maganar salla bata tsayiba ta lalubo no haj. Zakiyya ya doka mata kira,jim kad'an bayan ta daga babu sallama babu komai tace,
"Na shiga uku na na lalace" cikin rud'ewa haj. Zakiyya tace "lafiya k'awata me kuma ya faru daga rabuwanmu yanzu yanzun?
"Zakiyya'yar iskar yarinyar nan tana neman lalata mana shiri, nace zanyi maganin ta kin hana wallahi zata rusamin shirina na shekara goma sha bakwai adai dai lokacin danake hango nasara na kusantoni"
"Wai duk me yafaru kike irin wannan zantuka kamar na sambatu?" Haj. Zakiyya ta tambaye ta cikin sauri domin tanason tasan abinda ya firgita k'awar tata haka.
Batare da wani jinkiri ba haj. Sailuba ta kwashe duk abinda yafaru daga dawowar ta gidan ta fad'a mata ta k'ara da cewa "inajin tsoron kar su rusamin tsohuwar gabar da na dasa atsakaninsu tsayin shekaru,adaidai lokacin da nake son yarinyar ta kasance mara"""'''' da kata haj. Zakiyya tayi saurin katse ta "wai kina tantama akan aikin sabon bokannan ne?"
Haj. Zakiyya tayi mata tambayar cikin son karfafa mata gwaiwa" bana shakka amma ina tsoron tugun uban shegiyar matar nan kinsan shima tsohon d'an tsubbu ne"
"Karki damu k'awata idan yanzun yatashi mu atafe muka kwana" nan taci gaba da karfafa mata gwaiwa akan mugun shirin su.
Tana shiga d'akinta ta yi gaggawar shiga wanka domin ana shirin shiga massalaci ne lokacin, wanka tayi ta d'auro alwala ta fito d'aure da tawul bata tsaya wani shafe shafe ba ta zura doguwar riga ta saka hijab ta haye saman abin salla.
bayan ta idar da sallar ne tayi zikiri da sauri ta tashi ta cire rigan ta hau shafe shafe kafin tagama har an kira Isha kasancewar lokacin magriba ya kwace mata sosai.
Sai da ta gabatar da sallar tayi karatun alqur ani mai girma kafin ta shirya cikin wasu riga da wando masu masifar kyau da daukar hankali farare kar, sai wani bluen rubutu da aka yi agaban rigar ONLY FOR YOU shine abinda aka rubuta, wandon kuma da kad'an ya wuce gwaiwar ta kayan sunyi masifar yi mata kyau ta taje dogon gashin kanta tayi parking d'inshi takawo wani bluen Vandana ta sakawa kanta ba d'an k'aramin kyau tayi ba haka nan ta hauyiwa kanta salfie da wayarta.
Tana cikin d'aukan kanta a hotunan MD da Nassar suka shigo d'akin tana ganin MD tayi masifar d'aure fuska, saboda abinda yayi mata d'azu, murmushi ya saki yana shafar gefen face d'inshi.
K'arasowa yayi kusa da ita ganin haka yasa ta maida kanta kasa tana wani cin magani, kafeta yayi da ido yanajin kamar ya had'iye ta tsabar masifar kyuan da tayi masa,
Hannu yasa ya d'ago habanta ya manna mata kiss a goshi kafin amshe wayan ya d'an rab'a ta da jikinsa kad'an ya soma d'aukar su hotuna.
Nassar yace "wow gaskiya bross kunyi kyau sosai kamar wasu masoya" da sauri ya dafe bakinsa saboda kallon dayaga MD yana masa fuskansa d'auke da wani irin murmushi.
"Nima ayi dani Nassar ya fad'a yana shiga tsakiyar su haka suka kasance ashiriri ce yayin da halin na Maryam ya motsa dan bata kula MD ba saboda abinda yayi mata.
Suna haka wayan Muhammad yai k'ara yana ganin layin Baffa na nageria yai saurin d'agawa"Allah ya temaki Baffa na" cewar MD yana sakin wani k'awataccen murmushi, duk shiru Nassar da Maryam sukayi jin MD ya ambaci Baffa
"Kuzo ka d'auke ni ina airport" shine abinda Baffa yace wa MD ya katse kiran "yeee" MD yafad'a da d'an tsallensa,duk suka kafeshi da ido kafin Nassar yace
"Baffa ne ya dawo?"
Hannu ya mik'a masa suka tafa "dad'i na dakai gane wa" inji MD yana murmushi "zo muje mu d'auko shi" yafad'a yana kama hannun yaron
"Nima zani" ya tsinkayo muryanta d'an juyowa yayi ya kalli kayan dake jikin ta sai kuma ya d'an girgiza mata kansa "gaskiya bazamu iya jiran har ki canja kaya ba yafad'a yana d'aure fuska"
"Dan Allah after kawai zan d'ora akai" ta fad'a cikin marairaicewa
" Minti biyu ya fad'a suna ficewa rik'e da hannun Nassar.
Taku ce MAMAN Islam
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 26
Jikin mota ta same su sai zance Nassar yake zuba masa yayin da shi kuma hankalinsa yake kan phone d'insa yanata faman latsawa.
Kamshinta ne yasa shi saurin d'agowa ya kafeta da ido yayin da zuciyar sa ya hau wani irin bugawa har d'an rawa rawa jikinsa ya soma abinda bai tab'a faruwa dashi ba.
"Muje" ta fad'a cikin fad'uwar gaba saboda shegen kallon dataga ya kafeta dashi, aranta tana bitar kalaman Mama anya ba wani abun ta hangoba kuwa?
Take raya hakan aranta sanda take shiga cikin motar, "my princess dan Allah kintaho da wayarki ki aramin?"
Cewar Abdul Nassar da ya zuroda kansa ta b'angaren datake,
"Kayi me dashi?" ta tambaye shi batare da ta d'ago ta kalleshi ba
"Boy zan kira anty dan Allah"
Kafin tace mai wani abu wayan yayi k'ara hakanan taji gabanta ya fad'i ganin no ba suna da mamaki aranta tace waye Kuma yake kirana ?
"Ki daga mana" take tsinkayo muryansa,
Dagawar tayi ba tareda ta k'ara kallonshi ba kafin tayi magana taji ance
" Amincin Allah yatabbata agareki yake saurauniyar kyawawa" wani irin murmushi ne ya sub'uce mata, zuwa yanzun ta fara sabawa da halin d boy wanda yabi ya mak'ak'ale mata ga d'anbanzan iya kalami me sanyaya Rai"
"Tareda kai ma aboc...........wani irin burki da MD ya take ne yasaka tayi wani tsalle ta gwaru da murgin motar wayar Kuma bata fad'i ko ina ba sai saman cinyarsa.
Hannu yasa ya d'auke wayar ya zurata acikin aljihun sa ya ya zagayo a zuciye yace "zoki ki fice min a mota" da mamaki ta tsaya kallonsa domin bataga abinda tayi masaba da zaiyi irin wannan fusatar haka lokaci guda "zoki fita nace malama" ya fad'a cikin wani irin buga tsawa, ai batasan lokacin data fito cikin wani irin rawar jiki ba, tana kallonsa ya koma yaja motar sa da wani irin matsiyacin gudu ya bud'e ta da qura, agogon hannunta ta duba tara saura batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba ta daga kai tana kallon sama yadda wani irin hadari ya murtuke bak'i k'irjinta ta dafe dayake wani fitinannen bugu tace "na shiga uku ni mero, me kuma nayiwa wannan mugun mutumin da zai ajeni anan" ta fad'a afili cikin muryan kuka yayin da aka wani irin kece da ruwa mai mugun k'arfi ga Maryam da mugun tsoron hadari bare ya sauketa a wannan wajen da babu kowa sannan babu gida kusa, jitai wani irin tsanar shi ya dawo mata sabuwa dal, tafara takawa a hankali yayin da take kuka sosai jikinta na wani irin rawa.
Nassar kuwa ganin yadda bross d'in nasu yake wani irin tuk'in ganganci yasaka yai tsuru abayan mota yayin da tausayin Maryam ya cika ransa domin baiga abinda tayi masaba zai ajeta wajen da babu kowa sam bai kula da hadarin ba sai zuban ruwa yaji wanda yasa MD ta ka burkin dole.
Fashewa da kuka Nassar yayi da mugun k'arfi kafin yace fili "shikenan Addana ta mutu" yafad'a yana kuka sosai kafeshi MD yayi sosai kafin yajawo yaron jikinsa yana cewa "kai me kace?"
Memakon ya amsa masa sai cewa yayi"me tamaka bross zaka ajeta inda babu kowa ita kad'ai idan wani mugun abin yasameta fa?
Gashi kuma tana tsoron ruwan sama sosai idan ana ruwa babu inda take fita"
Sosai gabansa ya fad'i da maganganu yaron har baisan sanda ya tada motar batareda ya Kuma cewa komai ba ya figeta yana maijin haushin kansa akan abinda yay mata duk da cewa har lokacin zuciyar sa masifar zafi yake masa na yadda yaji tana magana da wani wanda yarasa me yasashi jin hakan?
Ita ko Maryam fara takawa tayi a hankali cikin wani irin tsoro jin yadda wajen yai tsit babu komai sai k'aran zubar ruwa yayin da zuciyar ta yake wani irin bugun dayasa jikinta rawa sosai tayi nisa da inda ya ajeta sosai tana tafi tana share ruwan dayake feso mata afuska wanda yake wanke hawayen dayake tafaman zubo mata babu ka'k'k'autawa.
Yana cikin tuk'in kiran Baffa ya k'ara shigowa faking yayi a gefe kafin ya d'aga "karka zo naga garin da hadari na hau tixi" abinda Baffa ya fad'a kenan ya kashe wayar batare da yace komaiba, saboda kar Baffa ya gane halin da yake ciki.
Sanda yazo inda ya sauketa ta ya rage gudu sosai zuciyar sa ya buga dan ganin bata wajen yayin da Nassar ya kuma fashewa da kuka dan a tunaninasa wani abun ne yasamu 'yar uwarsa.
"Dalla malam ka karka damemu ka rufe mana baki d'if ya d'in ke bakinsa saboda yadda yaga bross d'in yai wani irin canza kama fuskar nan tayi wani irin ja yayinda ya soma zargin kansa akan abinda yayi mata sam baiga kyautawar saba ko kad'an.
A hankali ya cigaba da jan motar yana d'an duddubawa ko zai ganta Maryam wacce taci kuka ta k'oshi ga d'an banzan dukan da ruwa yake mata wanda yasa wani mugun zazzab'i ya saukar mata lokaci guda ta sami gefen hanya ta zauna tana ta faman shashshek'a.
"Gata can bross" Nassar wanda shima yaci kuka ya k'oshi ya fad'a yana nunota tana zaune kan wani dutse data gani abakin hanya jikinta yana wani irin rawa.
Da mugun gudu ya bud'e motar ya fita yana cewa Nassar kar ya fito a cikin ruwan nan, bak'aramin sanyin jikinsa yayi ba ganin yadda ta had'e Kai da gwaiwar ta tana faman shashshek'a, a hankali ya durk'usa agabanta ya dafa kafad'anta.
D'agowa tayi a mugun firgice domin batayi tunanin ma zai dayiba asanin datayi mai na tsantsar rashin mutunci sannan kuma tasan ba wai yana sonsu bane kamar yadda mamanta ta fad'a Mata.
Wani irin kallo ta watsa masa da idanunta da sukayi wani irin ja wanda har lokacin basu daina zubo da ruwa "sorry" ya fad'a can k'asan mak'oshi cikin d'an rawa rawan murya "sorry for what?" ta tambaye shi cikin tsantsar b'acin rai da bak'in cikin abinda yai mata.
"Zo mu tafi" ya fad'a yana kallon yadda ruwa yake tsiyayo Mata tundaga kanta yana kwanrawa kayan jikinta duk sun wani lafe mata ajiki dake ruwa ake tsugawa bana wasa ba, banza tayi dashi kamar bataji me yace ba.
"Dan Allah" ya k'ara fad'a kamar maijin tsoro, yayin da shima sanyin ruwan yafara ratsashi " ba ruwana da kai kar ka k'ara shiga harkana babu ni babu kai mugu kawai" ta fad'a cikin rawan murya sosai yayin da wani irin sanyi yake k'ara shigarta hatta hak'orinta yana jin yadda suke bugan juna
"Dan Allah" ya k'ara fad'a kamar zai mata kuka mak'e mai kafad'a tayi tace "um um na tsan..........wani irin fisgota yayi kafin ta k'arasa ya had'e bakinsu waje guda yana mata wani irin shan mugunta sai da ta raina kanata kafin ya sakar mata bakin cikin wani irin b'acin rai yace "sai wancen dan iskan saurayin naki ne baki tsanaba ko?
Ni kikewa wannan abun akan na nuna b'acin raina akan kina kula wani banza can daban ko na gode" ya fad'a muryan shi na d'an rawa kad'an.
Sai yanzu ta gane dalilin dayasa ya gane mata wannan bala in yabarta a cikin tashin hankali da tsoro jitai ranta ya dad'a mugun b'aci zuciyar ta ya wani irin dakewa ta mik'e kawai ta kama tafiya dan taci alwashin bazataje a motarsa ba "ke meye haka?" ya fad'a cikin d'an tsawa tsawa ko kallon inda yake batayi ba taci gaba da tafiya.
Duk irin yadda yaso rarrashin ta abin gagara yayi hakan yasaka shi tattare hannun riga ya sunkce ta tana wuwulla k'afa tana komai ya nufi mota da ita
Plss manage
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 27
Bud'e motar yai ya wulla baya kusa da Nassar sai uban kuka take jijiyan kanta sunyi wani rud'u rud'u fuskar nan tayi jajur tsabar kukan da takeci.
Shiru Nassar yayi yana kallon yadda Adda nashi take kuka ga ruwan dayake ta faman diga daga jikinta rawan da jikinta yake kawai ya tabbatar masa da akwai zazzab'i atare da ita.
MD tuk'in yake amma ba acikin nutsuwa ba domin ba k'aramin bugun zuciyar sa kukanta yake ba ko kad'an baiji dad'in abinda yayi mataba sai dai ko kad'an zuciyarsa ta kasa amsar laifin ganinsa bai kamata ace ta tsaya magana da wani k'aton agabansa sosai abin ya masa zafi aransa, wata zuciyar Kuma cemai tayi inbanda abinka kasan waye da har zakayi saurin fushi haka "zai wuce d'an iskan mate d'in nan nata" ya fad'a asarari Kuma da k'arfi, duk suka bishi da kallo har Maryam datake kuka sai data tsagaita jin yadda ya bugi sitiyarin da mugun k'arfi.
Suna zuwa gida taba tsaya amsar wayanta ba ta balle murfin motar tayi cikin gida da gudu tana shashshek'a ta wuce mama da Ammey a falon duk suka bita da kallo, saida tasawa d'akin key tasan sarai sai Mama ta biyota jikak'k'un kayan ta cire ta shiga ta had'a ruwa mai mugun zafi har lokacin rawan sanyi take sosai ta shige cikin ruwan tana faman sauke ajiyan zuciya sai da ta gasa jikin ta sosai kafin tayi wanka ta fito ta shafa mai ta haye gado ranan bata had'u da Baffanta duk da irin yadda tayi kewansa.
Washe gari ma bata fito da wuriba sai da ta gama duk nuk'u nuk'un ta sannan ta salla wanka ta ta tsara kwalliya mai kyau da d'aukan hankali ta fito cikin nutsuwar ta duk suka bita da kallo har tayi wani fayau da ita.
Baffa ya dubeta yana murmushi ya mik'a ta hannu"zonan ki zauna, ya fad'a yana nuna mata gefensa nayi kewan ku sosai yarana" ya fad'a yayin da tasako hannunta cikin nashi ya zaunar da ita a kujeran kusa dashi.
Tunda ta fito ya kafeta da ido sai yaga ta k'ara masa wani fitinannen kyau, gaida iyayen nata tayi, kamar ta share shi sai kuma ta gaidaahi cikin sanyin murya amsawa yayi yana k'ureta da ido, tai masifar had'e rai tana had'a tea.
Su Mama suna gama karyawa suka bar wajen suka koma falon Baffa da akwai abinda suke son tattaunawa.
Yana ganin fitar su ya ture nashi abincin ya kwantar da kansa saman tebur d'in yana binta da wani fitinannen kallo Nassar na ganin haka ta d'auke ragowar abincin sa yabar wajen.
Gaba d'aya ya takura da wannan banzan kallon nasa sai dai bata son tayi abinda zai gane hakan, kasa cin abincin tayi sai ruwan shayin da take ta karb'a tashi yai ya dawo kusa da ita kofin shayin ya karb'a daga hannunta ya zauna ya kai bakin ta, d'auke kanta tayi tareda k'ara tamke fuska.
"Kiyi hak'uri dan Allah, ya jikin naki?" ya fad'a yana shafar gefen fuskar ta, banza tayi da shi idanunta yana cikowa da hawaye ko abinda d boy yai mata bai sosa mata rai kamar na MD ba.
Juyo da fuskar ta yayi kusa da shi yana k'ara kai mata abincin bakinta "karki min kuka, kiyi hak'uri dan Allah" ya fad'a cikin sanyin murya, batare da tace k'ala ba ta yunk'ura zata bar masa wajen ya daka mata tsawar dayasa ta koma ta zauna batare da tasan tayi hakan.
"Wallahi yanzu sai na tattaka ki dan kinga ina lallab'a ki shine kike neman ki kawo min rainin hankali karb'i dalla malama" ya fad'a yana kai mata abincin baki ganin yanda yai kicin kicin da rai yasa ta bud'e bakin ya zuba mata abincin haka ya dinga bata tana karb'a tana hawaye har saida ya tabbatar ta k'oshi kafin ya bata ruwa tasha ya kama hannunta ta suka nufi part d'insa.
Duk jiya bai iya runtsawa ba saboda tunanin abinda yayi mata iya binciken sa nason gano dalilin yi mata haka amma amsar d'aya ne tayi waya da wani agabansa dalilin fushin sa akan hakan simple words INA SON TA duk ta yadda ya juya al'amarin amsar d'ayace abin ya masifar tayar masa da hankali bai tab'a tunanin hakan daga zuciyar saba sam batayi masa adalci ba kuma ta zalunce shi tayi mai abinda zai hana shi cika alk'awarin daya daukarwa Baffa, dan iya jiya kawai ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba ganin halin data shiga sosai ya bama kansa laifi akan abinda yayi Mata.
Suna shiga falon ya zaunar da ita saman kujera ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta yana murzawa a hankali wanda hakan yasa taji wani irin yarrrrrrrr ajikinta da k'arfi ta k'wace hannunta ga mamakinta sai ji tayi yace "bani da lafiya" shine abin taji ya fad'a cikin wata irin murya wadda take taji wani irin kasala ya rufeta saboda salon dayai maganar kasa ce masa komai tayi sai ma k'asa da ta maida kanta tana faman cukwaikwauye gefen d'ankwalin doguwar rigan da yake jikinta
"Ni kaina bansan abinda yasa nayi miki hakan ba princess nasan ban kyautaba abinda nayi, abin yayi mugun damuna na rasa yadda zanyi na kasa runtsawa saboda neman dalilin da yasaka nayi miki hakan, sai dai dalilin dana samo bai min dad'i ba ko kad'an Maryam" ya k'arasa da kiran ainihin sunanta wanda sai yaune ta tab'a jin ya kira sunanta iya tsawon rayuwar ta, sai taji wani iri aranta sai dai bata d'ago kaiba bare tace wani abu.
Ga mamakinta sai ya kamo fuskar ta ya juyo da ita saitin tashi