Showing 45001 words to 48000 words out of 58385 words
Chapter 16 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt
shanyar taki ta bushe Allah badan gobe zan koma ba da tuni nayi tafiyata"
"Sorry dear gidan su name sake mukaje bamu tadda taba har sai da muka jira ta dawo"
"Naji kina jam u kedawa?"
"Tare da bross mana" wani irin waro ido Halima tayi tace "kedawa?"
Kunsan fa Halima bata da masaniyar shirin Maryam MD domin bata da yawan surutun mara dalili.
"Ai kinji abinda nace kema neman zance ne kawai irin naki"
"Ai abunne dole yabani mamaki yadda baku shiri da bross kuma kice tare kuka fita ai kinsan dole mamaki yamin illah"
"Humm wai kinsan ma wani abu kuwa?"
"A'a"
"Wai sona yake karkiga yadda yakemin naci kamar bashi ba duk ya wani susu ce"
"Ke dan Allah dena fadaymin dama ba babanku d'aya ba?"
Ta fad'a duk idanunta awaje tsabar mamaki
"To ni tsabar tsorata ranan da yace yana sona ihu na dinga zunduma masa nayi tunanin kwakwalwan sa ne ya tab'u wallahi"
Jinjina kai Halima tayi tace "haba wallahi wani lokacin nakan zauna nayi tunanin yadda Ammey take ba wata babba ace ta haifi kamar bross da ace kece akace yarta babu wanda zai yi mamaki ammafa bross abin yana d'aure min kai, ke amma kinsami dami akala wallahi na miki murna bross ai miji ne na yaw........
"Ke dalla rufewa mutane baki zaki fara halin naki babu fullstop ba qommer nace miki ina son sane da zaki wani fara yyyyyyyy murya kamar ta yan China"
Harara Halima ta galla mata tace "ank'i a rufe banza mara mutunci ai dama inka shekara dubu bakaga mutum ba tambaya halinsa ni zakiwa iskanci koda yake ni na kawo kaina bari nay tafiyana"
"Jeki mana seme dama duk kin isheni kin saka min ciwon kai"
Sai da sukayi halin naau da suka saba duk had'uwa kafin su daidaita su hau zance na gaskiya da gaskiya, wannan halin nasu tun suna yara suka taso fashi Halima surutu ratata Maryam kuma fad'a.
Sun jima sosai Maryam ta fad'awa Halima gaskiya itafa bata son MD Halima tace "karki damu yar uwa wata rana zakiso shi har kiyi kishin sa kawai dai mudage da addu'ar Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi amen"
Sosai Halima tabawa Maryam shawarwari masu kyau yayin da sukayi sallama dake hutunsu ya kare zata koma schl itama Maryam d'in sati mai kamawa zata koma.
Tsakanins Maryam da Halima akwai so da k'auna akwai yarda da amana akwai shak'uwa mai tsanani wanda yasamo asali tun suna yan yara alokacin basa rabuwa kullum suna tare ay fad'a a shirya kullum basa gajiya da dambe da f basa b'oyewa junanau duk wani abu har kawo wannan lokacin.
Name sake d'in ta kuwa k'awance ne irin na makaranta sannan babu abinda tasani akanta banda mahaifinta da tasan mai k'udi ne dan har yanzuma bata bata damar zuwa gidansu ba dan Maryam bata jan mutum ajiki sai ta gama karantar waye shi, itama dai bata da wani aibi tana da kirki ga kamewa wanna neyasa Maryam k'ulla kanwace da ita har takai ga tafara temakonta.
Bayan tafiyar Halima Maryam tayi wanka ta fito duk a dining room ta samesu har Baffa sai mama da har wannan lokacin bata dawoba, kujeran kusa da Baffa ta jawo ta zauna suka sakashi atsakiya ita da Nassar yayin da Ammey tata kujerar ke kallon ta Baffa "ke uwar taki bata fad'a miki inda ta tafi ba yau gashi har anyi issha?"
Dan yamutsa fuskar ta tayi itama yawon na mama yana mugun damunta tace "zai wuce gidan waccen haj. Zakiyyar ni bata fad'a min inda zata"
Kwafa Baffa yay cikin b'acin rai kafin yace komai MD ya shigo wanda gaba d'aya kamshinsa ya cikasu kujeran dake kallon ta Maryam ya ja ya zauna ya wani kafeta da ido ko kunyar su Baffan bayaji.
Tana ganin haka ta wani tsare gida yayin da Baffa yace "zamu yi magana daku keda Sailuba idan ta dawo a yawon nata"
Had'e rai Ammey tayi amma bata tanka ba yayin da Maryam ta sunkuyar da kanta k'asa tak'i yarda koda wasa ta kalli inda MD yake shikam ko ajikinsa ya fitineta da kallo yana cin abincin sa, bata wani ci abin kirki ba saboda yadda ya takurata ta mik'e , Ammey ta dubeta tace "ya haka baby banason fa zama da yunwa"
Had'e rai tayi tana hararan MD k'asa k'asa tace "k'oshi nayi ne" daga haka bata jira cewar suba ta bar wajen, duk suka bita da kallo, shima MD kad'an ya k'ara ya mik'e direct d'akinta ya wuce ilai kuwa ya sameta tayi d'ai d'ai asaman gadonta da ice cream tana faman sha sam bai ma kula da abinda takeyi ba sai da ya buga uban sufa ya fad'a kusa da ita sannan ya kula da kayan sanyin da take sha k'ala bai ce mata ba ya zare robar a hankali ya kai saman frich ya aje ya dawo ya kuma kwanciya tareda d'ora kansa saman kafafunta a wani firgice ta kai idanunta saman fuskar shi idanunsa ma shi a lumshe suke take jikinta ya kama wani irin rawa cikin tsantsar tashin hankali da rawan murya tace me mey meye ha ka ni fa ban a son is Kan ci tayi maganar a rarrabe tsabar tashin hankalin data shiga, wani muskilin murmushi ya saki yace
Muje zuwa daga
MAMAN ISLAM
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Gaisuwa ta musamman gareku hazikai kuma jajurtattu a kungiyata
Princess Aisha
Miss flower
Maryam H
Allah ya kara muku juriya da hak'uri. Allah ya kara had'e kanmu first class mu dad'e muyi k'arko 💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿
Page 37
"Nine d'an iskan princess?" Ya fad'a yana kallonta ko k'ibtawa bayayi had'e rai tayi tareda fashe wa da kuka maimakon ya saketa kamar yadda take buk'ata sai kawai ya rungumeta take zuciyar ta yayi wani irin mahaukacin buga ta fara k'ok'arin tureshi amma ina k'arfin ba d'aya bane.
"Na tsaneka" ta fad'a cikin kuka sakinta yayi a firgice yace "ni d'in baby ni Muhammad dinki kike cewa kin tsana?"
Harara ta galla masa da idanunta da suka koma launin ja ta murgud'a masa baki ta fice daga d'akin tayi d'akin Ammey wacce itama bata d'akin ta fat d'in Baffa.
Bata jima ba Ammey ta shigo hannunta d'auke da Leda da kaya aciki Nassar na biye da ita yana mitar ta hana Baffa siya masa ways.
Da kallo tabi Maryam wacce ta takure waje d'aya asaman gadonta, kana kallonta kasan akwai abinda yake damunta "Ammey zoki zauna dan Allah muyi magana" tayi saurin katse Ammey tun kafin tayi mata tambayar da bata da amsa,
A hankali Ammey ta tako kusa da Maryam tasamu ta zauna ita kuma tayi saurin d'ora kanta ajikinta tana sauke ajiyan zuciya sannan tace "Ammey zan iya auren MD?" ta fad'a kamar yadda ta tab'a jin m Bash ya kirashi da sunan
Gaban Ammey ne yai masifar fad'uwa a d'an razane ta dubeta tace "waye kuma hakan?" Ganin yadda tayi saida tai mugun bata dariya kafin tace "Muhammad dinki nefa MD nima abokansa naji suna fad'a shine na d'ana" ta fad'a tana b'oye face d'inta ajikinta.
Wani irin sanyi Ammey yaji har batasan sanda ta rungumeta ba tace "zaki iya mana baby me zaihana ai bazaki tab'a samun kamar saba kamilin mutum managarci wanda yasan darajanki"
"Oh ji Ammey saboda shi d'in na wajen kine kike irin wannan zuzuta shin?"
Dariya Ammey tayi ta lakace mata hanci tace ba haka bane baby ai d'ana d'aya ne tamkar da dubu nasan shi nasan halinshi yana da halin kwarai zakiji dad'in rayuwa da shi domin yana da kyautawa"
"Shikenan Ammey tunda kema kin amince da nagartar sa naji na amince zan aureshi kamar yadda ya buk'ata amma fa na sanar dashi cewa bana sonshi hasali ma ni ban tab'a jin sonsa araina ba kamar yadda babu son kowane d'a namiji a zuciyana, to yace yaji ya amince shikenan magana ya kare" daga haka ta mik'e dan fita daga d'akin Ammey ta bita da kallo har ta fice ba k'aramin farin ciki ta tsinci kanta aciki ba duk da cewa maganar ta na k'arshe bai mata dad'i ba.
Ba k'aramin mamaki tasha ba ganin har lokacin MD yana d'akinta akwance ya wani yi mata d'are d'are asaman gado kafeshi tayi da ido tana k'arewa baiwar ubangiji kallo MD ba k'aramin mai kyau bane ta ayyana hakan cikin ranta.
A hankali ta k'arasa rufe k'ofar ta tafi cikin sand'a tana lek'a fuskar shi ya kuwa fisgota da k'arfi ta fad'a kanshi ta bud'a baki zata zunduma ihu yayi saurin toshe mata bakin da hannunsa, tashi yai ya zauna itama ya zaunar da ita suna kallon juna yadda tayi wani tsuru tsuru da ita abin yaso bashi dariya sai kawai ya murmusa baice komaiba ba sai faman kallonta yake.
Yadda yake faman kallonta ba k'aramin takura ta yayi ba ta wani had'e rai tana tura baki bakin ya sumbata ta wani zaro idanu tana kallonsa da k'yar tace "Allah saina fasa aurenka idan kanamin irin wannan abun"
"Yi hak'uri my happiness na daina, amma kisani iya hakan ma ba k'aramin kokari nake ba princess sonki yamin illah bansan lokacin da sonki yayi min irin wannan kamun ba yabi jinin jikina ya mamaye JININA ba dan Allah ki zauna dani koda bakya sona zanfi samun nutsuwa idan kina kusa dani" daga haka bai jira cewar ta ba ya sumbaci goshin ta ya sauka yafice daga d'akin, binsa tayi da kallo kafin ta saki murmushin dabata san ko na menene ba asarari Kuma tace "maye kawai" sai kuma ta shek'e da dariya tana buga cinya.
Cikin sauran kwanakin hutunsu ba k'aramin hanata sakat MD yayi ba tun tanajin haushin sa har ta fara sabawa ya masifar nanuk'e mata duk inda zata sai ya bita matuk'ar yana gida idan ya fita office kuwa kafin ya dawo tana samun kiransa fiye da ashirin tun tana jin haushin sa har ta daina saima wani mugun shak'uwa da yafara shiga tsakaninsu sosai ta fara kamuwa da son MD batare da tasan hakan ba ita dai tasan cewa muddun yana nesa da ita ta rik'a kewar sa in yana kusa da ita kuma tana samun nutsuwa da farin ciki bata gajiya da daddad'an kalaman shi masu sanyata nishadi.
Cikin haka hutunsu ya kare suka koma makaranta karatu suke babu sauk'i kasancewar suna shekaran su na k'arshe hakanne yasa Maryam bata da sukuni har rama ta somayi duk da kasancewar tana samu temako daga MD dan shima idan baku manta ba saida ya fara karatun likita kafin ya koma ya zama soja.
"Na fad'a miki kiyi hak'uri ta k'arasa karatun kafin na tarwatsa komai"
"Bazan iya ba boka itace fa ta wargatsa min shirina na shekara ashirin da d'aya shirina na tundaga ranan haihuwar ta har zuwa yau boka badan ina tsoron rayuwar kurkuku ba da wallahi da hannuna zan kashe ta kamar yadda ta kashe min farin ciki na"
Shi kenan tunda kince haka amma kada kiyi kuka dani duk abinda yafaru ki kuka da kanki kasancewar idanunta sun riga da sun rufe tace taji ta gani kuma ta amince.
"Boka ana gama mata aikinta nima nawa yasamu kamar yadda muka alk'awarta"
"Ke zakiyya burinki zai cika kuma Deedah bata da irin halin ki gaskiya tana da wankakken zuciya amma fa wannan buri naki ba makawa zai cika sannan kuma komai zai wargatse"
Maguguna ya had'a musu tare da fad'a musu yadda za ayi kamar yadda aka saba sosai taji dad'in shirin su na wannan lokacin.
Suna fitowa haj. Zakiyya ta dubeta tace "maganar mu na zuwa India?"
"Yana nan amma ba yanzu ba sai komai ya kammala sai kawai nayi b'atan dabo aneme ni arasa koya kikaga?"
Suka shek'e da dariya haj. Zakiyya tace Allah k'awata kinsan takan tsiya kina ta sha'aninki hankali kwance"
"Inafa kwanciyar hankali buri bai cika ba ai CIKAR BURINA shine kwanciyar hankali na"
Haka suka tafi suna hiransu na mugun abu har suka cimma inda suke faking idan sunzo
Wannan karon zuwan bazata Baffa yay musu sai ganinsa kawai sukayi ranan ma Sailuba taje yankan busa dan tafiyar su yana ta matsowa kai ranan Baffa ba k'aramin ruwan tujara ya zubar ba ya addabi Ammey da fitina wai duk laifin tane da bata sanar masa abinda ke faruwa.
Cikin b'acin rai Ammey tace "kaga malam kada ka isheni ni nake aurenta da zan samata ido?
Tsayama da zakace haka naga agaban kama ficewar ta takeyi kataba cewa dan me saini daka raina zakasa agaba da bala i wallahi nagaji kar ka k'ara sakani a shirgin ku da matarka matuk'ar kana son zaman lafiya a tsakaninmu idan Kuma tashin hankalin kake so nima na iya"
Daga haka ta bige zaninta tabar masa wajen cikin b'acin rai, shima yasani k'ureta yayi shiyasa ta zage yau take mayar masa da martani.
Muje zuwa
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 38
"Dad dan Allah ka taimaka min na rasa yadda zanyi na fad'awa yarinyar nan irin son da nake mata gashi saura sati biyu mugama karatun mu kasan tare zamu gama dan Allah dad kayi min rai"
Wani mugun kallon Abba AL HASSAN ya jefawa d boy kafin yace "kaga Kamal ka fita daga idona na rufe karaba ni da wannan shed'anin yaron dan wallahi ko mata sun kare a duniya bazan bari ka auri wannan yarinyar ba yayanta da kake gani ba k'aramin aljanin mutum bane bashi da mutunci ko kad'an d'an iska kamar mai gani har hanji duk sanda kayana suka shigo saya yajamin babbar asara"
Fashewa da kuka d boy yayi dan har ga Allah yana masifar son maryam ga Dad d'in sa idan yakafe akan abu shegen taurin Kaine dashi.
Mahaifiyar sa ya kalla yana kuka sosa yace "mammy dan Allah kisa baki dad ya barni da wacce nake so"
"Uwata ce ita da zatasani yin abinta banga dama ba dagakai har Maimunan wallahi sai na had'a ku naci kaza kazanku" ya antayo musu wani zagi mai rai da lafiya.
Take ran haj. Maimuna ya b'aci ta kasa daurewa tace "ka daici naka uban me na maka kaji nashiga maganar ku bare ka dagamin hankali tsabar neman fitina kasan bazaka tab'a min in k'yale kaba wallahi tunda kai mutumin banza ne mara mutunci kawai"
"Iyayen kine marasa mutunci yar marasa tarbiyya wadda batasan girma da martaban na gaba da ita ba"
"Iyayen kadai sune iyayen banza suna kallon d'an su yana hark'allar miyagun k'wayoyi amma basa iya tab'uka komai tur da iyaye irin naka wallahi, ni kuwa iyayena sun bani tarbiyyan da har ka gani ka yaba kuma ka aure"
Nanfa rigima ta balle harda mare mare dan haj. Maimuna bata ragawa Abba AL HASSAN ko kad'an tunda ta fahimci tantirin d'an duniya ne ga zagi nacin mutunci.
Cikin fushi d boy ya fice yabar musu gidan yana hawayen bak'in cikin wannan halin na iyayen sa wanda ko kunyar idanunsa basaji idan fitinar su ya motsa.
Tun bayan da ta shige d'akin ta Baffa bai karajin d'uriyar taba ya tabbatar da fushi tayi, maganar gaskiya yana mugun tsoron fushin Amina dan bata iya fushi ba idan tayi masa fushi yana matuk'ar shan wahala.
Yana shirin tashi yabita har d'akinta haj. Sailuba tana shigowa fasa tashin yayi ya koma ya zauna ya kafeta da ido, ganin irin kallon dayake binta dashi yasa ta d'an sha jinin jikinta sai ta wayance da fad'in
"La Baffa yaushe ka dawo irin wannan dawowa haka babu sanar wa? sannu da zuwa" nan dai tahau masa borin kunya.
Shi kam k'ala baice mata ba kafeta kawai yay da Ido hukunci yake mata da haka, yayin da ta rasa yadda zatayi, sai da ya tabbatar da yagama sanyaya mata jiki sannan yace.
"Waye naki agarin nan da har kullum bakinan me kike fita yi ko me kike nema wanda baki sameshi anan gidan ba?"
Shiru tayi ta kasa magana sai faman rarraba ido take yayin da Baffa yaci gaba da cewa "maganar gaskiya Sailuba wannan shegen yawon gantalin naki ya isheni haka idan kuma baki gyara ba zan d'auki mummunan mataki akanki"
Hak'urin munafurci taita bashi har da kukan k'arya kafin yace ya hak'ura sannan ya d'ora da fad'in "tunda gobe weekend ne ki sanar da Maryam ta shirya zamu wajen Inna"
A mugun firgice ta d'ago tana duban Baffa yayin da maganar boka yafara kara kaina cikin kunnen ta kamar yanzu yake fad'a mata kar ta sake ta yarda Maryam ta had'u da Inna domin akwai babbar matsala ga had"uwar ta tasu domin Inna zaya ruguje musu komai ta yadda har abada bazasu tab'a nasara akanta ba kamar yadda har yau har gobe suka kasa akan Nassar domin akwai dafa in datake bashi yake sha.
"Lafiya wai me kike nufine Sailuba da hana maryam kusantar mahaifiya ta idan ke kin gujeta so kike yata ma ta guje rabon Maryam da taje garin nan tunda aka yayeta sai dai idan Innan ce tazo ta ganta so kike ki raba yata da mahaifiyata be?"
Cikin dauriya da k'arfin hali tace "a a Baffa ni wacece da zan raba baby da Inna naga nima Innan nan uwatace dan Allah ka daina yimin irin wannan bahaguwar fahimtar"
Nan dai ta kalalleme shi da dad'in baki har ya sauka daga fushin daya dauka sannan ta wuce d'akinta da tarkacen da tazo dashi daga wajen bokanta.
Karfe shida daidai ta dawo daga makaranta a mugun gajiye ga d'an banzan yunwar da ta kwaso tsabar yunwar har wani jiri jiri take gani ta fito a motar ta tana had'a hanya, shima MD shigowar babu dad'ewa wanka yai ya fito ya hango ta tana takawa kamar mai koyon tafiyar murmushi ya d'an yi kafin ya taka a hankali zuwa inda take ya d'an hura mata iska a fuska a d'an tsorace ta juyo dan bata ji zuwansa kusa da itaba tsabar bata nutsuwar ta jarrabawan yau ya azabtar da su fiye da tunanin mai tunani.
Kallonsa tayi da lumsasun idanunta wanda tsabar yunwa yasa suka wani d'an shige "me yafaru happiness naganki haka?"
"Yunwa" tace dashi tana dafe cikin ta da ya isheta da k'ugi "ayya baby muje ciki maza Ammey tagama tuwon dare" da sauri ta kalleshi "Allah tuwo tayi? kasanfa ina son tuwo sosai" d'an