Showing 42001 words to 45000 words out of 58385 words
Chapter 15 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt
ya masifar k'ona shi da k'yar yasamu ya rarrashi kanshi ya baro falon shi yasa ya kulle kanshi domin a halin dayake ciki baya buk'atar kusanci ga kowa atare dashi.
Ammey kuwa cikin fushi ta koma d'akin ta ranta a masifar b'ace tasha alwashin bazata k'ara yarda Sailuba ta rik'a juya ta ba tunda babu adalci a lamarin itama ya zama dole ta zage ta kwatar wa kanta yanci.
Haka da ranan mutanen suka kwana kowa zuciya babu dad'i da safe da zasu wuce islamiyya hankalinta yana kan k'ofar sa bata taba alamun ya bud'e k'ofar ba, sai ta tab'e baki a k'ok'arin ta nasan yakice tunanin shi aranta tunda shima fushi yake da kowa na gidan.
Sai dai duk irin yadda taso kore tunaninasa aranta hakan yak'i samu sosai tayi sanyi dan ko k'awayen ta na islamiyya sai da suka gane tana da matsala, sanda suke dawowa daga islamiyya shi kuma ya fito daga d'akin dake lokacin an yi kiran Azhar ne sai da ta d'an razana ganin har ya d'an fad'a daga jiya zuwa yau kacal bata kulashi ba ta d'auke kanta, Nassar ne kawai ya gaida shi, ya bita da kallo har tashiga ciki kafin ya juya ya wuce masallaci.
Koda ya dawo shima cikin gidan ya dawo lokacin har sunyi zaman cin abinci banda haj. Sailuba datake d'akin ta tun juya shima wajen ya tunkaro duk suka bishi da kallo har Baffa wanda yay mamakin ganin shi hakan Ammey tafi kowa shiga damuwar ganinsa a hakan.
K'arasawa yayi ya gaida su kafin shima su Maryam suka gaida shi Ammey ta zubawa kowa nasa abincin amma MD da kanta ta fara bashi dan ta riga tasan halinshi muddun yana cikin damuwa baya iya cin abincin sai dai yayi ta fama da tunani tana cikin bashi ya tsinci muryanta tana fad'in.
"Muhammad yakamata ka gane halin wannan matar ina rok'on ka daga yau komai zai faru kada ka k'ara cewa komai ka barta komai lokaci ne dan haka wata rana sai labari" sosai taci gaba da da tausar shi har ya kammala, itama Maryam ta tubure sai da ta bata itama kafin su bar wajen ta bisu da kallo.
Hannunta da Baffa ya kamo ne yasa ta juyo babu wannan walwalan dayaga tana yima yaranta yanzu, ya d'an murmusa yace "haba maratussaliha dan Allah ki saki ranki tun jiya ake fushi dani na takura da yawa" ya fad'a yana murza hannunta dake cikin nashi.
"Ai Baffa na lura baka Sona ko dan ni ba yar uwarka bace shiyasa kake nuna babanci muraran atsakanin mu"
"Dan Allah ki daina wannan batun Amina ta wallahi nima wani lokacin karkiga yadda abin yake damuna kawai dai tashin hankali ne bana so yasa kikaga ina biye mata"
Amma Baffa shekara ashirin sau d'aya ka tab'a bani kujeran nan ban tab'a cewa dan me ba yanzun ma nagane abin ba na K'are nane dan haka wallahi akan wannan komai zai iya faruwa"
"Dole na baki Amina tunda baki tab'a yi min haka ba sai yau dan haka komai zai faru kece da wannan kujeru na bana" nan dai yaci gaba da tausarta har yasamu ta d'an sakko sukaci abincin tare.
Kai tsaye suna fitowa d'akinta ta dosa dan yau tana buk'atar zuwa gidan su Maryam tana shiga suma suna shigowa yi tayi kamar bata gansuba sai da ya k'araso kusa da ita ya d'an dafa kafad'anta ta juyo ta harareshi.
Murmushi ya d'an saki ya sumbaci goshin ta bai ce komai ya juya ya fice daga d'akin ta raka shi da ido kafin ta juya tacigaba da shirinta.
Taku ce
MAMAN ISLAM
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 34
Cikin atamfa riga da sket kamar ajikinta aka dinka rigar tsabar yadda tayi mata d'as a jikinta, bata wani yi kwalliya mai yawa ba duk kuwa da yadda take da son kwalliyar, mayafin da ya dace da kayan ta dauka ta saka ta saka takalmi mai mugun tsini Allah yayi mata son takalma masu tsini ta fito d'as abinta.
Dukansu juyowa sukayi suka kafeta da ido ba k'aramin kyau tayi ba,kasa daurewa MD yayi sai da ya taso ya d'an matso kusa da ita yace,
"Bakiyi kyau ba" dan hararan sa tayi tace " ai daman badan kai nayi kwalliya na ba bare ka kushe" murmushi yayi tare da mata gwalo domin yasan taji haushi ai kuwa ta k'ufula ta wani had'e rai, ta juya ta wuce d'akin Ammey karab sai a idon mama da ta fito zata fita jitai wani irin fitinannen tashin hankali yakawo mata farmaki da k'arfi tace "ke gidan uwar wa zakije ne" ta fad'a tana kafe Maryam da wani irin kallo.
Ba Maryam ba hatta MD da Nassar sai da suka zabura suka zuba mata ido, ita ko Maryam babu wani shakka ko tsoro tace "haba Mama wallahi har kin bani tsoro irin wannan ihun haka kamar aradu?"
Wani irin tuk'uk'i ne ya tokare haj. Sailuba ta kafe Maryam da wani shegen kallo zuciyar ta yana suya yaushe Maryam ta sami damar fad'a mata magana haka lallai in batayi wasa ba wata rana sai Maryam ta zageta anata haukan tunanin kenan.
Amma azahir cewa tayi "ni nake ihun bab? wai ma tukun me zakiyo ad'akin matar nan bana hanaki mu a'mala dasuba?"
"Hummm mama kenan ai duk randa babu ke dole itace uwata, ko baki tab'a tunanin hakan bane? kuma kadafa ki manta mama ba a raba hanta da jini mun riga mun had'u babu yadda zakiyi tunda ta haifa kin haifa dole ne itama ta sarara agidanna dan Allah mama ki daina irin wannan abun bashi da amfani ko kad'an haba"
Fashewa kawai haj. Sailuba tayi da kuka saboda tsabar tashin hankali da bak'in ciki kasa yi mata magana tayi har ta shige d'akin Ammey tana kallon ta.
MD kuwa wani irin annushuwane ya kamashi sanda Maryam ke fad'awa haj. Sailuba magana wani arnen murmushi kawai yake saki, yana ganin Maryam ta shige d'akin Ammey ya k'arasa kusa da haj. Sailuba yace "hajajju makkatu me kike tunanin zai faru duk ranar da wannan yarinyar tagane cewa ke ba uwarta bace uwar rik'o ce?
Ya zakiji lokacin da tasan cewa mahaifiyar ta kike sawa tanawa cin mutunci da wulak'anci
Me zai faru idan tasan cewa ba dan Allah kike rok'on taba kina rik'on tane saboda wani banzan dalili naki mara amfani?
Hhhhhhhhhhhh kad'an kika gani Sailuba domin Allah baya bacci"
Babu kunya haj. Sailuba ta kuma fashewa da kuka tana kallon MD kafin tace "hummmm Muhammad kenan na maka alk'awarin bazan bar hakan yafaruba sannan kuma ina Mai farin cikin sanar dakai cewa komai ya kusa zuwa k'arshe rayuwar Maryam zaiyi wulakantar da babu wani rayuwa da zata kai tata lalacewa zata bi maza zata yi shaye shaye zata yi sata zata zama abin kwatance da misali na miyagu da munanan halayya"
Sosai gabansa ya fad'i da jin furucin ta domin yasan zata aikata fiye da hakama jiyai hankalinsa yai masifar tashi ya dubeta da tsantsar b'acin rai yace "Allah ya fiki yafi waninki Sailuba kuma duk abinda kike tak'ama dashi insha Allah hakan ki bazai cimma ruwaba"
Wata shegiyar dariya ta saki tace "zaka gani zaka kuma tabbatar muzuba nidakai shege ka fasa" daga haka tayi waje hankali a tashe.
Sosai maganganun ta suka tsaye masa rai sai dai kamar yadda yake tsaye wajen yiwa Maryam Adda a ya zama dole ya k'ara zage damtse.
Maryam kuwa tana shiga d'akin Ammey ta rufeta da fad'a akan maganganun da taji tana sakarwa haj. Sailuba tace mata koba komai matsayin uwa take awajen ta dan haka ta rik'a sanin irin maganan da zata fad'a Mata.
"Nifa Ammey indai akan kune babu abinda zaki fad'a min na fahimta matar da bata da lokacina sai na gantali kullum tana tafe a hanya ita ba kasuwanci ba ba komaiba, ai wallahi duk laifin Baffa ne da yasake mata haka dayawa shiyasa take iskancin ta son Rai"
"Ungo nan Ammey ta yiwa Maryam tace "idan har da gaske kina ganin mutunci na kamar yadda kika fad'a to kada ki sake kinji ko?"
"Naji Ammey, ina Baffa shi nazo nema"
"Lafiya kike neman Baffa?"
Bata b'oyewa Ammeyn komai ba ta fad'a mata tana son bawa baban k'awarta jarine ya fara sana a, sosai hakan yayiwa Ammeyn dad'i arai taji dad'i ya kasance yarta tana da zuciyar tausayi dan haka Ammeyn ce da kanta ta bawa Maryam dubu d'ari tace "gashi idan Kuma bai isaba kimin magana sai na k'ara miki?"
Rungumeta maryam tayi tace "na gode Sosai Ammey na Allah yaja da rai ta sumbaci Ammeyn tayi waje da sauri tana fad'in saina dawo"
Sosai Ammey ke jin dad'in yadda yarinyar ta soma sakewa da ita ta rage wannan d'an banzan yawon dayake sanyata fargaba da damuwa musamman idan haj. Sailuba ta dawo taga bata nan ko zata kwana basata tuhumeta taji inda taje ba.
Tana fita suka gabza wani uban karo da MD ai kuwa taji zafi sosai shima haka duk suka dafe wajen suna kallon juna kafin Maryam ta galla masa harara ta wuce tana sosa goshinta.
Da sauri yasha gabanta ya tsaya yana d'an diddira k'afa irin na shagwab'a yace"ni Allah Allah Allah sai ki bigeni kuma ki wuce babu hak'uri ni sai na rama" yadda yayi maganar dole abin yabata dariya batasan sanda ta saki murmushi ba tace "sorry"
Daga haka ta wuce kuma shan gabanta yayi yace "ina kuma zaki?"
"Gidan su Maryam ta bashi amsa dan har ga Allah sauri take ta tsai da baban Maryam yau baifita nema ba dan haka yakamata taje akan kari
"Wanda kike siyayyar nan awajensa?"
Ta tsinci muryarsa tana shirin fita "Eh shi"
Ta bashi amsa tana ficewa da sauri ya bita ya rik'o hannunta yana kallon ta tace "dan Allah yaya sauri nake sai batamin lokaci kake"
"Muje mana naganshi idan ya cancanta da amanar da kika bashi saiya cigaba da kula da su idan Kuma ba haka ba sai na amso ko?"
Sanin cewa sunyi maganar da Ammey yasa bata musa masa ba suka jera suka shiga motar yaja suka bar gidan.
Maman Islam ce
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 35
Saida tasa kashi suka biya wani spermaket ta d'an musu siyayya, dan Allah yasani hakanan Allah yasaka mata tausayin iyayen Maryam, saboda yak'i nin su da kamewar su hakanan sun iya babun su, dan malam Abdullah mutum ne jajir tacce tsayayye, akan iyakansa bai yarda da zubar da daraja da kimar gidansa ba, haka kuma baya daukar raini ko kad'an dan haka hatta iyalinsa suna shakkar sa saboda sam bai yarda da wulakanta kai ko zubda mutunci ba.
Yadda suke shiga cikin lungunan unguwar yasha mamakin yadda Maryam tasan wajen dan koshi dayake namiji bai tab'a yowa ta area dinba sosai ya rink'a binta da kallo yana mamakin ta.
Sai yanzu yake gane asalin halinta mai kyau ne irin na mahaifiyar ta wancen halin na aro ne wanda aka d'ora ta akai bisa wani dalilin mara tushe da makama.
Ita duk wannan kallon dayake binta dashi sam bata kulaba dan hankalin ta yana kan wayar ta suna chat da Halima sai yanzun ta d'ago dan taga ko sunkai inda ta kwantato masan ai batasan sanda tasaki kara ba ta maida hankalin ta kanshi ganin suna shirin taka wani k'aton dutse, shima da sauri ya taka burkin da sai daya janyo hankalin wasu daga cikin masu wucewa dake cikin unguwa be.
Harara ta galla masa kamar idanunta zasu fad'o tace "to kasheni ka huta tunda ka gaji da ganin rayuwata"
Murmushi ya d'an saki kafin ya d'an shafi fuskar ta yace "ina son ki princess dan Allah ki soni my happiness" hararan ta kuma masa kafin ta d'auke kanta yasa hannu ya kuma juyo da fuskar nata saitin sa ya kafeta da ido,
."dan Allah ki kalle ni nasan zaki yadda da abinda nake fad'a miki har zuciyana ne" bata musa masan ba ta d'an kalleshi na kamar 1 mint take taji ta fara d'an tsuma tsuma tasoma k'ok'arin kwace fuskar ta amma ya hanata damar hakan da sauri ta runtse idonta dan bazata juri kallon wannan fitinannun idanun nasa ba.
Murya na rawa tace ni kaina ya k'age ka sakar min fuskana, kuma ka daina yimin wannan kallon mayun" murmushi ya d'an saki kafin yace "indai akanki ne baby ki kirani lasan ma ba maye ba da da yadda zanyi na tsaga jikina na sakaki da tuni na jima da yin hakan na huta' dan Allah baby karki gujeni, idan kika gujemin hakan yana nufin abubuwa da yawa ciki harda rayuwana"
Yanayin da yayi maganar yasa dole ta kara bud'e idanunta akanshi yadda taga idanunsa sun koma ba k'aramin tsoratata abin yayi ba sunyi wani irin mugun ja ga wani kyalli kyalli alamun ruwan hawaye ne suka kwanta masa aciki, wani irin tausayin sa ne ya kamata tace
"Zaka iya aurata koda ace bana sonka?
Sosai maganar ta ya dakeshi, zaka iya aurata koda ace bana sonka?
ya sake maimata tambayar a zuciyar sa kenan akwai wanda take so Kennan tunda bata son shi?
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
"Baby wa kike so?
"Babu"
Ta bashi amsa atakaice sannan ta d'ora da fad'in ba kaine kakori muhseen ba yaron dayake masifar Sona kamar zaiyi hauka tundaga ranan yake masifar tsorona bama kaiba ko a hanya ya ganni wallahi canja hanya yake"
Sosai maganar ta ya masa zafi a zuciya amma sai ya daure tunda shine mai nema dole ya sauke duk wani zafin ransa gefe ya nemi masalaha
"Kina son muhseen d'in?
Ta tambaye ta cikin tsantsar zafin rai dana zuciya.
"Ni babu wanda na tab'a jin ina so arayuwata shima muhseen d'in saboda nacinsa da rashin zuciyar sa yasa na tausaya masa na fara kulashi" baisan sanda ya wani fisgeta ta fad'a jikinsa ba ya wani k'ank'ame ta atare suka sauke wata irin ajiyar zuciya kafin yasoma magana cikin sanyin da shi kansa baisan zai riskeshi a wannan lokacin ba yace
"Na amince baby zan aureki koda ace bakya sona nasan dole wata rana zanyi nasara zan mallake ki KE DA ZUCIYAR KI"
"Ya jima yana zubar mata da sak'onnin da suka cunkushe masa zuciya suka hanashi sukuni, bai tab'a sanin da akwai rayuwa irin wannan ba rayiwar da zaka kasa katab'us ka kasa sukuni ba sai da ya had'u da jarrabar SO wanda ya hanashi sakat yake sanyashi kasa baci cikin dare ya kasa runtsawa tsawon dare ya zubda hawaye ba adadi duk asanadin SO"
Tun bata fahimtar maganganun sa har ta fara fahimta sanadin da jikinta yayi sanyi bata san da cewa akwai ranan da MD zai iya kallon idanunta ya furta mata tsadaddun kalamai irin wannan ba musaman idan tayi tunanin yadda suke da shi.
"Bross muje na tsaida bawan Allah yanata jira" tayi maganar cikin sanyin jiki dan kalaman sa sun mugun kashe mata jiki sai da ya sumbaci goshin ta da idanunta da suka fi komai d'aukan hankalin sa kafin ya saketa ya tada motar suka k'arasa gidan su Maryam d'in.
A mota ya tsaya ta shiga kamar yadda ta zata Abban yana nan yana jiranta kamar yadda ta nema Umma ce tayi mata shimfid'a ta kawo mata ruwa da lemo, sai da ta gaida su sannan ta sanar musu ai tare suke da yayanta Abba yace "kuma kika barshi awaje kai wannan yara Allah ya shirye ku da rashin wayo"
Ya fita ya shigo da MD duk da kasancewar basu dashi amma yayin gidan kad'ai zai nuna maka mutanen gidan suna da tsananin tsabta, sosai suka gaisa da su kafin Maryam tayiwa Abban bayanin dalilin zuwansu, hakan ba k'aramin dad'i yayi wa Abban na ya zauna yayiwa MD bayanin duk abinda aka sai mata da kud'ad'en da take kawowa harda shanu da yaje can garinsu yasai mata da yake shi ba d'an garin bane.
Yanayin sa kawai yasa MD yaji hankalinsa ya kwanta da shi dan haka suka d'anyi shawarwari akan abubuwan nata yace "tunda shanun sun kai har guda goma kuma duk Yan k'anana wanda basu fara haihuwa ba kawai asai na mijin sa kamar guda biyar a had'a sai abada kiwo ga wanda ya amincewa.sannan gidajen kuma anemi yan haya masu mutunci da amana asaka su aciki"
"Nima tun farko shawaran da nayi da ita kenan tace in dakata tukun" murmushi MD yayi yace "kasan yar k'auye ce babu abinda ta sani sai k'auyanci" shima Abban murmushin yayi yace " banda abinka d'ana ai k'auye tushen kowa ne shima MD murmushin yayi suka ci gaba da tattanawa, sun jima a gidan har sanda Maryam ta dawo suka suka shige d'aki dake sanda sukazo bata nan Umma ta aike ta.
Umma ce ta lek'a tacewa Maryam ta fito zasu wuce sai da zasu tafi sannan Maryam ta kawo k'udin da Ammey ta bata ta mik'ewa Abba tace
"Abba gashi nan ka nemi wata sana ar ka fara Allah ya taimaka.
Tsabar mamaki Abba kasa magana yayi gashi kuma ta toshe duk wata hanya da zai mata godiya sai addu'ar da yay ta zuba Mata har suka bar gidan
MAMAN ISLAM CE
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 36
Suka shiga mota ya tada suka bar wajen saida suka d'an yi nisa da tafiya kafin ya d'an juyo ya kalleta " enye enye ashe yarinyar tana da hankali, to nima aban jarin mana"
Murmushi kawai tayi tasan tsokanar ta yakeyi dan haka ta d'auke kanta suna cigaba da chat da Halima wacce take zaman jiranta a gida.
"Ko bazaki baniba?" Ya sake tambaya, hararan wasa ta d'an yi masa ta dauke kanta tana d'an murmushi.
Haka dai yai ta janta da hira har suka koma gida kai tsaye d'akin ta ta wuce shima fat d'in sa ya nufa dan duk sun gaji.
Ita kam tana shiga falon ta tadda Halima tana zaman jiranta hararar wasa tayi mata tace " to hajiyata