Showing 48001 words to 51000 words out of 58385 words
Chapter 17 - BA JININA BACE Book Complete by Hassana Abdul'aziz Yakasai .txt
murmushi yayi danshi tsokanar ta yakeyi yayi zaton irin Nassar ce itama batason tuwo kamar sa.
"Tsokanar ki nake Baffa kawai Ammey tayima"
" Ai kuwa nima tuwon zanci yasin" ta wuce kanta tsaye dining room d'in, saida ta fara had'a ruwan zafi ta gasa cikin ta kafin ta bud'e tuwon Baffa da Ammey tagama shiryawa gwanim ban shi'awa ta d'auki malmala tasa aflat ta zuba miya ta soma ci a nutse, duk da bak'ar yunwar dake damunta hakan baisa ta rud'a kanta tayi irin cin yunwar nan ba, Ammey da ta shigo dan daukar abincin Baffa tsayawa tayi tana kallon Maryam dake aikawa da tuwo batare da tasan cewa Ammeyn tazo wajen ba, sai data k'arasa wajen Maryam ta ganta tayi wani wuri wuri da ita can kuma tace "wallahi Ammey bross ne yace kinmin tuwo"
"Na tambaye kine?"
Ta fad'a tana wurgawa MD harara wanda yake gefe yana d'an murmushi wayarsa a hannu yana faman daddannawa, bata k'ara magana ba ta d'auki d'an kwandon data jera abincin tayi waje MD ya dungure mata kai yace" da so kikai ki had'a ni da uwata ko?"
Bata ce komai ba sai harara data galla masa taci gaba da cin abincin ta sai data jita daidai kafin ta mik'e tana hamdala tawuce kai tsaye d'akinta ta nufa wanka tayi ta yo alwala tayi sallar la 'asar da ya k'wace mata tun a hanya ta jima tana addu'o'i kafin ta kama karatun Al qura ani mai girma da fita tasoyi d'akin Ammey ganin lokacin magriba ya karato yasa bata fitan ba ta jima tana karatun kafin a kira magriba tayi addu a ta tashi kawo sallar magriba bata bar wajen ba saida tayi issha Nassar ya shigo da murnan zasu gidan yayar Ammey wacce take sonshi "Adda zaki?"
Harara ta aika masa tace "bazani ba d'an rainin hankali da dani kuke zuwa?"
Nan dai ya fitineta da hiran anty shamsiyya wacce suke kira da momma har dai ya ja arayinta tace itama zata cikin farin ciki ya daka tsalle yay waje kaiwa Ammey labari, itama ba k'aramin dad'i hakan yayi mata ba ko ba komai anty shamsiyya zatasan cewa ansami cigaba kenan.
Ita ko Maryam Nassar yana fita ta mik'e ta wuce d'akin Mama mamaki ne ya kamata ganinta cikin damuwa ta k'arasa ta kwantar da kanta saman kafad'ar ta tace "Mama lafiya na ganki cikin damuwa ko baki da kud'i ne?"
Wani k'ululu ne ya tsayewa haj. Sailuba jin tambayar da Maryam tayi mata, amma sanin cewa ita ce silar d'ora ta akan hakan yasa tace mata "eh kina dasu ki bani?" Girgiza mata kai tayi tace "ai tunda naga yanzu Baffa ya bud'e miki bakin aljihu fiye da kima yasa na daina tambayar sa k'udi domin nasan cewa idan kina dasha nima inada shi kuma wanda kike bani ma yanzun baya isana saboda wani saurayi danayi d'an talakawa ne sosai shi nake kashewa" da gayya tayi mata wannan zancen dan son gane asalin gaskiyar batun MD dayace wai maman ta uwar ta bata ki taga ta saida mutuncin ta ba,kimar tafa tak'amar kowacce budurwa mai ji da son kara Martaba da kimar ta har zuwa gidan aurenta.
Ga mamakinta ta kuwa bud'ar bakin mama sai cewa tayi "ni dai duk abinda Zaki aikata kada kisake ki kwaso ciki ki rik'a amfani da matakan kariya"
A matuk'ar firgice Maryam take kalloan haj. Sailuba jikinta har rawa rawa ya soma dan tsabar mamaki kasa magana tayi saima tunanin da ta soma aranta na "anya wannan uwa tace kuwa?"
Da k'yar ta iya ce mata daman nazo ne dan Allah Mama ki barni naje garin da momma take Nassar yace kwana d'aya kacal zasuyi dan Allah......katseta Mama tayi cikin sauke ajiyar zuciyar samun mafita na kaucewa tafiyar ta da Baffa zuwa wajen wannan jarababbiyar tsohuwar tace "sai kun dawo" mik'ewa tayi k'udin da takawo mata sai da ya girgiza ta ta amsa yau ko godiyar batayi mata ba ta fice kai tsaye d'akin Ammey ta nufa har MD ma yana can ta mik'ewa Ammey k'udin ta fashe da kuka tace "wai mama ce take cemin duk abinda zanyi kada na d'auko mata ciki anya uwata ce kuwa dan Allah Ammey ki fad'a min itace ta haifeni?"
Ita kanta Ammeyn ba k'aramin girgiza tayi ba musaman da suka k'irga k'udin miliyan d'aya da dubu d'ari da hamsi itama Ammeyn fashewa tayi da kuka ta kasa magana ganin haka MD ya kasa cewa komai ya rungume maryam yana rarrashin ta ransa na masa wani irin suya sun jima a haka kafin Ammey ta janyo maryam daga jikin MD ta kasa magana saima sabon kuka daya kwace mata.
Muje zuwa
بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________
🔥 BA JININA BACE🔥
2021
NA
HASSANA ABDULAZIZ YAKASAI
MAMAN ISLAM
Page 39
"Innalillahi wainnailahi raji un" kawai Ammey take ta maimaitawa, ta kasa magana, hakanan kukanta yak'i tsayawa, jikinta har rawa yake, tsabar damuwa takasa cewa komai sai fad'a jan yar ta take cikin jikinta tana shafar ta.
Can kuma kamar wacce aka tsikara zumbur ta mik'e tayi b'angaren Baffa a mugun fusace, da k'yar ta iya yiwa Baffa sallama yanayin da yaji muryanta yasan cewa lallai akwai gagarumin matsala dan ba komai Ammey take d'aga hankalinta akai ba.
Da kallo ya bita tana takowa kamar me koyon tafiyar yayin da Baffa ya kafeta da ido gabansa na fad'uwa, har ta k'araso cikin rawan murya tace " Baffa yau ina so abani 'yata tunda ba kune kuka yimin nakudar taba"
Da kallon mamaki ya bita, me kuma ya faru take irin wannan maganar?
Ya sani sarai rashin kunya ba halinta bane tana da hak'uri da sanin ya kamata yau kuma me ya tab'ota har take irin wannan zancen?"
Ammey da ranta yai mugun b'aci akan abinda taji yau abakin 'yar tata yasa ta rufe ido ta rik'a fad'awa Baffa magana Kuma maganar duniya tak'i sauraran sa ga wani irin kuka da take yi mai cin rai.
Tun bayan fitar Ammey MD yaji wani sanyi aransa ya sani cewa shi zai fasa kwan dubuce ta cika yau shi kad'an sa sai murmushi kawai yake saki da maryam ta juyo zata kalleshi zai basar.
Gajiya yay da kukan nata ya matsa kusa da ita yace "kinsan wani abu?"
Tsaida kukan tayi ba tareda tace komai ba, ta dai zuba masa ido shikuma gane cewa shi take jira yasa yace "akwai abinda in kika sanshi sai kinji dad'i ranki zai miki sanyi zakiji cewa babu d'an gata kamar ki amma ina so kidaina min asarar wannan tsadaddun hawayen naki ki adana min su sai ranan da aka mik'a min ke a matsayin matana"
Ya fad'a yana d'age mata gira tareda murmushin da bata gane ko na meye ba, hararan sa tayi ta maida kanta can gefe tana shashshek'a, kafin ya k'ara magana aka kira wayarsa da sauri ya d'aga harda d'an russuna wa kamar yana gabansa, bataji abinda akace masa tadai ga ya amsa da to ya fice da sauri.
Lokacin da zai shiga d'akin dan amsa kiran Baffa sannan kuma Ammey ta fito daga d'akin cikin tsantsar tashin hankali da b'acin rai taci alwashin koda hakan yana nufin rabuwarsu sai an maido mata yar ta wallahi, ko kulawa da MD batayi ba ta fice ta ta wuce d'akin ta ta zari mayafinta rabonta da kwatanta yaji tun akan bada Maryam sai gaahi yauma ta k'ara kwatawa.
Yanayin da MD yasami Baffa na b'acin rai yasa MD ya k'ara nutsuwa ya k'arasa kusa dashi ya zauna kansa a k'asa Saida ya nutsu Sosai ya gaida Baffa wanda tsabar damuwa yasa ya kasa amsawa saboda tsabar tashin hankalin data jefashi.
"Muhammadu zan tambayeka ka dubi girman Allah ka fad'amin tsakani da Allah nake so kafad'a min iya abinda ka sani' karka min k'arya, kar ka min k'arya, karka min k'arya, Muhammadu kada ka duba halin da kuke ciki kai da Sailuba asalin gaskiyar nake buk'ata"
Shiru MD yayi na d'an wani lokaci yana son tuna komai ko abu guda baya son ya manta (🤣🤣) MD fa ka fad'i gaskiya banda heri😂😂
Kallonsa Baffa yake yana jiran amsa, dan haka ya kwashe iya abinda ya sani komai bai rage ba kafin ya k'arasa jikin Baffa yayi wani irin sanyi wata irin nadama ta saukar masa take ya hau zufa jijiyar kansa tayi wani irin tashi, waima me ya hau kanshi da har ya manta halin Sailuba ya d'auki tarbiyyan gudan JININSA ya bata matar da ita kanta tarbiyyar take buk'ata take ya kama hawaye abinda ya firgita MD kenan ya rik'a rarrashin sa tareda kwantar masa da hankali
Wasa ya fara
MAMAN ISLAM CE

MAMAN islam ce

Page 40
Bai saurare shi ba ya tashi a fusace ya fita, yana fita MD ya mik'e ya buga uban tsalle yana rawa har da d'ebo shoki a aransa yake fad'in yau wata zata kwashi kashin ta a hannunta yadda Baffa ya fusata dinnan.
Wani abun ta kaici Baffa a fitinensa ya shga d'akin Sailuba ya balbaleta da ruwan bala i amma tana d'agowa suka had'a ido sai ya nemi tashin hankalin ya rasa saima rarrashin ta da ya somayi ita kuma tayi wani kicin kicin da rai.
Sanda haj. Amina ta isa gidansu malam Babba yana k'ofar gida da daliban sa tsabar idonta ya rufe bata gansuba kanta tsaye d'akin Nanne ta wuce cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara, ita kanta Nanne ganin ta haka sai da gabanta ya fad'i da k'yar ta rarrasheta ta daina kukan da takeyi.
Ganin halin da yarsa take ciki yasaka ya sallami mutanen nasa ya taso kai tsaye d'akinsa ya wuce yasa aka kira masa duka matan nasa harda Amina wacce tai wani wujuga wujiga tsabar tashin hankalin data tsinci kanta a ciki.
Sai da malam ya fara yimata fad'an fitowa da tayi batare da sanin mijinta ba dan duk wanda yaga yanayin ta yasan ba fitowar lafiya tayi ba sannan ya tambaye ta abinda yake damunta.
Cikin zubar da hawaye ta kwashe tun daga ranan data fara jan Maryam har zuwa yau ta fad'a musu komai, ba matan ba hatta shi kanshi malam Babba saida hankalin sa ya tashi danjin masifar da ake son d'ora masa jikar tasa akai sosai ransa ya b'aci ya rik'a maimata innalillahi wainnailahi raji un sosai yaiwa haj. Aminatu nasiha sannan yace tacigaba da jan yarta a jikinta ta kuma rik'a nusar da ita cikin hikima ta rika sata a hanyar data dace kada tace zata yi mata hayaniya shi yaro da dabara ake tarbiyyan sa ba da hayaniya ba.
Sunan zaune sai ga Baffan yazo hankali tashe tun bayan da ya fito daga d'akin Sailuba ya fara tuhumar kansa dalilin da yasa yakasa yimata bore kamar yadda ya fita da niyyar yi mata.
Bayan sun gaisa da malam ne yake bashi hak'uri kuma yake rok'on abawa Amina hak'uri sannan yace koda yaje da niyyar daukar mataki akanta sai tayi masa kwarjini ya kasa tab'uka komai.
Malam yace" babu komai kaci gaba da addu a kuma kadaina sake wajen yin azkar insha Allah komai zaizo maka da sauk'i yanzu dai maganar gaskiya Baffa ya zama dole kasa ido akan tarbiyyan yarinyar nan"
Komai ya kusa karewa ma malam dan na tsaida auren Maryam da MUHAMMAD k'arahen watan nan da muke ciki insha Allah" ba malam Babba ba hatta Ammey ba k'aramin sanyi taji aranta ba sai taji duk abinda yake damunta ya kau, sosai malam yayi musu nasiha, kafin su baro gidan.
Acan gida kuwa suna fita haj. Sailuba ta fito nan ta sami MD da Nassar a falon ta saki wani wawan tsaki ta k'arasa kusa da su tace " su agola ansami wuri kana tunanin d'an k'aramin makircin ka zaisa kay nasara ne? ni kumurcin kan dutse ne ban fito ba saida na shirya"
"Haba Sailuba karfa ki manta rana dubu na b'arawo rana d'aya na mai kaya ne yanzun dai ki mai da hankali kici lokacin ki amma ki sani komai lokaci ne karshen ki ya kusa fajirar banza"
"Kai dan ubanka ko Hasan ya isa ya zag........ " Ke tsohuwar banza gyara kalaman ki kada ki kara zagin bawan Allah yana kwance a raminsa yana hutawa kinsan wanda yasami shaidar mutane ya dace dan haka ya fi k'arfin ki shi d'in bawan Allah ne ba masoyin duniya bane dan haka na k'ara jin kin zage shi wallahi saina gurji bakin ki"
Ganin yadda ya rikice mata idanunsa sunyi wani irin juyewa tsabar b'acin rai yasa tai gum da bakinta sai d'an uban harara da take aika masa shima dataga ya d'ago zatayi saurin k'asa da kanta.
Sai da ya gama masife ta tare da zubar da ruwan rashin mutuncin son ransa kafin ya buga wani d'an uban tsaki tare da sakar mata hararan da yasa 'yan hanjin ta kad'awa babu shiri ta shige d'akin ta tana tsine masa a ranta.
Su Ammey suna dawowa gida tasa maryam ta hau shiri dan tasawa ranta cewa 'yarta tabar hannun wannan azzalumar matar, hakan yasa ko Baffa baisan da Maryam akai tafiyar ba sai da yagama shirinsa yasauko yana tambayar haj. Sailuba maryam ta gama shiri shine take sanar masa tare da Ammey suka tafi ransa ba k'aramin b'aci yayi ba ya rufe ta da fad'a domin yasan dan kar ya kaita w ajen mahaifiyar sa yasa ta bari aka tafi da ita yasan Sailuba yasan waye ita, yasan abinda zata iya aikatawa da wanda baza tayi ba, ya rasa mai Inna tayi mata da zafi haka da ta daina zuwa inda take kuma ta hana maryam ta kusance ta matar da ta rik'e ta ta kula da ita bata bari tayi kukan maraici ba yau itace abar wulakantawa awajen ta kwafa yayi ya fice cikin tsantsar b'acin rai da bak'in cikin yadda yake kasa d'aukar mataki akan abinda take masa ko yaso hakan sai tayi masa wani irin kwarjini yaji tausayin ta ya baibaye shi.
Maryam kuwa yau cikin wani irin