Showing 51001 words to 54000 words out of 68402 words

Chapter 18 - ZAMAN HOSTEL COMPLETE BY RAHEEMA.txt

RAHEEMA   

20 Jul 2024

21378

furta komai yayi sai kallon salma da yakeyi.




Hannu yabama doctor game daciwa nagode sossai, kafin ya juyu salma tafice daka office din, hawaye kezuba a idonta harta isa bakin titi kekenapep ta tsayar ya kaita gida dan bazata shiga motar najib ba.




Ko a napep din kuka take tana nanata maga'nan doctor, ne salma nashiga ukuu karya kakeyi doctor wallahi zan haihu saina haihu.




Driving najib yake zuciyarshi cike da tinani barkatai, a fili yafurta da wuya mahaifarta ta dauki ciki sakamakon magungunan hana daukan ciki datai amfani dasu, rintse idonshi yai ya bude sanan yafurta zargina ya tabbata mazinaciya na aura, hakan yana nufi salma ta aikata zina fiye a kirga... da tinani barkatai a zuciyarshi ya karasa gida.




A fusace yafito a motarshi ko rufe kofar motar beyeba yai cikin gida cikin sauri.




A daki ya sameta tana hada kaya a trolley dinta hawaye nazuba daka idonta.




Yanda ya bude kofar da karfi ya firgita salma wuyanta ya shago game da watsa mata mari sanan yashiga dukanta muryanshi na rawa yake fadin ki fadamin ke wacece?
Saikin sanar dani wace irin rayuwa kikayi a baya, meyasa kikaimin karya?
Ashe daman ke mazinaciya ce karuwa wace tagama tantal badi a titi, Allah yaisa tsakanina dake salma Allah yaisa.















Keep following me i need more and more comments read and share😘😘😘
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–




*ZAMAN HOSTELπŸ’ž*




πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–




STORY
AND
WRITTEN BY


RAHEEMAπŸ”₯




DEVOTED TOπŸ‘‡πŸ»
(YUSUF)πŸ’‹






DEDICATED TOπŸ‘‡πŸ»


*Real Anty Zeey πŸ’žπŸ’‹*
_Gaisuwa ta musamman gareki hajiyan gurguraπŸ€­πŸ˜€ Allah yaqaro zaqin gurgura agun oga🀭_






πŸ…Ώ63-64






Saida ya duketa iyasan ranshi sanan ya rabu daita zama yai a gefen gado sanan ya dafe kanshi hawaye nabin fuskarshi




Najib wani irin mutum ne wanda yake kyaman zina sanan ya tsani duk wani mai aikatawa.




Kwance take a kasa sai kuka take kamar karamar yarinya, hannu yasa ya dagota game daciwa tashi kizauna, tashi tayi tazauna cikin kuka tace me kake jira ka kasheni kahuta yaya najib ka kasheni kawai dan Allah.




Tsawa ya daka mata hade da nunata da yatsa yana fadin zakimin shiru kusai na karyaki anan, kafin kitafi gidan ubanki saikin sanar dani wacece ke?




Da jajayan ido ta dubeshi tace abinda bazaka taba sani ba kenan koda kowa zaka kasheni ka bani takardata na shiga duniya kawai




Koda baki nime saki ba yazama dole na sakeki salma, amma wallahi kinyi babban asara domin daka gidan mutunci kika fito sai kikayi watsi da tarbiyan da aka baki kika kasance shaidaniya kije na sakeki saki daya.




Tashi tayi batare da tace komai ba bathroom tashiga ta wanke fuskarta sanan tadau dogon hijab tasa hade da daukar akwatinta. Yana zaune yana kallonta har takai kofa sai ta juyu ta kalleshi hawaye nazuba a idonta tace




Tabbas nayi ladaman rayuwar dana aikata a baya, daka randa aka daura aure na, na sakejin tsanan rayuwan dana aikata a baya daka lokacin da aka kawuni gidan'ka nadau alkawarin zan zauna dakai lafiya zanyi zaman aure zan bika sauda kafa ton daka wanan lokacin nake niman yafiyan Allah akan rayuwan da nayi a baya hakika nayi ladama kuma na tuba ga Allah danko ba abinda yakai rayuwar aure dadi hmmm abinda nayarda dashi shine mutum baya taba kauce wa kaddarar'shi kowa nada nashi kaddarar a rayuwa ZAMAN HOSTEL ne sanadiyan lalaciwata duk halin dana tsinci kaina ayau sanadin zaman hostel ne tabbas nayi ladaman abinda na aikata.




Amma ayau zan kuma rayuwata nada, idan nabar gidanka duniya zan shiga bazan taba iya komawa gidanmu ba, me kakeso na sanar wa iyayyena?
Ce musu zanyi likita yace mahaifata tasamu matsala sakamakon magungunan hana daukan ciki danai amfani dasu... Saboda haka ka yanke igiyar auren sake tsakanin'mu, murmushi mai ciwu tayi sanan tace har abada bazasu tabajin wanan zancan daka bakina ba dan bansan halin dazaso shiga ba ton balle mama.




Karasa maganan tai dasa kafarta daya a waje sanan tace alfarma daya nakeso kamin karda kasanar da iyayena harsai nan da kwana biyu na tabbata zuwa wanan lokacin nayi nisa da garin kaduna tana karasa maganan ta fice.




Maganar salma sunsa jikinshi yai sanyi saikuma yaji tausayinta ya kamashi amma hakan besa ya dakatar daita ba.




Babban trolley dinta ta dauka duk wani sarkar gold dinta dawani abu nata mai tsada tasa shi a ciki saida tacika trolley din da kaya, dayan karamin trolley kuma takalma da jaka sai tulareka da man shafawa tacika a ciki dukda haka bata gama kwasan abinda takeso ta kwasa ba amma haka tabar kayan dan ba gurin dazata sasu sai wata karaman jaka data rataya a wuya wacce tasauka har cikinta, dakyar takejan akwatinan harta karasa bakin titi bus tahau hade daciwa zan sauka a KAWU.




Wani complementary card ta dauka a jakarta number jiki naga tana kwashewa wanda dauke da sunan CAPTAIN FAROUK yake tana gama kwashewa tai dialing number




Kamar baza'a dauka ba sai taji an dauka
Hello
Shiru salma tayi saboda muryan mace taji
Matar ce tasakeciwa Hello
Dauriwa salma tayi sanan tace
Sallamu Alaikum bata tsaya jira a amsa sallama ba tace please captain farouk nake nima




Matarce tace Allah sarki baiwar Allah hala kun jima bakuyi waya ba Allah yayi mishi rasuwa wata uku da suka wuce matarshi ce ke magana.




Mantawa salma tayi a motan haya dake danko da karfi tafurta whatttttttttttt?
Farouk ya rasu a'a it's unbelievable yaza kincemin farouk ya rasu a'a




Hawaye ne yazuba a idon matar domin babu ranan dazata fito ta fadi batare da tayi kuka ba idan tatina mijinta, jin shiru yasa salma ciwa aunty dan Allah kicemin wasa kikeyi?




Matarce tace meyasa zanyi wasa da mutuwa baiwar Allah? Allah yayiwa mijina rasuwa sunje wani operation a zamfara anan aka harbeshi sai gawan shi aka kawumin yau kimanin wata uku da kwana shida kenan.




Kuka salma tasa tana fadin innalillahi wa'ina ilaihi raji'un farouk meyasa zaka tafi kabarni a lokacin da duniya taimin zafi ne salma Nashiga uku duniyar ba tabbas Allah yajikan'ka




Wata matace da take kusa daita tace yar'uwa kiye hakuri, sai anan salma ta tina wai a motar haya take ashe bata kashe wayan ba. Aida sauri ta kashe wayar.




Juya wayan take a hannunta tana nanata kalaman salma kasa dauriwa tayi saida tasake kira, kamar salma bazata dauka ba saikuma ta dauka k'ara wayan tai a kunnenta batare da tace komai ba.




Matar farouk ce tace baiwar Allah naji kinyi wasu magana danAllah kozan iya sanin halaqarki da mijina?




Shiru salma tayi na tsawan minti uku tare da nazarin abinda zatace sanan tace nidai sunana salma mijina ya rasu shekara biyu da suka wuce yabarni da yara uku farouk ne kedaukar nauyin karatunso shi yake musu komai shiyasa mutuwarshi ta firgitani




Matar da take zaune kusa da salma jitayi tausayinta ya kamata a fili tafurta Allah baya barin wani dan wani yaji dadi.




Matar farouk kowa jitai salma tabata tausayi cikin tausayawa tace Insha'Allahu bazaki rasa wanda zai taimaka muku ba amma a wani gari kike?




A garin bauchi nake dakatar daita salma tayi gudun karta sake mata wani tambaya ta hanyar ciwa sai anjima nagode sossai hakan yayi daidai da karasowa inda salma zata sauka.




To a bangaran najib kowa shiryawa yayi ya nufi gidan yaya sa'ad dan yasanar dashi halin da ake ciki(wato yayan salma)




Yaci sa'a yaya sa'ad na gida bayan sungama gaisawa yaya sa'ad ya dubeshi yace yau najib ne a gidan nawa dafatan dai kuna lafiya ya ummusalma uwar rigima.




Murmushi najib yai sanan yace ai maganan dake tafe dani akan salma ne yaya sa'ad.




Maida hankalinshi yai kan najib sanan yace to Allah yasa lafiya ina sauraranka.




Gyara zama najib yayi sanan yafara ma yaya bayani ton daka farkon auren'shi da salma duk abinda yafaru a first nite dinso saida ya kwashe ya fada mishi har izuwa wanan lokacin.




Tashin hankalin da yaya sa'ad yashiga takasa boyuwa a zuciyarshi har a fuskarshi saida ta bayyana cikin tashin hankali ya furta innalillahi wa'ina ilaihi raji'un




Ummusalma ummusalma amma kin cuce kanki kinyi kadan kibata wa zuri'armu suna wallahi kinyi kadan, ya mace tilo daya a gidanmu ta zaman mana shaidaniyya kodan tana ganin ita kadaice mace.




Najib ne yace yaya kafin salma ta tafi university ba haka takeba jami'a ce ta maidata haka sanan da bakinta tacemin sanadin zaman hostel rayuwarta ta lalace karasa maganan yai daciwa yaya dan'Allah asan abinyi kar a bari tashiga duniya dan abun bazaiyi kyau ba.




Yaya sa'ad ne yace yanzu zanje gida najib za'asan abunyi.




A haka sukai sallama kowa zuciyarshi ba dadi




Cikin tasha tashiga dan d'ako masu tura wheelbarrow suna biye daita da kayanta, tinane take wani gari yakamata tanufa?
Inda batasan kowa ba takeso taje so take tayi nisa da danginta dan bataso tazama sanadin bugawan zuciyar uwar data haifeta ta tabbata idan yaya sa'ad yasamu labarin abinda tayi kasheta zaiyi har lahira dan bazata manta da kalaman daya fada mata ba a lokacin daza'a kaita dakin miji




Idan kinga dama karki zauna lafiya ummusalma idan kinso ki kashe auren ki koma bin maza hotel hotel, ki bude kunnenki kijini da kyau kinyi kadan ki kashe mana iyaye lokacinso beye ba. wallahi idan baki zauna lafiya ba kikayi sanadin daya kuroki gida saboda kicigaba da iskancin da kikasa wa zuciyarki to baki da masauki a gidan'nan idan kowa kinsamu masauki da hannuna zansa pillow na kasheki kibar ganin ke kadaice mace a gidan'nan kibar ganin an shagwabaki tare da nuna miki gata hakan ba yana nufi zamu zuba miki ido ki lalace bane. ki zama yar iska wace zata bata mana suna ta goga wa gidanmu baqin fanti gwara na kasheki kowa ya huta karasa maganan yai daciwa Allah ya bada zaman lafiya




Murmushi hade dawasu hawaye masu zafi yasauka a fuskan salma hannu tasa ta goge sanan tace tsaf yaya sa'ad zai iya kasheni idan yaji abinda na aikata Allah kadai yasan halin da mama zata shiga. Hmmm gwara nashiga duniya kawai




Tinanin garin da zata nufa take so take taje inda basu dakowa inda batasan kowa ba




Motar Lagos ta tambaya nan aka sanar daita akwai mota amma tafiyan dare sukeyi sai magriba zata tashi jin haka yasa salma ta yanke shawaran shiga motar sokoto dan bazata iya zama har magriba dan yakamata tasan takonta kafin a nemo inda take a gida.




Haka kowa akayi motar sokoto tashiga batare da tasan kowa a garin ba tonda take bata zuwa sokoto ba.




Kusan watan nabeela biyar da komawa dakin mijinta yaronta sai girma yake yana kara kyau.




Nabeela ce zaune a parlor Abubakar wanda suke kira da sadiq na zaune a cinyarta tv take kallo, ummi ce tafito daka daki hade dazama kusa nabeela tana fadin aunty sannu da hutawa gobe zan kuma gida fa




Bata fuska nabeela tai kana tace haba ummi kibari sai admission din naku yafito saiki kuma gida




_*Kuye hakuri dajina shiru kwana biyu banda lafiya ne ko wanan'ma dauriwa nayi nai muku😒*_






Keep following me i need more and more comments read and share😘😘😘
πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–




*ZAMAN HOSTELπŸ’ž*




πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–




STORY
AND
WRITTEN BY


RAHEEMAπŸ”₯




DEVOTED TOπŸ‘‡πŸ»
(YUSUF)πŸ’‹










πŸ…Ώ65-66






Murmushi ummi tayi sanan tace a'a Anty gida nakeso na koma kawai.




Gani da nabeela tai yarinyan ta matsa saita kuma gida yasa ta amince da maganarta




Yaya sa'ad ne zaune tare da matarshi ya sanar daita abinda ke faruwa. Abinda salma ta aikata be mata da dadi ba nan tabama yaya sa'ad shawara karda yasanar dasu baba gudun kar hankalinso ya tashi kallon matarshi yai kana yace ummu hanif nima nayi tunanin hakan mahaifiyata nake tausaya mawa gashi tana da ciwan zuciya Allah yasa kar ummusalma tai sanadin da zuciyarta zata buga karasa maganan yai da dafe kanshi cikin tsananin damuwa




Shiru ummu hanif tayi na wani lokacin sanan ta dube yaya sa'ad tace Abban hanif ga wata shawara mana




Kallonta yai batare dayace komai ba, cigaba da magana tai.... Mezai hana muja bakin'mu muyi shiru karda kasanar dakowa abinda ke faruwa, ka kira najib ka rugeshi ya rufamana asiri ya maida salma dakinta tonda akwai sauran zama a tsakaninso har idan ya amince zai maidata inaga mun shawu kan matsalar batare da hankalin iyayan'mu ya tashi ba.




Nazarin maganan matarshi yake sanan yafurta ummu hanif kina ganin najib zai maida salma?
Idan ya amince zai maidata ai bamusan inda ta nufa ba




Murmushi tayi kana tace nemo inda salma take wanan abu mai sauki ne har idan da waya a hannunta koda bata dawu da kafarta ba sai muyi tracking inda take muje mu tawu daita... Dafa kafadan yaya sa'ad tai sanan tace kayi tunani mijina be kamata kuzuba ido tashiga duniya ba karda ka manta duk lalaciwan daza tayi jinin kace.




Hmmmmm hakane ummu hanif kin kawu shawara mai kyau nagode sossai shiyasa a koda wani lokaci bana shayin fada miki matsalata domin Allah yabaki fasahan dazaki warware min ita cikin sauki, nagode sossai




Murmushi tayi sanan tace yanzu dai kakira najib kace yazu gida kanason ganinshi idan kungama saika kira salma




Haka kowa akayi yana gama waya da najib yakira salma




Wayar tana hannunta ko zaria basu kaiba... Gani datai yaya sa'ad ke kiranta yasa gabanta yai munmunan faduwa rintse ido tayi ta bude sanan tace hmmm najib yasanar dasu kenan.




Five missed calls yai mata bata dauka ba
Aje phone din yai tare da kallon ummu hanif yace five missed calls nai mata bata dauka ba nasan bazata dauka ba zataji tsoro




Murmushi ummu hanif tai sanan tace nima nayi tunanin hakan zataji tsoran amsa wayarka, katura mata message amma karda ka tsoratata ruganta zakai musamu ta dawu.




Wayan na hannunta taji message ya shigo dasauri ta bude
_Ummusalma aduk inda kike ki tabbata kin dakata da tafiyar kidawu gida kizu gidana, ki kwantar da hankalinki ba abinda zan miki zaki kuma dakin mijinki dan girman Allah ummusalma kidawu gida dan'Allah dan'Allah, dan'Allah_


Ta karanta sms din yafi a kirga tana fadin anya ba wayau yake mata ba dazaice ta dawu kuma ta sauka a gidanshi wata zuciyarce tace mata kinga shikenan saiya kasheki ya birne gawan a gidanshi batare dakowa yasaniba tonda yace ki sauka a gidanshi.




Matar yaya sa'ad taga tana kiranta, kamar bazata dauka ba saidai ta dauka
Hello salma dan girman Allah aduk inda kike kidawu gida ki kwantar da hankalinki babu abinda za'ai miki....
Muryan ummu hanif ce tafara rawa saboda network din ba kyau a hanya salma take




Jin haka yasa salma ta kashe wayar hade da tura mata text
_Anty kiye hakuri amma bazan dawu ba wallahi yaya sa'ad kasheni zaiyi idan nadawu kuye hakuri kawai_




Karanta ma yaya sa'ad abinda salma tace tayi, nan yasa ummu hanif ta tura mata text
_A'a salma bazai kashe kiba kedai kidawu kisamu ki kuma dakin mijinki karkiyi wasa da wanan damar haba ummusalma me kika hango a zaman bariki? Menine abun burgewa a karuwanci babu wata riba karshenso baya kyau a wulakance rayuwarso take karewa bana fata kizama haka kiye tunani sanan ki gagauta dawuwa danAllah_




Hannu salma tasa ta share hawayan da suka zubo mata maganan da ummu hanif ta fada mata sun shiga zuciyarta, nan ta daga murya tace wa driver zata sauka a zaria akwai abinda ta manta dashi dole saita kuma gida.




Haka kowa a kayi a zaria ta sauka wata mota tashiga wanda zai kaita kaduna.




Muneera ce a kitchen blanding kayan miya tayi, gas ta kunna hade dasa pot akai sanan tazuba mangyada a ciki saida mangyanda yai zafi tazuba kayan miyan juyawa take tana ya mutse fuska hade da toshe hanci.




Tsaki tayi sanan ta kashe gas din ruwa ta dauka a fridge sanan tafita parlor tazauna fuska a daure tadau waya takira mansur




Herty idan zaka dawu ka tsaya kasiya abinci dan banyi girki ba
Tohm qalbe abinda kenan yace mata.




Kitchen ta kuma cornflex ta hada sanan tafito parlor tazauna, hannu tasa ta shafa cikinta game daciwa Allah yasa ciki gareni dan canjin da nakeji a jikina yai yawa yanzu.




Tana zaune a gurin taji ana knocking tashi tayi ta bude
Rungumeta yai a jikinshi yana fadin qalbe amsan ledan hannunshi tai hade daciwa sannu dazuwa herty i missed u.




Kitchen tanufa hade da dauko plates da spoon, bude takeaway take tana kokarin zuba abincin a plate.




Mansur ne ya dubeta sanan yace qalbe meyasa bakiyi girki ba?
Aje abincin tai a gabanshi game da miga mishi spoon tana fadin bismillah sa hannu muci.




Girgiza kai yayi kana yace ai nakine ke kadai nasaba da abincin gida bana iyacin abincin waje yanzu. ki dafamin indomie daukar plate din abincinta tai hade da durawa a kafarta sanan tace herty kenan aikam saidai kayi hakuri bazan iya girki ba shiyasa nace kasiyo abinci a waje ai.




Shiru Mansur yai yana kallon Muneera a kwanakin nan tafara canza mishi batason girki sanan abu kadan zai mata saita nuna ranta yabaci tafara fushi, bece mata komai ba harta gama cin abincinta tasha ruwa.




Saida yaga tagama sanan yace qalbe yunwa nakeji nace ki dafamin indomie, migewa tai tana kwashe plates kana tace herty ya kakeso nayi dakai ga abincinan kasiyo kaci mana, gaskiya bazan iya girki ba kayi hakuri kamshin abincin tashin zuciya yake samin tana karasa maganan tawuce kitchen aje plates din tayi sanan tafito dakinta tawuce ko kallon inda yake batayi ba.




Shima daki yabita kayan jikinshi yake ciriwa towel ne daure a waist dinshi sanan ya dube Muneera yace ki nemamin abinda zanci kafin nafito wanka sanin kankine nariga dana saba da abincin ki idan kinga naci abincin waje to bana gari ne.




Turo baki Muneera tayi jitayi ranta ya baci cikin fushi tace ne wallahi bazan iya girki ba ne gaskiya na gaji haka rayuwan auren yake life in kitchen koda yaushe mutum bashi da huto karasa maganan tai dajan blanket ta rufe jikinta.




Da mamaki mansur yake kallonta gaba daya ta canza kulawan da take mishi a baya yanzu bata mishi ba kamar daba




Babu wani bata lokaci saiga najib yazu kiran da yaya sa'ad yai mishi.




Zaune yake a kujera cikin girmama yake sauraran maganan yaya sa'ad




Yaya sa'ad ne yace najib tabbas kayi matukar hakuri da salma kuma naji dadi daka rufa mata asiri Allah yasaka da alkhairi, wata alfarma nake nima a gurinka dan'Allah ka taimaka mana ka rufa mana asiri kamar yanda Allah ya rufa maka




Najib na matukar ganin mutuncin yaya sa'ad cikin girmamawa yace yaya me kakeso kafada kanka tsaye ba damuwa




Yaya sa'ad ne yace kayi hakuri najib kayi hakuri ka maida ummusalma dakinta dan girman Allah.




Najib ne yace yaya sa'ad wallahi koda bakace na maida salma ba daman ina da niyyan maidata idan har tadawu, nayi tunani sossai akan lamarinta tabbas tayi ladama kuma ta shiryu kamar yanda tasanar dani kuma gashi tana kokarin kyautatamin.




Yaya sa'ad yaji dadin abinda najib yace sai yaji zuciyarshi tadan mishi sanyi tashin hankalin daya tsincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login