Showing 21001 words to 24000 words out of 68402 words
salma tayi hade da fadin shegiya nabeela wato ton kafin kishiga gidan zaki fara juya uwar gida. Muneera ce tace haba nabeela kidinga tausayin uwargida mana dukanso dariya sukayi.
Salma da Muneera hostel suka wuce ita kuma nabeela gidan dazata zauna ta nufa bayan tagama duba komai tafito daka gidan, gidan uwargidanta ta nufa wato maimuna da yake basa da nisa
Maimuna na zaune a parlor tana bama yaronta abinci Wanda be wuce shekara hudu ba wato khalil, knocking taji anayi, cikin sauri ta mige tsaye tana fadin Ana zuwa bude kofar parlor tayi, fuskar data gani yasa gabanta yai munmunar faduwa dakyar ta daidaita nutsuwarta gagaro murmushi tai tasa a fuskarta hade daciwa baiwar Allah shigo daka ciki.
Shiga cikin parlor tai kanta a sama tana taunan chewgum gas gas gas da alama matarnan batasan nice nabeela ba amaryarta a zuciyarta ta fada haka, itama maimuna shigowa ciki tai hanyar kitchen tanufa tana fadin baiwar Allah barin kawu miki ruwa, tana shiga kitchen ta fashe da kuka tana fadin ya Allah kabane ikon cin jarabawanan ya Allah kabane juriyan da dauriya. Share hawayan tayi sanan tacika try din da kayan fruits hade da drinks da snacks
A gaban nabeela ta aje tana fadin bismillah yaruwa, harara nabeela ta watsa mata, baiwar Allah saidai kuma bangane kiba daka ina kike?
Dariya mai sauti nabeela tai sanan tace ton farkon shigowata abinda kenan yakamata ki tambaya, kinsan mijinki zaiyi aure kowa?
Murmushi dauke a fuskar maimuna ta amsa nabeela da Eh nasan zaiyi aure
Smiling nabeela tayi kana tace good wane mataki kika dauka kokuma kike da shirin dauka akan maganar auren?
Hade fuska maimuna tayi kana tace wanan wace irin tambayace baiwar Allah?
Ina ruwana da aureshi dahar zan dauki mataki abinda Allah ya halakta mishine, aine dadi nane idan yayi auran domin haryanzu ban tabbatar aure zaiyiba amma ina rugan Allah yasa ba lalata yar mutane zaiyi ba kamar yanda yasaba lalata sauran
Kallon banza nabeela taimata sanan tace ban fahimce maganarkiba daman lalata yake da yaran mutane?
Shiru maimuna tayi nadan wane lokaci sanan tace nagaji da zigan mutane, nagaji da maganganun mutane akan auren da mijina zaiyi nikadai nasan halin da nake ciki gwara yayi auren nuna yaronta Khalil tayi da yatsa sanan tace kinga wancan yaron
To dan shegeni mahaifiyarshi da Alhaji ba karamin soyayya sukaiba yar gidan malamai ce. haka ya yaudareta da Kalmar zan aureki harta kudin sadaki ya biya tonda yasamu abinda yake bukata a gurinta ya watsar da maganan auren bayan ta haihu mahaifin yarinyar da kanshi yakawumin jaririn a Randa ta haihu abun tausayi koda Alhaji yadawu saiyace bashine mahaifin yaron ba, saida nasa shi agaba mukaje asibiti akai DNA test anan aka tabbatar mana da danshine
Ummi, ummi. daka wane daki yarinyan tafito tana ciwa na'am mummy, nuna yarinyan tayi da yatsa kana tace jeki abinki maida kallonta tayi gurin nabeela sanan tace kinga ummi itama ba yata bace kamar yanda aka samu khalil haka aka sameta, sauran yaran guda biyu kuma yarana ne Ameera a waje muka sameta fatima kuma itace tsabtaciyar ya.
Wane irin gume ke karyu wa nabeela dukda sanyin A.C dake busawa a parlor amma gume takeyi tine maimuna taga tashin hankali kwance a fuskar nabeela, a zuciyata ta furta da alama zanci nasara akanta, maganan da maimuna tayi yadawu da nabeela cikin haiyacinta.
So Dan haka karda kibama kanki wahala gurin bane shawara babu abinda yadamene da auren dazaiyi hasalima tausayin yarinyan nake dan na tabbatar tana dauke da ciki idanko bata dashi tana gabda dauka
Gyale tasa ta goge gume take goshinta sanan tace kekuma kinsan mijinki bashi da hali mai kyau shine kike zaune dashi?
Dariya maimuna tayi kana tace aizama dashi farilla ne a gurina saboda bane da gidan da yafinan, ne marainiyya ce
Tashi nabeela tayi hade da daukar Jakarta tana fadin to Allah ya kyauta, hanyar kofa tanufa, baiwar Allah baki fadamin sunan kiba gashi zaki tafi
Tsaki nabeela tayi sanan tafita. Tana fita maimuna ta kwashe da dariya hade daciwa karaman yar'iska kawai.
Zaune take a kasa salma da Muneera sai hakuri suke bata haba nabeela meye abun tada hankali ki kwantar da hankalinki Alhaji shehu saikin auren'shi dan zamu shiga mufitane idan yasaba yaudaran yan mata wallahi beisa ya yaudareki ba, hmmm salma bawanan bace matsalar.
Ai auren'shine baxan iyaba yanzu duk yayan shegu yatara pha, yar halak din guda dayace, meyasa zan zabama yaranan uban banza Muneera ce tace wallahi duk lalaciwarki nabeela gwara ke akan shehu karda kifara kuskuran auren'shi nidaman ton farko banso abunba amma tonda naga kinaso shiyasa nasa ido na albarkaci abun da addu'a, gashi matar bata sankiba bata taba ganin kiba amma saboda suruton mutane da ziganso tafada miki abinda ke zuciyarta.
Tashi tsaye nabeela tayi tana fadin Kawayena barinje gida nasanar wa mama halin da ake ciki dan kunsan gobe zasu kawu komai na auren lokaci daya zasu kawu komai. Gwara a dakatar dasu, hakane nabeela saikin dawu
Nabeela nafita salma tai tsaki hade daciwa ikon Allah wato yanzu haka rayuwan takuma Allah yabamu mazaje nagari, murmushi Muneera tayi sanan tace abun dariya lalatace na niman miji nagari, kin nutsu kinkama mutuncinki yakika kare gurin samun miji nagari inaga baki kama mutunci kiba
Mtsssschew Muneera karki batamin rai kinajina kor?
Banason maganan banza, babu yanda za'ai mutum yai magana saikin cutar dashi da baqar magana.
Keep following me i need more and more comments read and shareπππ
ππππππ
*ZAMAN HOSTELπ*
πππππ
STORY
AND
WRITTEN BY
RAHEEMAπ₯
DEVOTED TOππ»
(YUSUF)π
π
Ώ33-34
Mtsssschew Muneera karki batamin rai kinajina kor?
Banason maganan banza, babu yanda za'ai mutum yai magana saikin cutar dashi da baqar magana
Itama Muneera tsaki tayi hade daciwa kanki akeji
Koda tashiga parlor bata tarar da mummy anan ba masu aiki ta iske sai amal cousin dinta wace bata wuce 14years ba da yake a gidanso take zama. aunty nabeela sannu da zuwa
Yauwa amal mummy pha?
Tana upstairs
Ok
Kuka nabeela take mummy na lalashinta tana kiye hakuri yar mummy kidaina kuka kigodema Allah daya baiyana mana halinshi ton kafin ki aureshi, nabeela bata boyewa mummy komai ba tasanar daita komai kallon mummy tayi cikin sanyi murya tace mummy yakamata ki fadama daddy dan kinsan gobe zasu kawu komai
Aikam Babanki baya kasa maganar aurenki kuma daman a hannun Babanki lawan yake shida sauran yan'uwanshi zasu gabatar da komai, to mummy ki kirashi dan'Allah, karki damu nabeela zan sanar dashi amma barin fara fadawa mahaifinki.
Nabeela nazaune a gefe mummy da daddy sukai waya suka gama, mummy na aje waya nabeela ta matso kusa daita me daddy yace mummy?
Bata fuska mummy tayi sanan tace Babanki yace maganan da kika kawu duk shirme ce yaza'ai kidauki maganar kishiyar'ki tayi hakane danta watsar da maganan auren, mummy matar bata taba ganina ba balle nace tayi haka ne danta watsar da maganan auren. Murmushi mummy tayi sanan tace nabeela ke yarinya ce haryanzu, Babanki dai yaqi yarda da lamarin yace zaikira yayanshi lawan yasanar dashi asakeyin bincike akan lamarin ayau za'ai bincike basai gobe ba, kuka nabeela tafara dafa shoulder dinta mummy tayi kana tace kiye hakuri nabeela amma sanin kankine mahaifinki magana daya yakeyi ba canji ki kwantar da hankalinki za'a sakeyin bincike har idan aka kamashi da abinda kikazu dashi wallahi koda.
mahaifinki yace saikin aurenshi nikuma bazan yarda ba domin ke kadai na mallaka duk duniya bamu da wata ya ko da bayan ke.
Kwanciya tai a lap din mummy, kina da exam gobe ne?
Aa mummy sai next tomorrow
Ok Allah ya taimaka
Har dare salma da Muneera basu sakeyin magana a tsakaninso ba, gani da Muneera tai dare yayi nabeela bata dawuba yasa takira nabeela
Hello nabeela ya kike zaki dawune yau?
Muneera ba lafiya ba bazan dawu yauba sai gobe kinji abunda daddy yace.......... Kwashe duk abinda yafaru tayi tasanar da Muneera tabbas Muneera ta tausaya wa nabeela, tohm nabeela Allah yashige miki gaba akan lamarin nan, salma ce tashigo dakin a guje tana fadin Muneera Muneera
Nabeela zamuyi waya anjima kashe wayar tayi meyafaru salma kikemin irin wanan kiran?
Kinsan Husna friend din kareema?
Eh amma sun dade dayin fada ai meyafaru?
Ina zaune a Gossip center ina amsa waya sai husna dawata kawarta suka zauna a gefena dayan yarinyan kamar ba hostel takeba to kinsan akwai duhu ba lallai su gane nice ba.
Hotan nabeela husna ta nuna wa friend dinta tanaciwa jiya sister na tamin sending picz din nabeela wai ko nasanta yakuma tarbiyyanta yake bansan meyafaru ba amma nikam na yabi nabeela nace mata tana da hali mai kyau dan ba abinda yataba shiga tsakanina daita, sai friend dinta tace to meyasa sister dinki take tambaya akanta?
Wallahi nima bansaniba amma xanje gidanta gobe
Wace unguwa take?
..........
Kin fahimce abinda nake fadamiki Muneera?
Daga kai Muneera tayi sanan tace tabbas na fahimta sunan unguwan da nabeela zata zauna husna tace yayarta take, karde ace sister husna itace kishiyar nabeela, gyara zama salma tai hade daciwa hmmm nima abinda nake tunani kenan but yazama dole a daranan muyi investigation akan lamarin
Hakane salma to tayaya zamu fara bincike?
Murmushi salma tai sanan tace sato wayar husna zamuyi, zaro ido waje Muneera tayi hade daciwa lallai salma aiwanan ba karamin aiki bane
Keee dalla karki bane kunya saikace ba masscom student ba.
Daddyn nabeela yasa brother dinshi yayi bincike sossai akan Alhaji shehu harta akan yaranshi anyi bincike dukda yaran kanana ne basu samu wata munmunar shaidaba kuma an tabbatar musu daciwa duk yaran'shine, da misalin karfe tara na dare nabeela na kwance akan makeken bed dinta mummy tashigo dakin kamar daman mummy take jira
Dasauri ta tashi tana fadin mummy ya ake ciki?
Dariya mummy tai sanan tace ki kwantar da hankalinki yar mummy yanzu Babanki yakirane yace babu abinda za'a fasa zuwa gobe zasu kawu kayan aure an tsananta bincike sossai ba'a sameshi dawata muguwar dabi'a ba wanan makircin kishiyarkice kawai shiru nabeela tayi nadan wane lokaci sanan tace to shikenan mummy, dafa kafadan nabeela tai hade daciwa yauwa yar mummy ki kwantar da hankalinki kinji.
Blue Jumpsuit ne a cikin Muneera Wanda bekai gwiwa ba haka itama salma jumpsuit dinne sanye a jikinta salma ce ta dube Muneera sanan tace duk abinda nafada miki shi zaki fadamata idan wanan hanyar bataiba zamu shigo dawata dabara bata fuska Muneera tayi kana tace salma dan dole zanma husna magana kema kinsan ba magana nake da yarinyar ba.
Tura Muneera gaba salma tai hade da fadin kedai tafi duba gossip center ko sunanan basu tashiba, wallahi kidaina miskilanci kowa kice baki magana dashi.
A gossip center ta hango husna kusan su biyar a zuciyarta tafurta shegu kawai mayun zaman gossip center. Koda Muneera takarasa gurin bawace ta kalla a cikinso balle sannu ta hadata dasu a gaban husna ta tsaya hade daciwa husna Barka da dare, ya kike?
Abun yabama husna mamaki dan ba magana suke da Muneera ba da tana mata magana aduk inda taganta saitai mata magana wane lokacin dakyar take amsawa wane lokacin kuma taqi amsawa idan husna batai mata magana ba kozaso hadu sau dari ita bazatai mata magana ba ganin haka yasa husna tadaina wa muneera magana.
Fuska cike da mamaki husna ta amsa da lafiyalau, friends din husna kowa kallon banza suka watsa wa Muneera kowace a cikinso tafara danna wayarta... Uhmm husna daman gurinki nazu nace dan'Allah idan kina film kituramin, murmushi tayi hade daciwa eh Ina da film amma phone din na daki nasa chargi yanzu kikeso?
Eh yanzu nakeso nagaji da zama shiru inaso nai kallo, wata daka cikin friends din husna tace Muneera naga kamar kina da exam next tomorrow kor?
Harara Muneera ta watsa mata hade dayin tsaki maida kallonta gurin husna tai sanan tace yaza'ai husna zaki turamin ko yaya?
Key husna tabawa Muneera hade daciwa take room din a rufe yake idan kin bude zakiga phone dina a chargi saiki dauka kiye sending, amsar key din tayi hade daciwa I hope ba password a phone din?
And then wane irin waya ce?
Wane room kike ma?
Kamar husna bataji dadin questions din Muneera ba amma dayake bata da zafi saita bata amsa
Room 9 nake
Samsung Galaxy S8 ce
Chowchow shine password din.
Juya idonta tayi hade daciwa alright thanks dear, but zantafi da phone din room dina kinsan it will take time bansan zama a room din mutane idan babu kowa tana karasa maganan tawuce, Muneera nawuciwa friends din husna suka bude chapter dinta.
Muneera ce tashigo room dinso hannunta rige da wayar husna hannu salma tabata game daciwa that's my Beb aidaman nasan saita baki, murmushi Muneera tayi sanan tabama salma wayar, bincike suka fara a cikin wayar WhatsApp dinta suka shiga, shiga chart sukai suna dubawa ko zasuga Wanda aka turo picz din nabeela sun bude mata unread messages dayawa sanan sukaga wane chart Wanda aka turo picz din nabeela, an rubuta sis maimuna
A tare suka kalla juna smiling sukayi batare da sunce komaiba karanta chart din sukai, Muneera yanzu meyakamata muyi?
Shiru Muneera tayi sanan tace kunna Data zamuyi muyi chart da maimuna a matsayin husna
Zare ido salma tai tana fadin Muneera muyi chart daita kikace fa?
Idan fa muna cikin charting husna ta shigo, murmushi Muneera tayi sanan tace kedai kiye yanda nace miki tashi kisa mana key a kofar.
Salma ce takira nabeela tana dauka kuka tasa sanan tasanar wa salma yanda sukayi da mummy. Kedai ki kwantar da hankalinki nabeela yanzu kinsan menakeso dake?
A'a
Kituromin number Alhaji shehu
Mezakiye dashi?
dayake wayar a loundspeaker take, kedai kituro da number Muneera tafada haka, ba musu nabeela taima salma sending number
Sallama sukaima maimuna
Bata online, kiranta sukai a waya saida tadauka suka kashe wayar, text Muneera tai mata kamar haka
Aunty please kihau WhatsApp muyi magana akan maganan yarinyan da kika turamin picz dinta wato nabeela
Maimuna na shirin kiran husna saiga message dinta yashigo tana karantawa tai saurin ta kunna Data hade da hawa WhatsApp danta matso taji abinda husna zatace mata
Haka itama Muneera bata fita a chart din ba, message tagani yashigo
Husna naga text dinki Ina sauraranki
Hannu Muneera tabama salma suka tafa hade da kwashewa da dariya, salma ce tace aidaman nasan dole zata hau online wato taji sunan nabeela
Keep following me i need more and more comments read and shareπππ
ππππππ
*ZAMAN HOSTELπ*
πππππ
STORY
AND
WRITTEN BY
RAHEEMAπ₯
DEVOTED TOππ»
(YUSUF)π
π
Ώ35-36
Husna naga text dinki Ina sauraranki
Hannu Muneera tabama salma suka tafa hade da kwashewa da dariya, salma ce tace aidaman nasan dole zata hau online wato taji sunan nabeela
Message suka tura wa maimuna kamar haka...
Anty dazu naga Abban Khalil da yarinyar nan wato nabeela wai menine a tsakaninso?
Dan'Allah karki boyemin komai Aunty
Voice note maimuna tai musu tana ciwa husna ai itace matar dazai aura kinsan zai kara aure kor to itace, wallahi ba yarinyan arziki bace har hotunan batsa take turomishi wa'iyazubillahi, kallon juna salma da Muneera sukai karban wayar daka hannun Muneera salma tayi sanan tarubuta
Aunty hotunan batsa kuma amma ya akai kika gani kokuma ince waya fadamiki?
Voice tasakeyi husna ba fadamin akaiba nida idona nagani nan maimuna ta kwashe duk abinda yafaru tafada, salma ce tai dariya hade daciwa shegiyar mata wato shine ta nuna kamar batasan nabeela ba to zamuyi maganinki Dan naga alama kin iya shirya makirci
A hankali Muneera tafurta a gaskiya salma matarnan taban tausayi babu macen dazataso ai mata haka. Hararan Muneera tayi sanan tace to uztaziyya knocking sukaji anayi a hankali salma tace jekisa kunne a kofa kije ko waye, muryar husna taji tana sallamu alaikum.
Cikin sauri Muneera ta dawu a hankali take magana tonda munsamu abinda mukeso kiye sauri ki deleting chart din kashe mata data
Ok but kafinan zanyi saving number Dina inaso nai forwarding chart dinmu zuwa WhatsApp dina
Cikin sauri sukai komai suka gama kallon salma Muneera tayi kana tace gashi bantura film ko daya ba kuma kinsan zender zai nuna mata idan natura, shiru salma tai sanan tace hakane sa film ki kalla a wayarta sai kice a phone dinta kike kallo Ashe nafita da wayarki. Ok
Barin bude kofar nafita, salma na tafiya da kusan 10minuntes saiga husna ta shigo dakin. Muneera na kwance tana kallo earpiece na kunnenta, tana ganin husna ta tashi ta zauna murmushi dauke a fuskarta cire earpiece din tayi hade daciwa sorry ban dawu miki da wayar ba, ashe salma tafita da wayata to sai nace barin kalla a naki.
Karban phone din tayi A'a karki damu bakomai kozuwa gobe sai kizu kitura films din, tashi Muneera tayi kana tace barin rakaki har daki ta raka husna sanan tadawu room dinso
Salma ce tashigo dakin tana waya da nabeela kedai kihau online nace, zama kusa da Muneera tayi forwarding chart dinso taima nabeela sanan taimata bayanin komai, koda nabeela tagama sauraran voice note din farin cikine ya kamata a fili tafurta Allah nagode maka daka hadane da kawayan arziki wayanda damuwata suma tasuce Alhamdulillah, dakin mummy tashiga a guje tana mummy mummy, bayani komai taiwa wa mummy batare data sa mata voice note dinba gudin kar taji maganan nude picz, albarka mummy taita shima Muneera da salma
Koda husna tahau WhatsApp ganitai duk an bude mata chart abun yabata mamaki but bata fahimce komai ba haka yasa tacigaba da hidimar gabanta.
Babu abinda aka fasa an kawu kayan auren nabeela an biya sadaki, kudin sadaki naira dubu dari, kudin gaisuwa naira dubu hamsin, kayansa rana suma ankawu harta lefe ankawu akwati dozen biyu a cike suke taf dakyar ake rufewa, rabi da kwatan kayan duk bana 9ja bane kadan ne nanan, komai mai tsada ne a ciki anzuba mata gold manya manya masu tsadar gaske. wata biyu akasa bikin ba'a wane ja lokaci ba nabeela da friends dinta suna daki gidan yadan cika da yan'uwa
Muneera ce tace to nabeela Allah yasanya alkhairi muma Allah yasa muga namu haka da ameen suka amsa, kallon salma Muneera tayi sanan tace kema yakamata kifito da miji musha biki hhhhhhhhhhhhh dariya salma tai hade daciwa ba yanzuba sai natafi I.T zanyi aure dukanso murmushi sukai hade daciwa Allah yakaimu.
The next day husna na hango zaune a kujera a gidan maimuna bayan sungama gaisawa maimuna tace husna kinji fa halin da nake ciki, narasa inda xansa kaina jiya yakai komai na aure da karuwar tashi. Cikin rashin fahimta husna tace aunty ban fahimce kiba wallahi, karuwa Abban Khalil zai aura?
Cikin bacin rai maimuna tace ya kikemin tambayoyi kamar bakisan komai ba bayan kina sane dakomai.
Saukowa kasa husna tayi tana fadin aunty wallahi ba abinda nasane nidai nasan kinsanar dane Abban Khalil zaiyi aure amma bansan wazai aura ba.
Dalla