Showing 57001 words to 60000 words out of 68402 words
goge tv da show glass dincan wallahi sunfita sossai.
Smiling yai sanan yanufi kitchen yana fadin kedai zuki zauna kici abinci dole nayi miki aiki tonda baby na bayaso kina wahala
Zama tai a dining tare dasa hannu ta shafa cikinta a zuciyarta tafurta Allah yasa idan munje asibiti ace ina da ciki bansan yanda zaiji ba idan ba ciki bane duk wahalan nan da yakeyi dani.
Chips and egg yai frying, nan yazuba mata sanan ya hada mata tea, feck yasa ya debu chips din har yakai bakinta saikuma yaqi samata a baki turo baki tai hade da bata fuska tana fadin nikam kabani
A baki yasa mata yana fadin sarkin shagwaba kawai, shafa face dinshi tai tana fadin herty wanan chips din yai dadi sossai irinshi zakana min kullum, murmushi yai sanan yace qalbe amma kamar nacika gishiri egg din kuma maggi yayi yawa
Cika feck tayi da chips sanan takai bakinta tana fadin a'a nidai banjiba a haka yamin dadi herty kayi kokari sossai
Yanda ta yaba mishi ba karamin dadi hakan yamishi ba
(Idan mijinki yai surprising dinki ta hanyar girka miki abinci daure kiye appreciating kice yayi dadi koda kowa beyi dadi ba daure kici koda kowa dakyar kike hadiyewa hakan zaisa yaji dadi gobe yai miki abinda yafi haka.... Duk dadai a zamanin da muke yanzu da wuya a samu namijin dazai zage yaima mace girki buuuuuuh nasan dai baza'a rasa ba shawara ce daka marubuciyar๐)
Driving yakeyi tana zaune gaban mota hannunta rige da waya tana buga game... Uhmmm herty
Kallonta yai sanan yace qalbe ya akai?
Wani asibiti zamuje ne herty?
Smiling yai sanan yace wani hospital kikeso muje
Shiru tayi nadan wani lokaci sanan tace muje hermony private hospital ne asibitin su aunty sadiya
Sai murmushi nurse sadiya take tonda taga Muneera da mansur zama sukai sanan suka shiga gaisawa
Muneera idonki kenan ko?
Murmushi Muneera tayi kana tace aunty sadiya kiye hakuri ai inanan zuwa gaishe ki har gida.
Tohm shikenan
Kasa tayi dakanta tana fadin aunty sadiya daman so nake amin gwaji koina da ciki
Murmushi Aunt sadiya tayi sanan tace tohm hajiya Muneera
Kusan 30minutes suna zaune kafin komai ya kammala, cikin farin ciki ta miga musu wata takarda tana fadin congrat Muneera kina da ciki, rungume Muneera mansur yai yana fadin na fadamiki kina da ciki amma kinqi yarda kinji ko
Herty yaza'ai nayarda bayan nayi period this month kuma ance masu ciki basa period, nurse sadiya ce ta katseta daciwa waya fadamiki haka
Akwai wayanda koda suna da ciki suna menstruation nan tashiga mata bayani
Murna da farin ciki fal zuciyar mansur haka suka kuma gida yana tarairayan Muneera kamar kwai a cokali.
Dukda Muneera batason mai aiki amma ba yanda ta iya danko mansur saida yasa aka kawu mata yar aiki saboda aike aiken gida Muneera bayi takeba cikin yasa mata kasala dasan jiki bata da aiki sai bacci.
A yanzu salma da najib zaune suke lafiya bawani tashin hankali a tsakaninso amma saidai data tina zai kara aure sai taji ranta na baci
Zaune suke a parlor suna kallon news magana nacinta amma tana tsoran furtawa candai ta daure tace
Yaya najib nace yaushe ne daurin auren naka?
Batare daya kalleta ba yace saura two weeks
Ta6e baki tayi kana tace har abun ya matso haka lallai karasa maganan tai daciwa Amaryan yar kaduna ce?
Eh a kaduna take causin dita ce ma!
Gaban tane taji ya fadi a zuci tafurta lallai wato yar uwarkace auren zumunci shikenan za'a hademin kai
Wata tambayar tasake jefa mishi aina Amaryan zata zauna?
Sai a wanan lokacin ya juyu ya kalleta kana yace anan gidan zata zauna a wancan flat din zata zauna amma zata fara zama anan zuwa lokacin dana karasa gini saita kuma gurinta
Zare ido waje salma tayi tana fadin zata zauna aina
Haba dai yaya najib sanin kanka ne two bedrooms ne anan bata karasa ba ya katseta daciwa a dakina zata zauna ba naki ba
Cikin bacin rai salma tace ok fine idan kace a dakinka zata zauna karda ka manta kayan dake dakin ai daka gidanmu naxu dasu, sanan kuma kitchen daya zamuna sharing shima kayan kitchen din ai mallakinane and then parlor ma haka kayan ciki duk daka gidanmu naxu dasu.
Fuska a hade najib yace wanan duk mai sauki ne bed dinki dake dakina za'a fitar dashi amarya zatasa nata kafin nakarasa mata gini, sanan kuma maganan kitchen da parlor da kikeyi babu abinda za'a taba miki anan da kayanki zatai amfani kafin takuma nata bangaran bawani dadewa zatai anan ba befi tayi wata biyu zuwa uku ba, hakuri zakiyi idan takuma bangaranta sai a dawu da bed dinki dakin.
Saboda kishi tine salma taji zuciyarta na zafi kamar zata fasa kirjinta tafito cikin daga murya take fadin haba haba aiwanan cin fuska ne wallahi. Saboda an rainane kuma ba'a daukeni da daraja ba shine za'a wulakantani ta wanan hanyar gaskiya bazan yarda ba. Tonda baka da wajan dazaka ajeta saika hakura da auren har zuwa lokacin dazama kammala gini
*WATA SABUWA ANYA AMMA SALMA ADALCI KOWA???*
Keep following me i need more and more comments read and share๐๐๐
๐๐๐๐๐๐
*ZAMAN HOSTEL๐*
๐๐๐๐๐
STORY
AND
WRITTEN BY
RAHEEMA๐ฅ
DEVOTED TO๐๐ป
(YUSUF)๐
_Wattpad๐๐ปFatimamuneera001_
๐
ฟ71-72
Migewa najib yayi batare da yacema salma komai ba, itama tashi tayi tabishi a baya tana fadin yaya najib dakai nake magana kaima kasan baka kyautamin ba kor?
Be saurareta ba ya shige dakinshi hade dasa ma kofar key.
Jingina tayi a jikin kofar wasu hawaye ne masu zafi suka wanke fuskarta a fili tafurta ne kenan kullum cikin tashin hankali daka wanan sai wancan.
A bangaran nabeela kowa ton daka wanan ranan bata da kwanciyan hankali Alhaji shehu ya matsa mata ya takura mata abu kadan zatayi sai masifa yanzu abun nashi yaci tira ya matsa mata da sex a rana saiya nimeta sau uku da daddare bayan sallan Asuba guraran karfi daya saiya zankado yadawu gida koda kowa tana school tosai ta dawu gida.
Duk tabi ta rame yasata a gaba magana kadan sai duka, kwance take a gado yayin da take kyarma tana rawan sanyi sama sama take sauke numfashi saboda azababen ciwan kai da takeji wanda ko yaya ta juya sai taji kamar an kwada mata guduma.
Kuka sadiq yakeyi hakan yasa ta rungume shi a jikinta kana tasa mishi nono a baki taci sa'a yayi shiru. Tana kwance a haka taji a budo kofar batare da sallama ba
Kan gadon yahau sanan ya dauke sadiq wanda yariga da yayi bacci a karamin gadonshi ya ajeshi sanan yadawu gurin nabeela, tana kallonshi tayi shiru zuciyarta cike fal take da tsanan'shi tasan abinda yazu nima.
Hannun'shi taji a nononta yana shafawa numfashi tasauke sanan ta maida nono cikin riga kana tace dan'Allah kataimakamin da magani ka kaine asibi banda lafiya nikadai nasan yanda nakeji a jikina
Dafa goshinta yayi sanan yace tabbas baki da lafiya ga jikin'ki yai zafi amma inaso kisani babu wani asibiti dazan kaiki tonda kikaqi aminciwa a zubar da cikinan to babu wani kyautatawa a tsakanina dake harki haihu karasa maganan yai daciwa zoki hau kaina a bukace nake.
Sake rufe jikinta tai da bargo sanan tace baka ganin banda lafiya ne Alhaji wanan rashin imanin dame yayi kama?
Bata karasa magana ba ya janye bargo data rufe jikinta dashi sanan ya tube kayan jikinshi kwanciya yai yana kallon sama kana yace tashi kimin abinda kika sabamin, maza kitashi ki hau kaina irin wanan style din nakeso yanzu take.
Hannu tasa taja bargo ta rufe jikinta saboda sanyin da takeji batare da tace komai ba, sake bude bargon yayi yana fadin ne zaki maida dan iska ina miki magana kinajina, tonda kikace bazaki zubar da ciki ba saiki jure duk wani laulayi dazaizo miki dashi maza kitashi kihau kaina ko jikinki ya gaya miki.
Hawaye kezuba a idon nabeela a fili tafurta ne nabeela nashiga uku da wanne zanji ga azababan ciwan kai da nakeji gashi wanan ya takura min, bata kulashi ba tasa kafa tasauka daka gado hartasa hannu ta murda handle din kofar saiji tayi an shagu wuyanta ta baya mari ya zabga mata sanan ya hankadata gado
Ihuuu tasa hade da sakin kuka tana fadin kasheni zakayi?
Gurin kofa yanufa yasama kofar key sanan ya dauko belt yashiga zaneta kuka take tana ihuuuuuu wanda hakan yasa sadiq tashi daka bacci a razane shima kuka yasa saboda razanan da yayi.
Dukanta yake da belt tana zagaye daki a guje tine ya fincikota hade da damgar wuyanta yana fadin ne ubanki zanci har idan kikace zaki kawumin iskanci karasa maganan yai da hankadata gado yana fadin maza kicire kayan jikin ki kimin abinda nasaki.
A kwance take amma jiri ne ke dibanta ciwan kai da takeji ba'a magana yanzu danko tamkar kanta zai rabe biyu.
Hawuwa gadon yai yana fadin dan kinga ina binki a hankali tona daina daga miki kafa yar iska kawai, mari ya zabga mata wanda saida tasaki kaaaara
Zanga wanda yafi taurin kai tsakanin nida ke har idan bazakimun abinda nace ba to nikuma bazan gaji da dukan kiba, kuka sossai sadiq yakeyi kamar zai shide amma kota kanshi Alhaji shehu bebi ba.
Tashi yai yacigaba da zabga mata belt kota ina yake dukanta kuka take da karfi tana fadin kayi hakuri zanyi yanda kace wallahi zanyi karka kasheni
Ba shiri nabeela ta tubi kayan jikinta... Jikinta na kyarma hawaye da majina dukya wanke fuskarta ta kwanta kana ta bude kafa cikin kuka tace zu kayi abinda zakayi kayi kagama inaso na lalashi yarona.
Cikin nuna isa yace nafada miki ke nakeso kihau kaina kor?
Kuka tasa sanan tace wallahi bazan iyaba ba karfi a jikina bazan iyaba, bazaki iyaba?
Kina da taurin kai yau zanga wanda yafi wani kafiya tsakanin nida ke karasa maganan yai da zafga mata belt a jiki kara ta saki saboda ya shigeta gashi ba kaya a jikinta harta mai gadi saida ya tausaya wa nabeela dukda akwai tazara a tsakanin inda yake zama da dakin nabeela amma yana jiyu kukanta da yake yaje bama flowers ruwa.
Gani da nabeela tayi idan bata kwaci ganta ba kasheta zaiyi hakan yasa ta dauki babban kwalban humra wanda ke aje gaban madubinta a goshi ta kwada mishi aiko sai jini yafara zuba dafe gurin yai cikin azaba yana fadin kasheni zakiyi?
Jikinta ba kwari dan jiri take gani ta nufi gurin sadiq daukarshi tayi sanan ta dawu tasa kaya a jikinta game da goya sadiq hijab tasa sanan tanufi gurin kofa
Alhaji shehu na dafe da goshin shi jini na fita harta bude kofa tasa kafa daya a waje taji motsin shi ta bayanta juyuwan daza tayi kwalba ce ya buga mata a goshi yana fadin saidai muyi mutuwan kasko masiyaciya dukda azaban da takeji ga jiri dake dibanta a guje tafita daka dakin jini nazuba a goshinta.
Mai gadi, mai gadi, mai gadi budemin gate abinda kenan nabeela keciwa yanda mai gadi yaganta ba karamin tausaya mata yayi ba, danko jini duk ya bata mata hijab a hanzarce taja mota tafita a gidan sadiq kowa har izuwa wanan lokacin be daina kuka ba
Allah ne kawai yakai nabeela gida lafiya dan bata gani hanya da kyau driving kawai takeyi koda me gadi ya bude mata gate danna kan motar ta tayi cikin gidanso batai packing motar a inda yakamata ba tafito cikin sauri sadiq rige a hannunta.
Bata kaiga shiga jikin gida ba jiri ya debeta ta fadi a gurin. Cikin tashin hankali mai gadi yasa hannu yadau sadiq wanda tare suka fadin da nabeela, kallonta yakeyi yana fadin accident tayi hala kafin ta karasu gida barin shiga gida nasanar da iyayanta.
_Kuye hakuri da wanan ba yawa da ace banyi typing ba gwara ayi koba yawa nayi busy ne kwana biyu but next page zan muku mai yawa karku damu๐ค๐ป_
Keep following me i need more and more comments read and share๐๐๐
๐๐๐๐๐๐
*ZAMAN HOSTEL๐*
๐๐๐๐๐
STORY
AND
WRITTEN BY
RAHEEMA๐ฅ
DEVOTED TO๐๐ป
(YUSUF)๐
_Wattpad๐๐ปFatimamuneera001_
๐
ฟ73-74
Cikin sauri ya fada parlor ko sallama babu sadiq sai kuka yake... Mummy ta mige game da amsan sadiq a hannunshi tare daciwa nabeela tazu kenan
Hajiya gatacan a haraban gida ta fadi kamar tayi hatsari kafin ta karaso... Har rige'rigen fita ake tsakanin mummy da daddy ton kafin suga nabeela hankalinso yatashi, kuka mummy tasa tana fadin Alhaji kalla fuskarta duk jini innalillahi wa'ina ilaihi raji'un.
Daddy ne yadauketa yasata a mota sanan ya kalla mummy yace dauko mayafinki ki kibar sadiq a hannun Amal.
Koda sukaje asibiti nabeela ta farka amma saboda allurai da sukai mata saita kuma bacci, daka mummy har daddy suna zaune kusa daita basu matsa koina ba dan gani suke kamar zasu dawu ace muso ta mutu
Gani da da daddy yai mummy tashiga damuwa sossai sai yaji tausayinta dukya kamashi dafa shoulder mummy yai yana fadin ki kwanta da hankalinki dan siririn hawayeni yafito daka idon mummy kana tace Alhaji ka dube jikinta fa karasa maganan tai da daga hannun nabeela tana fadin kalla shatan bulala kalla wuyanta, kalla gefen fuskarta dukta ba fara bace amma saida jikinta yai rodu rodu alamun duka.
Mummy bata karasa rufe bakiga nabeela ta bude ido dasauri ta matsa kusa daita tana mata sannu
Mummy ina sadiq?
Abinda kenan nabeela tace
Daddy ne yace yana gida hannun Amal
Mummy ce ta rige hannun nabeela tare daciwa Autan mummy accident kikayi a hanyar ki ta zuwa gida?
Hawayeni suka zuba a idon nabeela batasan lokacin da bakinta yafurta miji nane yamin haka harda duka.
Atare daddy da mummy suka furta shehu dinne yai miki haka?
Tine daddy yafara masifa ke daya kwal na mallaka a duniya shine yake kokarin kasheki to wallahi bazan yarda ba sainayi Shari'a dashi ko yanzu ba kyaleshi zanyiba
Tine mummy tashiga tsine ma shehu saida suka zageshi sanan mummy tace me kikai mishi?
Har yake kokarin kasheki?
Cikin kuka da tausaya makai nabeela tace mummy ciwa yai saina zubar da ciki bayason haihuwa yaro daya ya isheni rayuwan dunuiya nikuma na dage akan bazan zubarba inason abuna, shikenan ya dauki tsana ya dauramin sai duka da zagi tsakanina dashi karasa maganan tai da fashiwa da kuka tana fadin mummy wallahi na gaji dakyar nasha da saidai kuji na mutu ba karamin duka yaimin ba dazan nuna muku gadan bayana saikun tausayamin yayi kaca kaca da shaidan bulala.
Lalashinta suka shigayi mummy ce tace amma kema baki da hankali nabeela dukda irin bakar wahalan da kikesha shine kika gwadige kika zauna kikai shiru da bakinki.
Nabeela nafita daka gidan shima Alhaji shehu yasa kaya yafito goshin'shi nazubar da jini, kallon mugu mara imani mai gadi yake mishi gani da mai gadi yai goshin shi nafitar da jini sai yaji dadi a zuciyarshi yafurta aigwara da itama tai maka haka kullum kaita dukan yar mutane.
Mahaifin nabeela koto yasu yakai karan Alhaji shehu amma Allah ya taimakeshi dan be bari an kwana ba, a daran ranan ya biyuta gidanso.
Daka mummy har daddy sun wankeshi tas da baqaqen magana inda sai yaji dukya raina kanshi dan beye zatan nabeela tasanar dasu ba saboda sauda dama takanzu gida idan haka ta hadasu amma bata sanar da iyayanta.
Hakuri yashiga basu nan daddy ya nuna mishi ai hakuri ta kare... kawai yabama nabeela takardan saki dan bazata kuma gidanshiba karda a waye gari aga ya kasheta, mummy ce takira nabeela
Da takarda ta biro tasauko kasa, daddy ne yace nabeela kin amince zaki kuma gidanshi
Gurin shehu tanufa hade da migashi takarda da biro tana fadin maza ka rubutamin saki anan nida kai har abada gaba daya zaman gidanka yafita raina nalura baka da imani tsaf zaka iya kasheni dan taka bukatar.
Wani gume yaji yana karyu mishi dukda sanyin AC tabbas yana son nabeela bazai iya rabuwa daita ba
Kasa yai da murya yana fadin dan'Allah kiye hakuri wallahi nagane kuskure na Allah inason matata bazan iya sakin taba.
Magiya yashiga musu yana bada hakuri duk yanda sukai dashi akan yabata takardanta amma haka ya gagara.
Ita kowa nabeela har zuciyarta zaman gidanshi yafita ranta gwara ta nime saki kafin ya kasheta ta hakura da auren, tonda yakuma gida yakasa samun sukuni sai text yake mata naban hakuri akan bazai sake daukan taba ko zaginta yadaina sanan ya amince ta haihu zai bata kulawan daya dace
Gani da yayi bata mishi reply hakan yasa ya dafe kanshi yana fadin aina shiga uku idan nabeela ta kufcemin yarinya mai dadi cakwai cakwai tamkar zuma.
Nabeela na kwance wayarta ta shiga ringing salma ce ke kiranta
Hello salma
Naam mara mutunci kwana biyu shiru kinyi likimo
Hmm kedai bari kawai matsala ce ta kunnomin kai bani da kwanciyar hankali amma yanzu Alhamdulillah
Hmm Kawata nima shawara nazu nima wajanki aure mijina zaikara a flat dina matar zata zauna gadona dake dakinshi za'a fitar asa nata kiji wata magana tare zamu dinga sharing kitchen da parlor kuma duk kaya'nane a ciki babu tsinke nata.
Ashar nabeela tasaki tare da fadin lallai kekuma kika yarda?
Lallai ai wallahi karki yarda ki tada masifa kice ya dakata da auren harsai yagama gyaran inda zata zauna, ne abun mamaki yake bani ko shekara biyu bakiyi ba amma zai miki kishiya anya kowa kina kula da kanki salma?
Yar dariya mai sauti salma tayi kana tace nabeela kenan ai matsalan ba dakanan take ba, kinsan kowa likita yace da wuya mahaifata ta dauki ciki sakamakon magungunan hana daukan ciki danai amfani dasu a baya... Nan salma tashiga bama nabeela labarin duk abinda yafaru
Ai wata nutsuwa ce tasaukan wa nabeela kasa furta komai tayi harsai da salma tace kinajina kowa
Hmmm salma ina jinki wato farouk ya rasu lallai duniya ba matabata bace ummusalma kinga yanda rayuwa ta juya mana baya kor?
Kinga masifan da muke fuskanta kor?
Babu abinda muka nima muka rasa daka gurin iyayan'mu amma hangen nisa da rashin godiyan Allah yasa muka bata rayuwarmu, muka dauki duniya da fadi sai yanzu nayarda da akeciwa duniya makaranta ce salma wallahi na tausaya miki kuma na tausaya ma kaina tsakanin nida ke bansan wanda yafi ganin masifa ba
Amma Alhamdulillah mugode ma Allah dan namu yazu da sauki room mate dinmu kareema Hiv ne daita ta kwanta asibiti Hafsa ce ke zaune daita na shiga bayi dauro alwala saboda naga la'asar tayi sai Hafsa ta shigo batasan ina bayi ba naji tana ciwa ki kwantar da hankalinki kareema ba a kanki aka fara cutar Hiv ba, yanzu HIV bawata ciwu bane wanda zaki daga hankali ga cututtuka nan masu saurin kashe mutum lokaci daya har idan kinsan yanda zaki kula da kanki ba wanda zaice kina da cutar karda ki manta nina ina dashi fa
Sallati salma tasa tana fadin HIV tafdi jam ita kowa kareema rayuwarta