Showing 24001 words to 27000 words out of 68402 words

Chapter 9 - ZAMAN HOSTEL COMPLETE BY RAHEEMA.txt

RAHEEMA   

20 Jul 2024

21361

dakatamin wane irin rainin hankali kikazumin dashi kina nufi da aljanu nayi chart day before yesterday?
Chart kuma?
Aiton ranan da kika turomin picz din nabeela bamu sake chart ba bari kiga hannu tasa cikin jaka tafito da wayarta, shiga chart din tayi sanan tabawa maimuna wayar.




Amsar wayar maimuna tai murmushi tai hade daciwa a iya zamana dake husna nidai nasan baki da aljanu balle nace dasu nai chart duk yanda akai akwai wane boyayyan al'amari dauko wayarta tayi game da shiga chart dinso hannu husna tasa ta karba wayar.




Tana gama karanta chart din a fili tafurta during uwarcan aiko zamu kwashe tashin hankali nida Muneera, kallonta maimuna take cikin rashin fahimta tace wacece kuma Muneera meyafaru?
Aunty Muneera friend din nabeela ce su ukune a group dinso nanta kwashe komai tasanar wa maimuna, tonda na amso wayata a hannunta naga duk an budemin chart amma ban kawu komai a raiba.




Hmm lallai kam ikon Allah wasu hawayene suka gangaro a idon maimuna sanan tace kinga sunyi hakane danso gasgata maganar dana fada wa nabeela ko ya akai sukasan ke sister nace ohuuuu.




Aunty kiye hakuri ai wallahi bansan nabeela itace kishiyar kiba, wallahi saidai idan yanzu nabeela ta lalace ada ba haka take ba, suna zaune Alhaji shehu yashigo gaisheshi husna tai amma ko kallonta beyeba, mari ya zabga wa maimuna zaro ido waje husna tayi game da bude baki




Nuna ta yai da yatsa yana ciwa meya kaiki yimin bincike a waya?
Wato Danna baki babban waya shiyasa har kike kokarin hana auren dazan kara to wallahi baki isaba hannu yasa yadauki wayarta dake gefenshi simcard dinta yacire sanan yatafi da wayar yana ciwa anjima mai gadi zai kawu miki karamar wayar yana karasa maganan yafita.




Zama tai a kasa ta fashe da kuka, itama husna kukan takeyi amma kokari tai ta boye nata tashiga lalashinta, jakarta husna ta dauka tana fadin aunty nizan tafi na rantse Allah kadai zai rabani da Muneera yau dinan domin itace silan wanan matsalar tayi chart dake a matsayin nice, ta turawa mijinki duba halin data jefaki a ciki. A sanin danaiwa mijinki mutum ne mai hakuri Sam bayason bacin ranki amma lokaci daya nabeela ta juya mishi kwakwalwa tana karasa maganan tafita.




Jeans trouser ne a cikin Muneera sai white vest zaune suke a gossip center salma na koya musu calculation din statistic shi suke dashi gobe, salma ce zaune a tsakiya husna ce tayo gurinso itama ta canza kaya Riga da wando ne a jikinta, fuskanta ba annuri, a gabanso ta tsaya hade da ciwa Muneera dago fuska da Muneera zatayi yatsun husna ne kwance a fuskarta tana sauke hannu itama ta watsa mata hudu lafiyayu tas tas tas tas tas kawai akeji kamar kiftawan ido, kallon juna salma da nabeela sukai hafsa kawar kareema na zaune daka nisa dasu a fili tafurta ita kowa wanan meya kaita maren Muneera, yarinyan dako kallon banza kaimata bata bari inaga kakai hannu jikinta.




Hannu Muneera tasa tacire belt din dake jikinta tana fadin ke kina zaton har kinyi girman dazakisa hannun ki marene wato kin girma kor, wallahi kinyimun kadan na hada gashi dake zaneki zanyi,tsoro ne yacika zuciyarka husna tabbas maren da Muneera taimata ya shigeta.




Lallai yarinya ta girma to bari kiji ko yaryarki maimuna ta mana kadan balle ke, salma ce tace wato tazu daukan matakine to kinyi kadan kizu da sauran kawayenki, juyawa tai zata wuce hannu nabeela tasa ta fusgota hade da watsa mata mari itama salma Marin ta watsa mata sanan ta rigeta, zabga mata belt Muneera tafara kota Ina kokarin kwace kanta take amma ina mugun rigo sukai mata, kafin wane lokaci mutane sun taru a gurin, amma babu wand yace wane abu sai kallo kawai, security ne suka shigo da alama labarin fadan yakai musu fada ganin haka yasa Muneera ta rabu daita salma da nabeela suka saketa, hawayene kezuba a idon husna batare da tayi kuka mai karfiba danko tana da dauriyya, tine jikinta duk yayi shaidan bulala abinki da farar mace ga yatsun Muneera kwance a fuskarta, security ne suka sasu a gaba zasu tafi Deen office, nabeela ce takuma room dinso danta dauko musu hijab itama husna friend dinta ce takawu mata hijab




Koda sukaje security office bawane mataki aka dauka ba saboda shugaban security saurayin nabeela ne amma yaja musu kunne sossai yai musu fada haka husna tadawu hostel zuciyarta cike da danasani dama bata tunkari Muneera ba gashi tabar mata abun kunya.




Zaune suke a daki sai hiran dukan da Muneera taima husna suke, kareema ce tashigo
Yan mata sannun'ku ashe abinda kenan yafaru Ina shigowa aka shafamin labari dariya salma tai hade da daga kwalban coke sha tayi sanan ta migawa kareema tana fadin yan'mata sha coke mai sanyi ko zuciyarki zatai sanyi, Dan naga kin matso dajin labari




Karba kareema tayi bayan ta sha ta maida kallonta gurin Muneera wace take danna waya da alama chat take, fusge wayar tayi hade daciwa wanan yarinyar maiyar chatting ce. Murmushi Muneera tai, hhhhhhhhhhhhh kareema duniyar Allah kinji yanda mukai da kawarki husna kor, zaneta nayi ita karaman mara kunya ce?




A'a, A'a niba Kawata bace tintine nai disowning dinta kinsan yanayin life Dina ita kuma uztaziyya ce dan akwai wa'azi.




A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah su nabeela sungama exam gashi aurenta saura 5weeks




Kwanan salma da Muneera biyu a gidanso nabeela, yauta kasance zata kuma kaduna mummy ce ta rakaso har gate gani datai driver na gogarin fita da mota yasa ta daga muso hannu hade daciwa salma mungode Allah yashi albarka kigaida umman ki, Muneera aike muna tare tonda a bauchi kike gari daya muke.




Har pack suka raka salma kallon salma Muneera tayi kana tace kinsan idan bamu samu YANKARI ba bazaki shiga wata mota ba saidai kibari gobe kya tafi, murmushi salma tai hade daciwa zamu sameta aiyanzu suna bata lokaci kafin motar ta tashi da idan bakizu da sasafe ba saidai kizu kiga ba babu.
Aiko motar takusan cika hunging din nabeela salma tai hade da bata peck cheek, haka taima Muneera itama, hannu ta daga musu kana tace amarya ainan da three weeks zan dawu bikin yarage two weeks zanzo
Byee luv u
Murmushi Muneera tayi sanan tace luv u more, nabeela ce tace muaaaaaaah๐Ÿ’‹
Be safe
Nan suka wuce a gidan baba Bello driver ya aje Muneera idan baku mantaba gidan da ake rigeta kenan, hunging nabeela Muneera tayi hade daciwa kawata i will miss you
Wallahi nima haka Muneera, hannun nabeela ta rige hade daciwa Dan girman Allah kikama kanki karda kisake budewa namiji kafa, yanzu gyara yakamata kiye duk dadai Alhaji shehu yasan komai but yakamata yajiki kamar wace bata taba aikata komai ba.




Murmushi nabeela tai hade dasake hunging din Muneera kana tace insha'Allah kawata zan dauki shawararki akoda yaushe Ina godema Allah daya bane kawaye masu sona nagode Allah yabarmu tare.








Keep following me i need more and more comments read and share๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–




*ZAMAN HOSTEL๐Ÿ’ž*




๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–




STORY
AND
WRITTEN BY


RAHEEMA๐Ÿ”ฅ


DEVOTED TO๐Ÿ‘‡๐Ÿป
(YUSUF)๐Ÿ’‹




```Dedicated to zulaihat, my heart in human form much luv to u```






๐Ÿ…ฟ39-40






Mota yasata sanan yaja motar. zuciyar farouk a bace ya
Kwashe gyalenta da dankwalinta hade daciwa bulshit.




Horn yaya sa'ad yakeyi da karfi hannu salma tasa zata fita a motar tsawar daya daka mata ya dakatar daita, gidan uba waye zakije?
Muryarta na rawa saboda tsoran daya kamata tafurta zan bude gate ne na aike ki? kaga shegiya mara mutunci naga kinfita, fitowa yai ya bude gate bayan yashiga da motar yafita ya rufe, tabbas gidanso salma babban gidane dan flat din dake gidan yafi hudu ga flowers da aka shuka wanda yasake fito da kyan gidan, waya taji yaya sa'ad na amsawa
Eh muhadu a babban parlor, tine taji cikinta na juyawa dan basai an fada mata ba tabbas da sauran yayanta maza yake waya, sunkuyar da kanta kasa tai hade da dafeshi da hannunta tana fadin waiyo ne ummusalma tawa tazu karshe bude kofar motan da yaya sa'ad yai yasa tai saurin dago kanta ta dubeshi




Hannu yasa ya finciko gashin kanta wanda kitson attachment ne na Ghana weaving yasauka har duwawu gashi blue nd black ne, ba shiri tafito a motar tana fadin yaya dan'Allah kayi hakuri Jan gashin kanta yake yana tafiya kamar yanda akejan akuya idan an daureta a haka suka karasa babban parlor hankadata ciki yai a tsakiyar parlor ta tomu ta fadi sunkuyar da kanta kasa tai domin parlor a cike yake da brothers dinta ga mama da baba a gefe(mai karatu karku manta salma itace auta a gidanso kuma ita kadaice ya mace)




Yaya zakari ne yatashi game dasa kafa ya tokareta yana ciwa baqar munafuka dagu da kanki wato iskanci kika zaba kor? sauran yan'uwanshi ne suma suka fara zaginta, yaya sa'ad ne yace tashi tsaye kowa yaganki kuka take sossai game da migewa tsaye, nunata yaya sa'ad yake yana ciwa baba kadube salma kamar bayar musulma ba duba kayan da tasa ya matseta tsam kamar zai yaqe ga dinki na yan'iska ga kitson attachments mai colour, yaya zakari ne yace wallahi ko karuwai dasuke tsayawa a bakin titi suna suturta jikinso. mama ce ta fashe da kuka hade da migewa tsaye tana fadin wallahi salma har idan kikasa duniya ta zagemu taga kamar bamu tarbiyantar dakeba Allah ya..... Baba ne yace A'a Binta karkiye mata baki aisai lalaciwarta tafi haka.




Hannun mama ya rige hade daciwa zumu fita mubaso guri kallon yaya sa'ad yai hade daciwa sa'ad kayi duk abinda yadace ka tabbata tayi ladama abinda ta aikata kafin gobe na yake hukunci akanta
Tohm baba
Hawaye nazuba a idon mama tafurta ka tabbatar ka karyata idan yaso saimu kaita a dorata daka baya.




Ihuuuuu salma tasa tana fadin mama Dan girman Allah karki barne dasu kitaimakamin wallahi kashe ne zasuyi, a fusace yaya zakari yafita waje sai gashi yadawu da ITACE dukanta yafarayi kota ina ihuuu takeyi sossai tana kuka hade da bashi hakuri kafa yaya sa'ad yasa ya tokareta, goshin tane ya bogu ta kujera aiko sai jine yafara fita, sauran brothers dinta tine suka fita a parlor




Hannu tasa ta taba goshinta gani datai jini nafita ba karamin sake tada mata hankali yaiba
Waiyo Allah na yaya sa'ad zaku kashe ne Dan girman Allah kuye hakuri wallahi natuba




Yaya zakari ne ya daga icen hannunshi yana ciwa wayanan sune kafafuwan da suke zuwa hotel kor tozan karairaya'so buga mata yai a kafa, wane irin razananin ihuuuu tayi saboda azaban zafin da taji ya ratsata har cikin brain dinta




Muryarta a shaqe domin yadaina fita da karfi tafurta kuye hakuri wallahi zan mutu, yaya sa'ad ne yace ai kasheki zamuyi gwara mu kasheki gobe da asuba mu sanar a masallaci kinyi accident Allah yadauki rayuwarki




Shaqe wuyanta yaya zakari yai yana fadin gwara ki mutu akan kidauko mana abun kunya kuka take amma baya fita saboda tsananin azaban da take ciki a zuciyarta ta furta dan'Allah karku kasheni kubarne natuba ga Allah, tokarinta a kirji yaya sa'ad yai wane irin dogon ajiyar zuciya tayi tadaina motsi




Yaya zakari ne yace karde ace ta mutu rai a bace yaya sa'ad yace aigwara ta mutu dauketa ka ajeta a dakinta idan ka ajeta ka kulleta ta baya yanda ba wanda zai yayafa mata ruwa idanma suma tai, idanko mutuwa tayi Allah yajiqanta.




Kamar yanda ya sa'ad yafada mishi hka yayi bayan ya direta a gado amma saiya kasa tafiya yabarta batare daya yayafa mata ruwaba nikam Raheema nace Allah sarki tsakanin dan'uwa da dan'uwa sai Allah, toilet din dake dakinta yashiga ruwa ya debo a cup yayafa mata saida yaga ta bude ido sanan yatashi yafita




Bude ido tayi tana kallon sama batare data motsa jikinta ba domin koina a jikinta radadi yake mata kuka ta farayi wanda muryar baya fita tashi tai tazauna kafarta da hannunta taji suna wane irin radadi kamar ta karye haka dai tana kuka tasamu tacire kayan jikinta, short gown dinta dake gefen pillow tadauka tasa, dafe kirjinta tayi saboda wane irin azababen zafin da yake mata.




Koda farouk yakuma daki kwanciya yai hade da lumshe ido a fili yafurta yau Allah ne kadai zai kwace salma a hannun azzalumin yayanta ton a titi yafara dukanta inaga sunce gida, phone dinta dake jaka yake ringing
Gosh bag dinta da phone dinta duk anan tabarshi, daukar wayar yayi Muneera yaga anrubuta to yasan yanda take da Muneera dan tana bashi labarinta picking call din yayi




Hello
Shiru Muneera tayi saboda muryan namiji taji
Muneera ya kikai shiru?
Farouk ne
Gyaran murya tayi sanan tace kuna tare kenan?
Da'Allah salma nake nima




Bayanin duk abinda yafaru farouk yai mata saboda salma tasanar dashi tsakaninta da Muneera da nabeela basa boyewa junanso komai






Tonda farouk yafara magana innalillahi wa'ina ilaihi raji'un Muneera ke furtawa murya a sanyaye tace farouk kajanyo wa salma masifa Allah kadai yasan halin da take ciki yanzu domin family dinso babban gidane, gashi ita kadaice mace kuma auta, numfashi farouk ya sauke tausayin salma cike fal a zauciyarshi.




Dan girman Allah farouk na ruqeka karabu da salma da girman Allah tonda ita batajin magana sau nawa na shawarceta akan ta rabu dakai amma taqi aigashi asirinta ya tono na tabbatar tana cikin masifa yanzu, bata tsaya jin abinda zaice ba ta kashe wayar.




Aje wayarta tai a gefe tana ciwa Allah sarki salma barin kira nabeela nasanar daita
Hello nabeela!!!
Kawata ya kike ya gajiyan jiya?
Lafiya lau keee ba lafiya bafa kinji kinji abinda yafaru da salma..... Nan Muneera taimata bayanin komai
Hmmm Allah ya kyauta itama salma bataji, gaba daya bata daukar wa'azi da shawara a rayuwarta idan kikai mata wa'azi bazata dauka ba saidai taji tabarshi a gurin, gaskiya banji dadin hakaba amma watakila hakan shine hanyar shiryuwanta kowane shiriya yana tare da sila kamar yanda kowane shaidanci yana tare da sila, Allah yasa haka shine alkhairi a gareta.




Ameen nabeela
Turomin number mama tanan zamu iya kiranta tonda kince wayarta na hannun farouk din, tohm shikenan nabeela.




Yanda salma taga rana haka taga dare jikinta duk yayi tsami dankwalinta ta dauri goshinta dashi wanda kezubar da jini, tonda ta kwanta a bed ko motsawa bataiba domin idan zata motsa jitake kamar ana yankan naman jikinta hawayene kawai kefita a idonta
Koda asuba tayi tanajin kiran salla amma ta gagara tashi domin dakyar ta tashi ta zauna




Da misalin karfe shida na safe taji anbude ta ta baya, tsoro ne yasake cika zuciyarta dan ta zata yaya zakari ne, dasauri anty saudat ta karaso gurin salma tana fadin auta(matar yaya zakari kenan) a gidan take da zama, rungume salma tai a jikinta tana ciwa auta kiye hakuri inajin ihuuuu ki jiya. amma bana da hurimin zuwa na amsheki ko yanzu a sace na dauko key din danna bude ki




Kallon salma take
Tausayi tabata a fili tafurta yau ummusalma kece a cikin wanan halin salma yar gata diya mace tilo daya a gidanso, wacce kowa ke tarairaya bayason bacin ranta, meyasa kikabi namiji hotel?
Haba salma meyasa kikeson dauko abun kunya.




Kuka salma tasa mai karfi tana ciwa Anty saudat kiyarda dane ba halaiyata bane, dan an ganmu a hotel hakan bayana nufin munyi lalata ba, Barbiecue mukaje anty.




Shiru saudat tayi nawane lokaci sanan tace kema kinsan ko tsayuwa da namiji ba'a barinki saikin kai 300level zaki fara tsayawa da namiji nidai tashi muje na taimaka miki ki gyara jikinki.




Tanasa kafarta a kasa tafara kuka wai bazata iya takawa ba zafi yake mata, haka dai anty saudat ta taimaka mata tai wanka first aid box tadauko taimata dressing goshinta daya fashe fuskarta ya kunbura kamar wace tai accident




Ba laifi ta danji dadin jikinta, hawaye nazuba a idonta tace anty saudat nagode. Salma ki godema Allah kuma kicanza hali zoki zauna na kwance miki kai saboda naji yayanki yace aski zai miki da kitson a kanki zai aske.




Saida tagama kwance ma salma kai sanan ta kwashe attachment din a leda hanya kofa tanufa hade daciwa nizan tafi Dan naga karfe tara karsuzu su dameni anan.




Daga mata kai kawai salma tai tana fita ta kulleta ta baya..... Kuka takeyi sossai zuciyarta cike da danasani gashi batasan wane irin mataki za'a dauka a kanta ba.




Muneera ce takira mama a waya
Sallamu alaikum
Bayan mama ta amsa sallaman sai Muneera ta sanar daita kowacece sanan kuma salma take nima, cikin fara'a mama suka gaisa da Muneera saboda bayau suka fara wayaba
Salma batanan abinda kenan mama tace mata.




Da misalin karfe goma yaya zakari ya bude salma a daki beye mamakin ganinta haka ba dan bayan komawan saudat yakamata zata aje key nanta sanar dashi gurin salma taje yai mata fada sossai




Harara ya watsa mata hade daciwa maza kifito yanzu inason ganinki a babban parlor, cikin karfin hali tasanya kafarta a kasa zata mige tsaye ihuuu tasake hade da zama tana fadin yaya zakari wallahi bazan iya taka kafata ba, Anty saudat dake bakin kofa tace duk yanda akai kunyi mata targade, barin fito daita fita yai daka dakin yanaciwa kidaura mata alwala idan kuntashi fitowa




Yau farouk zaikuma bauchi haka yasa yadauki jakar salma da veil da dankwalinta dan yakai gidanso, wane yaro yagani yafito daka cikin gidan, kiran yaron yayi
Dan samari ya sunanka
Abulkhairi
Salma nanan?
Eh tana nan
To gashi ka ajemata wanan a dakinta karka bama kowa kaji, dubu daya yabama yaron kyauta Abulkhairi bazai wuce 11years ba




Koda yaje daki bega salma ba dakin mama yaje begantaba haka yasa yatafi babban parlor salma na zaune kanta sunkuye a kasa Abulkhairi yashigo hannunshi rige da jakarta sai wata farar leda wanda veil da dankwalinta ne a ciki
A gabanta ya aje yanaciwa Anty salma gashi wane a waje yace nabaki, one thousand din dake hannunshi yadaga yanaciwa yabani kudi yace nasiya aeroplane




Baba ne yaima yaron tsawa a guje yafita daka parlor, ita kowa salma kasa dago kanta tayi, yaya sa'ad ne yadauka jakar hade da budewa yanaciwa kunga yakawu mata jakarta. iPhone'x max din salma yafito dashi yana ciwa.




Salma waya siyan miki wayar nan? ninasan wayar da kike riqewa domin da hannuna nasiyan miki iphone 7+
Yaya zakari ne yace kwanakin baya da suka wuce tamin magana akan nacanza mata waya zuwa iphone x nace tabari ending of this year wato shine bazata iya jiraba




Mama ce tace ya subhanallahi salma me kika nima kika rasa?
Menine ba'a miki?
Duk abinda kikace kinaso har idan befi karfinmu ba zamuyi miki abinda kenan zaki saka mana dashi salma?
Wane irin gatane ba'a nuna miki ba?




Hawayene kezuba a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login