Showing 63001 words to 66000 words out of 68402 words

Chapter 22 - ZAMAN HOSTEL COMPLETE BY RAHEEMA.txt

RAHEEMA   

20 Jul 2024

21360

yatafi masallaci dan bayason yayi nisa da Muneera tausayi take bashi sai kuka takeyi tana surutai




Addu'a yai mata sossai akan Allah ya sauketa lafiya sanan yakuma gurinta.




A yanzu karfe takwas ne na safe ton Muneera na kururowa tana ihuu yanzu bakinta yafara mutuwa haihuwan tazu gadan gadan hannunta na jikin na mansur ta rige gam taqi barinshi yafita yayinda take kuka shima kukan yakeyi




Duk yanda nurses din sukai dashi yafita waje amma yaqi fita a idonshi kan jariri yafara fitowa inda ake fama da Muneera tayi nishi kuka mansur yake wiwi kamar shine mai haihuwan saboda tausaya mata da yakeyi




Allah ya sauketa lafiya inda ta haifu yarta mace cikin jini ya amsa yarinyan ya rungume a kirjinshi ko cibi ba'a yanke mata ba. Nurse ce ta amsa yar a hannunshi tana fadin bari a gyarata




Bayan angama gyara mai jego da yarta sai mansur yakai dubanshi ga Muneera wace akema dinki sai kuka take nurse din naciwa kiye hakuri bayan kingama mai wahalan haihuwa fa kikayi ai dinki karamin abune.




Tausayi yaji tabashi wai allura akesawa a private part dinta gaskiya mata na kokari. Suna wahala a zuciyarshi yashiga shimata albarka kaunanta da soyayya ta na sake ratsa zuciyarshi




Saida komai ya kammala sanan mansur yakira gida yasanar dasu Muneera tasauka lafiya nan yashiga kiran yan'uwa yana sanar dasu




Komawa yai yazauna kusa daita kana ya daura babyn a kafarta hannu tasa ta rige yarinyan zuciyarta cike da kaunan jaririyan, a daidai saitin kunnenta mansur yafurta qalbe nagode sossai tabbas kin bani farin ciki kin gamamin komai tonda kika haifi mai kama dani kin wahala kafin ki haihu bani da abinda zan biyaki dashi bayan addu'a nagode sossai qalbe




Murmushi Muneera tayi kana tace herty kamarku ya baci da babyn nan kamar kayi kaki, rungume yarinyan yai a kirjinshi yana fadin nima naga haka qalbe.




Washe garin ranan da Muneera ta haihu ta kasance Tuesday kuma wanan ranan itace ranan SIGN OUT dinso a school.




Black jeans with white t-shirt tasa inda tasa takalminta mai kyau light makeup tayi, after dressing ta dauko ta daura akai sanan ta yafa white veil juyawa tai ta kalle mansur wanda ke zaune a gefen gado hannunshi rige da baby zama tayi a kusa dashi tana murmushi kana tace herty nayi kyau kowa?




Qalbe kinyi kyau sossai har inajin kishi a zuciyata be kamata kifita haka ba. Dan shagwa6e fuska tayi sanan tace eyya herty nafa rufe jikina
Nasan kin rufe jikin ki amma karki manta duk wanda zai miki sign out saikin sauke after dressing dinan k'asa qalbe mezai hana kisa farin hijab?
Sai ai miki signing din a jikin hijab din kawai




Kicin kicin tai da fuska sanan tace shikenan idan har haka kakeso zansa amma kafinan, ga wanan inaso kazama mutum nafarko dazai faramin signing.




Mansur bayason bacin ran Muneera yalura bataji dadin abinda ya fadaba dukda yana matukar kishinta haka zai hakura yabarta tafita a haka kawai.




Kallon permanent marker dake rige a hannunta yake red colour ya dauka sanan ya daura maker daidai saitin zuciyarta yai signing




Karanta abinda ya rubuta take


_Qalbe, I didnโ€™t know what love felt like until the day I met you. I love you with all my heart and I always will, I wish you the best of luck in your life... I love you_




Hunging dinshi tayi tare da hada bakinta da nashi tashiga kissing dinshi, dan matsawa gefe yai kana yace kiye a hankali ga Noor nan karki danneta
Murmushi Muneera tayi danta manta da jaririyan ma migewa tsaye tai sanan tace herty nagode I luv you more




Farin hijab ta dauko a wardrobe dinta sanan tacire gyalan data yafa akai tasa hijab din jaka ta dauka tana fadin herty tashi mutafi bakwai da rabi yawuce takwas zamu shiga exam nasan kafin naje an manna venue




Hijabin yai mata kyau amma mansur gani yake kamar ya matsa mata.. nan yace mata tacire hijab din ta maida gyale.. Ita kuma tace bazata cire ba ai yafiso tasa hijab




Da taga ya dage akan ta maida gyalanta saita maida gyalan sanan suka tafi




Zarah mai aiki suka bari a gida Noor na rungume a jikin mansur saida zasu shiga mota ya migama Muneera




Koda suka karasa school an riga da an manna venue inda zasuyi exam din, mansur ne yafito a mota Noor na rungume a kirjinshi yana biye da Muneera a baya harsuka gano inda zatai exam din. Saida mansur yaga Muneera tashiga sanan yajuya yakuma mota




Bayan sunfito exam mutane sai murna suke mata inda suke tayata murnan haihuwan da tayi.




Nabeela ce tanufu gurin Muneera tana fadin, Kawata kin sauka lafiya Allah ya raya me aka samu




Kamar Muneera bazata amsa ba saikuma ta amsa da Amin
Mace ce
Nabeela ce tasake ciwa jiya kika haihu kenan
Eh jiya na haihu
To masha'Allah ina yarinyan take
Fuska a daure Muneera take amsa nabeela tana mota gurin babanta.




Hafsa kawar kareema ce ta karaso gurin Muneera tana fadin Muneera ashe kin sauka lafiya Allah ya raya, barin miki signing




Daman tasauke after dressing din kasa nanta juya mata dan tayi mata singing, idon nabeela ne yasaukan akan signing din dake gaban rigan Muneera, batasan sanda tai murmushi ba sanan tafurta nikam ina nasamu irin wanan.




Bayan Hafsa tagama ma Muneera signing ne tanufi gurin nabeela tana fadin a katon cikin nan zanyi miki signing kema kin kusa haihuwa fa




Kamar yanda Muneera tayi dressing haka nabeela tayi amma saidai ita baqin gyale ta yafa akai.




Kusa da Muneera nabeela ta matsa tana fadin idan ke bazakimun signing ba ne bari nai miki bata tsayajin abinda zatace ba ta daura maker a kafadarta kana ta rubuta
_She easily get angry but she's a kind hearted person please forgive me Muneera. I will miss you frm nabeela_




Koda Muneera ta karanta abinda ta rubuta murmushi tai sanan tace Allah ya yafe mana gaba daya nagode itama daura maker dinta tayi a faran rigan nabeela kana ta rubuta
_Gonna miss you my disowned friend yours Muneera_




Sallama tayi da mutanan gurin sanan tawuce dan mansur nata kiranta a waya




Har Muneera tawuce nabeela na sake maimaita signing din datai mata, wato tayi disowning dinta hmmm




Anyi taron suna na gani na fada inda yan'uwa da abokan arziki sukazu nakusa dana nisa harta yan Muneera novel group ba'a barsu a baya ba sunzu taron suna. yarinya taci sunan mahaifiyan Muneera ana kiranta da Noor, harta nabeela saida tazu taron sunan kokari take taga ta daidaita tsakaninso




Muneera bata yarda takuma gida wankan jego ba, cikin yan'uwa aka samu dattijowa wace zata zauna daita harsai tayi arba'in.




Hankalin Muneera ya kwanta bata dawata matsala yanzu danko ta kammala karatunta taci sa'a kuma tayi nasaran fita da grade mai kyau




Duk yanda Muneera tasu ta guji amince da nabeela haka ya gagara dan har gidanta nabeela tazu ta bata hakuri haka dai suka satsanta kanso harta salma sun shirya da Muneera saidai kuma bata saki jiki dasu kamar a baya ba.




_Bayan shekara daya da rabi_




Nabeela ta haihu lafiya inda ta haifi diya mace a yanzu yarinya hartayi wayau zumunci sukeyi sossai da Muneera.




Salma kowa tasamu admission harta fara zuwa makaranta karatun baya mata wahala saboda duk wani abu da ake musu tariga data wuce gurin kuma ta iya dan masscom tasake applying a wanan karon ma.




Yaya sa'ad na matukar tausaya wa salma hakan yasa yake mata duk wani hidima daya dace kuma yake mata alheri.. Har mota yasiya mata yace tadinga zuwa school dashi sanan yabata million daya yace taja jari danta dogara da kanta basai abinda miji yabata ba




Tana karatunta tana business dinta, bata saka damuwan kiyayyan da dangin mijinta suke mata a zuciya ba hakama bata saka damuwan najib a zuciyarta ba saidai tai kuka ta share hawayanta ta fadama Allah, a yanzu ko ba'a fada mata ba tasan yafison khadija akanta kawai dai yana zaune daita ne dan ya rufa mata asiri.




Khadija kishiyan salma ta haifa yarda mace mai suna asma'u wani cikin ne daita yanzu




Izuwa wanan lokacin salma tacire rai da haihuwa tabar komai a hannun Allah inda ta dauki son duniya ta daurama yar mijinta wato Asma'u har zuciyarta tana kaunan yarinyan kuma tanajin yarinyan kamar ita ta haifeta dukda talura khadija bason bata yar take ba amma haka take kai zuciyarta nisa take zuwa ta amso yarinyan.




Ko fita salma tayi da taga yar riga mai kyau ko kayan wasa ko takalmi saita tsaya tasiyan wa Asma'u




Itama yarinyan ta saba da salma... najib yalura salma nason yarshi hakan yai mishi dadi kuma hakan nakara bata matsayi na musamman a zuciyar najib




Salma ce sanye cikin riga da zani na atamfa wanda ya karba jikinta dan takara kiba wacce tai mata kyau.




Key din mota ta dauka sanan tanufi part din khadija taci sa'a kofar parlor a bude yake nanta shiga knocking kofar dakin khadija




Koda khadija tabude kofar a wulakance ta kalla salma sanan tace ashe kece da sasafe haka?




Salma ce tace hala bacci kikeyi kiye hakuri na tashe ki, dama Yata naxu dauka zamuje birthday party yaron brother dinane yake birthday




Ta6e baki khadija tai sanan tace bata tashi bacci ba birthday dinne za'a tafi ton yanzu?




Eh yanzu yakamata natafi akwai aikin daza muyi bata karasa magana ba saiga Asma'u tafito daka cikin daki a guje ta rungume salma tana fadin mama oyoyoyo.




Daukarta salma tai kana tace yauwa yar albarka gwara da kika tashi




Khadija ce tace yoai ba haka zaku tafi ba sai an mata wanka kuma taci abinci tukunna, daukar Asma'u tayi a jikinta sanan ta kalle khadija tace wanan ba damuwa bane zanje daita part dina nai shiryata nariga dana siya kayan dazansa mata karasa maganan tai dayin gaba tana fadin saimun dawu.




Tsaki khadija taja wanda saida salma taji sanan ta shige daki ita kowa salma ko a jikinta a fili tafurta yanda kike tagama ke kika haifeta haka nima nake tagama daciwa yar miji nane.




Najib na kwance yanajin duk yanda salma sukai da khadija, tashi yai yazauna kana yace khadija meyasa kikeso kidinga hana salma daukan Asma'u?




Kidaina haka Sam hakan ba dadi kamata yai kiji dadi kiduba kiga yanda takeson yarinyan, wasu fa idan basa sonki tohar abinda kika haifa zasu tsana




Hanyar bathroom tanufa tana fadin kishiya ba abun yarda bace banason tana daukarmun yata gudon karta cutar daita, wayasan zuciyarta watakila badan Allah take daukan yarinyar ba




Sai bayan sallan isha'i salma tadawu gida.




Sun riga da sunci abinci acan dan haka koda suka dawu wanka tayi sanan taima Asma'u, kayan bacci tasama yarinyan dan yanzu kayan yarinyan sunfara yawa a dakin salma ita take siyan mata kaya ta aje a dakinta.




Shimfide yarinya tayi suka kwanta sanan tai musu addu'a. Da yake najib ba dakinta yakeba




Cikin bacci taji ana dukan kofar parlor dinta a hanzarce tasauko daka gado sanan tanufi parlor tana fadin waye?




Ki budemin kofa kibani yata. Bude mata kofa salma tayi sanan ta kalla agogo karfe goma ne na dare.




Hannu biyu tasa a waist tana girgijje girgijje sanan ta kalla salma tace ina Asma'u jeki fitomin da yata ai wanan rainin hankali ne kifita daita ton safe sanan ki gagara kawumin ita ton dazu naji shigowarki inata zuba ido naga kin kawumin ita amma shiru




Maza jeki daukomin yata duk abinda kike shiryawa Allah yafiki




Tine salma taji ranta ya baci tasu ta rabu daita amma sai taga yakamata ta nuna mata itama ba ka'nwar lasa bace danma tayi sanyi yanzu.




Tsawa ta daka mata hade da daga hannu tana fadin kee malama da katamin kuma ki gagauta fita anan kona miki dukan tsiya idan kina tagama Asma'u yar kice to nima haka nake tagama daciwa yar miji nane kuma yar miji tamkar ya take a gurin mata ina fatan kin fahimta?




Hayaniyan da najib yafaraji hakan yasa yanufu gurinso




Tafdi jam wallahi karya kikeyi Asma'u ba yarki bace babu ta inda tazama yarki idan kinji haushi Kema kiye ciki ki haihuwa juya kawai wace bata haihuwa maza kifitomin da yata kuma daka yau kin'bar sake daukarta tonda bakisan kawai'ciba, duk abinda khadija take fada a kunnen najib hakan ba karamin zafi yai mishi a rai ba




Hawaye ne yafita a idon salma wanda itama batasan lokacin daya fito ba, cikin bacin rai ta daga hannu zata dauke khadija da mari saiji tayi an rige hannunta




Najib ne ya rige hannunta kana ya saukeshi kasa sanan ya dube khadija yace ashe baki da mutunci daman haka kike?
Kinyi kadan ki kawumin tashin hankali a cikin gidana dukjan kunnen danai miki akan karkizu saida kikazo kika sameta naji duk furucin da kike furtawa




Maida kallonshi yai gurin salma wace ta duka tagume tana daka tsaye sanan yace kiye hakuri salma kamar yanda kika fada Asma'u yar kice tonda yar mijin kice wanan haka yake kuma a yanzu basai anjima ba inaso kisani na baki kyautan Asma'u halak malak daka gobe komai nata zai dawu hannun'ki ta dawu wajanki da zama.




Kuka khadija tasa tana fadin wallahi bazan yarda ba ina dalili da raina ban mutu ba aimun kyauta da yarinya barinje nakira mama nasanar daita hakan bazai taba yuwuwa ba. Wata tara ai bawasa bane




Najib ne ga dakatar daita daciwa sanar da mama daza kiye daidai yake da mutuwan aurenki saiki zaba daya a ciki karasa maganan yai da fita daka parlor




Wani irin farin cikine ya lulube salma, kallon khadija tai hade da mata gwalo sanan ta shige daki




Tanaji khadija tafita tafito tasa key a kofarta sanan takuma dakinta. Farin ciki fal zuciyarta da zuciya daya take kaunan Asma'u tanaji kamar ita ta haifi yarinyar kodan yarinyan tayi kama da najib ne ohuuu






Keep following me i need more and more comments read and share๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–




*ZAMAN HOSTEL๐Ÿ’ž*




๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–




STORY
AND
WRITTEN BY


RAHEEMA๐Ÿ”ฅ




DEVOTED TO๐Ÿ‘‡๐Ÿป
(YUSUF)๐Ÿ’‹




_Wattpad๐Ÿ‘‰๐ŸปFatimamuneera001_




๐Ÿ…ฟ77-78






Duk yanda khadija tasu taga ta amsa Asma'u a hannun salma haka ya gagara ta bama najib hakuri ta lalashe shi amma ina aikin gama yagama danko magana daya yakeyi




Tafe suke su biyu Asma'u na dauke a hannunta. Salma kedai baki gajiya da daukan wanan katowan yarinyar




Murmushi salma tai sanan tace feena kenan ai banaso ta wahala ne naga hostel din naku da nisa




Feena ce tace karki damu aimun karaso, text book din entrepreneur zan baki ko?




Haka suka karasa hostel dinso feena suna hira




Koda suka shiga dakin mace daya suka tarar wace naji feena takirata da hassana




Zama salma tai a gadon feena sanan ta zaunar da Asma'u kana ta dauko cheese balls a jaka tabata




Feena ce ta dube hassana kana tace ina sakina?
Tabe baki hassana tayi sanan tace gantalaliya zakice dariya feena tai sanan tace watsa'tsiya dai ina tausaya mata wallahi bakiga tayi iPhone 11promax ba sai kadifiri takemana tana iyayi a zuciyata nace dadin abun saida aka budema yan iska kafa sanan akasamu




Hassana ce tace kema dai kya fada daukar kanta take tamkar yar wata shararan mai kudi a 9ja. Yar banza yar talakawa wace ko ruwa aka baki a gidanso bazai shawu ba amma tazu nan tana mana kadifiri




Tonda suka fara magana salma ta maida hankalinta kanso tana sauraran'so.




Wata budurwace baqa kyakyawa bata da jiki ta shigo dakin tana fadin munafukai Allah ya tona asirin ku daman baton yau ba nasan idan bana'nan kuna zama ku zageni to kanku kukai mawa.




Iskanci iyawa ne idan wani yayi yaci riba wani kowa faduwa zaiyi, ba tare muke yawu ba amma kun'min Qazafin zina na barku da Allah tsinanu kawai




Nan hassana da feena suka shiga zaginta cacan baki suka fara suna zagin junanso.




Ganin haka yasa salma tashi tafara basu hakuri, taci sa'a hassana da feena sunyi shiru amma sakina kowa taqi yarda tayi shiru sai zaginso takeyi




Hannunta salma ta rige kana tace sakina kike da suna ko? zumu karasa bakin gado muzauna nasanar dake wata magana kiye hakuri kidaina zaginso kinji




Akan gado suka zauna sanan salma ta dubi sakina tace tonda su feena suka fara maganarki hankalina ya karkata kanso domin naji sun tabo wani bangare daka cikin rayuwata.




Cikin rashin fahimta sakina take kallon salma sanan tace ban fahimce kiba




Gyara zamanta salma tayi sanan tace zan baki wani tarihi kadan daka cikin rayuwata ko Allah zaisa ki dawu hanya basai lokacin dazakiye ladama mara amfani ba... Ladama irin tawa wace bata da amfani mai cike da bakin ciki da zubda hawaye




Hawayeni yazuba a idon salma sanan tace a yanda naji su hassana na maganarki na fahimce rayuwa kikasa a gaba dakuma son rige duk wani abu mai tsada kamar waya kayan sawa jaka takalmi da sauranso.




Murmushi salma tayi kana tace sakina karda kiye ZAMAN HOSTEL irin tawa mai cike da ladama mara amfani. Kin ganni nan babu irin iskancin da banyiba lesbian ne kawai ban taba aikatawa ba kafin nazu school dinan nayi wata makaranta wato ATBU Bauchi a hostel nake zaune inda dakinmu ya kasance room of 4 mu uku department dinmu daya nida nabeela da Muneera kareema kuma ba department dinmu daya ba




Nida Muneera da nabeela munfi shiri tamkar yan'uwa muke tonda muka shiga muke tare bama boye wa junan'mu komai.....




Yanayin yanda kareema take tafiyan da rayuwarta shi yafara jan hankalinmu dukda ba abinda muka nima mukarasa daka gurin iyayan'mu mahaifin nabeela mai kudi ne sossai babu abinda tanima tarasa haka nima ba alfahari nake ba daka babban gida nafito inda na kasance yar gata daka gurin mahaifina dakuma manyan brothers dina maza.. sakamakon nice auta kuma nikadaice mace a cikin yara tara da mahaifiyata ta haifa.




Babu wayan da bamu rige ba duk wata waya mai tsada dazata fito to zaki ganta a hannu mu daka Samsung har iPhone. wanan iPhone din dake hannun'ki ce itace ban rige ba.




Karda ki manta ba talauci bane yasa muka fara bin maza ko muka canza hali a'a rashin godiyan Allah ne kawai danko har idan muka sanar a gida munason abu to za'a siya mana saidai kawai a dauki lokaci kafin a'siya to mukuma wanan daukan lokacin ne bamaso.




Hmmm ZAMAN HOSTEL shiya bude mana ido yasa muka farabin maza nida nabeela ba'a bin maza kadai muka tsaya ba harda zuwa club wani lokacin muna taba shaye'shaye idan an gayyace mu party.




Da mukaga Muneera na mana nasiha tana mana fada sai muka fara boye mata wasu abu. Abun takaici rayuwa kawai mukasa a gaba mudai musa gold mai tsada mu rige waya mai tsada keee harta jaka idan tafito a hannun mu za'a fara ganinta.




Tabbas munyi rayuwa munyi mu'amala da maza manya masu kudi ba kananan yara ba, mun rige kudi masu yawa




Amma yau ina suke?
Ina kareema yau?
Ina nabeela yau?
Ina ummusalma?




A cikin mu waye yaci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login