Showing 1 words to 3000 words out of 45361 words
Chapter 1 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: GIRMA YA FADI ! 3
Na zauna dum, naki ko motsi, har ya gama fiddo jakunkunan da yazo da su a but din motarsa, ya zagayo ya bude min kofa ya ce "you are welcome to gwauro's house…" na hadiyi miyau da kyar nace “zai fi kyautuw ka fara shiga, ka yiwa mutanen gidan bayani na, ba wai kawai su ganni a kansu ba, idan sun yarda da bakuntana falillahil hamdu, idan basu yarda bama babu damuwa, sai muje ka kama mun (Guest House) wannan ma ba karamin taimaka ne kayi mun ba and I really appreciate”. Ya sarke 'yan yatsun shi cikin na juna,yayi baya dasu suka bada kara, kas. Yana murmushi yace "you seem lacking confidence in everyone' kina da gaskiya, Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro ne. Allah ya kiyayeki da kwana a (Guest House), domin da jin muryarki an ji 'yar mutunci, wanda ta san ciwon kanta. Ki yarda da ni, bani da niyyar cutarki, hanyace ta hadamu kuma Allah ya kulla zumuncin mu.
Yadda kowanne dan uwa na jinni, ba zai ci amanar 'yar uwarsa da suka fito ciki daya ba, haka ba zanci amanar ki ba. Feel free with me, am not that type of person, don haka fito ki biyo ni, nayi miki alkawarin ba zaki yi nadamar bina ba”. Sai kawai nayi kundumbala na bude motar na fito, muka jera zuwa ciki, yayin da maigadi ya biyo mu da kayan sa.
Tun daga falo ya daga murya yana cewa (Manma na dawo), daga can kuryar daki ta amsa “mon fils tu ed rtour (sannu da zuwa dana)” kafin ta dogaro sandarta ta fito tana laluben bango. Idanuwanta a bude farare tar-tar amma na fahimci bata gani. Da sauri ya karasa ta lalubi kanshi ta rungume suna magana cikin harshen su. Na yi tsaye tamkar an kafeni, ina kallon dattijuwar da nan take wani abu ya tsirga min a cikin kirji, a dalilin kamanninta da Innata.
Ya ce “bani kadai bane Manma, ina tare da bakuwa ne, har da ita 'yan fashin suka tare mu, gashi bakuwa ce a Nijar shi yasa na taho da ita, ta sauka a wajen mu kada ta fada mugun hannu" tace “ina fata kasa an kamesu duka? Tunda ka tafi nake maka addu'ar Allah ya kara daukakaka akan aikinka” da alama bai ji dadin hakan da tace a kunnena ba, ya basar ta hanyar kamo hannunta zuwa kujerar da nake. Tasa hannu tana lalubani sai kyalle take ji. Na zare niqabin ta shafa fuskata sosai, sai kuma tayi murmushi tace “budurwa ce ko? Da alama zatayi kyau, tunda ga dogon hanci ina ji, gashi kace ba daga alkaryarmu take ba".
Na daga ido na dubeshi yana kallona, da baki a bude, amma ya kasa magana. Ta ce "kawo mata ruwa mana? Ko sai na buge maka kai da sandata?” Ya hadiye mayataccen kallon mamaki da tsoron da yake mani, ya nufi kofar da jikina ya bani kitchen ne, ya dawo da gorar ruwan (Ragolis) da lemon (Don Simon) masu sanyi, sai raba suke, yake ya ja tebur ya aje mani har yanzu idonsa akaina, ya ce “Laliya bata zo ta dafa miki abinci bane Manma?” Ta lalubi kujera ta koma ta zauna ta ce "bar Laliya da son kudI, yanzu haka wai ta tafi karBo zakkane gidan KANGIWA, bayan albashinda ka bari na bata jiya-jiyannan". Ya hade rai sosai yana cewa "ni kam zan sallameta, ya zan dauko yarinya ina biyanta, domin ta kula da cikin uwata amma ta fita ta bar min uwa da yunwa, Allah bata isa ba tayi kadan, ko ita 'yar Uban wane ne” daga ni har gyatumar dariya muka yi, ya soma tattare hannun rigarsa da alama kitchen din zai shiga da kansa, ta ce "dadi na dakai kenan Mon Amour (masoyina), babu hakuri.
Mutumin dake yi maka hidima kullum ranar Allah, rana daya da bai samu yayi ba sai ka yi masa uzuri". Ya ce “nayi uzurin Manma, me kike so na dafa miki cikin mintuna goma sha biyar?” Ta ce “dafa mun kabeji, bakuwarka kuma ka tambayeta abinda take so" ya juyo gareni "bakuwata ke kuma mai kike so?” Tsohuwar tace "au ko sunanta baka sani ba?” Kunya ta kamani, domin ban kyauta ba, na ce “sunana Zaynab, shine bai fada min sunan sa ba Mama, shi yasa nima ban fada masa ba".
Yayi murmushi, amma bai dago daga abinda yake yi ba, wato zuba lemu a tambulan ya kai bakinsa, ta soma laluben sa wai zata dake shi, ta ci karo da bango kamin ta kai kas yayi maza ya cafo ta, ya kwantar da ita akan doguwar kujera, ya ce "dukkan ku kuyi hakuri, sunana mai tsada ne. Ina fadarsa ne kawai ga matar da nake matukar so, don haka Manma ki tambayamin bakuwata, shin ta shirya amsa na a matsayin mijin aurenta, in gaya mata sunana?” Kafin gyatumar ta amsa na yi hanzarin tarar numfashinta da cewa "ban shirya ba, ba kuma zan amsa ba, don haka ka rike sunanka mai tsada, bana son ji”.
Ya russuna ya kwantara da kansa a cinyar gyatumarsa, cikin matsananciyar nadama yace "ina fatan ba fushi kikayi da tsokanata ba?” Nace “ta yaya zanyi fushi da mutumin da ya karBi bakuncina, alhalin bai san ko ni wace ce ba, bai ji tsoron kada in cutar da gyatumarsa dake da lalaru ba? Bai sani ba mutum ce ni koko ina daga jinsin jinnu? Bana daga cikin mutanen dake yin fushi da wanda yayi musu alheri, komai kankantarsa. Daga baya kuma ya bata musu, sai iny masa uzuri. Jeka dafowa Mamarmu abincinta, mon amour, ko ba haka ne sunan da na ji Mama na kiranka ba?” Ya mike yana dariya yace "inda kinsan menene ma'anar Mon-amour, da baki kirani da shi ba".
Daga kwance tace “rabu dashi diyata, ko kin rasa masoyi me zakiyi da wannan tsololon?” Daga can (kitchin) ya amsa “lala Manma, amman kin yanke ni. Na rantse, duk fadin garinnan, kafin a samu saurayi mai kiba ta aiki ne ja" ta ce "a inda babu masu kibar ba". Haka sukayi tayi tana tana yankansa yana kare kansa, kamar wasu kaka da jika. Akwai alamun shakuwa da matsananciyar kaunar juna a tsakaninsu. Yana ji da ita, tana ji da shi, sun fahimci juna, don haka ne bata wani tsaurara magana a kaina ba, don tasan ba zai kawo mai cutar ta ba.
Cikin mintuna goma sha biyar din da ya ambata, sai wani irin kamshi ya game gidan gabadaya. Ya iso rike da kwanon silver mai fadi, dafadukan kabeji ne da aka dafa ruwa-ruwa, an kuma yanka kabejin manya-manya. Ban taBa ganin irin wannan abincin ba, kamar in tambaya amma ina tsoron gwasalen da ya yi min dana nuna ina son jin sunan sa. Don haka naja bakina na yi tsit.
Ya koma ya shiryo min farin kuskus da aka dafa da koren wake da karas sunyi shar a ciki da miyar hanta, da aka yanka hantar kanana-kanana, a gefe kuma soyayyen nama ne irin wanda ake soyawa a ajiye, domin bukatar gaggawa da lemun (7-alive) ya ce “to Zaynabu, aci da hakuri kinsan girkin gwauro ne" Maman ta ce "gwauro, ko tuzuru?” Ya koma gabanta yana bata kabejin a baki da cokali, yace "duk wanda kuka ga ya dace da ni, dai-dai ne."
Maman ta ture lomar da zai sanya mata a baki, ta ce "nidai don Allah ka daure kayi aure Babana, na gaji da wannan wahalar da kake da ni bata dace da kai ba, da wane zaka ji? Da wannan aikin mai hatsari koda kula da gyatumarka, alhalin kai baka da mai kula da kai?” Ya sunkuyar da kai kasa bai ce mata komi ba. Da lama bai so tayi maganar a gabana ba.
Na sauko daga kujera na dawo gabanta na karbi silvern a hannunsa, nace “ni idan na baki zaki ci? Ki yi masa hakuri Mama aure ai lokaci ne" na cigaba da bata tana karba tana ci bata ce komai ba. Ban juya na kalle shi ba amma jikina ya bani kallona kawai yake yi.
Sai data koshi na bata ruwa tasha, sannan na karasa cin nawa, na lura har zuwa lokacin zaune yake a inda yake, bai tashi ba. Na daga ido na dubeshi, don ganin abinda ya hana shi Magana, fararen idanunsa har yanzun akaina suke, cikin kollon da ba yau na fara ganinsa a idanun maza ba.
Na ce cikin basarwa “kai baka ci abincin ba" ya lumshe ido a hankali, maimakon ya masa min abinda na tambaye shi, sai ya mike yana cewa “idan kin gama kiyi amfani da wannan dakin, (ya nuna dakin da dan-alinsa) duk abinda zaki bukata akwai a ciki, domin kanwata ke yin hutu a dakin idan tazo daga makaranta, duk abinda babu kiyiwa Mamana Magana, zata fada miki inda yake".
Ya fita daga falon ba tare da ya waiwayo ba tace "yarinya jeki kiyi sallar azuhur, ki kwanta ki huta zuwa la’asur, ai kinga duniya nidai wannan aiki bana sonshi, to ya kafe ne, amma wannan sai da rai dame yai kama?” Na so in tambayeta kowa ne irin aiki yake wanda bata so? Naga wannan ba damuwa na ba ne. Damuwa na shine in samu masauki, in gabatar da abinda ya kawo ni, sannan in nemi dangin Innata. Kenan abinda ya kawoni daban, suma rayuwarsu daban. Saidai babu shakka tsarin rayuwar su shi da mahaifiyarshi ya burgeni. Cikin 'yan awannin da nayi tare dashi, na fahimci abubuwa da dama game da shi. Duk matar da tayi sa'ar aurensa ta yi babbar sa'a, domin zata zauna lafiya. Kasancewarsa mutum mai saukin kai da duk wasu qualities da ake nema daga da namiji, uwa-uba irin mazannan ne da albarkar Uwa ke bibiyarsu, saboda tsananin biyayyar da suke mata da nuna jin kai a gareta, tamkar zasu kwanta mata.
Karfe tara na dare muna falo tare dashi muna kallon labarun Jiha, duk da cewa ba abinda suke fada nake ji ba, kasancewar faransanci ake yi amma ai ina ganin hotuna, aka nuno 'yan fashinmu da aka kama daren jiya, ina kallonsa yana ta murmushi ko me ya tuna? Oho can kuma ya dubeni ya ce "wai don Allah menene a katuwar jakar nan ne da kika riketa kamar rai?” Na harareshi, Maman tace "yau naji ikon Allah, wannan shine kaka uwarka ta haifeka, wai naci abinci acikin cikina ace in amayar da shi aga kalarsa. Akan me zata gaya maka abinda ke cikin jakarta? Kana binta bashi ne?” Ya yi dariya yace "Allah Manma, in da kinga irin rikon da ta yiwa jakar, duk karfin dan fashinnan kasa kwatarta yayi a hannunta, sai babbansu yace "ku miko min ita in rage dare da ita, tunda ta hanamu jaka, ta bamu abinda yafi jaka" ta wawuri filon kujera ta saita inda yake azaune ta maka masa, bata san cewa ni ta makawa ba. Ya dinga yi mata dariya ya tashi ya fita ba tare da ya lura da (wallet) dinsa data fado daga aljihun gaban rigarsa ba.
Na kai hannu na dauka na bude, don tsabar neman magana irinnawa, kudi ne irin nasu (Saifa) a jere gwanin ban sha’awa. ina zaro ID card kamin in duba sai gashi kamar an jeho shi yayi wuf ya karBe yace "Eye, bin kwaf, na tambayi menene a cikin jakarki, ance nayi miki tambar kaka Mamanki ta haifeki, shine ni zaki yi mun tsirara?” Na fiddo ido nace "ka fassara wane irin tsirara kake nufi, kada Mama ta dauka ‘nakedness' wannan kazafi ne," ta wawuro kofin dana cika mata da ruwa ta kwara masa ta ce “fita ka bawa mutane wuri, kasa yarinya agaba da magana kamar Aku? Ni ban san ma yaushe ne bakinka ya bude ba".
Yana kokarin hada kwayan idonsa da nawa, yayi murmushi “nima ban san sanda ya bude ba, Manma, ba mamaki sabida zuwan Zaynab ne".
'Yar tsohuwar taji kunya, tayi gum, da bakinta, ta kurawa allon talabijin ido kai kace tana ganinsu, ta koma sauraron abinda ake cewa, can kuma tace "kaga bana cikin shirmen ku, karo min sautin, naji kamar ana ambaton diyata”.
Kyakkyawar fuskarta ta cika akwatin talbijin din, kamar ta fito tayi magana. Kasancewar (t.v)n katuwar gaske ma’abociyar kyakkyawan hoto (flat-screen). Tana gabatar da jawabi cikin faransanci da accent din Paris mai burgewa, a wani taron bude makarantar yaki da jahilci a babban birni Niamey, Nuratu Mainasara ce.
Ni kadai naji ina gwama numfashi, domin yakar burgenin data yi da matsananciyar kiyayya. To amma ko (hasidin iza hasada), dole Nuratu ta burgeshi.
Hutu da jin dadi sun Boye zahirin shekarunta, sun maidata kamar wata matshiya 'yar shekara ashirin da biyar, ko ni da nake budurwa in my tenth ba zan nuna mata komai ba, sai a zaBe ta da gudu a barni. In kuwa aka koma ta fannin gyaran jiki sai ka dauka tana ‘modeling’ ne.
Duk wannan kallon kurullar da nake mata, da hanci da nake hurawa, ashe yana hankalce da ni. Ya fice bai kuma dawowa ba.
Gaba dayan hankalin Maman yana kan akwatun talbijin, na matsa jikinta sosai nace "Mama a ina gidan talbijin din garin nan ya ke ne?” Tana fadamin ina daukewa da biro cikin ‘jotter’ na, nace “baku da gidan Radio ne?”
Ta dauko fankon idonta ta daura mini, ta ce cikin zargi “me ya hadaki da gidan radiyo da talbijin?” Nayi murmushi mai wanke zargi nace “lah! Ba wani abu, cigiya nake so in bayar a kan dan uwana da ya Bata, shine kuma dalilin barowata gida, ance ana kyautata zaton an ganshi a cikin garin nan."
Jikinta yayi sanyi tace "amma da kin gayawa Mon amour, wannan karamin aiki ne a gareshi, cikin kwana daya in har yana cikin garin nan zai nemo miki shi."
Na yi shiru ina tunani, wannan na nufin shi dan sandan ciki, ko kuwa Security na jiha (SS). Gaskiya kam biri ya yi kama da mutum. Kenan shine yayi cunen da aka kama 'yan fashin mu? Dole in yi taka-tsan-tsan dashi kenan kada ya zamo silar rugujewar cikar burina.
Gaskiya mana bai tsaurara tambaya akaina ba, me nazo yi, wa nake nema da sauransu; a tafin hannunsa kawai yake kallona. Jin nayi shiru tsohuwar tasha jinin jikinta, tayi nadamar sakin bakinta da katoBarar da tayi, sai ta yi hanzarin gyara zancenta da cewa
“Ina nufin zai iya sawa a nemo miki shi, tunda shi dan gari ne kuma namiji. Amma mace kamarki tace zata yi neman wani cikin babban gari irin Damagaran, ai ta hada kanta da aiki ". Na yi murmushi nace "wai ai cigiya kawai zan bayar" ta fada mini kwatancen nan ma na dauke da birona ba tareda ta san ina yi ba.
Washegari mai aikinta Liliya ta dawo, sai muka hadu ni da ita muka shirya abin karin kumallo, cikin dan lokaci na saba da ita domin 'yar kauye ce ta sosai mai shegen surutun tsiya. Cikin dabara muna hira da ita na sako zancen Mainasara, nace “na ji ace jiya kinje karBar zakka, ke nan Mainasara tana garin nan?” Ta kama baki ta ce "tabdI, bafa ita ce take rabon zakkar ba, aikowa take yi, ita tafi zama Niamey sabida acan mijinta da 'yan uwanta suke. A gidan kakanta ne ake rabon zakkar cikin (Kangiwa Estate). Gabadaya tushen su arziki ne domin marigayi Kangiwa Mainasara, kakanta kenan, yayi shugaban kasar nan shekaru ishirin a baya.
Babanta Alhaji Sani Kangiwa, yayi ministan kudi anan Damagaram. Bayan ya sauka ya nemi kujerar Gwamnatin mu, gab da zai lashe zaBen ya je Nijeriya kai diyarshi neman magani sukayi hatsari shi da ita suka mutu, Nuratu kadai ta tsira.
Saida ta yi shekaru masu yawa a Nigeria, rana daya sai gata ta dawo, shinefa tun daga lokacin ta rungumi siyasar mahaifinta, ta kuma sami nasara a kowanne fanni na rayuwarta, duk a dalilin kyakkywar zuciyarta da taimakon talakawa. Ba don neman kudi take siyasa ba, sai don daukaka tushenta a tsakanin sauran jihohi tsararrakin ta. Idan nace zan gaya miki abinda wannan baiwar Allah ta mallaka a kasar nan, cewa zakiyi karya ne domin babu wata mace cikin kasarnan gabadaya data mallaki rabin-rabin abinda ta mallaka, to amma ita kanta gada ta yi.
Tana da rijiyar man fetur nata na kanta, don haka gidan mai wannan tanada akalla guda goma na kashin kanta” ta sunkuya ta tube takalmanta, irinnasu ne tafka-tafka na fata “hatta wadannan takalman da muke sawa, da jakunkuna da muke ratayawa da sauran kayan amfanin cikin gida da ake sarrafawa da fata kamar su tuntu, filallika da sauran su da akafi amu gidan manya duka daga fatar Mainasara ne. kasurgumar 'yar kasuwar fata ce da take baiwa kasashen Italiya, Farisa da Tailan (Thailand) suna sarrafawa zuwa takalman kwalisa, da ake shigo mana da su.
Nuratu nada bankuna na kashin kanta, wadanda mafi yawa dukiyarta ce kadai a ciki, wadanda duka ta gaje su ne daga Kangiwa, kada ki dauka mahaifinta ne kadai dan sa, a’ah, yana da wasu 'ya'yan duk suna Niamey, suma suna da gadon arzikin su dai-dai da nata. Abinda yasa ta zarce su kuma ya kara mata arziki fiye dasu shine kasuwancin fata data fi maida hankali akai. Kiyi fatan Allah ya hadaku watarana a cikin gidannan, zakiyi bankwana da talauci…..". A razane na daga ido na dubeta “a cikin gidannan?” Na fada cikin raina, amma a zahiri murmushi nayi. Cikin raina nace ko a mafarki kada Allah ya hada ni da ita balle a zahiri. A fili kuwa sai na ce "nan gidan kuma?”
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791:
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel