Showing 15001 words to 18000 words out of 45361 words
Chapter 6 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
bata yi min laifi ba, Ubangijinta ta yiwa. Idan kuma ta rokeshi ya yafe mata, ni ba komai ba ce. Babu wadda zata so ta haife Da babu aure, sai dole, sai tsananin rabo da kaddara. Babu kuma wanda ya isa ya kaucewa kaddarar duk da Allah ya rubuta masa. Sai kuma wani hukunci na Ubangijin mu da yake son nunawa na baya darasi. Amma al'umma bazamu taBa hankalta ba.
Laifinta daya gareni, shine na biris din da tayi da Innata, abar ma ta ni kaina, alhalin tana sane da wahalar data barta da ita, da bakin-ciki gami da abin kunyar data jawo mata wanda fadar sa ma bata baki ne, musamman a cikin karkara.
Duk da haka 'yar uwarta bata taba budar baki ta fadi kalami na Allah wadai agareta ba. Duk wasu kalamanta akan Nuratu na kauna da alheri ne. Ta ce dole ce ta sa ta gudu ta barta, amma Nuratu mutuniyar kirki ce.
To ko bayan Innar, wane ne ya budi baki ya fadi wani abu wanda bana yabo da kauna gami da fatan alkairi a gareta bane? Ko Ya Faruq wanda zai kasance karamin yaro a lokacin da ya santa, yace ba halinta bane, kaddara ce ta afka mata. Hakika halin mutum da makomarsa ana gane su ne daga shaidar da ya samu daga mutanen dake tare da shi. Kamar yadda yace; dukkannin mu masu saBo ne in one way or the other, na wani ma idan kaji sai kaji kamar ka roki Allah ya kifar da duniyar, domin babu komi cikinta sai saBo, kalilan ne suke yin saBon suna kuma tuba. To idan Nuratu ta tuba, Ubangiji ya amshi tubanta, ni menene makomata? Abin nufi, meye makomar dan da ya bankada mutuncin Uwarsa a duniya? Ya tozartata a idon al’ummar dake matukar ganin GIRMA da kimar ta? Abar ta zancen hukuncin rashin yarda da kaddara da fawwala komai a gareshi, wanda ke daga cikin rukunan musulunci, a koma ta hukuncin mai daukar fansa, wanda bai yarda da hukuncin da Allah ya zartar a kansa ba.
Ubangiji (S.W.T) yace "kuyi hakuri, hakika Ubangiji yana tare da masu hakuri” ya kuma ce “kuyi afuwa (ga wanda ya saba muku) hakika Ubangiji mai afuwa ne". To ni banyi hakuri ba, banyi afuwa ba kamar yadda Faruq da Halima suka Bata muhimmin lokacinsu suna nuna mini.
Mafi tashin hankalin ma daukar fansar tawa akan UWA, wadda sai ta daga min diga-diganta ne zan wuce aljannah, wadda Bacin ranta zai kaini wuta, hawayen ta ya turani jahannama. Wadda (S.A.W) yace “a bita, abita, ya kuma cewa a bita, kamin yace abi Uba….”.
Nasan inda duk take a yanzu tana can tana zubar da hawaye, ba don bakin-cikin hanata sisaya ba, sai don bakin-cikin FADUWAR GIRMAN ta, bacin suna da zubewar mutunci, duk a sanadiyyar diyar data tsugunna ta haifa a cikinta.
Ni ban gyara lahirata ba, gashi dama duniyar tawa gurBatacciya ce. Na kuma kara gurBatata. Idan da na yi tunani, ai kirari ne nayi na zurmawa kaina wuka, ko babu komai na baro inda aka sanni, saboda gudun kar a kirani da ‘shegiya’.
Maimakon da nazo inda ba a sanni ba, in rufawa kaina asiri, in nemi dangin uwata da ita kanta, mu taru mu rufawa juna asiri, a'ah, suma na kawo musu guzurin Bacin suna da abin gori har 'ya'ya da jikokin su….
Numfashi na naji yayi sama, kamin ya gagareni fesarwa, kirjina ya shiga wani irin zafi da radadi, kwakwalwata ta shiga bugawa dam-dam saboda zazzafan tunanin dana takurata da shi. Idona ya shiga lumshewa yana budewa a hankali, ban kara tsinkayar abinda yake faruwa da ni ba, illa jin hannun Qassim daya taroni ina shirin zamewa cikin seat dina, yana cewa "Ayya Zaynab! Me yayi zafi haka?” Na lalubo shi na kamo kansa dai-dai kunne na, muryata ta dushe gabadaya, nace
"ko bayan raina… ka roka min gafararta, ka gaya mata nima bada son raia na aikata mata hakan ba, zuciya ce tafi karfina……, na-nayi in lankwasata, na kasa, na yi kuskure babba da bani da inda zan sa kayan nadamar shi…." yace “Insha Allahu Zaynabu, ko zaki mutu sai a kirjin mahaifiyar ki. Ko wannan shine abu na karshe da zanyi a rayuwata, zan yi iya kokarina in sadaki da ita…”. Bayan wannan, ban kuma tsinkayar meke faruwa a duniyar ba.
*** *** ***
A NIAMEY
“Aunty Zaynab, muna yi miki barka da zuwa cikin (family) dinmu na MAINASARA KANGIWA". Zazzakar muryar wata matashiyar yarinya da bata fi shekaru sha hudu ba, na ji a cikin kaina kamar a mafarki.
Wadda ta kitsa mata fadin hakan ta kara ce da ita “ki gaya mata dama mun san ko ba-dade, ko-bajima zata zo ne, in har tana raye”.
A hankali na bude idanuna da suke a rufe, a baryar da sassanyar muryar matar ke fitowa. Fara ce sol, doguwa mai ginannen jiki. Fatar jikinta sumul-sumul jawur, kamar kana tabawa jini zai yi tsartuwa. Sumar kanta yalwatacciya baka kirin, nannade a gadon bayanta. Hancinta a mike kamar biro, sai murmushi take tamkar furen fulawa, hakoranta farare tas kamar kankara, yatsunta na kafa da hannu sun sha adon bakin lalle sunyi shar, santala-santala dasu jajawur kamar na jariri sabuwar haihuwa.
Mayuwanci ne ka kimanta shekarunta a lokacin daya, za dai ka kirata babbar mace, mai babban al'amari. Idanunta dara-dara farare sol da kwayar ido mai sheki kamar an diga zyl, sun sha (kohl) sun fito dara-dara cike da barazana da rashin son waigi. Sanye take da ruwan hodar lesi (Cotton) watau (dark-pink) mara nauyi, shara-shara, shafal-shafal kuma mai saukin ado. Wuyanta da kunnenta ya dauki siraran ‘pearls’ na farin dutse, riga da zane ne a jikinta, daurin kallabin ya zauna sosai a kanta kamar nadin inji.
Gabadayanta sai kace sabon kwai ne da Dawisu ya nasa yanzu-yanzun nan, domin haka take very delicate. A Bangaren jinsin dan adam (personality) tana cikin rukunin 'phlegmatic people’ watau mutanennan masu fara'a, rashin kuzari da wadatar jini a jika. Mahaifiyatace, Hajiya Nuratu.
Kallonta nake cike da mamakin yadda za'a ce matashiya kamar ta, ta haifi katuwar budurwa kamana. Zai fi dacewa idan akace ni kanwarta ce, mai bi mata a haihuwa. Lokaci guda wata irin kauna ta UWA (maternal love) irin ta da da mahaifi, wadda Ubangiji kadai yasan adadinta, ta rika keta zuciyata. Ba abinda zan so a lokacin kamar ta rungumeni a cikin jikinta, inji me 'ya'ya suke a dumin jikin uwa?
Amma batayi hakan ba, baya ta juya min tana abinda yafi mun kama da sharar hawaye. kofar dakin ta bude, mata ne suka rika shigowa farare tas-tas manya da kanana, tsofaffi da masu tsaka-tsakin shekaru. Kallon sittirun dake jikinsu da yanayin fatar jikinsu kadai ya isheki kimanta sune iyalin Kangiwa. Tambaya suke ta yi “ina Zaynabu din? Ku matsa na ganta………. Ku gafara mu ganta. Kauce nan na hangota. Zaynabu ina Yaya Rabi? Zaynabu wa ya kawoki Niger? Ina kika baro Yaya Rabi, ba tare kuke ba…?”
Na maida idanuna na lumshe, wasu irin hawaye na fita suna shiga cikin kunnuwana. Cancarakas suka dagani suka tsayar da ni akan kafafuna. Daga masu rungumata sai masu kama hanuna da masu tube dankwalina don ganin kalar gashin kaina.
Kowanne na fadar albarkacin bakinsa game da kamannu na da mahaifiyata da 'yar uwarta Rabi. Wata gyatuma tukuf a durkushe tana dogara sandarta ta dogaro ta shigo tana "gafara nan ku gani in bugi shashasha…” ta daga sandarta ta muka min a baya, wata mace mai tsaka-tsakin shekaru daga cikin wadanda suka zagayeni ta rufeni ruf da bayanta tace “sai dai ki bugemu tare Yadudu, amma Zaynab kuruciyarta ke dibarta, ta kuma gaya mata miki abinda take tunanin shine dai-dai da ita, ko ni ce hakan zanyi. Kuskurenta daya bata fara tunkarar Nuratu ta ji bayani daga gareta ba.
Zaynabu Allah baya ramurar gayya ba kuma ya son masu yinta. Idan kece hakan ta faru dake, zaki so 'yar ki ta yi miki abinda kika yi mata?”
Ni dai sai kuka nake na rasa ta cewa. Ganin al'amarin nake kamar a mafarki, na kasa gasganta wannan rana. Wai wadannan duka dangin Inna ta ne jinin ta ne, tsatsonta ne. Na daga kai domin hango karshen su, iyakar ganina banga adadin su ba, da alamama akwai wasu a waje, wadanda duk girman da dakin ke da shi, basu samu wurin tsayar da kafafunsu ba.
Na jinjinawa zuciya irin ta Innata, da ta iya rayuwa ‘lonely’ cikin karkara, shekaru ashirin da doriya ba tare da kuwa nata ba, duk da wannan bataliya da Allah yayi mata, ba kowadanne mutane ne masu zuciyar Inna ta ba.
A cikin su dai na ci gaba da hange, don karin ganin fuskar dake yawo in my imaginations, kwana da kwanaki, wata da watannni, shekara da shekaru; Nuratun Inna Rabi.
Muka yi ido hudu, kallona take babu ko kiftawa, fararen idanunta cike da tarin kaunar da biro ba zai iya rubutawa ba.
Duk da haka hawaye basu bar ambaliya daga idanunta ba. Ta tako a hankali suna darewa suna bata hanya, zuwa gadon da nake zaune, na tura 'yan yatsuna guda biyu cikin bakina, domin toshe kukan dake son suBuce mini, ta tsaya a kaina ta ce “ina Yaya Rabi?”
Da karfi kukan ya kufce, na yi ta yi babu sassautawa, cikinsu babu wanda ta katseni amma jikkunan su sunyi sanyi, har na yi mai isata ya isheni. Cikin dusashshiyar murya nace “Allah yayi mata rasuwa sati biyu da suka wuce……..”
Gabadaya falon ya rude da kururuwar mata da tsofaffi, barin tsohuwar da naji an kira da Yadudu, faduwa tayi tana tana makyarkyata tace "ashe rabon zamu sake ganawa dake ba Rabi? Cikin wannan satin muke shirin tafiya gabadaya gareki, wayyo Rabi baiwar Allah bamu rike amanar mahaifinki ba….." hankalin su duka ya koma kanta, suka cicciBeta suka dora akan gado suna yi mata fifita da bakin mayafan laffayansu, daga baya na fahimci ita wannan dattijuwa kaka ce ga Innata domin ita ta haifi mahaifinsu Alhaji Sani. Ita kadai ta saura cikin matan marigayi Kangiwa.
Bana son tuna irin halin da Nuratu ta shiga da jin mutuwar 'yar uwarta. Ta zama jawur kamar jinni, tana kuka da hawaye da majinarta, ta fita daga dakin ta hau matattakala zuwa sama, har dare bata kara saukowa ba.
A lokacin ne iyaye maza suka iso daga sammacin da 'yar uwarsu tayi musu. Suka tarar da wannan labari sukace "Allahu Akbar, haka Allah ya so bamu da rabon ganawa dake Rabi sai a Darusallamu, ki yafe mana ki yi mana aikin gafara, bamu sauke hakkokinki dake kanmu ba. Tunda Alhaji ya rasu babu wanda ya bi sawunki, tunda 'yar uwarki ta iso ta ce mana kina lafiya zaman aure kikeyi, babu wanda ya kara bi ta kanki. Hakika idan baki yafe mana ba akwai hisabi a tsakaninmu, ga gadonki muna ta ajiye da shi har yau ba wanda ya ci, don haka zai zamo sadakatul jariya a gareki…". Dacin mutuwar 'yar uwarsu ya shafe nawa al'amarin, suka taru kaf a babban dakin ‘meeting' dinsu dake cikin gidan Nuratu, suka bude al'qur'ani mai tsarki suka yi ta sassauke mata, aka kada Rakuma, shanu da raguna aka yi ta sadaka. Tun daga ranar garar abinci kawai ake fitarwa daga (Estate) na Kangiwa nau'i-nau'I zuwa ga kushewarta, har tsayin kwanaki (7). Ni da Qasism sai dai hange daga nesa a dakin addu'a, ya yi min murmushi in maida masa, sai ranr bakwai Liliya ta kawo Innarsa daya manto a asibiti.
Jin abinda ke akwai ai sai ta kara faduwa ta suma, ban taBa ganin rarraunar tsohowa irin wannan ba. Hibbani cousin din Innata wadda ke kareni da Hajiya Yadudu na duka, ita ke gaya min Goggo Azzo, kanwa ce ga kakan mahifiyata watau Kangiwa Mainasara.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Da na tattago radiyon Rabi, na sauke masa a baki, sai ga haBo ya biyo baya, na guda-gudan jinni, suna sauka akan hannayensa nace "kadan kenan daga abinda zaka gani, a duk ranar daka sake gigin shiga harkata".
Yadda duk ya dauki abin da sauki, to ba haka yake agareni ba. Ya dauka wannan karon ma zai sake samun kaina da irin kalaman yaudararsa, bai sani ba, kishi yana maida soyayyah, kiyayya, sannan, zama da kishiya is not the type of life I planned for.
Rabi kam ta yi tsalle gefe tace babu ruwanta da shirgin mu, tunda sanda muka kulla soyayyar, ai boyewa muke bama so ta sani, saboda mun maida ita 'yar bukulu, saida ta kwaBe masa zaizo ya isheta da 'yar murya. Haka nace da Malam Ali, muddin ya daura min aure da Sa'idu, to zan guda kasar mu, cikin dangina, ya samo mai zama da matarsa.
Na kara gasgata rashin tabbas, karya, yaudara, da ha'inci irin na da namiji. Wai zai dubi Sa'idu a haka yace ya taBa yin aure ma balle ya haihu? Wa zai ce ya taba yin soyayya ba a kaina ba? Na rokI Allah ya saka min akan wannan yaudara da Sa'idu ya yi min, ba kuma don komai ba yayi min hakan ba, sai don ganina da yake yarinya karama, mara wayo, domin da yayi aure da wuri tabbas da ya haife kamata.
Wai ma ashe tare da matar tasa suke, ya taho da ita ganin gida da kuma bikin auren mu. Ban san haka ba sai da yamma da tazo ana take mata baya, cikin atamfa English marun kala, ta yafo wani dan yalolon gyale, kamar na tatar koko, tana tafe kai a sama, kamar kada ta shaki iskar kauyen, ita a dole ga baturiya. Ta zo har cikin dakinmu yaronta Imran na biye da ita yana ta kuka, ta coge a bakin kofa don dakin bai isa ta taka baturiyar kafarta a cikin sa ba, ta ce "zuwa nayi inga BARAROJIN data kanainaye min miji, zuwa nayi inga SADAKA-YALLAR dake shirin aure min miji?
Ba dai wannan berar bace mai kama da dorawa?” Muka daubi juna ni da Yaya Rabi, cikin mamaki, dimuwa da rashin abin cewa, ta cigaba da cewa "Bararoji Nijar babu abinci, kun gudo daga jeji, domin BARA da KARUWANCI, ai da kun tsaya a karuwancin, amma mijina? Yafi karfin auren sadakar-yallah, koko ince, naïf karfin yin kishi da sadaka-yallah". Ta Balle bakin jaka ta debo (pounds) na kasar Ingila curi guda ta watso min a fuska tace Yallah, ga sadaka nan, don Allah a kara gaba. Sa'idu sai Sa’a, sai gani sai hange, ance dake ana yin mata biyu a Ingila ne? karya yake miki baskwata ya gyara miki, duk kuma mai zaune a baskwata, 'yar wanke-wanke ce.
Kenan gara miki zamanki cikin kauye, yafiye miki rufin asiri, ko kuma a koma Niger ayi tallan cukui, a kora Rakuma sahara. Muddin kika sake kika biyo shi, wallahi 'yar wanke-wanke na samu, amma nafi karfi in yi ‘sharing’ miji da sadakar-yalla da tsafta ma bata ishe su ba".
Ta juya tana kada mazauna ta fice abinta, daga ni har Yaya Rabi, gudun jini ya daskare a jikinmu. Ba'a taBa yi mana wulakanci irin wannan ba a tsayin rayuwar mu. Duuiya mai yayi! Wai mu jikokin Kangiwa ne yau ake kira mayunwata, karuwai, sadakar yallah! Allah sarki!
Mukai ta kuka har muka ji babu dadI, nace "wallahi ko zan mutu babu aure, bazan auri Sa'idu ba" Rabi tace “shirmen banza, bazaki aure shi ba kawai idan bakya son shi, amma ba don wannan busashshiyar da aka bashi sadaka ba. Da ta isa ta yi mana wannan zagin a gaban sa, wallahi saki uku zata karBa babu nadama!”
Nace “kayya Yaya Rabi, son ma na daina, indai na Sa’idu ne, koda kuwa shine autan maza. Yau mu ake kira karuwai Rabi, har ke da kike a dakin mijinki? Allah ya isa tsakanina da wannan matar dana bari ta fita ban tara mata gajiya ba….”
Rabi sai ta koma yi min dariya, ta ce “a hakan? Da dai kanwar ta kar tsami". Na fada jikinta ina kuka nace "Allah sai na rama akan wanda ya janyo miki zagi a rayuwarki".
Sa'idu kam da gaske yake, ya cigaba da shirye-shiyen aure batare da ya kara bi ta kaina ba. Dana ga dai da gaske Malam zai daura auren nan, sai na hada kayana da asuba na fice da niyyar in tafi tasha in hau motar Niger, ko yaya Rabi bata ga fitata ba tana barci. A lokacin kuma Malam da Sa'idu suka fito daga masallacin dake daura da gidan mu daga sallar asubahi, suka hango ni ina ta nikar sauri da akwati rindimeme aka kamar wata zararriya.
Gabadayan su suka biyo ni, Malam Ali ya sha gabana, ya ce "Nuratu me yayi zafi, kawo akwatun ya daukar miki, kin san dai bazan taBa yi miki auren dole ba, domin kuwa ke amana ce a hannuna da idan naci sai Allah ya tozartani duniya da lahira". Jikin Sa'idu ya yi sanyi, ya tabbatar wannan karon da gaske nake. Babu komai cikin kwayar idona sai kiyayyar shi tsagwaronta. Shi ya dauko akwatin muka dawo, Malam yana ta fada wa Yaya Rabi, kan sakacinta har na fita bata sani ba, yanzu da Allah bai sa sun ganni ba wa yasan inda zan fada?
Nikaina fada kawai nake, amma in za'a kasheni
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel