Showing 36001 words to 39000 words out of 45361 words
Chapter 13 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
yake, suka tsaya suna Magana, ba tare da ya juyo ba.
Dukkanninsu suna sanye cikin farar shadda dinkin Dakar, da hula zanna-bukar. Ban san abin da ya dauki hankalina haka kan wadannan matasa ba, tunda ba'a yau na fara ganin kyawawan maza ba. Karewama ga jar fata nan sunata sha'anin su a harabar ‘airport’ din, amma wadannan masu duhun, su suka dauki dukkan (attension) dina.
Kamar yadda suke cikin shiga daya, to ba haka halittar su take daya ba. Daya dogo ne, siriri mara kauri, sannan yana da hasken fata, wanda ya hadu da jin dadin rayuwa ya maidashi kamar wani ‘half-caste’, watau ruwa biyu. Daya mai matsakaicin tsawo, baki kuma kakkaura, yana sanye da farin (medicated glass) wanda ya zamo (everyday-glasses) a gareshi. Kirjina na ji ya fara bugawa da sauri-da-sauri, numfahsina ya soma samun tangarda, kafafuna suka soma kokarin kayas da ni. Gabadaya suka juyo fuskarsu dauke da murmushi. Suka nufoni cikin sassarfa da takun GIRMA kai kace wasu 'ya'yan saraki ne. Idan har ba karya zuciyata ke gaya min ba, ba kuma gizo idanuwana ke min ba, to IMARAN ne bakin mai hasken kuma UMAR FARUQ din Nuratu da Inna Rabi.
To gun wa zani? Yayan ko Faruq din da har yau ban san matsayin da zan kirashi ba? Ko dai inyi amfani da Kalmar nan ta bature da yace (blood is thicker than water?) In tafi ga dan uwana da nake nema ruwa a jallo? Kwana da kwanaki wata da watanni? To amma anya Faruqun ya cancanci hakan?
Wani zubin ruwan ya kan fi jinin karfi, koda shi jinin ya fishi kauri. Don haka maimakon haka. Sai na juya da gudu na kankame Mamie. Nuratu zata kashe ni da ban mamakinta.
Na kasa gasgata abinda idanuna suka gane min. Watakila dai irin mafarke-mafarken nan ne da bana rabo da su, masu nuna min wai wata rana….,, zamu hadu da Ya Em a inda ban zata ba.
Dariya suka yi suka karaso gaban Mamie, suka zube a kasa suna gaisheta ita kuma sai kokarin kwakwaleni take a jikinta cike da jin kunya ta ce "wallahi ko ki cikani ko ince su koma inda suka fito”.
Da gudu na saketa na karasa da gudu na rungume Ya Em, sannan ne wasu irin hawayen farin ciki, suka zubo mini. Yana sharemin da hankicin sa yace "is o.k Zaynab, ina nan tare dake, muddin rai, ba zan kuma zuwa ko'ina ba" ya cirani yayi min nuni da Faruq din daya juya mana baya yana masa waya. Dai-dai lokacin shi kuma ya juyo yana cewa "eh, muna nan Singapore har shi Imran din, ita Hajiya zasu yi wata sabga ne sai sati mai zuwa.." ya kashe wayar yana karasowa inda muke. Imran yace "shi Faruq ba za’a gaishe shi ba?”
Na kai hannuna na rufe fuskata ina murmushi, yau wata matsananciyar kunyar Faruq nake sosai, irin yadda ban taba jin kunyar wani da namiji ba. Yayi kwafa yace “kada ta gaishenin, kyale yarinyarnan Imran yadda ka ganta, muguwa ce”.
Ko kallona bai yi ba yayi gaba wajen su Mamie. Abin yayi min ciwo kwarai. To amma ganin Ya Em a yau yasa na soma tunanin babu abinda zai kuma sani bakin-ciki a rayuwata.
Mota ce ta musamman tazo ta debi su Mami, ni kam nace kafata-kafar dan uwana. Faruq ya harareni, harara sosai ya ce "wannan mota tawa ce, bata dan uwanki ba, babu ko kwabon shi wajen siya min ita, kuma bana daukar mugaye a cikinta.
Wadanda basu damu da halin da wasu zasu fada a dalilin su ba, kansu kadai suka sani da nasu farin cikin. So ki nemi mai daukarki a mota, tun wuri, tun dare bai miki ba, ko ki jira in maida dan uwan naki gida, ya aro mota ya dawo ya daukeki, don shima tsintarsa nayi, a titi, bashi da komai sai muguwar zuciya irin taki, data kware wajen jefa iyayenku a halin kaka-ni-kayi….” sakin baki nayi galala! Ina sauraron cin mutunci, amma shi Imran da yake bashi da zuciya ko a jikinsa, sai dariya yake yana gyada kai kamar kadangaren bakin tulu. Ai ni ko mayyace wallahi na hakura da motar nan. Ban ankara ba ya ja kayarshi a guje suka yi gaba. Na tabbata da da kura a wurin, da sun bade ni, mugun badewa kuwa. Sai Allah ya taimakeni duka wajen ‘ceramic’ ne.
Motar su Mamie ce tayi ribas ta dauke ni. Raina ya baci sosai da wannan wulakancin da Faruq ya yi mani, ban san sanda hawaye suka zubo min ba. Na ce babu komi, indai nice maganin 'yan maza ce. Wanda ya fika wulakanci ma na ganshi ya dawo, ya zube gwiwoyinsa a kasa da hawayensa yana rokona gafara. Kai haye kayi ba gada kayi ba. Moiram da karin abin haushi tace “ya basu daukeki ba?” Hibbani ta ce “sabida batayi wanka ba, ta kwana a jirgi, tana tsami”. Mamie abin ya bata dariya, don haka ta yi murmushi.
Wani gida ne hawa daya, korran (grass carpet) sun yanyame shi tun daga kofar shiga har rufin gidan. Karamin gida ne (Flat) babu gate sai kofar shiga gidan. Fasalinsa kamar kwale-kwale, sannan gefensa (stream) ne mugadanar ruwa yana bulbular da ruwa, garai garai. Mamie tasa mukulli ta bude muka shiga falon, kowanne ya zube a kujera a gajiye. Gidan a gyare yake fes, kai kace da mutane a ciki, tuni Moiram ta hau barci. Mamie 'shower’ ta je tayi ta kwanta a dakin barci bata kara saukowa ba, ni kuwa zugum nayi cikin tagumi. Ina son in tambayi ina su Ya Im bana son taga gajen hakuri na.
Na shiga tunanin inda Faruq ya samo Imran, to ko dama wajensa ya gudo? Dana ga wannan ba zata kai ni ba, na yi dakin da Mamie ta shiga, tayi nisa cikin barcinta sosai sabida kwanan zaune da mukai cikin jirgi, na bude jakarta na fiddo wayarta na dawo ‘corridor’ din gidan na jingina da karfen (balcony) ina fuskantar mugudanar ruwan dake gudana garai-garai da shi (Spring), na soma laluben sunayen mutanen dake cikin wayar a nutse, har na iso wada ta yi ‘saving’ da wani suna Dan dukusuru, hakanan akwai “Imin Sa’idu”.
Na sha mamaki kwarai, ashe tuntuni Nuratu tasan inda Imran yake? Ko da yake bai kamata inyi ta bata lokacina wajen mamaki ba, tunda ‘kudi’ sune kare magana. Na kira IMIN SA'IDU (kamar yadda ta kirashi) tayi ta ‘ringing’ har ta kusan katsewa kamin ya amsa, cikin tsananin ladabi yace
"Yello Mamie, kun huta ne, mu zo?”
Nayi ajiyar zuciya nace “kuna ina ne Ya Im?” Yace “ba zaki kwanta ki huta ba?” Na ce "ni dai don Allah ka gaya min inda kuke” Yace “muna gidan Faruq, cikin ma’aikatar su (Informatics)” nace “to ka yi min kwantance in zo” yayi dariya yace “iye, ‘yar gari, zaki bata, kuma ke don baki da zuciya duk wulakancin da yayi miki yanzunnan sai ki zo gidansa?” Na girigiza kai nace “babu ramuwar gayya tsakanina da shi” yace “wonderful! Sai da ni Imran ko?” Na lumshe ido ina dariyar TUNA BAYA…. “kai haba Ya Im, shi Faruq din ne ni kaina nasan ban kyauta masa ba".
Yace "zancen gaskiya Allah-wallahi kika zo korar kare zai yi miki, ranshi a bace yake dake fiye da tsammaninki" na ce “babu komi, kome zai min zai jure, karewa ma hakuri zan bashi" ya ce “to ki bari zamu zo anjima, idan Mamie ta tashi bakyanan bazata ji dadi ba, kafin nan zan dage wajen lallasar miki shi, kin san mai hakuri da tausasawa bai iya fushi ba” na ce “to nagode, my precious."
Sai azuhur Mamie ta tashi, ta sake wanka ta zuba alkyabba tazo ta zauna ta harde kafafu a falo tana amsar sakonni, wasu cikin (pocket-computer) dinta wasu cikin waya, wasu kuma daga ‘post’ aka kawo mata yanzunnan. Ta ce Hibbani ta dafa mata abinci, bata son na Otal. Hibbani tace “tun kan ki sauko na duba firjin kichin din babu komi ciki”. Ta dubeni ta ce “jeki ki kirawo min direban nan a waje”. Na mike tsam na fita muka dawo tare dashi, tana zana masa aike kala kala, sannan ta shiga buga waya kantuna da masana’antu tana fadin abinda take bukata. Cikin minti ashirin sai ga motoci a kofar gidan suna sauke katon-katon na lemuka da kayan abinci, danyen kifi da danyen nama kilo-kilo. Da kansu suka jera kowanne a mahallinsa cikin kitchen. Na taya Aunty Hibbani muka shirya abinci sannan na shiga shirya wani na musamman tace "wannan kuma fa?”
Na yi murmushi kawai, ta ce “au to, na maigida Faruqu ne kenan? To shin yanzu Yaya zaki da Qassim, da alama bahaushen ya fimu samun shiga” na dinga dariya don ban san amsar da zan bata ba.
Na fito daga wanka kenan ina shafa na jiyo sallamar su Ya Im, hakannan na nasamu kaina da rashin jin dadin fushin Ya Faruq dani, na yi gaggawar shiryawa na fito cikin fararen riga da siket yan kanti (Nina-Ricci) na feshe jikina da turaren (final touch) na cakuda da (Mont blanc), na nade gashin kaina cikin bakin ribbon na taddasu duka a falo suna cin abinci bias ‘dining’. Kallo daya Ya Faruq ya min ya dauke kansa ya maida hankalinsa ga maganar da suke yi da Mamie, Imran ne kurum yayi min murmushi.
Mamie da Faruq suka mike, Hibbani ma ta fito cikin shiri sakale da Jakarta, Moiram kuwa tana mike akan doguwar kujera (tana fama ne da laulayin karamin ciki, don haka ta faya kwanciya). Ya dubi Imran a gicciye ya ce "yaa! Kai ba zaka bimu ba ne?” Ya girigiza kai, ya kada kafada "ina bukatar privacy da ‘yar uwata” wani dadi ya ratsani, ina satar kallon Faruq sabida kyan da yayi min cikin kananan kaya, wadanda ba al’adarshi bace sanyasu.
Ya kyabe baki yace “kai madallah, ai dama mugu shi ya san makwantar mugu, kuma mugu baya sirri sai da mugu dan uwansa…” amma a hankali, yadda su Mami da sukayi gaba bazasu jiyo ba.
Na lalubi kujerar da Mamie ta tashi, na zauna da kyar zuciyata na tafasa, na dukar da kaina ina zukar numfashi da kyar ina fesarwa da kyar. Imran ya maido hankalin shi akaina yayi ajiyar zuciya yace “kiyi hakuri da Faruq, nima bansan sanda ya koma haka ba".
Na ce “kyaleshi kawai, amma kome me nayi masa, ai sai ya sameni ya gaya min in bashi hakuri, sai yayi ta ce min muguwa, muguntar me nayi masa?” Yayi murmushi “kin yi masa mugunta mana, kin daga masa hankali. Duk nasihohin da yayi miki kika shure kika tafi, inda bai san inda kike ba. Alhalin yana shirin angwancewa. Don ko a kansa bai taba kawowa wai kinsan sunan Damagaram ba, ya ce min lokacin ya shiga tashin hankali sosai har ya kusan zaucewa. Musamman wasikar da kika bar mishi wai zaki je yin ramuwar gayya akan mahaifyarki, alhalin kina mace.
Ya ce inda kin san kina son zuwa wajen Mamie, ki tambayeshi mana? Ki gani idan bai kawo ki ba, sai kawai ki yi wasa da rayuwarki, ki kama hanyar Nijar ke kadai wannan kasada ce babba.
Haka Malam da Halima har yau basu da cikakkiyar lafiya, sabida zullumin inda kika fada da halin da kike ciki. Halima duk ta dauki laifi ta azawa kanta, domin kuwa amana malam ya bata ke. Banda BABAN KI, da akace nisan kwana ne kadai ya kawoshi yau inda muke”.
Na yi ajiyar zuciya nace cikin wata irin murya abin tausayi. “Ya Em ina BABA SA'IDU?” Ni kaina ban zaci har abada zan kuma furta wannan kalmar ba. To amma BABA SA'IDU, wani bangare ne na zuciyata, da matsayinsa ya zarta na kowa har da Mamie da Innata.
Ya sadda kansa kasa yana duban kyawawan yatsun kafafunsa yace "nima har yau ban kara sa shi a idanuna ba. Amma ina samun labarinsa wajen Faruq. Ya ce ya ji sauki har ya koma aiki. Hajiyarmu ce dai ta gamu da ‘stroke’ (shanyewar barin jiki) tun wata faduwa da tayi data samu labarin komai, sai dazu ne kawai Faruq ya gaaya mishi cewa duk muna tare anan Singapore, har Mamie, yace zasu zo Yamai su same mu. Faruq ya ce ya bari sai sati mai zuwa sabida ita Mamin wata hidimace ta kawota. Amma ni lallai kamin sati mai zuwa zan je gida, don an ce jikin Hajiya yayi tsanani sosai kuma kullum ni take kira”. Na lumshe idon cikin tausayawa rayuwar mu bakidaya nace "Allah ya bata lafiya" yace “amin” daga haka sai duk mukayi shiru, cikin rashin sanin abin cewa.
Na dago bayan wasu 'yan dakikai na dubi ya Im, cikin jin nauyi nace "Ya Im, aure fa, sai yaushe?”
Yayi murmushi, bayan ya turo hularshi gaban goshinsa ya ce "sai nayi naki da Faruq” nayi murmushi nima nace "ai ni a yanzu haka Ya Im, babu soyayya cikin al'amarina, sai kauna, kana tunanin zan iya auren mutumin da bani da birbishin soyayyarsa, ko digo daya, sai kauna ta ‘yan uwantaka?”
Ya ce “wannan shine aure, na hakikah, Zaynab, mai karko, albarka da dorewa. Amma fa ga masu hankali.
Soyayya ba komai bace, domin abu ce mai gushewa, musamman idan an kawar da sha'awar dake tsakanin masoyan.
Amma ita kauna ta fisabilillahi, itace wadda ake aure da ita, daga baya ta sayo soyayya mai ‘lasting’ har tsufa, har mutuwa. A kuma tashi ranar gobe kiyama, cike da kaunar juna.
Kin ganni nan nima ba zan taBa yin auren soyayya ba, zan yi aure ne saboda Allah, da kare kai daga dattin zina da rudin shaidan. Idan muna da rabon soyayyar, sai ki ga mun sameta a gaba. Ma’ana a gidan auren. Koda bayan hayayyafa ne.
A wurina soyayya ba komai ba ce face wani abu dake sanya zuciyoyin ‘yan adam cikin halaka, bakin ciki, nadama, tashin hankali, kiyayya, da kaka-ni-ka-yi. Duk da haka tana da dadi; so sweat, yet so painful.
Don haka ki auri Faruq da zuciya daya, ina mai tabbatar miki duk duniya bayan iyayenki da ni, sai Faruq a masu kaunarki.
Ya soki tun kina jaririya, cike da sanin (who you are). Ya cigaba da son ki a girman ki, cike da tabbacin (ba zai taba aurenki ba). Ya tsayawa rayuwar ki tamkar Uwa da Uban ki. Kuma har abada wannan itace kauna, wadda ba’a ko’ina ake samunta ba, sai mai sa'ar gaske. Ina kara tabbatar miki ba zaki taba yin dana-sanin auren Faruq ba…..!”
Na kai hannu na yarfe hawayen da suke ta zuba, nace “nima nasan da hakan, kawai ina ganin shi kamar wani Baba na ne….” yayi murmushi yace "as time goes on, zai wuce kamar ba'a yi ba. Zaynab ke mai sa'a ce; iyayen dake matukar son ki, mijin dake mutuwar kaunarki, dan uwan dake shirye da sadaukar da rayuwarshi kan duk wani mai shirin illata mutuncin ki, saboda haka ki gode Allah, ki manta komi.
Babu dan adam din da yake cikakke 100%, dukkanin mu muna da gibi a wani fannin daban. Idan Allah ya baka wannan, sai ya hana maka wancan, domin ya jarrabi imanin ka. Ina cigaba da yi miki addu'ar samun dawwamammen farin-ciki a gabadayan tsayin rayuwarki……".
Na zamo daga kujerar da nike zaune, nayi zaman rakuma agabansa. Cikin muryar girmamawa, matsananciyar kauna da tsananin ladabi nace "Ya Im, kai kuma fa?
Me kake shiryawa taka rayuwar? In gaya maka gaskiya, farin-cikina da kake ambato, ba zai taba cika ba ina ganinka haka incomplete, shattered….!"
Ya kamo hannuna cikin nasa yace "kada ki damu da ni, namiji ne, zan iya karbar rayuwar a duk yadda ta zo!!"
Sai na fashe da kuka sosai, na ce "ni dai don Allah kayi aure, ka koma gida, ka koma aikinka ko ka nemi wani. Ka nemi gafarar Baba Sa'idu, me yayi maka haka da zafi? Ni aka yiwa kuma tuni na yafe mishi, tun ma kafin in san laifin da yayi min na gayawa Innana NA YAFE MISHI, kaima ka yafe mishi in har da gaske kana son farin cikin nawa…".
Ya fiddo hankici yana share min hawaye yace "is o.k Zaynab, na yi miki alkawarin yin duk abubuwan da kika lissafa. Amma bayan kema kin daure kin nemi gafarar laifin da kika yiwa Faruq, kun koma dai-dai" na ce “nayi maka alkawari Ya Im”.
A dai-dai lokacin da Faruq ya shigo, niki-niki da kwalaye, Mamie ta biyo baya sannan Hibbani. Ya dire kwalayen bisa kujera, ya dubemu yayi dariya yace “Allahu Akbar! Mamie kin ga yadda ake hirar 'yan uwantaka, har da hawaye da majina sabida kauna" ta yi murmushi ta yi daki ta rabu da shi, shi Faruq sam baya jin kunyarta kamar ba mai shirin zama sarakuwarshi ba.
***
A cikin kwanaki hudu, duk sayayyar da za’a yi wa Haiti an gama ta, sai dai Mamie komi biyu-biyu take dauka. Mun samu hutu da nutsuwa sosai, amma duk yadda na so da in ba Faruq hakuri, ya ki hakan, ya ki saurarena. Ana I jibi zamu baro Singapore ne suna tare da Mamie a falo, suna wasu tsare-tsaren sabon gidan da zata saya a nan don tace wannan da muke ciki nawa ne, da sunana ta saye shi tun da dadewa. Na karaso na kwantar
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel