Showing 18001 words to 21000 words out of 45361 words
Chapter 7 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
bana ce ga hanyar da zan bi inje Nijer din ba a lokacin. Ta dinga salati ta ce “haka kike da taurin kai Nuratu ? To shikenan Sa’idu ya fasa aurenki, ko kece autar mata don Allah ki zuba ruwa a kasa ki sha”. Sabida haushin dana bashi daga ranar bai sake shiga sabgata ba, suka soma shirye-shiryen komawa.
A dan tsukin kwata-kwata bana cikin nutsuwata sakamakon mafarke-mafarken da nake masu ban tsoro da Sa'a, kullum sai na ganta cikin barcina dauke da jariri tana miko min ina kin karBa, sai tace “karbi abinki, kiyi gaba, in dai don wannan ne aka ce dole sai kin auri mijina”. Ni kuma sai in yi ta gudu tana bina da shi, da taga ta kasa cimmani, sai ta wurgo min shi. Yana fadowa jikina, kafin in rungumeshi, sai ya mike da kafafunsa ya bita da gudu ya rike kafafunta gam-gam tayi ta kurma ihu. Jariri fa sabuwar haihuwa don haka wannan firgicin ya maidani wata karamar zautacciya.
Babu kuma ranar da zan kwanta in tashi, ban yi wannan mafarkin ba, idan na farka cikin dare sai in zauna a tsakiyar gado, inyi ta gursheken kuka. Rannan kuka na ya tayar da Rabi, hankalinta yayi matukar tashi ta rika lallashina akan in fada mata abinda yake damuna, in dai auren Sa'idu ne wallahi an fasa, ba zata taBa yi min abinda bana so ba. Na ce da ita ni mafarkin da nake yi da Sa'a da jariri ne yake bani tsoro.
A hankali ta matso jikina ta ce cikin karamar murya "wane irin mafarki ne Nuratu?” Na fada mata tiryan-tiryan, ta yi shiru tana kallona cikin nutsuwa can ta ce "in dai zaki ji shawarata Nuratu, kin san dai bazan taBa kaiki ga abinda nasan zaki cutu ba. Sa'idu yana matukar son ki, Sa'a Malam ne ya bashi sadakarta bada son ransa ba. Ya gaya mun don bazai iya yiwa Malam musu bane amma wallahi baya sonta.
Ki kwantar da hankalinki ki fidda ita a lissafin ki, ki auri Sa'idu ina tsammanin akwai rantsatstsen rabo a tsakaninku, wanda Sa'a ke son yin sanadin salwantar dashi. Ni ban san wane irin kishi ne dake ba, ni bakya ganin kishiyoyi biyu nake zaune dasu me ya sameni? Wa kika ga ana so cikinsu yadda ake so na? In gaya miki abinda baki sani ba, matan abzinawa basa boranci ko kankani". Nace “wallahi Ya Rabi ni ba kishin Sa’a nake ba, kawai dai auren da Sa’idu ne nake jin ko za’a tsige min rai, bazan taBa yi ba. Na gwammace in shiga duniya. Amma don so har gobe babu wanda zan so tamkar sa".
Sai tayi tsai da ranta tana kallona cikin tunani, tace “Nuratu kwanta kiyi barci, lamarinki na bukatar addu'a, ina tsammanin ba haka Sa'a ta barki ba. To idan ita asiri take, ni kwana nake sallah! Aurenki da Sa'idu bazai yiyuwa ba kadai idan dama ba rubutacce bane".
Ta bani addu'oi irin wadanda Malam ke bata, tace kullum kafin in yi barci in karanta in shafe jikina.
Washegari da safe ta bani karin kumallon Sa'idu tace na kai masa, duk dai a kokarinta na son ganin mun shirya kan mu. A yau ban san me yasa kwata-kwata ban yi musu ba, karewa ma cike nake da dokin ganin sa, dana azabtu kwarai da rashin yi har tsayin sati biyu.
Dama na shirya koda bata aike ni ba, ni din zan je da kaina idan ta fita, domin tun jiya take shirye-shiryen tafiya Bindawa dubo Uwar Sa'idu da bata ji dadi ba, tace zata kai dare. Shatar mota guda Sa'idu yayi mata ya biya zuwa da dawowa tun daga Gwarzo har Katsina.
Tun safe nake jin wani irin motsi-motsi a cikin kwakwalwata, kamar ana yi min kida, haka komai nake yi ji nake kamar umartana akeyi da yin hakan. Hatta kokon dana duka zan dauka, sai naji kamar ance dani “baki zuba masa sukari ba”.
Na kuwa dauko sukari wurin gongoni hudu na antaya a kwanon koko. Na sunguma na tafi idanuna na wani irin juyawa ko hanyar dakin Sa'idun na manta, amma sai na ji kamar an kama hannuna, ana yi min jagora.
Ina shiga shi kuma kamar dama jirana yake yi, sai ya taso ya karBi kokon daga hannuna. Cikin mu babu mai iya kallon fuskar dan uwansa, ya mika hannunsa ya rungumoni ya ce "Nuratu mai-dogon-gashi yaya? Har yanzu kina nan nan akan bakanki, na bazaki aure ni ba?
To 'ya'yan da kikayi alkawarin haifa mani fa? Wallahi bazan iya rayuwa mai kyau agaba ba, in kin guje mani Nuratu...." Daga haka ya soma rabani da duk wasu suttirun jikina. Ban yi wani yunkurin ba ko kankani na hanashi hakan. Sai ma kara armasa mishi al’amarin da nayi. Don haka ba zan kirayi al'amarin da sunan ‘raping’ ba illa ‘cooperation’ na dukkannin mu”.
Ta sunkuyar da kai daga kallona, tana wasa da kyawawan yatsunta da suka sha adon lalle. Bata yarda mun hada idanu ba. Ta kai yatsunta ta dauke wasu makalallun hawaye daga idanunta. Ni kuma sai na kai hannuna biyu na rufe fuskata da karfi, na kwantar da kaina a cinyoyinta. Domin yanzu na fara fuskantar abinda ada, ban fahimta ba. Na kuma fara gane Hajiya Sa'a mahaifiyar Ya Em, itace silar shigar mahaifiyata cikin halin da ada, nayi alkwarin har abada bazan yafe mata ba.
Bata saurari sheshshekar kukan da nake yi mata ba kasa-kasa, ta cigaba da cewa “koda Ya Rabi ta dawo ranar, ta so ta fuskanci wasu sauyuka a tare da ni. Domin na koma daga kwanciya, sai kwanciya, daga daki sai daki. Data matsa min da tambaya na sanar da ita ciwon marana ke matsa min. Da yake kuma ta san yadda nake fama da shi duk wata, wani zubin har suma nake, sai bata wani tsaurara bincike ba. Illa ta hadani da kwayoyin felgin.
Wannan shine ya zamo mafari.
Daga ranar kullum da kafafuna nake fakar idon kowa in tafi dakin Sa'idu, kullum ta Allah babu fashi kamar masu ibada. A lokacin Sa'a bata gari, taje Gombe can wajen dangin mahaifiyarta. Wata irin kazamar soyayya muke aiwatarwa wadda a duk ranar dana tuna, na kan ji na tsani kaina Zaynab, inyi kuka inyi istigfari, in yi nadama in la'anci soyayyah, domin komi dai mene ne, akwai sharrin soyayya a ciki. Na samu kaina a wata irin sabuwar rayuwa, da ban taBa mafarkin tsintar kaina ba. Sa'idu ya koyar dani wata irin soyayya mai wuyar bari. Yayin da ni kuma na bada hadin kai da zuciya, gangar jiki da ruhina duka.
Kaka-tsara kaka! Kwanakin da zasu yi suka kare, suka yi shirin tashi washegarin wata litinin. Zuwa lokacin ya lallasheni na hakura da zancen auren mu, to ma idan ban hakura ba, ina zan iya barin wannan rayuwar mai gardi daya jefa ni a ciki.?
Ya samu Malam Ali suka gama magana kan cewa bayan watanni uku zai sake neman sarari ya dawo a daura mana aure mu tafi. Hatta kudin auren da wanda za'a yi min kayan aure ya barsu a hannun Malam. Ita kuwa Inna Dubu ya bata na sayen kayan sa rana.
Faruq yafi kowa murna da jin za’a yi mana aure da Yaya Sa'idu, ya ce "Nuratu mai dogon gashi nine dan zamana dakin ki" na ce “to dan dukusuru, in ba kai ba dama waye?” Sai Rabi ta bige min baki, wai bani da kunya, da kaina nake zancen aure na.
Tun komawar su Sa'idu, ban sake ganin al'ada ta ba. Ban damu ba don a wautata ai na huta da shegen ciwon dake naman hallakani duk wata. Koda yaushe muna waya da Sa'idu muna sanarwa da junan mu kewar da muke ciki. Ya kan ce “kiyi hakuri Nuratu, wallahi karatu ne yayi min zafi, ga (financial difficulty) dan kudin da gwamnati take bamu na tallafin karatu ya tasamma karewa. Dama wani bature nake yiwa aikin gidan gona yana biyana kuma a komawar nan da nayi na taras Allah yayi mishi rasuwa shiyasa abubuwan suka cude mini. Ita kuma Sa'a shegen kashe kudi ne da ita, bata barina in tara komai balle in kama maki wani gidan hayan, wannnan da muke ciki daki daya ne sai kitchen da toilet. Ga rayuwar London mai tsada sosai, ko abinci zaman kansa yake. Amma alhamdulillahi idan na hada wadannan takardun ne Masters da nike yi, Jami'ar mu sun yi alkawarin zasu bani ‘lecturing’ daganan komai zai dai-daita, don haka ni da zuwa ina jin sai farkon sabuwar shekara”.
Ko ciwon kai ban taBa yi ba, bana amai bana tofe-tofen miyau, sai dai na ji cikina yana wani tamkewa da kumbura kadan kamar sabuwar kwarya. Abinki da dagowar mace sambal. Ga kuma manyan riguna dinkin Nijar na shadda su nake zurmawa, hankali na a kwance, don ni har zuwa lokacin ban taBa kawowa a raina wai ciki ne dani ba, har tsayin watanni biyar ris.
A lokacin ne jarrabawar mu ta fito, na fito da (credentials) bakwai cif. Na yiwa malam Ali maganar inason cigaba da karatu kamin Allah ya dawo da Sa'idu, ya ce sam ba zai barni in tafi Kano ni kadai ba, inyi hakuri in Sa'idu ya dawo shi da kansa zai samar min gurbin karatu kamar yadda ya samarwa Sa'a a Ingila. Kwanaki suka shura har watanni bakwai a bayan tafiyar Sa'idu. To a wannan lokacinne fa ciki ya soma bayyana kansa.
Kafafuna suka kumbura, kumatu na sukayi sutu-sutu da yake irin cikinnan ne na samu mai bin jiki. Na bude na zama wata ingarmar mace danya shakaf. Yaya Rabi mamakinta ya kasa Boyuwa, rannan ta ce “Nuratu maganin kiba kika hadiya ne?” Da yake ita bata taBa haihuwa ba, bata san wasu alamomin ciki ba. Na yi dariya na ce “hutu ne kawai Yaya Rabi, tunda babu zullumin karatu”. Ta ce “haka ne fa, Allah dai yayi gaggawar dawo da Sa’idu mu sha biki”. Nayi murmushi.
Duk wasu al'amuran gidan na daina shiga, na koma kullum ina kuryar daki, manne da hoton abin kaunata. Shiga bandaki kawai ke fito dani. Sai dai ni kaina abun yana damuna, sabida nauyin da jiki na yayi da kumburin da kafafuna ke kara yi. Ga wani wutsil-wutsil da nake ji cikin cikina lokaci zuwa lokaci kamar mai macijin ciki. Ni da kaina sai na fara zargin kaina.
Al'amarin ya samo asali ne ranar wata talata, na fito domin yin alwalar sallar mgariba. Inna Dubu ma ta fito da butar ta ta zauna a wani kututturen icce kusa dani zata yi alwala, ni kuma na zauna bisa wani dutse. Zamana ke da wuya nepa suka kawo wata wuta mai karfi, ta dago tana yi min magana ganin yadda na gacire kugu ina yamutsa fuska na kasa yin alwalar.
Ta yi kasake! Tana dubana kafin idanunta su sauka a kafafuwana. Ta ajiye butar idanunta a jirkice ta mike, har tana tuntuBe da turmi, tayi turakar malam shi a lokacin ma ya fito zai tafi masallaci. Sai ganinsu na yi sun fito tare sunyo dakin Yaya Rabi.
Suka kulle kansu me suka ce, me suka ce Allah a’alam. Na kammala alwalata na nufo dakin sai na taras sun sa sakata. Sai na jingina da bango duk nasha jinin jikina, a sannan ne na samo jiyo sheshshekar kukan Malam Ali. Hankalina ya tashi, don ban taBa jin malam yana kuka ba, ko a sanda aka aiko mai rasuwar gyatumarsa da ke Funtua.
Ji nayi an zare sakatar, Inna Dubu ta fito ko kallona bata yi ba ta nufi dakinta, nasa kai cikin dakin Malam yana ta kuka, ita kuwa Yaya Rabi sai ta sa min ido kawai tana kallona.
Can anjima ta soma wani irin gurnani da huci kamar macijiya. Mika hannun nan da zata yi, sai ta zaro wata sharBeBiyar wuka da suke yankan naman sallah ta yiwo kaina. Ban taBa sanin Rabi nada karfi haka ba sai ranar, don kuwa daga ni ta yi cancakas ta kayar dani dai-dai lokacin da Dubu da Rakiya suka shigo suka rirrikita suna “Subhanallahi. Rabi kada ki yi kisan kai ayi nadama goma da ishirin”. Tuni ta watsar dasu ta yiwo kaina ta dora min wukar a wuya ta ce "Don Ubanki, gidan Uban wa kika je kika yo cikin? Wallahi ko ki gaya min ko in kashe ki, in yaso nima a kashe ni daki jawo min bakin-cikin da zai kaini kushewa…” Idona suka firfito ganin mutuwa muraran. Malam Ali ne yasa karfi ya kwace wukar a hannunta, sai ta sakeni ta soma kuka. Ta ce “Nuratu kin cuce ni, Allah sai ya saka min ya sakawa mahaifinmu. Ki fita daga dakina ki koma wajen wanda yayi miki cikin, bani ba ke ko a lahira kada ki ce kin sanni….
Allah ya gani Malam Ali bashi da hakkinki. Duk wata tarbiyya da ubanki mahaifi zai baki ya baki. Ya baki sani na Alqur'ani, addini dana book. Ya daura dukkan burin sa na samun nagartattun jikoki daga gareki, amma sakamakon da ya samu daga gareki kenan, ki tashi ki fita, ki tafi duk inda zaki bana son ganinki…….” Malam Ali ya tsagaitar da hawayen idanunshi, ya kirayi sunan Allah nutsuwa ta zo mishi, cikin lallashi da kwantar da murya yace
"yaki Nuratu!”
Jikina in banda tsuma ba abinda yake, hankalina ya tashi, tsigar jikina gabadaya suka tashi. Na soma rokon Allah ya dau raina da wannan abin da nake ji. Na roki Allah ya dau raina kafin furucinsu ya zama gaskiya.
Na ja jiki na rarrafa gaban Malam Ali, hawaye ko dis basu diga daga idanuna. Lallai ne da ake ce wani tashin hankalin yafi gaban kuka.
Idan ya tabbata cikin ne da gaske a jikina, ni Nuratu yaya zanyi da rayuwata? Cikin zuri'armu kaf, babu wanda ya taBa yin wannan abin kunyar. Abar ma ta kunyar duniya mai sauki, to kunyar lahira fa, da tsaywa gaban Sarki Allah!
Sai a lokacin al'amarina da Sa'idu ya soma dawomin tar-tar. Tamkar wadda ta warke daga shafewar kwakwalwa (lose of memory). Shin ya aka yi ma har na bari hakan ta faru da ni? Ya aka yi na bari soyayyar Sa'idu ta rufe min ido har hakan ta faru? Ni Nuratu na yi asara! Haka Sa'idu ya cuce ni!! Duk wata soyayya da nake masa na nemeta na rasa. A karo na farko na ji na tsaneshi, na tsani kaina na kuma tsani soyayya a rayuwata.
Malam Ali ya lura na koma kamar mutum mutumi, ya tabbatarwa kansa ni kaina bansan cikin ne dani ba. Dubu da Rakiya duka sun hada tagumi, sai gumi ne yake yanko musu. Yaya Rabi kuwa kuka take kashirBan, irin wanda ban taBa ganin ta yi ba a rayuwarta, har kuwa lokacinda aka anar da ita rasuwar mahiafin mu, kuma ba abinda zai sa, ba abinda zai rage.
Ba abinda yafi damunsu a lokacin kamar mutuncin Malam Ali a idanun jama'ar Gwarzo. Ba karamin abun kalubale bane a ce haka ta faru a cikin gidan sa. Malam Ali shahararren malamin Alqur'ani ne, da babu ya shi a garin Gwarzo, haka halayensa da tsoron Allah irinnasa, sun zamo ababen koyi ga duk wani da ya kwana ya tashi a Gwarzo.
Su kenan. Ni kuwa tunani na ai rayuwata bata da sauran amfani; 'ya mace nike, wadda wannan tabon bazai taBa goge mata ba, har 'ya'ya da jikoki. Maganar tunanin aure da Sa'idu ma kwata kwata bana yinta, na shafe ta kamar yadda ake shafe mataccen abu a doron kasa. Yo wane aure kuma bayan abinda ake yiwa auren an gama samunsa a titi! Mutunci ya zube, ganin GIRMAN juna YA FADI! Sai a sannan ne na samu wasu hawaye dunkulallu, suka mirgino a kundukukina.
Na kai bayan hannu na ina sharewa, a yayin da dan cikina ya shiga wutsil-wutisl! Cikin koshin lafiya, da tuna min yana jin yunwa. Na runtse ido da karfi, wai ni Nuratu ce yau zan haifi SHEGE! Wannan tunanin kadai ya kusa sani in fita a hankalina.
Cikin tattausar murya Malam Ali yace "Nuratu cikin jikin ki na wane ne?” Babu musu, babu ja’in’ja, babu jinkirtawa nace "wallahi Malam, Sa'idu ne!".
Sai ganin Yaya Rabi mukayi ta yanke jiki ta fadi. Malam ya fita da gudunsa ya debo ruwa yayi bisimillah ya shiga yayyafa mata. Tun daga ranar ta koma wata shiri-shiri, ba mai hankali ba, ba taBaBBiya ba. Kullum sambatu ta ke da Sa'idu, da cin amanar da ya yi mata, da take cewa har abada ba zata yafe masa ba!
Tun daga ranar ko nan da can ban kara lekawa ba. Bayan kunyar Malam Ali da sauran mutane, ina jin kunyar Ubangiji na. Abinci sai Dubu tasa ni a gaba da fada kamar ta duke ni, sannan zanci kamar ina taunar madaci. Fassara halin da zuciyata ke ciki ma a wannan lokacin ba zai yiwu ba. Dubu ce ta tsaya tsayin daka wurin ganin cewar na dage da yin istigfari, da kuma Innalillahi… domin samun gafara wurin Ubangiji da sauki acikin kwakwalwata.
Ban taBa ganin kishiya irin Inna Dubu ba, har inda nan ke motsi. Zuciyarta me kyau ce, kudurinta na alkairi ne ga kowa. Itace tace abar maganar nan a
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel