Showing 12001 words to 15000 words out of 45361 words

Chapter 5 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt

har suka haife ni ba. Tabbas da bata dinga aibatani akan su Hassan ba. Da bata dinga yin fariyar "su da gidan Uban su ba". In haka ne akwai sauran kallo a gaba. Domin kuwa ko ba-dade, ko ba-jima, sai na je na tsaya a gaban Hajiya Sa'a, na gaya mata ko ni WACE CE? In tabbatar mata da cewa BARAROJI kuma SADAKA YALLAH 'yace ga V.C Professor Sa'idu Bindawa.
Na kai hannu na shafe hawayena. Idanuna ya kai ga shafin karshe, wanda ya warware min rudanin da zuciyata ke ciki, na kokonto da tunanin ina zan dosa? Wa nake da shi a halin yanzu da ya wuce Baba Sa'idu?
Wani farin ciki ya ziyarci zuciyata, ban san sanda fatar bakina ta suBule da murmushi ba, naji kamar an dauke min wani nauyayyan dutse ne aka. To amma ina da tabbacin in sun san ta hanyar da 'yar tasu ta haifeni, zasu yarda su karBeni a matsayin JININ SU har su bari in zauna a cikin su? Inada tabbacin in sun san cewa ita kanta 'yar tasu, gudu tayi ta barni, tun ranar data haifeni don tsira da mutuncinta, zasu yarda su karBeni?
Wata zuciyar tace " na Allah basa karewa Zaynab, a ko'ina ba'a rasa na Allah, irinsu Ya Faruq da Yaya Halima, wadanda tunanin su ya sha banban dana sauran mutane, ra'ayin su ya banbanta dana sauran al'umma. Su irin wadannan mutanen kamar wasu mala'ikun Rahma ne da Allah ke saukarwa bayinsa masu matsala irin nawa. ‘They are just like angels in the midst of people' wadanda suke a shirye da sadaukar da kansu domin farin cikin wani.
Wannan ne ya kara sani dubar rubutun da nayi shekara daya da wata daya da ya wuce, daga bakin Inna ta;
"Kyauta mu ba baroroji bane, sune 'yan kasarmu dake daji, mu 'yan kasar Nijar ne, 'yan usulin wani gari Damagaram, amma iyayen mu da 'yan uwan mu a babban birni Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can”.
“In kika shiga Niamey, kika ce kina neman wani daya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan.."
Don haka na cusa littafin cikin jakata, na kishingida ina jiran garin Allah ya waye in kama hanyar kasar Nijar neman dangin Innata, in gaya masu rasuwar ta, in rokesu alfarmar su barni in zauna tare dasu, ta hanyar cewa ni ‘yar ta ce. Kamin a hankali in nemo Imran, inyi masa aure da Adda Mami, daga nan nasan ina da Uban da zai rikeni ya kuma cigaba da yi min addu'a ko bayan raina. Wato in zauna tare da shi da iyalinsa muddin rayuwata.
Na dauko wasikar da na rubutawa Ya Faruq, na sake binta a nutse, ko akwai wani gyara a ciki? Na tabbatar, babu. Ga abinda na rubutawa dan uwana rabin jiki UMAR FARUQ;

"Ya Faruq .
Zuciyata ta kasa amincewa da wai in cigaba da zama da Yaya Halima, bayan sanin ko ni wace ce?
Gangar jikina ta kasa amincewa da kai wai a matsayin miji, domin tana ganin baka cancanci hada jiki da kazamtacciya kamata ba;
You are pure as a clean glass, and I'm a green, but rotten leaf. Har ila yau, zuciyar ta takasa yafewa Nuratu da V.C Sa'idu, don ni ba zan taBa kuma kiran sa ‘Baba’ ba, ba zan taBa iya kiranta ‘Inna’ ba. Don haka na tafi, inda a hankali nake tunanin zan samu labarinta.
In tambayeta dalilin shegantani da tayi, ta kuma nemo min dan uwana a duk inda yake cikin duniya a dalilin bakin cikinta. ‘I know it will hurt, but you donno how deeply it hurts the victim’. Faruq ka yafe mani, ka yi mun godiya ga Innarmu, ina nufin (Inna Dubu).
Ina fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa".
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Ta ce “eyi mana, baki san makauniyar matarnan tana da alaka ta jini da ita ba? Amma da yake mai bakin kashi ce bata tara komai daga gareta ba, sai dai ita ta dauki nata takai mata" nayi dariya a raina ina kara jin tsoron mutane, dubi yadda Maman keta kareta daren jiya a wurin danta, kada ya koreta, amma ita yanzu gashi tana zaginta.
Tace "unh, bari dai inyi shiru da bakina, don kema dai naga kina yanayi da su, ko dai 'yan uwanki ne? Kada inje ko shuka ke nake a idon makwarwa”.
Nayi murmushi nace "mutane da yawa sun fadi haka tun shigowata Damagaram, kin san akan samu haka, baka san mutum ba amma sai kayi kama da shi, ni daga Nijeriya na ke". Ta jinjina kai cikin amincewa.
Can an jima na sake tambayarta "ko 'ya'yan Nuratu nawa?" Ta sake jinjina kai cikin jimami tace "abin tausayi da wannan baiwar Allah, bata taBa haihuwa ba. An je turai anje Paris an dawo jiya I yau. An kwakwale mahaifa an tsageta an wanke, ko kan 'yar tsana, bata haifa ba. Yanzu kam ta dangana, sai dai tana rikon 'ya'yan kannen mahaifinta, kuma duk ita keyiwa ‘yanmatan zuri’ar su aure, ko kwannan ta aurar da guda biyu a Chadi. Gidansu babban gidane mai dadadden tarihi a Damagaram, don haka ba zaki taBa gane bata haihu ba".
Wasu zafafen hawaye suka zubo min, na yi saurin dauke su da 'yan yatsuna, a raina ina cewa su masu abin kunya ai haka suke, da sanya rigar mutanen kirki, son kai da rashin tunawa da wanda ya zame masu dole, balle halin da yake ciki. Sai wanda ba dolen su ba.
Inna na yanzu tana can ta zama kasa da turbaya, da tunanin inda take, da halinda take ciki. Itako tana nan tana cin mulki, wasu na can cikin bakin-ciki da kuncin rayuwa duk a dalilinta. Danadam kenan, mai ban mamaki.
Muna karya kumallo amma hankalina sam-sam baya tareda ni, yana ga tunanin labarin dana samu ayau na Nuratun Inna Rabi, ganinki yafi jinki. Ya janye ido ga jaridar da yake karantawa, wadda ke rubuce da harshen faransanci yana kallona.
Na kurawa kyakkyawan hotonta wanda ya zamo (cover) na jaridar idanu ta baya, bana ko kiftawa. Tana magana akan (racial discrimination) na farare da bakaden abzinawa, tana nasiha akan su rungumi juna su daina wariyar launin fata a tsakaninsu. Duk yadda naso ta daina burgeni, na kasa, amma hakan baya nufin zan fasa kudirina a kanta.
Ya ajje jaridar ya tashi kamar mai dauko wani abu cikin madafi (kitchen), wannan ya bani damar daukar jaridar na rubuce adireshin gidan jaridar dake jiki cikin (address book) dina da lambar waya. Ya dawo a dai-dai lokacin da na aje jaridar inda take, na kuma zuge katuwar jakata bayan na jefa dan littafin. Ya dubeni yayi murmushi yace "Hajiya babba da jaka, me zamu ne a cikin jakar?” Nima na mayar mai da murmushin yake na ce "kawunan Damagarawa ne nake tarawa a ciki” ya yi dariya ya buga kafarsa daya a carpet yace "kin san Allah, kawunan mu ba (common) bane sabida GIRMAN su, kyawunsu da ingancinsu sunfi karfin shiga jakar bako" na ce "sai ta dan gari?” Ya basar da zancen yace “in na fita yau sai asubah zan dawo, ko kina bukatar wani abu in taho miki da shi?” Nace “babu abinda nake bukata, sai kudina da zan baka kayo min canjinsu da saifa" yace "to ni in baki mana? Ki bar naki in kin koma Nijeriyarku, jaga-jaga, su yi miki amfani?” Na ce “zan yi godiya kuwa, idan har kayi hakan". Bai fita ba sai da ya aje min damin Niger-Saifa. Bai dade da fita ba na dauko bakin niqabina na maka, na fito rataye da jakata. Laliya na gani na ta zura kitchen da gudu wai na bata tosoro, meye wannan? Na wuceta zuwa dakin Mama na gaya mata zani gidan Radio in sa cigiyar amma ba dadewa zan yi ba, ta yi addu'ar fatan alkairi ta ce in dauki Liliya muje tare kada in bata, na nuna mata babu damuwa ai shata zan dauka daga nan bakin titi da zai kaini ya dawo da ni har gida.
Na tari Taxi na nuna masa dukkan adiressikan da zai kai ni, daya bayan daya, ya jira ni in fito sannan ya maidoni, in mun dawo sai muyi balance. Da haka ya ja motar muka mika gidan talbijin na jihar Damagaram, ban sha wahalar samun ganin shugaban gidan talbijin din ba kuma da yake yana jin turanci sosai na gaggaya masa abinda naga dama. Karya da gaskiya harda shaci fadi, har da cewa a gidan marayu na tashi. Da fari ya nunamin ba zai yarda ba, domin bani da hujja. Na daga nikab dina muka yi ido hudu nace “ga hujja ta".
Ya dade yana kallo na, ya tabbtar wannan (photocopy) na Nuratu ne a gaban sa, wadda duk duniya ta yarda bata da kwan haihuwa a doron kasa, ai sai ya dauki camera ya dora min ina turancina tiryan-tiryan, wani ma'aikacin gidan talbijin din a gefena na fassarawa. Suka sallameni na fito muka karasa babban gidan Radion kasa wanda keda reshe daga babban birni Niamey. Gidan jarida kuwa da naje ai abin nema ne ya samu, wai matar dan sanda ta haifi Barawo, labari da dumi-duminsa;


"Mainasara ta haifi 'ya ba aure a Nijeriya, shekaru goma sha takwas a baya. Ta guda ta barota da rayuwa gidan marayu duk wannan tarin arziki da Allah yayi mata. A yau ga yarinyar tazo da kafafunta, tana neman mafaka a inuwar Gwamnatin Damagaram domin daga can inda take aure a Nijeriya an koreta, a sabili da ganewa da iyayen mijin suka yi ita shegiya ce…. Ga kuma wanda ya karyata, to yazo ofisoshinmu mu hadashi da yarinyar suyi Magana baki-da-baki, budurwa 'yar kimanin shekaru sha takwas, wadda a kamanni da zubin halitta bata da maraba da Mainasara…”.


Na dawo gida a gajiye likis, da yamma lis. 'Yar gyatuma tana zaune a gaban allon talbijin ta bude kunnuwa tana saurare, na yi mata sallama amma bata amsa ba, bakinta sai kumfa yake tana masifa cikin abzinanci, da zage-zage cikin harshen hausa, tare da mikewa ta laluba ta angazo talbijin din daga mazauninta jikake taratsatsatsa…!
Talabijin din ta soma fidda wani irin hayaki. Laliya dani muka zura da gudu muka zare soket din daya soma cin wuta, ta fadi kasa tana kuka tana birgima tana cewa "duk wanda yayiwa Nuratu wannan sharrin sai Allah ya saka mata, siyasar banza, in banda siyasa mai bankadar da mutunci, wa ya isa ya yi mata haka…?” Haka muka kwana a kanta ba yadda take, gabadaya ta birkice mana kamar mai tashin jinnu, tanata jan Allah ya isa da Li'ilafi ga wadda aka hada baki da ita akayiwa Nuratu sharri, ba zata taBa yafewa ba'
Da asubahin fari ya shigo gidan, ya tadda gyatumar sa cikin wannan hali. A kidime ya dagota daga gado ya rungumeta yana tambayarta abinda ya faru, sai cewa take ita dai ya kaita Niamey. Ya dubeni cikin tashin hankali "wai don Allah me ke faruwa ne Zaynab?” Na jinjina kai kamar gaske "tana magana ne cikin French, bansan me take cewa ba”, ya dauketa muka tafi asibiti aka bata gado. Aka zurkuda mata allura ta samu barci sannan ne muka kamo hanyar dawowa don tafiya da abin bukata.
Akan hanyarmu ta dawowa daga dauko kayan amfani ne ya kunna radiyon mota, abinda ya fara ji shine, an dakatar da Nuratu Mainasara daga takarar gwamnatin Damagaram a karo na biyu. Tare da koro bayanai dalla-dalla, daki-daki, wannan kuma Oda ce daga kotun kasa (Federal High Court) a turance, har sai sunyi kyakkyawan bincike akan al’amarinta, daga tsarin mulki ne littafi kaza, shafi na kaza sakin layi na kaza. Mai tabbatar da haramcin mutum mai tsohon laifi daga shugabanci.
A nutse yake sauraro, babu alamun razana a tare dashi, niko wani gefen daban nake kallo gabana na dakan tara-tara ba uku-uku ba. A hankali naga bakaken gilassai suna maye gurbin farare a cikin motar. Ya fiddo bakin gilashi mai duhu sosai ya saya fararen kwayan idanunsa. Da na juyo na dube shi don neman karin bayani, game da canzawar glassai, sai da nayi nadamar juyowar. Gabadaya ya rikide zuwa wani irin mutum mara imani, mara kyawun gani, tamkar bai taBa dariya ba. Hatta kalar fatarsa sauyawa tayi, daga ja zuwa ‘yellow’, a hankali cikina ke bada sauti “Kululuuu…!”


Ya sauke motar a gefen titi tsayin mintina biyu kansa na sunkuye bai ce komi ba, ni kuwa tuni na cure na dunkule wuri guda kamar kashin awaki. Na ji wani abu yana zungurina a wuya, juyawar nan da zanyi sai na yi arba da hancin 'yar karamar bindiga da nake gani cikin fina-finan Amurka ‘revolver' a dokin wuyana. Ya rausayar da kai gefe yace "hmh, tell me, who are you?”
Nayi narai-narai da ido, ina yi masa kallon (ka tuna alkawarin daka yi mun kafin in bika cikin gidan ku? Ka tuna alkawarin da kayi mun na ba cuta ba cutarwa a tsakanin mu? Ka tuna alkawarin da kayi mun na zamowa dan uwana na jinni?)
Ya gyada kai sama, tamkar ya san me nake tunani yace "imagine you ‘ve never set eyes on me, let us draw to my profession….. " ya fiddo katin shaida (ID card) ya manna min a ido "State Security, Qassim Mainasara".
Maimakon inji tsoro, in amsa masa tambayarsa, kamar yadda yayi tsammani, sai na yi murmushi na dubeshi cikin bakin (dark-glass) dinsa, na ce “ai ba tun yau ba, na san kai (SS) ne, kaine dai baka san ko ni wace ce ba. Duk da kasancewar naka mai binciken kwakkwafin dake alfahari da aikin sa”. Ya ce cikin muryar razanarwa "shine nake tambayarki who are you? Ko kinsan wadda kika zo kika yiwa sharri, kika bata mata suna wace ce a gareni?”
Na taBe baki nace "tarwatsa kwakwalwata kawai ka daukar mata fansa, ban san wace ce dinka ba, ba kuma na son in sani. Burin da nazo da shi kasarku a yau, ya cika, don haka ko a yau rayuwata ta kare ALHAMDULILLAH!”
Yace “kin isa ki mutu, ba'a tagayyaraki an tara maki gajiya a Damagaram ba? Shirmen banza kike, kin dauka wannan shirmen ne zai cika burin naki? Sai ince kuruciya na dibar ki, amma Aunty Nuratu ba sa'ar yin ki ba ce, ke har wadanda suka kulla miki karyar su ta sha karya su ja da Mainasara, domin ita dashen Allah ce, ba dashen mutum ba."
Na ce "shine nace ka tarwatsa kwakwalwata da harshashin bindigarka, sannan ne zan yarda da kaunar daka ke mata. Suna kam na riga na Bata mata, wadanda ma basu yarda ba in na fito a gidan talbijin suka ganni a zahiri zasu yarda, sannan kotun kasa dake shirin yin bincike don tabbatar da zahirin maganata zanje su debi jinni na su auna…” yace “…. over my dead body! A bayan raina ba, amma in har ina raye, bazaki kuma zuwa wani gidan talbijin ba, masu diban karya da gaskiya sabida su jahilai ne irin ki, sai dai in mika ki ga al'ummar gari su jefe ki, su kacaccala wannan fuskar da kike tinkaho da ita mai kama data Aunty na…."
Nayi murmushi cikin komawa kallon wautarsa, ga gaskiya kiri-kiri yasa kafa yana takewa da gangan don son Auntynsa, nace “kai ni tsakiyar gari Qassim, a yagalgala fuskana mai kama data Auntynka" ya ce “ai idan na yi hakan kuma ban kyauta mata ba, don na tabbata zata so ganin wace jarumace ce ta aikata mata wannan sharrin? Don haka daga nan, Niamey zan kaiki, koda akan iska ne.
Ki je gabanta ki maimaita abinda kika fadi, in har kin cika mai tsaurin ido da jarumtaka….” Ya figi motar da gudu sai filin jirgi, ya kulle ni a cikin motar ta ko’ina yadda ko ihu zan yi ba mai ji na, ya fita. Bai san cewa ko a bude ya bar kofar bau inda zan je ba.
Nidai tunda burina ya cika, ina maraba da kowacce irin rayuwa ce ta sameni a gaba. To don ya daukeni ya kaini gabanta sai me? Iyakaci tasani a inji, ta markade, ko jama'arta su harbeni da bindiga sai me? Bani da wai sauran ‘hope’ a rayuwa sai na fatan cikawa da imani.

Haka kawai kuma naji hankalina ya tashi, bugun zuciyata ya tsananta, wasu irin hawaye kuma da bana ce ga dalilin su ba, suka zubo mini, na nadama ne koko na dakacen me kenan na yi? Me yasa nayi haka? Ban kyautawa Innata ba. Nasan duk inda take a yau tana cike da Bacin raina, ban ji maganarta ba, banyi amfani da gargadinta ba ko daya.
Ramuwar gayya bata dace da dan musulmi ba, musulmin kwarai afuwa yake da rangwame cikin al'amarinsa. Ramuwar gayya da daukar fansa aiki ne na yahudu da nasara, wadanda basu yarda Allah ke shiryawa bawa rayuwa ta duk yadda ya so ba. Gaskiyar Yaya Halima ne bacin rai zai sani fita a imani na, zai rauna imanin da nayi da Allah guda daya, shine mai sakamako, da bin hakikin wanda aka zalunta.
Babban abin takaicin ma ga UWA, wadda ta dauki nauyina cikin mahaifarta wata tara ras, ta haifeni bayan mawuyanciyar nakuda da Allah kadai yasan adadin azabar dake cikinta.
Idan kuma an bi salsala Nuratu

24, May 2025
Ibrahim

Thanks alot for the best novel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login