Showing 33001 words to 36000 words out of 45361 words

Chapter 12 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt

da yaronsu Imran kamar Faruq, a cikin gidannan aka yanka ragon sunan sa………"
Na dora dukkan hannuwana aka na kwarara ihu, nace "Wayyo Allah! Wayyo Babana….."
A take na fadi a wurin na suma. Wuni nayi bana cikin hayyacina, koda na farfado surutai kawai nake barkatai ina cewa "Sa'idu ka cuce ni…. ka yaudareni sai Allah ya saka mani……"
Sai bude ido nayi na ganshi tsaye a kaina, rike da hannayena da suka yi sanyi kalau. Yana murmushi kamar a mafarki naji shi yana cewa "ban cuceki ba Nuratu, ban yaudareki ba. Yaya za'ayi in yaudari abinda nafi so fiye da rayuwata? Shine me, don inada mata, sai aka ce Allah ya haramta mani yin aure uku a gaba?”
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na fiddo ido cikin kaduwa, ta yi murmushi ta girigiza kai cikin tabbatarwa,
“Zaki iya tuna ranar da kika hawo Acaba daga makaranta? Motar da nake ciki tana biye dake, har kofar gidan. Imran da abokinsa suna tsaye jikin mota, da alama daga ke har shi ranku a Bace yake, don duk kuna ta hararar juna, kika shige cikin gida baki kula su ba. Sannan naje makarantar ku watarana inada daga cikin mota mai duhun gilassai, ina ganin ki da wata malama, Kabila, a zaune bisa benci a bayan ajin ku, kun dade kuna magana da bansan me kuke cewa ba kina ta kuka. Sai na ji hankalina ya tashi, don abinda na kawoma raina kawai Sa'a ce take takura miki.
Na yi wa Faruq magana yace kwata-kwata ba haka bane, shima ya lura a kwanakin kina cikin damuwa, watakila sabida tafiyarshi Singapore ne. (Ni na samo mishi makarantar ba tare da sanin ku ba, ba don komi ba sai don jin Sa’idu ya samarwa dan shi aiki mai tsoka shi bai samu ba, to ashe gajen hakuri nayi, don ba’a fi sati uku a tsakani ba ya sanar dani shima nashi aikin ya fito a Bankin Nijeriya (central bank) a lokacin komi na tafiyar ya rigaya ya kammala, sai ya zabi tafiya karo karatun akan aikin) yace amma Hajiya Sa'a babu ruwanta da ke, sannan ne hankalina ya kwanta.
Faruq kafin ya tafi Singapore ne ya zo Damagaram ta jirgi, na yi masa kyakkyawar tarba a gidana (Govt. House Damagaran), ya kawo min wadannan zobban naki na (Sepphire) da kika bashi ajiya, tsayin shekaru goma, yace “halin rai, komi na iya faruwa”, sai na ce “balle ma insha-Allahu zaka je ka dawo lafiya, sannan komai na Zaynab ai naka ne”. Na dade ina bashi takardun kadarorina da shares gami da takardun wani gida dana dade da saye a Paris, duk da sunanki. To duk ranar sai ya tattaro ya dawo min dasu, jikinsa a masifar sanyaye yake. Na ce "Faruq zaka tayar min da hankali. In hakane ka fasa tafiyar mana, ka kama aikinka?”
Yace “nima dole ce zata sani tafiyarnan Yaya Nuratu, akwai dalilina na zaben karatun akan aikin. Al'amarin yana neman kwaBewa; ZAYNAB IS DEEPLY IN LOVE WITH IMRAN, and I cannot tolerate it". Nace saboda me?”
Ya sunkuyar da kai cikin matsananciyar kunya da fidda rai, yace "don nima ina sonta".
Nayi murmushi na ce “kawai kace Zaynabu ta kusan nemana da kafafunta, ta kusan biyoni mu zauna tare. Shine me don tana son Imran, ba dan uwanta ba ne?”
Ya zazzaro ido yace “baki gane irin soyayyar da nake nufi ba, soyayyah, ta soyewa fa Zaynab kewa, Imran?”
Na tuntsire da dariyar data kara kular da shi, nace “so what, wanene mahaukaci tsakanin Sa'idu da Malam? Ka kwantar da hankalinka, inshaAllahu Zaynab bata da miji sai Umar Faruq".
Sai yayi murmushi. Na kuma cewa “ka yarda dani, am her mother, kwanannan zata biyo ni cikin tsana da kiyayya, and am ready to welcome her (a shirye nake da in karBeta) da duk wacce ta zo". Ya ce “ni nasan Zaynab bazata yi miki da dadi ba. Kuma tafi son Babanta a kanki, idan ta gane shine Babanta, bazata gujeshi ba, amma ke baki da uzurin da zata karBa, she is quite strict (me ra'ayin rikau ce) ba zata taBa karBarki a matsayin Uwa agareta ba…..”
Na lumshe ido cikin jin zafin kalaman shi, na budesu a kanshi na ce "sai dai idan BANI NA HAIFE TA BA". Da wannan Faruq ya tafi".

Ta yi shiru tana murmushi, nima murmushin nake kamar gonar auduga, cike nake da kunyarta kuma. Ta dago haBata tace "to Zaynabu 'yar Babanta, kin ji kowace ce Nuratun da kike zagi…. da gaske ne ba zaki taBa karBata a matsayin UWA a gareki ba….????”
Nayi azama, na rungumeta, ita ma ta rungumeni, sai hawaye sharr! sharr!! Daga idanun kowannen mu. Na ce “ki bar fadin ina zaginki, waye zai zagi mahaifiyarsa? Sai mai nemawa kansa masifa. Na koyi wani abu ne daga Ya Im, na rashin Boye abinda ke cikin zuciyata, koda zai Batawa mutum, zan ji dadi idan na amayar da shi. Allah tun daga jin sunanki a bakin Innata, nake kaunar ki, nake begen in ganki…kawai ina yakar zuciyata ne da yin hakan, sabida haushin ki da nake ji akan Innata…"
Na zame daga gefen gadon, na kwantar da kaina a cinyoyinta, gwiwoyina bisa kafafunta nace
"ki yafe mini".
Ta kai hannunta cikin lallausar sumar gashin kaina, tana shafawa a hankali ta ce "ya wuce Kyautar Inna, nima ki yafe mini, Allah ya yafe mana bakidaya”.

BAYAN WATA DAYA
Yadudu, Hajiya Azzo, Hibbani da Moiram matar Baffa Aliyu, suna zaune falon Nuratu suna tattaunawa akan tafiya sayayyar kayan auren Haiti da za'a tafi Singapore.
Na fito daga daki rike da shaddodi guda biyu 'yan Mali, yellow da brown dinkakku dukka dinkin Mali na manyan riguna. Nace "Nuuratu wanne zan saka?” Ta dago ta dubeni tace “sanya wanda duk yayi miki, ai na Nuratunki ne". Hibbani tayi salati tace "wannan ba kayanki bane?" Yadudu ta muskuta ta ce "umh, Zaynabu me kika ce? Sunan Uwar taki kike fadi gatsar-gatsar?” Na juya daki da gudu ina dariya, in ajiyo Aunty Hibbani tana cewa "yanzu saboda Allah Nuratu kaya daya kuke sawa? Ai sai ku sa a samu a jarida, wannan ai tsiya ce" ta yi dariya tace "nayi-nayi ta bari taki dainawa".
Na fito shar da ni cikin yellown shadda babban riga da zane da dan gyale. Wuyana da kunne na cikin ‘emirald’ rike da karamar jaka, na coge a bakin kofar dakin barci ban shigo cikin falon ba na yi kan-kan da ido, ina murmushi nace "Nuratu.., au Mamie…, yaushe zamu je ki sayo mini kayan?” Ba tare data juyo ta dubeni ba, tana fuskantar Hibbani, tace “sai ranar da nayi arziki, har yanzu bani da arzikin da zan saya maki kaya…."
Na karaso da gudu na rungumeta nace “haba-haba Mamie, ni da ke bata Baci.. " Hibbani kallon mu take, muna burgeta, ta yi murmushi tace "kyaleta ki shirya tare dake zamu tafi Singapore, siyayyar kayan auren ‘yar uwarki, daga nan sai ki sawo duk duk abinda kike so" nayi tsalle na makalkaleta.
Qassim ya shigo cikin shiri har da trolley dinsa, kamar hadin baki mun yi ankon yellown kaya, sai dai shi shet ce yellow da bakin wandon Jeans, idanunsa akaina ya dubi Mami yace "Aunty ni nayi harama, zan koma bakin aiki” tace "to Qassim, Allah hokku sa'a”.
Ya dubeni yace "inye, su bera anyi kilin, to a zo a yi mun rakiya ‘airport’ mana? Irin wannan kwalliya bai kamata ki dankare a gida ba” nayi murmushi (tun ranar da muka fahimci ‘yar mace, da dan namiji muke, muke bugawa), ba don komi ba nake bude baki ina ramawa ba sai ma don kada zancen Haiti ya tabbata, wato ya furta min soyayyar da ya dade yana Boyewa. Gashi a yanzun ta gaza Boyuwa ta fito karara cikin fararen kwayar idanunsa. Na ce “ba dole in yi kilin ba, ko na dinga razana matar ka, tana nan-nan- da ni ba?”
Haka muka fita muna tayi, suka bimu da kallo cikin jin dadi. Muna fita Yadudu ta soma furzar da abinda ke ranta, wanda ya taso da ita takanas tun daga Damagaram, wato burinta na a hada mu aure da Qassim, babban abinda ya faranta mata kuma shine fahimta da tayi yanzunnan muna son juna.
Shiru tayi bata yi magana ba, amma su Hibbani suna ta sawa abin albarka.
Muna bayan motar Nuratu Roll-Royce wadda (personally) ta hawanta ce ita kadai, ni da Qassim, sanyin raBa na ratsamu. Direban Mami na jan mu. Ya lumshe ido ya kwantar da kansa a bayan kujera cikin damuwa. Hasken hantsi yana haska bakin gashin kansa, wanda ke kwance lub, a wuyansa sai sheki yake kai ka ce ‘shampoo’ yake yi, amma wannan halitta ce. Qassim jajur yake fiye da ni, kamar ka taBa jini yayi tsartuwa, ga kuma yanayi irin na arzikin da hutu sai suka taru suka mai dashi kamar wani balaraben Kuwait.
Ganin damuwar da yake ciki duk sai nima na ji na damu. Nace "yaya ne my Qassim?” Sai ya bude idanunsa da suka kankance, cikin mamaki yace “don Allah sake fadi, 'yar kanwalle?” Na harareshi nace "wannan ne kuma baka isa ba…" maganar ta makale a makoshina, ganin irin kallon da yake yi min cikin kwayar idanun shi, da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, jikina yayi sanyi, ya mace murus. Na sadda kai ina wasa da yatsun hannu na dana kawata da jan lalle, tun sanda na fahimci yana daga cikin abinda Mami ke ado da shi, yake kuma kara maida ta cikakkar mace, nima na dimance shi.
Yayi murmushi yace "wannan (pretending) din naki, bashi zai hanani furta maki abinda bakya so in furata ba, Zaynab ina sonki, ina kaunar zamowarki abokiyar rayuwata a tun ranar da na fara haduwa dake, tun kuma kafin in ganki. I love you in your veil (na sonki cikin niqabinki) kuma na so ki yau a zahirin ki. Mene ne amsar ki? You are no more a child now (ke ba yarinya ba ce a yanzu) nasan tuntuni kin fuskanci inda nasa gaba, sai dai ban san dalilin da yasa kike basar da ni da gangan ba”.
Na yi shiru banyi magana ba, a dai-dai lokacin da direban ya karya kan motar muka shiga cikin airport, ya tsare ni da ido cikin jiran amsa. Na bude murfin motar zan fita, ba tare da nasan amsar da zan bas hi ba, cikin wata rarraunar murya ya ce
"May be am not good enough to be your husband)……”


Na juyo cikin mamaki nace "me ya sa kace haka?” Jinin mu daya, tushen mu daya. Sannan kana da wani matsayi mai GIRMA a gareni, domin kayi mun abinda har in koma ga mahalicci na, bazan taba mantawa ba.
Kai ne ka hada ni da mahaifiyata, kaine silar cikar farin cikin rayuwata, wanda ban taba tunanin zan tsinci kaina ba a tun barowata gida…." “akwai wani matsayi da zaki bani Zaynab, daya wuce na zama mijin ki?” Ya katseni. Na girigza kai “baka gane bana Yaya Qasim, ba zan taba yin auren soyayya ba…...”
Idanuwansa sunyi nauyi sosai, da kyar yake iya bude su yace "….well-well, sai wane iri? Kodayake na gane; you are a multi-millonnaire, waiting for a billonnaire like you…. (ke miloniya ce, kina jiran biloniya dan uwanki), haka ne ko ba haka ne ba?”
Ya tsatstsreni da idanunwasa da suka kada suka yi jawur. Na soma tababar ko Qassim ya sha kayan maye ne? Kai, babu kama, tunda nake a gidan su ko taba, sigari, ban taBa ganinshi da ita ba. Kenan soyayyar dake idanunshi ta bugar da shi babu mamaki.
Na fita daga motar na barshi nan, na jingina da sassalkar motar cike da tunanin al'amuran rayuwa. Na mika tunanina ga kalamin Qassim, eh, nima na yarda a yanzun kam (billonnaire) ce. Ko daga motocin da aka mallakamin makullansu, ba'a maganar abin banza sarkokin (Gold). Duwarwatsun ado na Diamond (farin yakutu), emerald (jan yakutu), sapphire (shudin yakutu) da ni kaina bansan adadin su ba.
Inada gidaje guda biyu nawa na kaina cikin birnin Paris da Singapore, (inda harkokon Nuratu suka fi yawa) da makeken shagon sayar da turarurruka ‘designers’ nawa na kaina shima a Paris, ba’a maganar (estate) guda cikin Damagaram da makeken gida a unguwar plateux (Niamey), banda kananun abubuwa watau hannun jari na bankuna. To amma Qassim ya manta cewa duk wannan dukiyar shi ya fini GIRMA?
Ya fini gata, ya fini daukaka ya fini komai. Ko babu komi tsarkakakken asali shine komai, amma duk wannan agareni aikin banza ne. Ko na daga ido na dube su nayi farin-ciki, tunani daya zanyi ya sani dakacen…. inama ba'a haifeni ba.
Wannan ciwo ne da har abada ba zai gushe daga zuciya ba, sai karfafa Imani kadai. Ban taba tunanin yin tutiya da dukiyar Nuratu ba. A tunanina da ni da shi duk daya ne a gareta, tunda tare na gansu.
Shi kansa ya lura zancensa ya taBa zuciyata, don haka ya fito ba tare da ya kara magana ba. Muka jera tare cikin (reception) kai kace wasu zarah ne cikin taurari, muna matukar kama, mun kuma yi bala'in dacewa da juna, sai dai zuciyar kowanne babu dadi.
Sai da naga dagawarsu na juya muka komo gida. Ina dakin da ya zamo nawa ina rage nauyin kayan dake jikina. Ta shigo niki-niki da butar shayi da 'yan kananun kofuna irin nasu, nayi hanzarin karBarta na ja kankanin teburin gilashi na aza, ta zauna akan ‘stool’ ta zuba tana firfitawa, ta kurBa a bakinta taji zafin yayi dai-dai yadda take so, sannan ta miko min. Raina a jagule yake, duk da haka na daure na amsa na kai baki na. Dacin shayin yayi min dadi, zafinsa ya ratsa har cikin hanjina, na samu relief daga bacin ran da na samu kaina aciki babu gaira babu dalili.
Idanunta masu kaifi a kaina tace "me ya dadar dake haka? Kun biya wani wajen ne kamin ku je (airport) din?”
Na yi murmushi, tuni na gano tsabar tsoron, dake cikin kyawawan idanunta. Amma sai na yi kamar ban gane ba, ina kurbar shayin ina kallonta ina murmushi nace “ina kuwa zamu je bayan can din?”
Ta dan saki fuskarta ta ce "ko nan gaba, kada ya kuma cewa ki zo ki raka shi wani waje ki kwashi jiki ki bishi, duk wata rakiya ayi ta iyaka bakin gate….,” nace “to Nurtu….” Karaf, a kunnen Yadudu dake shigowa, ta dauki kofin shayi daya ta muka min a tsakiyar kaina ta ce "ba zaki daina kiran Nuratun nan ba?”
Na dafe kaina ina dariya, ita kuwa ta mike tana hada kan kofunan shayinta ko a jikinta, tace da Yadudu “rannan ma cewa ta yi wai Nuratu Mainasara, yaushe zamu je wajen Haiti?”
Yadudu sai muka koma bata dariya. Don ta lura itama Mamin, ta fi son Nuratun da nake kiranta da shi.




*** *** ***
Mun sauka a Singapore, da sanyin asubahin safiyar litinin. Nade nake cikin jar liffayar Mouritania mai ratsin fari. Takalmina mai tsayi ne sosai sanan na yi amfani da abin kare hancin da na fito da shi daga jirgi, na toshe hancina, daga sanyin dake barazanar jawo min mura.
Nuratu na cikin shudiyar liffaya itama, takalminta ‘flat’ ne, don haka da muka jera yau sai na fita tsaho. Aunty Hibbani da Moiram suma suna tare suna hirar su, sai 'yan sandan ciki mata guda biyu cikin fararen kaya, dake bin Mamie inda duk ta aje kafarta.
Ta fiddo waya cikin ‘reception’ ta bude ta sanya layinta na kasar ta maida ta rufe ta shiga lallatsawa, na kwantar da kaina a gefen kafadunta na dama, domin ba karamin gajiya na yi ba. Sai muka yi wani irin kyau kamar kawa da kawa. Tana magana cikin harshenda ta san ko (alif) bana ji a ciki, (french). Tun daga fuskarta har cikin zuciyarta cikin nishadi take.
Ta dubeni tana cigaba da maganar ta, sannan ta rufe wayar. Ta kai hannunta na dama ta rufe min ido, ta ce " I 've a green, great, giant surprise for you… what would I 've in return? (Menene tukuici na?)"
Na ce “karki damu Mamie, fara bani albishir din tukunna, zan baki kyautar turare, bayan shi kuwa zan kai ki makkahh….” Maganar ta kakare a makoshina. Sakamakon wata 'yar ubansu mulmulalliyar motar da ban taBa ganin irinta ba, ta yi parking nesa damu kai kace kwai ne. A kullum malam bature na kara kero motoci, da kusan ba wacce ban gani a (Kangiwa Estate) ba, amma ban taBa ganin irin wannan ba.
Domin kankantarta ta isa, har nayi tunanin yadda mutum uku zasu iya zama a cikinta. Glassanta masu duhu ne, amma ba (tinc) ba, domin zaka iya ganin adadin kawunan mutanen dake cikin motar, saidai banda kamanninsu. Na kuma fahimci mutum biyu ne a ciki.
Gabadaya hankalina ya tafi ga maotar, da son ganin wadanne irin mutane ne zasu fito daga cikinta? Don haka Nuratu ta zame ta bar ni nan ina kauyancin mota, ta nufi inda su Moiram ke zaune suna cin gugguru.

Matasa ne guda biyu masu jini a jika, suka bude murafen motar suka fito a tare, dayan ya saya idanunshi cikin bakaken (dark glasses), ya zaga baryar da dayan

24, May 2025
Ibrahim

Thanks alot for the best novel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login