Showing 27001 words to 30000 words out of 45361 words
Chapter 10 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
ciki yayi masu, ita Zaynab din dake fuskantar kofar shigowa itace kadai taga shigowarshi, don haka Hibbani sai ganin shi kawai tayi a gabanta kamin ya soma kokarin cire riga. Ya ce “nima ayi mun dilkan, ai nima, ango ne!" Hibbani tayi salati ta yar da wanda ta kunso a hannunta ta mike ta fice tana cewa “ban san baka da kunya ba Faruq sai yau".
Duk da abin ya bata dariya amma ta sha mur ta ce “haba don Allah Ya Faruq, zuwa fa zatayi ta gayawa su Mamie…." wani kallo daya watso mata, ba shiri ta kama bakinta ta dinke. Duk da dilkan dake jikinta da karnin danyen kwai da ba’a kai ga wankewa ba. Haka ya tarairairayo kayarshi yana sakin wata irin ajiyar zuciya mai karfi, tare da cigaba da abinda yake ganin shine kadai kwanciyar hankalinsa, cikin ranshi yana yiwa Allah mai girma, godiya mara iyaka.
Hibbani ta fito tana ta fada, ta ce "kun san Allah ku ba yarannan matan su hakannan, bikin nan na menene? Tun ana abu cikin marmari ana dariya har ya gundire su. Duk hakuri da kawaici irin na Faruq yau kun kureshi yayi muku keke da keke. To wallahi in baso kuke a maida su mata cikin dakunan ku ba, akan idanun ku, to yau dinnan ku lullube matansu ku kai masu".
Hajiya Azumi ta iso bakin kofar tana kwankwasawa da yatsunta, amma bata shigo ba, tace “Faruq” ya ce "shigo mana Mama, dilkan da Hibbani ta ki karasa mata nake karasa mata" ta ce “to hakan yayi kyau, amma fito in shiryota in kawo maka ita gabadayanta yanzunnan”. Daga shi har Zaynab suka sa dariya yace da ita cikin rada "kin ga ai na yi mana maganinsu" ya dago murya yace “Allah Mama ki shigo, ko kwarzane ban yiwa 'yar ki ba, hira kawai muke yi” ta ce "wai ina wasa da kai ne? Nace ka fito ko?” Ya fito yana murmushi, ta daddage ta zuba mishi rankwashi a tsakar ka ta ce "bace min da gani, mara kunyar banza" sai da ya kai bakin kofa ya juyo yayi mata gwalo. Tuni Nuratu ta bace a sama.
*** *** ***
Acikin gidan-gonar Zaynab da ke garin Gwarzo, walima ce ta musamman Zaynab ta hada musu su takwas kacal. Tana sanye da fararen ‘wedding gown’ dogaye har suna jan kasa, tayi lullubi da farin ‘net’ amarya dai sosai sai walkiya take ta inda duk ta juya, ta matsa jikin bishiyar ‘guava’ ta aje ‘yar karamar (automatic video camera). Bata kai ga dagowa ba Faruq ya karaso ya kwantar da kanshi a bayanta, yace I luv u Zaynab".
Qassim ya sakar masu flash din Camera a hakan. Imran dake zaune can gefe kan wani dutse, Haiti na zaune daga gefen kafafunshi, tana yi mishi jan yatsu a hankali, suka juya suna hango abinda ake yi, wato irin soyayyar da ake zubawa tsakanin Zaynab da Faruq dinta, ya lumshe ido yana murmushi yace "kin ga inda ake soyayya can, ba irin tamu ba" ta harareshi, cikin wata siga mai jan hankali tace “au daga gareni ne ma?”
Ya dirgo daga kan dutsen ya kwantar da kai a kafafunta, ya rintse ido yace “na yarda daga gareni ne, amman nima daga yau na daina Haiti I luv u, I luv u more than I can say. Don Allah mu rike amanar juna.
Ba soyayyah ce ta hadamu ba, iyaye ne, daga baya kauna ta hadamu, in sha Allah bazamu taba ganin ba dai-dai ba a rayuwar auren mu".
“Ya Im! Ya Im!!”
Zaynab ce ke kira daga nesa, cikin siririyar muryarta "ka taho gashi na yi ‘serving’ dinka” ya ce “to Zaynab dina”. Ya kama hannun Haiti suka nufi inda suke.
Makekiyar ledar cin abinci ce aka shinfida, aka shaketa da ‘warmers’, sunkin ‘foil-papers’ da tangarayen abinci. Manyan ‘picinic-coolers’ suma shake suke da nau'i-nau’in kayan abin sha masu dan karen sanyi. A gefe tirkeken rago ne guda aka gashe. Yana tsaye jikin karfe cikin ramin da ake gasa shi sai naso yake ya gasu yayi lugub, mai so sai ya je ya yanko iya yadda yake so ya ci.
Suka soma cin abincin suna nishadI, aka ci aka sha akayi hani'an. Ko kafin su gama duhun dare ya fara shigowa, wato an kirayi sallar maghriba. Suka matsa ga (pipe) din da ake ban ruwan shukoki suka dauro alawala. Faruq ya ja su jam'in sallar magriba, sukayi addu'a ta musamman akansu, domin neman zaman lafiya a tsakaninsu da zuri'ar da zasu haifa a gaba. Ko kafin su shafa Inna dubu ta aiko Halima ta kwaso mata amaren za’a kaisu gidajen mazajensu.
Faruq da Zaynab suka ce da Halima, ta gayawa Inna Dubu su a cikin gidan gonar-nan zasu kwana cikin (Hut), wato irin bukkar nan ta zamani, da ake yi cikin gidan-gona, tuni sun sa an sanya masu dindimemiyar katifa, gobe zasu tafi nasu gidan da kansu.
Halima ta kama baki, cikin dimuwa. Ya daga mata gira yana murmushi yace "Yes, muna son kafa tarihi ne!”.
Ta ce “to Allah ya tashe mu lafiya". Ta juya tabi bayan su Imran.
Har ta kusan tadda su sai ta dawo, ta kamo hannun Zaynab ta jata gefe tace “sai kin yi hakuri da Faruq, don na sha gaya miki yana matukar son ki. Wannan rubabben son na shekaru goma sha takwas, duk a yau zai nuna miki shi. Kiyi dauriya ki kiyi juriya ki zama mace tagari Zaynab, kuma in gaya miki Imran ya cika alkawarin da ya daukar min. Bamba goma sha biyu, suna nan ya bani na kai miki dakinki”.
Dariya tayi cikin annashuwa, hasken farin wata na kara haskaka kwalliyar amarcinta. Tace “Yaya Halima bani da kalmar da zan gode miki".
Ya karaso cikin kaguwa ya kasa kunne yace “wai gulmar me ake yi ne? in ji dai ba gulmata bace. Ke Yaya Halima dadi na dake in baki ki kulla nunkufurci ba bakya jin dadi ('yar mace, da dan namji suke)”. Ta harareshi, ta juya tana cewa
"kai nan har ka isa in nunkufurceka? Sai dai in maka kan mai uwa da wabi" (ta zuge Zaynab taki yarda da shi). Yana dariya ya sakalo Zaynab suka shige bukkarsu.
*** *** ***
Duk wata rawar jiki da karkarwarshi, ZAYNAB ta fishi. Duk wata zakuwa da nuna zalamarshi, ZAYNAB ta fishi. Duk wani kokarinsa da jarumtakarsa da kyar ya iya ya gamsheta. Halittarta na daga cikin halittar matan da turance ake kira ‘nymphomaniac’. To amma shima ai namijin gaske ne. Yayi mamaki amma yai shukurah ga Allah abisa halin da ya risketa. Ya rungumeta sosai tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, hasken farin wata da alfijir daya soma kokarin ketowa, ya haskaka mishi kayatacciyar fuskarta, yace cikin shauki “Zaynab are you O.K?”
Gyada mishi kai kawai tayi, kamin wasu irin hawaye su mirgino su jika kundukukinta. Tana fatan Allah ya dorar da soyayyarsu da rayuwar su da Faruq cikin GIRMA da daukaka kamar yadda ta faro. Shi kuwa addu'a yake Allah ya bashi tsawon rai, karfi da lafiyar da zai cigaba da iyawa bukatar gangar jikin ZAYNAB, har zuwa ranar da suka daina numfashi.
***
GIRMA YA TASHI!
SHEKARU ASHIRIN A GABA.
Zaynab Mainasara, na daya daga cikn jami'an majalisar dinkin duniya (United Nations) dake wakiltar Nijeriya, sannan (member) ce a kungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Africa ta yamma da aka fi sani da (ECOWAS). Gabadayan karatun ta har zuwa digiri na kololuwa, ta yi shi ne akan tattalin arziki (Economics) daga Jami'ar Porstsmouth, U.K.
Danta na farko data haifa tun a shekarunsu na biyu da aure (Aliyu) ta bada shi ga Mamie Nuratu tun daga shekarun yaye. Ta yi masa aure da Sa'adatu diyar Haiti da Imran, yana da shekaru goma sha takwas. Ta aurar da Rabi'a tun tana da shekaru goma sha hudu, ta aurar da Nuratu (Mamie) tana da shekaru sha biyar. A nan gaba kadan tana shirin aurar da Halima (Dubu), da kanwarta Hibbani, wadanda ke aji uku na sakandire. Sai dan autanta Sa’id, mai kimanin shekaru goma a duniya.
Na daga jaridar (New-Nigeria), mai dauke da kanun labaran bikin cikar su shekaru ishirin da aure. Ban taBa ganin fuskokin mata da miji da suka dace da juna irin ZAYNAB da FARUQ ba. A kasan hoton an rubuta “an extraordinary lady, ZAYNAB MAINASARA, in celebrating her 20th wedding anniversary” da aka yi a Niamey, cikin wannan shekarar. Duk da irin runguma mai cike da kauna da maigidanta yayi mata, cikin hoton, tana kuma murmushi, akwai wasu dunkulallun hawaye cikin fararen idanunta.
Na samu kaina da maimaita lakabin da akayi mata watau ‘extraordinary’, kwarai sunan ya dace da ita. Ban taBa ganin mace mai ban mamaki irin Zaynab Mainasara ba; mijin da Allah ya nufe ta da samu, dukiyar da Allah ya hore mata, ilimin da Allah ya bata, da daukakar da yayi mata cikin kasar mu mai dinbin albarka, bai goge Bacin ran dake cikin zuciyarta ba, bai shafe Boyayyen bakin cikin dake boye cikin kwayar idanunta ba.
Masha Allahu lakuwwata Illa Billah!
Masoyana a duk inda kuke cikin duniya, wadanda na sani, da wadanda ban sani ba, na gode da yabo da fatan alkairin da kuke yi min. Kamar Zaynab, nima nake cewa ;
"Da fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa!"
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: A kasuwancin fatar shi ya tara duk abinda yau nake da shi, ko in ce muke dashi nida marigayiya Innarki. Duk wannan arziki da Allah ya keta buda masa, hankalinsa ba’a kwance yake ba saboda larurar Ya Rabi, da wani lokaci zasu nannadeta kamar alkaki ko su hana hannaye da kafafunta motsawa. Aka dukufa neman magani har Tumbuktu, Morocco, Mali da Mouritania. Amma mayun sunki rabuwa da ita, ko sun tafi kwana biyu sais u dawo. Mahaifinmu yana da dadadden burin yin Gwamna a Damagaran, ba don komai ba sai don ya kara fito da jiharsa ta tserewa sauran jihohin mu, don haka a dai –dai wannan lokacin ya kacame cikin hayaniyar siyasa Allah kuma ya bashi jama'a magoya baya kamar me, domin al'umma Nijar bakidaya sun yaba da shugabancin Kakanmu Kangiwa, don haka ne duk wani da ya fito takara daga tsatson Mainasara nan da nan yake lashewa, sai dai in bai tsaya ba.
Su kance “Mainasara ba don sata kuke mulki ba, sai don kishin mu”. Ana sauran watanni ukku zaBen, a irin tafiye-tafiyen da yake cikin Nigeria, ya jiyo labari Malam Ali Mai Almajirai ta hanyar wani dan kasuwar fata mazaunin garin Kano, shine ya bashi labarin irin wahalar da yake yi na nemawa Rabi magani, inda shi kuma yayi mai hanyar Malam Ali, ya je suka gana yace ya je ya zao mai da Rabin.
Da fari Yadudu taki aminewa, inda ta ce sai dai shi Malamin ya biyoshi wato a daukoshi yayi mata maganin a can gidanta, inda ya nuna mata Malam Ali ba malamin ciwon hauka bane kawai makiyayi ne mai nasibobi daga Allah, baya karBar ladar aiki sai sadaka, itama ba ko yaushe ba.
Ni kuwa nace kafata kafar 'yar uwa ta, don haka ne mahaifinmu ya dauko mu mu biyu kacal ya taho da mu Kano ta jirgi, muka yi a kalla sati biyu gidan Malam Ali ana yiwa Ya Rabi magani, muna kwana dakin Innar Faruq wato Inna Dubu. A lokacin Faruq bai fi shekaru biyar ba, inda ni kuma nake da goma sha biyu, Yaya Rabi sha biyar.
Allah cikin ikonsa yaba Malam Ali sa'a ya rabata dasu cikin 'yan satittika, muka soma shirin tahowa. Lokacin da Babanmu ya tambayi Malam Ali me zai bashi ladar aikinsa? Budar bakina sai cewa ya yi, ya aura masa Rabi, baya karBar ladar aiki sai sadaka. Baban mu bai duba yanayin rayuwar karkara ta malam Ali ba, ko wadata ko waninsu, illa tunanin ya zai yi dani idan ya rabani da 'yar uwata? Alhalin ko barci baya rabamu. Yana tuntuBar Ya Rabi ga mamakinsa sai ta amince farat daya, ni kuwa nace kafata kafar 'yar uwata.
Haka ya aurawa Malam Ali Ya Rabi, akan sadaki kalilan. Damuwar sa shine, me zai ce da Yadudu da su Baba Aliyu? Da wannan damuwar ya hawo jirgi, kwata-kwata baya cikin nutsuwarsa, akan hanya ne Allah ya aiko a jalinsa, jirgin su ya kife, babu wanda ya tsira a cikin jirgin.
Malam Ali ya samu labarin hatsarin a radio. Hankalin sa ya tashi, don bai san kowa namu ba, sun rabu ne akan bayan zabe zai dawo tare da dangin mu su ga inda take, nikuma su tafi dani in cigaba da makaranta. Ya yiwa mahaifinmu addu'a sosai tare da alkarwarta ma ransa rike mu amana.
Shi da bakinsa rannan yace bai tunkari mahaifinmu da neman auren Rabi haka kai tsaye ba, saida ya kwana uku yana Sallah yana rokon Allah a kansu shi da Rabin. Don haka da yaji rasuwar mahaifinmu ya kara kafe Rabi a cikin gidansa kar ta gudu, domin ba karamin so yake yi mata ba.
Sai kuma Allah ya hada jinin Rabi da Faruq, kullum yana dakinmu, tare da shi muke zuwa makarantar boko shi yana aji uku ni ina aji biyar. Haka in mun dawo muna tare muke daukar karatun allo sai dai shi ya wuceni nesa ba kusa ba a karatun allo saboda inada tangarda a harshe, har rige-rigen wanke allo muke yi, inda ni kuma na yi masa fintinkau a makarantar boko saboda na samu tushe mai kyau a makaranta mai tsada a Damagaram.
Innar Faruq mutuniyar kikice, bata dauki Rabi a matsayin kishiya ba sai kanwa, domin a haife ta haifeta. Rabi shekarunta goma sha biyar kacal a lokacin. Wannan sai Goggo Rakiya (kishin).
Sunan da Faruq ke kirana dashi a lokacin shine (Nuratu-mai-dogon-gashi), ni kuwa ince Faruq dan dukurkusu), don ni na fisi tsayi sosai, haka nake kama hannunshi mu tafi makaranta ko in daura hannu a tsakiyar kanshi in tasa shi a gaba, shi kuwa haushin hakan yake ji, domin shi a lallai sa'a na ne, bayan shekaru bakwai rigis na bashi. Idan na dora hannu a kafadunsa sai ya ture, shi sai dai mu jera, bayan kuma rabi na ne.
Akwai wani daki a soron gidan Malam, da kullum yake a rufe, tunda muka zo gidan ban taBa ganin an budeshi ba har na kammala karamar sakandire, da yake makarantar kwana nake yi a Garko wato (Garko Science) ban san Sa'idu a gidan yake ba, kuma wannan dakin nasa ne, ban kuma san sanda suka shaku da Ya Rabi ba fiye da Faruq, ya zamanto hatta kwanon sa a dakin Rabi yake, kuma da yake yana da cutar gyambon ciki (ulcer) sai take tsaye sosai akan abincinshi. Rabi ita ce uwar dakin Sa'idu, wanda yake almajiri ne ga Malam, kuma Malam ya sanya shi a makarantar boko cikin Kano, sanda yake zuwa gidan sau tari ina makaranta. Rabi na son Sa'idu sosai fiye da duk 'ya'yan rikon dake gidan da sauran almajiran Malam, har ta kai ta kawo duk wani sirrin shi da Rabi yake yi, idan zai koma makarantar haka take kulla 'yan canjinta ta bashi, haka ko daga can makarantar yana aikowa ta aika masa da abinda yake so ko ta karBa a wurin Malam ta bayar akai masa.
Rannan shiryawa tayi ta tafi Bindawa zaman makoki, wai Baban Sa'idunta ne ya mutu. Lokacin da Sa'idun zai zana jarrabawar tafiya kasar waje. Rabi bata yi barci ba, kwana take sallah da addu'ar Allah yaba Sa'idunta sa'a. Har bashi take ci wurin Goggon Dubu ta baiwa Sa'id yayi hidimar karatunsu, inta dauki adashinta ta biyata.
Sanda ya soma daukar alawus daga kwalejin horas da malamai ta jihar Kano sai ya sayo mata keken dinki da gabadayan kudin ta soma dinki, amma wallahi duk abinda ta samu a dinkin a wani katon banki take tarawa, idan na tambayeta me zatai da kudin da take ta tarawa a banki, sai tace gudunmawa take tarawa Sa'idu in yazo yin aure.
Amincin dake tsakanin Rabi da Sa'idu ba zan iya kwatantashi ba. Ta daukeshi tamkar dan data haifa a cikinta, shi kuma ya dauketa da muhimmancin uwar sa. A haka ya tafi Turai ya soma karatu, amma duk sanda ya samu dama sai ya yo mata aike ita da Malam.
Zuwansa hutu na farko daga Turai ma ina makaranta, sai tangamemen hotona a dakin Rabi. Ya dade yana kallon hoton yace "amma nan baki fi shekaru goma sha bakwai ba, aka dauki hoton ko Innata?” Ta yi dariya har taba uku lada, tace "yanzu da gaske Sa'idu baka san kanwarka, Nuratu ba?” Ya cika da mamaki ya ce "itace ta zama budurwa haka? Lallai girman 'ya mace, ba wuya,
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel