Showing 3001 words to 6000 words out of 45361 words
Chapter 2 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
Dana tabbatar Yaya Halima ta yi nisa a barcinta, sai na dora mata a gefen filonta dai-dai inda tana bude ido zatayi tozali da ita. Na mike na dauro cikakkiyar alwana na shimfida darduma a tsakar gida, na dasa Sallah, yi nake kamar bazan daina ba, ina rokon Allah ya yi min jagora, ya kareni daga sharrin abin hawa dana mutum da aljan, a cikin wannan tafiyar da zanyi. Har aka yi kiran assalatu. Na samau jam'in sallar asubahi ina idarwa na koma dakin na canza kayan jikina, na fara da sanya ‘vest’ Kaman yadda yake a al’adata kana na daura atamfa (Super Holland) shudiya mai ratsin ruwan hoda da kore, na fiddo sarkarnan na daura a wuyana, kunne da hannayena gudun kada wani ya kwace jakar, na kawo bakar abaya (after dress) mai kauri na dora, na kawo niqab na rufe fuskata ruf, sai kwayar idanuna kawai, na rataya jakar hannuna wadda take mai girma sosai da takalminta marassa tudun dunduniya, (suna cikin kyayyakin da iyalin V.C suka hada min a dawowata), hatta abayar da ke jikina sabuwa ce dal a ledarta, Hajiyar Imran ce ta bani, a matsayin sallamrta, ban dauki kaya ko kala daya ba sai na jikina, komi ina yinsa ne cikin takatsantsan, yadda na tabbatar motsina ba zai tada ta daga nauyayyan barcinta ba.
Har na fito na sake komawa ina kallon Yaya Halima, dake barci cikin nutsuwa, amma ga busassan hawaye nan like a idonta. Tausayinta ya kamani, na tabbata nayi sallama da mai kaunata. Ji nake kamar ina yi mta kallon karshe ne. Na juya da baya da baya na fito daga dakin sakamako wata zuciyar dake neman raunana min gwiwa, da tunanin anya abinda kike shirin yiwa Faruq da Halima kin kyauta? Da gudu-gudu na karasa soro na zare sakatar, a lokacin da na jiyo motsin fitowar malam Harisu mijin Yaya yana fitowa daga bandaki, da yake yau ba'a dakin Yayar yake ba, yana dakin amaryarta Hadiza ne.
Na soma taku a hankali a gefen titi, garin babu haske sosai domin ga dukkan alamu alfijir bai gama ketowa ba, misalin karfe biyar da rabi na asubahin safiyar litinin. Idan ka ganni a lokacin sai na baka tsoro, saboda shigar bakaken kaya da niqab dake fuskata, hatta takalman kafata bakake ne kirin. Ina tunanin yaushe zan kai tasha da wannan tafiya da nake yi mai kama da ta mai ciwon cinya, sai na kara sauri.
Gab da zan shiga tashar garin Gwarzo wata bakar mulmulalliyar mota mai walkiya (pg 406) dana tabbatar ta Ya Faruq ne da muka dawo cikin ta jiya, ta zo ta gilma ta gabana, na yi saurin boyewa a bayan wata Daf da tayi lodin shanu zuwa Lagos, cike da mamakin me ya fito da Ya Faruq cikin wannan duhun asubahin, kuma ina zai je? Domin in banyi kuskure ba, zance hanyar fita gari ya dauka, ko dai Kana ko kuma Sokoto.
Na yi ajiyar zuciya cike da wani matsanancin tausayinshi daya tsirga mini, shin ko yaushe Allah zai kuma yin saduwar fuskokinmu? Shin ko yaya zai ji a ransa, idan ya sami wasika ta? Abubuwa ne da idan na tsaya tunanin amsar su, zai sani fasa kuduri na in zauna tare da su, wanda zaman ba wani amfani ke gareshi ba, illa in shirya nadar bakin cikin rayuwar shegantaka cikin garin Gwarzo da dangin Faruq . Kada Allah ya nuna min wannan auren.
Na karasa cikin tashar wani dan kamasho yana ta tambayata "Hajiya Kano, Kaduna, Lagos ko Abuja?” Hawayen ne dai suka kara ciko idona, ban san sanda bakina ya furta ba a hankali "Nijar”.
Yyace babu motar kasar Nijar a nan, sai dai ki hau ta Katsina ki sauka a Jibia, daganan sai ki hau ta Nijar din” bani da zabi banda na ce masa “to", ya yi min jagora zuwa wata (Peugeot Station Wagon) mai zuwa garin Jibia, na biya kudin da suka cajeni na nufi can ‘seat’ din baya na zauna a jikin taga, ina ta kalle-kalle na tunda nasan babu mai gane ni, balle a kaiwa Malam labari.
Sai da muka Bata a kalla rabin awa har na fara tunanin sauya mota, kada Yaya Halima ta tashi tasa mijinta ya biyo bayana, ni ko na rantse ko zan dinga kwana a kango, ba zan kara kwana a cikin garin Gwarzo.
Sai Allah ya kawo pasinja hudu ris a lokaci daya motar ta cika, muka daga zuwa garin Jibia.
Sha biyu da rabi na rana muna cikin tashar garin Jibia. Ba da wani Bata lokaci ba direbanmu ya sanya ni a motar Niger ita ma peogeut ce, wani yaro ya zuro min tallar gorar Yoghurt din (Mai dabino) mai sanyin gaske, sai a lokacin na tuna rabona da abinci tun kokon da muka sha kwanaki biyu da suka wuce da marigayiya INNA TA. Na karBa na biya tare da ledar ruwan (pure water) guda biyu, kafin minti daya duk na zuke su. Na fiddo (Al'ma'asurat) cikin jikata na soma karantawa har motar ta cika, muka tasamma Jamhuriyar Niger.
Da aka zo (boarder) wato iyakar Nijeriya da kasar Nijer ne muka samu mukai sallahn azuhur da la'asar (kasaru), bayan gama bincike-binciken su suka daga mana kafa muka wuce. Tafiya ake babu cin zango akalla awanni biyu, sannan ne na soma hango Dogayen RAKUMA da rairayin SAHARA. Wata nutsuwa da ni'ima sauka a zuciyata, muka shiga cikin Maradi. Sai na daga niqab dina ina kallon mutane irin INNATA; farare sol, masu fararen idanu, dogaye masu lange-langen jiki da yalolon bakin gashin kai. Na maida nikab dina na rufe a sanda muka shiga cikin tashar da za'a sauke mu.
Na fito daga mota nayi mika sosai, kasusuwana suka ce kakas, na matsa ga direban daya kawo mu nayi masa sallama, ya amsa nace "don Allah Yayana Damagaran zani" ya ce "Wai, ashe kuwa kina da sauran tafiya, bus zaki hau koko fijo in hadaki da wasu direbobin?” Na ce “gara bus din, saboda bana son irin wannan gudun saida rai da kuke, yayi yawa” yayi dariya yace "da bama gudun, da yanzu baki shigo Jamhuriyar Niger ba. Amma in gaya miki gaskiya zakiyi dare, ki kuma yi saukar dare, domin tafiyace ta awanni uku a gabanki kafin ki kai Damagaram tunda kince a bus zaki. Ga kuma motar can ina hangowa fasinja biyu ne kacal a cikinta, don haka babu lokacin tashinta koda za’a kwana ne kuwa sai sun cika zasu tashi. Don haka ina baki shawarar ki nemi wajen saukar bakI, ki kwana, gobe in Allah ya kaimu kiyi sammako domin hanyar bata da kyau" na yi tsuru-tsuru a raina nace na shiga uku ni Zaynab! Ina zani in kwana ina 'Ya mace? Kai gara duk abinda zai faru ya faru amma ba zan yarda da kowa ba, mutum abin tsoro ne, kuma mugun mutum bashi da kama a fuska. Na nisa nace indai akwai motar to ka taimaka ka sani, saboda ban san kowa a garinnan ba, kuma kasancewata mace, kana ganin ya kyautu inje Hotel in kwana ni kadai?” Ya girgiza kai “a’ah bai kyautu ba kam, kinyi tunani yarinya, shige muje, waccan (J5) din Damagaram zata je, Allah ya tsare ya kaiku lafiya".
Nice a kujerar karshe cikin mota J5 mai zuwa garin Dagamaran daga MaradI, gajiyar mota gami da duhun mangariba daya fara shigowa suka saukar min da kasalar data sanyani gyangyadi a hankali, daga nan kuma sai barci na sosai, na kwanaki biyu cif da ban samu nayi ba. Bani na farkaba sai da naji rurin motar ta soma tafiya wato pasinja sun cika, na duba agogon hannuna misalign karfe shabiyu na dare. Naji zuciyata ta buga, nayi dakacen karbar shawarar direbannan. Tafiya ta mika duhun dare ya shigo sosai muna ta wuce bukkokin buzaye wani lokacin kurar sahara ta turnike sabida rashin kyawun birjin ta yadda direban ke kasa ganin abinda yake gabansa duk da fitilar motar mai hasken gaskece. Na maida kai na kwanta jikin kujerar gabana. Barci na yayi nisa cike da mafarkai barkatai, masu dadi da marasa dadi duk a game da abinda zan tarar a tafiyar da nake yi. Wanda ya fi daukar hankalina shine na Innata, cikin korayen kaya ciki wani wawakeken koren lambu, zaune bisa wata kujerar azurfa sai murmushi take, fuskarta cike da annuri.
Dana karaso kusa da ita sai ta ce dani "na gode Kyauta, da cika min burina na shekara da shekaru da zakiyi, wato neman Nuratu. Sai dai bana farin ciki da kudurinki akan mahaifiyarki, domin iyaye duk yadda suke, duk lalacewar su, sunfi karfin ayi ramuwar gayya a kansu…”
Daga haka ta shige cikin koren lambun nan, ba ko waiwaye, ta barni anan ina cizon yatsa, ina son ta tsaya in yi mata bayanin dalilina na daukar fansa akan 'yar uwarta? Sai bata bani wannan damar ba. Ta juyo tana mai daura hannu bisa bakaken laBBanta ta ce "Shhhhh! Nuratu mai kirki ce".
Daga haka ta shige abinta, ko waiwaye bata sake yi min ba…… kuuuuuuuuu! karar wani irin cin taya da neman hantsilawa da motar ta yi, tare da ficewa da tayar baya tayi ta nufi jeji, motar ta tsaya cikin kudurar Ubangiji a tsakiyar titi tamkar wani kututture ya tokareta, shi ya farkara dani daga dogon barcina cikin matsanancin firigici da tashin hankali. Mutanen motar nata kwarara salati cikin saddakarwa da mutuwa, direba ya fita tare da wasu fasinja daga cikin motar suna dubawa inda suka fahimci wani karfe ne mai tsini aka ajiye a tsakiyar titin da gangan, wanda in bai Bula taya ba, to ya jawo hatsarin da zai yi sanadiyar rasa rayukan al'ummar da ke cikin motar duk da tazo wucewa. Ganin wannan karfen yasa cikin gabadaya matafiyan ya duri ruwa, don alama ce dake nuna akwai 'yan fashi a kan titin, wadanda suka sassauka suka dawo cikin motar da gudu sai direban motar da karen motar ne kadai suka yi ta maza suna kici-kicin zaro safayar taya su daura.
Sai gasu suna fitowa cikin bakar shiga, daya- bayan daya, fuskar kowanne sunke cikin bakin kyalle, jibga jibgan da su ko a lahira bana fatan kara tuna wadannan fuskokin, da suka yi sanadiyar zubowar fitsarin daya kulle min mara, 'ya'yan hanjina suka hautsina bansan ya akayi nayi hankalin cizgo sarkar wuyana na cusa cikin (brazier) ba, karkarwar jiki ya sani kasa taBuka komai bayan hakan sai Innalillahi wa Inna ilahi raji'un nake ta ambato, ba aya ba wakafi. Suka yi magana cikin wata irin murya mai kama da karar saukar aradu cewa kowa da ke cikin motar ya fito ya kwanta a kasa, ko kamin su rufe baki duk mun aikata yadda suka ce.
Amma fa ni ina makale da jakata, ban barota a motar ba kamar yadda sauran jama'ar sukayi. Tsayin minti goma sai kwashe kayan motar suke suna shigewa dasu maBoyar su cikin wani irin zafin nama cikin mintuna uku kacal sun kwashe komi kamin babbansu ya umarci a caje mu duka, a kwaso abinda ke jikin mu. Suka dinga bin mu daya bayan daya suna lalubewa har aka zo kaina, suka daka min tsawa na ciro masu zobunan hannuna da 'yan kunnayena, duka haka na zube musu jikina babu inda baya karkarwa, idanuna a rufe gam don ganin munanan fuskokinsu shine babban tashin hankali ga dan adam ba wai abinda zasu kwace masa ba. Daya daga cikinsu ne ya haska da tocilan ya kyalla ido akan bakar jakar dake makale a kafaduna wadda da fari ta saje da kayan jikina, ya fizgota naki saki, ya-ja na-ja don ina ganin babban tashin hankalina to shine rabuwana da wannan jaka, a kasar da ban san kowa ba, ban kuma san in da zani ba.
Daga can gefe babbansu ya hango mu muna kici-kici da jaka, karfin halina ya bashi mamaki, ya daga murya yace "kai Fetso, sakar mata jakar ka daukota aka ka kawo min ita nan in rage dare da ita, Allah yasa ba tsohuwa bace" ya kuwa kinkimeni aka ya direwa Ogansa, yasa hannu yana kokarin cizge niqabin nawa yana cewa "idan bazaki bamu jaka ba, kya bamu abinda yafi jaka" ya cizge nikabin ya cillar, yasa hannu ya salube abayar jikina cikin wani irin gwaninta ya cillarta gefe, ya keta rigar atamfar dake jikina tat sage gida biyu tun daga sama har kasa, na kwala ihu na kamo yagaggiyar rigar na kankame da dukkan karfina, yace
"wow! What a sweet voice!” Tare da dallare fuskata da tocilan dinsa yana cewa "…may be the face may be as sweet as the sweet voice…….."
Ragowar maganar kakarewa tayi a makoshinsa, shima ya kwala wani irin ihun tare da cillar da tocilan din yace "Her Execellency, Mainasara….” Gabadaya yaran suka hau gudu cikn daji, shima cikamin rigar yayi yana ja da baya tamkar bai yarda da kansa ba. Wata zuciyar kuma na ce masa in ita dince sai me? Ka tsaya ka kwashi rabonka… Allah ne ya kawo ma tsuntsu daga sama gashashshe……. Wata kuma tana cewa a’ah, kama ce kawai, me zai kawo Mainasara motar kasuwa? Ya za’ai ta fita haka sakaka batare da shamaki ba? Ai ita mai jiki ce, kuma zatafi wanan shekaru…….. to bai dai samu hakikanin matsaya ga tunaninsa ba, karar motocin 'yan sanda da harbin bindiga gami da watsuwar su cikin jejin ya sashi rantayawa ana kare domin tserar da rayuwarsa. Ina ji wani matashi a bayana, wanda tun tahowar mu a kusa dani yake zaune sai dai ban juyo na kalli fuskarsa ba ko sau daya, ya yi tsaki yace "Wadannan kananan ‘yan fashi ne, sun ci mu da buguzum, ko bindiga basu da ita" ni dai saboda tashin hankali, tuni na shide, numfashina ya yi sama, na durkushe akan kafafuna kankame da jikina.
Wannan matashin ya daukomin abaya, jakata da niqabina dake yashe a kasa, ya matso ya mikomin yanayi min magana a hankali "ki kwantar da hankalinki, Allah ya tserar da mu, ungo kallabinki daura, ga jakar ki ma basu dauka ba".
Hausarshi bata fita sosai, na mika hannu na karBa amma naki dagowa, shi kuma durkushe yake a gabana cike da zakuwar son ganin fuskar da aka kira da ta (Mainasara) kamar ya sanya hannu ya dago kan nawa. Ya sake cewa "nan da dan lokaci za'a gyara tayoyin motar mu, mu karasa cikin Damagaram" nan ma ban ce komai ba, kamar da dutse yake magana, rokon Allah nake ya kyaleni in samu in daure igiyar abayata sosai, duk da cewa akwai doguwar shimi (vest) a cikin jikina. Shi da kansa ya gane tsugunonsa ya takura ni, ya ja tsumman rayuwarsa ya kara gaba.
Na yi ajiyar zuciya na daura igiyar sosai na rataya jakata na doshi sauran abokan tafiyar mu, ashe duk abin nan da nike yana biye dani a baya kamar tsohon maye. Mutanen motar tare da 'yan sandar dake tare damu suna yi musu tambayoyi suka shiga yi min barka da arziki, wata dattijuwa ce ta bani dariya da tace "bude rigar in gani, ince ko basu cire miki rigar mama ba?” Na daga mata kai cikin matsananciyar kunya, ta ce "ita ce kadai ce mai gwal a cikin mu, kuma sun kwace” sukace "Allah ya biyaki da alheri nace "amin". Wani daga bayan mu yace “a’ah ‘yan sandannan zasu dubo su baki abinki in har sunyi nasarar damko su”.
Har karfe hudu na asuba ana abu daya, domin gabadaya tayoyin motar sun yi faci, ‘yan sandan kuma wasu na tare damu wasu sunyi ciki sun watsu a dajin har Allah ya basu nasarar kamo wasu daga cikin ‘yan fashin da jibgin kayan al’umma, suka dannasu a mota suka yi gaba, ragowar guda biyar kuma sun tsaya suna ware mana kayan mu kowa yana fadar nashi amma ni ‘yankunne na ba’a maganar su, sabida kankantarsu babu wanda ya gansu sai sunga tashin mu tukunna.
Daga can gefe cikin hasken farin wata na hangi saurayinnan tare da 'yan sanda suna ta magana ta tsayin awa guda, ban san me suke cewa ba kasancewar da harshen faransanci suke magana. Daga baya ne da motar ta gyaru muka mika yana zaune a Barin dama na kujerar da nake, ni kuma ina Baryar hagu, sai wasu mutum biyu a tsakanin mu. Ba muyi tafiyar awa daya ba muka tsaya wani masallacin kauye muka yi sallar asubahi daga nan muka mika. Karfe shidda na safe muka soma shiga yankin Damagaram.
Dam-dam-dam! Na ji bugun zuciyata ya karu, wani irin dummm! Na ji a cikin kaina, haka idanuna sunyi min nauyi saboda wani irin kwarjini da Allah yai mata.
Na daga kai ga kototon (advertisement board) wato irin allonnan da ake amfani da shi wurin yin kamfen ko talla a manyan tituna da manyan hanyoyi, wanda shine ya janwo min faduwar gaba. Na kura mata ido, bata da maraba da Innata, sai dai ta fita haske da kyakkyawan jiki. Ko’ina postarta ce a ciki da wajen garin Damagaram, masu nuna goyon baya a gareta ne zarcewa da gwamnatinta wanda aka rubuta da harshen faransanci. Nayi tir, na yi Allah wadai a zuciyata, nace a raina, shin idan sun san cewa ta aje shigiyar diya a kuruciyarta, ta gudo ta barta, ta sanya 'yar uwarta cikin bakin cikin da yayi sanadiyyar danganarta da kushewarta, zasu yarda su kara zaBarta a matsayin gwamniyar su a karo na biyu?
Idan har mutum mai tabo a rayuwarshi baya shugabanci, na rantse, NURATU MAINASARA, ba zata kuma hawa kujerar Gwamniya ba! Sai na lalata siyasarta, sai na lalata sunanta, sai na dauki fansar bakin cikin rayuwar
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel