Showing 21001 words to 24000 words out of 45361 words

Chapter 8 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt

tsakanin su. Babu maganar zubar da ciki, domin ya shiga wata na shidda, kuma malam Ali yace ko da wata daya ne, shi bazai zubar da halittar Ubangiji ba, da bai ji ba bai gani ba.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Data farfado ne ta fara kuka, ta laluboni ta rungumeni tace "'yar ikon Allah kenan, Allah yasa kece jarrabawa ta karshe da zamu gani cikn zur'armu, Nuratu kam bata kyauta ba, to amma ta tuba taga isharori iri-iri a kanki, sannan kuma wannan al'amari ba yinta bane, kaddarar Allah ce. Mu nan Musulmi ne masu imani da yarda da kaddara don haka bamu bambance ki da sauran jikokinmu duka daya kuke. Allah yayi miki albarka Allah ya sanyaya miki zuciyr ki, Allah ya baki hakuri. Mantawa nayi da al'amarin data bamu labarinsa tun dawowarta, shiyasa nayi tunanin abokan adawa ne suka kulla mata sharri. Ashe ni ina zaune da jinina tsawon sati biyu rashin ido bai sani na gane ba. Sau tari na kanji kamar muryar Nuratu cikin gidan ashe diyarta ce, kai amma (Mon amour) anyi sauna da bai gane ta ba". Ashe yana tsaye a bakin kofar shigowa falon ya tokare hannunsa na dama da kofar yana murmushi yace “wa yace maki ban ganeta ba? Dalilina na takurawa da nacewa ta biyoni ai sabida dan fashin dana ji ya fasa ‘raping’ dinta saboda kamanninta da Gwamna Mainasara….." gaba daya suka hada baki “'yan fashi? Menene kuma raping?" Ya yi musu bayani dalla-dalla suka yi salati ni ko don kunya sai na ruga daki da gudu wurin Haiti diyar Aunty Habbani, da zamuyi tsara da ita, ina gaya mata shi Yaya Qassim baya jin kunyar tsofaffin nan. Daga can fa lo suka ce "shi yasa ake ce ka shuka alkairi, a ko'ina zaka tsinci abinka. Alkairin Nuratu ga al'ummarta, bazai bari a taBa tozarta jininta a duniya ba".

Ranar da aka yi addu'ar bakwai ne Alhaji Aliyu Mainasara, Alhaji Kamilu Mainsara, Adam Mainasara, Shettima Mainasara, da mijin mahaifiyata Senator Alhaji Kabiru Bedeggi, wadanda suke masu fada aji ga iyalin Mainasara suka keBe mu ni da ita, daga ni har ita kamar surukai muke, ba mai iya kallon dan uwansa cikin ido sai satar kallon juna kasa-kasa. Nafi sakewa da Hibbani, kome nake son gaya mata sai dai in gayawa Hibbanin ta gaya mata, gashi a ranar ne zata koma can kasar Chadi in da take aure. Haiti kuma zata koma makaranta a Kuala Lampur (Malaysia) dama tazo hutu ne al'amarin ya ritsa da ita. Ita kadai ce budurwa don tace duka tsarrakinta a family dinmu anyi musu aure, itama da sanya ranarta akanta da masoyinta Ahmad yana aiki a Abidjan, watanni biyu ya rage ta kare karatunta ayi bikinsu, cikin kwanaki bakwai ita ta yi min bayanin kowa cikin zuri'ar da matsayinsa gareni.
Ita Aunty Hibbani diya ce ga wan Baban Nuratu Alhaji Aliyu Mainasara kuma itace mahaifiyarta. Ta ce mu anan family dinsu tun daga kan labarin Aunty Nuratu, ba'a aje budurwa sama da shekaru sha shidda ba'a yi mata aure ba, nima don ban samu mijin da wuri ba ne, har Baba yace wai sadaka zai bada ni, sai kuma ranan na raka Aunty Nuratu taro Abidjan muka hadu da Ahmed, ma’aikaci ne a ‘airport’ muka kulla. Ada ta ce bata yarda ba wai bare ne, sai dai a hadani da Qassim, shi kuwa yace ko sama da kasa zata hade ba zai aure ni ba". Na ce “me yayi zafi, duk kyannan naki Haiti?” Ta ce “uhm Yaya Zaynab, kece baki san Qassim ba, bai aje kansa anan kusa ba, kema wallahi ba karamin mamaki nake ba da naga yana shiga shirginki, amma kafin ni 'yammata biyar cikin family dinnan duk yaki su, wasu kwailaye yake kallon mu, rannan yace cikin mu har yanzu ba'a haifi matarshi ba”.
Dariya nayi sosai. Na ce “ya akai shi kadai naji yana turanci sosai a cikin ku?” Ta ce “oh! Qassim bai yi karatu anan ba, dukkan karatunsa na (Criminlogy) yayi shi a Jami’ar Dundee, U.K”.
Jiya da daddare daya leko yi min sai da safe, ni da ita munyi shirin kwanciya muna addu'o’I, tayi murmushi ta dauko filo ta aza a karkashin kanta tace "Allah na lura kamar Qassim na sonki" cikin rashin kulawa nace “don me kikayi tunanin hakan?” Ta ce "his actions…..baki ji an ce idan kada kare na sunsunar takalmi dauka zai yi ba?" Nace "to ki ma bar wannan tunanin, babu wannan cikin rayuwata, duk wani abu da zai sa a binciko mun wannan usulin ina gudun shi ina nesantar shi Haiti…" Idnuna suka ciko da kwalla, duk da munyi ‘light-up’ taga kyallin su cikin idanuna, ta mike ta kunna fitila dakin ya gauraye da haske. Ta dubeni sosai ta ce "in har kuwa zaki cigaba dasa wannan tunanin a zuciyarki, kina tare da Bacin rai kullum. Ki manta da komi ki dauki komai ‘as a bygone’ ki fuskanci sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da kika samu kanki a ciki Yaya Zaynab, bazaki dauwama haka ba, dole zakiyi aure ko kinso ko kin ki za'ayi miki bada jimawa ba, in har ke jinin Mainasara ce.
Idan har da gaske ne abinda kike gudu kenan, to ki auri Qasim, shine ya da ce da rayuwarki, tunda dan uwanki ne na jini, wanda ba zai taBa goranta miki abinda kike gudu ba, haka duk danginsa.
Mu tsintsiyane a madauri daya, da wuya kiji an samu saBanin ra'ayi cikin zuri'ar mu, tunannin su daya, zuciyarsu daya, haka kowa na jin dan uwanshi a cikin jikinshi. Qassim is the right man for you; shine wanda zai rike ki kamar kina a gaban mahaifiyarki, ba tare da ya kaiki inda za'a taBa goranta miki ba, tunda abinda kike gudu kenan, haka zai yi duk iya kokarinsa wurin kare miki martaba da mutuncinki a idon kowa, ko don sabida kaunar dake tsakanin shi da mahaifiyar ki. Baki sani ba, a hannunshi ya daukoki ya kawo ki har gadonta tun daga Damagaran, a sume, bakisan in da kanki yake ba.
Yace koda wannan shine aiki na karshe da zai gabatar a rayuwarsa, sai cika maki burinki". Na ce "amma ai a jirgi? Ta ce "eh, a jirgi”. Na yi murmushi nace "to menene abin wahalar anan? Akwai wanda yayi shekaru goma sha takwas yana kaunata, duk da a san ko ni WA CECE? Bai taBa furta min ba, ba don komai ba sai don gujewa rayuwata shiga cikin garari idan na gane matsayina.
A sanda na gane ni din wace ce, ya tsaya mani, ya gaya mani cewa koda daga sama na fado he'll continue standing by me, ina kuma da yaqinin abinda ya fadi, haka yake har zuciyar shi. Domin ya nuna min na gani a zahiri”. Ta ce "don Allah waye wannan?” Na yi murmushi, tare da jin wani sabon abu da ya dunkule min a zuci, ya hanani sukuni, game da Ya Faruq. Na kai hannu na latsa makunnin fitilar dake jikin gadon fitilu koraye suka maye gurbi masu haske, na ja bargo na rufe har kaina saboda raBar A/C dake ratsa kasusuwana nace "sai da safe Haiti".
Ire-iren hirarrakin da muke da Haiti kenan, gashi a yau zata tafi ta barni da kewa, daga ni sai Nuratun da ko gaisheta bana iya yi, don haka kewar tafiyar su ta addabeni, ta hanani sikit, hakanne yasa da Babannin suka keBe mu a falo, ni da Nuratu, duka raina a jagule yake. Ita kanta na lura bata son tafiyar tasu sai don ba yadda zata yi ne tunda kowannen su zai koma dakin mijin sa/bakin aikinsa tare da iyalansa.
Alhaji Aliyu yace “to Nuratu mu zamu wuce, sai mu kara addu’a mu kara Istigfari, wannan wata ishara ce Ubangiji Subhana ya nuna mana, Allah ya jikan Yaya Sani”. Ta share bawayen idonta da kyakkyawan hankicinta, ciki-ciki ta amsa da ‘ameen'. Ya cigaba da cewa "ku kwantar da hankalinku, ke Zaynabu kin zo gida, cikin dangin mahaifiyarki inda ake kaunarta, don haka ko shegu dubu ta haifa ba zamu juya masu baya ba, zamu kaunace su kamar su Haiti, wannan tsakaninta da Rabbil Izzati ne.
Sannan ke muna rokonki da ki yafe mata, kiyi mata sassauci ki zamo mai afuwa, ki barta da bakin-cikin da kika kunsa mata. Alas! Ba rikicin sisaya yanzu, Zaynabu ta rabashi, sai ki zauna agida, ki huta, ki cigaba da biyayyar aure, dama mun yanke shawarar bazaki cigaba da kujerar ki ba, su mutane ne suke son ki da hakan, amma Kabiru zai nema a madadinki (mijinta) tunda shima 'tenure’ dinsa a Sanator ya kare daga wannan shekarar. Allah yasa hakan shine mafi alkairi”.
Alhaji Badeggi ya amsa "Zaynabu feel free with us, ki saki jikinki da mu, ki dadukeni tamkar Alhaji Sa'idu, inada ‘ya’ya nima don haka nasan ciwon haihuwa, don haka na yiwa Allah godiya daya karo mana da ke rana daya. Na dade ina shawartar mahafiyarki da mu dauko ki, tana ki, sabida a lokacin tana kan kujerarta kinsan yanayi na siyasa mai cike da abokan adawa da bin kwakkwafi. Nida mahaifiyarki kauna ce mai tsabta da yarda da juna a tsakaninmu. Don haka ki dauki kanki tamkar diyar cikina, kada ki kara tunanin wai ke daban ce cikin al'umma, babu wanda ya fi wani, sai wanda ya fi tsoron Allah.
Ina fatan daga rana irin ta yau, ba zan sake jin wata kalma wai ita ke "shegiya ce" daga bakin ki ba".
Na share hawayena na ce "insha Allahu Baba bazan sake ba" ya ja doguwar addu'a muka shafa, aka rufe taron da raha da dariya. Nasa kai zan fita sai naji Alhaji Aliyu na cewa "Ya kamata mu nemo shi V.C Sa'idu, don yasan tana hannun mu ko hankalinsu ya kwanta”.

Mun raka su Haiti filin jirgin saman Yamai (Mano-Dayak) inda zasu tashi zuwa Chadi. Sai da muka ga tashinsu muka dawo ni da Qassim wanda ke jan motar. Muna tafe shiru, babu wanda yayi magana har muka iso unguwar mu inda ‘estate’ din Mainasara yake watau (Plateux), anan ne ya rage gudun motar yayinda hankalina ke ga tsari da kyawun anguwar plateux, na kare nace "da alama babu anguwa mai kyawun wannan a Yamai" ya ce "eh, ai shugaban kasarmu ma a cikinta yake, shima jini ne ga Mainasara. Zaman anguwar mun gaje shi ne tun iyaye da kakanni, kuma a kalla mu muka cinye rabinta, kinga tun daga farkon ‘estate’ dinnan har zuwa karshen sa, gidajen Kangiwa ne" na ce “amma me yasa kuka fi son Damagaram?” Ya yi murmushi yace "kowa ya bar gida…. Zaynab. Duk cikin Niger babu inda nikeso irin Damagaram, donnhaka ne ma zabi da inyi aiki tare da gwamnatinsu, waddannan gyatuman da kika gani duk daga can suke, don ke suka zo, matasa-matsan ke zuane a nan domin itace (capital territory) namu, akwai wadatar (infra-stuructures) fiye da ko'ina.
Mijin Aunty Nuratu, Alhaji Badaggi, Sanator ne na Damagaram a nan, don haka ne rabin rayuwarta na nan, ko a sanda take gwamniyar mu. Data sauka kuma kwata-kwata sai ta dawo nan gabadaya, amma duk da haka duk karshen wata tana Damagaran”. Hirarrakin da muke ta yi kenan har muka kawo gida.
Tana tsaye a jikin madubin dogon yaro tana kulla sarka a wuyanta, na murda kofar dakin na shiga da sallama. Ta cikin madubin take kallona bata juyo ba, tace "har kun dawo? Jirigin nasu ya tashi?”
Kaina a sadde na amsa da "eh" tace "zo nan ki daura min sarkar wuyana” na karasa na amshin sarkar ina sanya mata. Ta cikin mudubin na gane ashe tsawon mu daya, illa ita ta fini kauri da murzajjen jiki.
Na sanya mata sarkar na juya zan fito daga dakin, har na kawo bakin kofa ta ce "Zaynabu me zakiyi yanzu?” Nasa hannu na dauke hawayen da suke cike min ido, batare data gani ba, na ce "sallah zan yi" ta ce “to in kinyi sallar kizo kiyi mun kitso, ai kin iya ko?” Na girgiza kai da sauri na ce "a’ah ban iya ba". Daga haka nasa kai na fita.
Dakin da muke kwana ni da Haiti, wanda a yanzu ya zamo na kwanana ni daya wanda ke daura da nata na nufa, a bakin gado na zauna. Na kifa kaina cikin tafukana soma girza kuka. Na yi kuka har naji babu dadi tamkar zuciyata ta fashe. Wai uwar data haifeni ne wannan, amma kwakkwarar magana wannan ba zamu iya yi a junan mu ba.
Wasu tausasan hannuwa naji sun rungumeni tsan-tsan, dumammun hawaye na sauka a gadon bayana. Na yi hamzarin dagowa na dubeta, Nuratu ce. Nayi wata irin ajiyar zuciya mai karfi, wata rahmah ta sauka a zuciyata, nima na rungumeta sosai mukayi ta kukan mu tare, kuka maras dalili, maras tushe, illa na huce takaicin da zuciya ke ciki, da kuma matsananciyar kauna irin ta da da mahaifi da bazaka iya ganin dayan cikin damuwa ka iya jurewa ba.
Akalla mun dauki mitiuna goma a hakan, kamin ta ce cikin sanyin murya
"Zaynab kin yafe mani?”

Na mike tsaye a hankali na bata baya. Na isa ga taga ina kallon kifayen da ke watsalniya cikin akwatin ‘aquarium’ dake kudu maso gabas na dakin. Tunanin Inna na ya dawo mani. Na bude idanuwa sosai na kalli irin rayuwar daular da take ciki. Girman gidanta da alatun dake cikinsa, fadansa sai ya zama kauyanci. Motocin hawanta da gwalagwalai ba zasu lissafu ba, fadin abinda ta mallaka da nau'in rayuwarta, abu ne da ba zai taBa yiwuba, illa ince samanta da kasanta, hagunta da damanta duka arziki ne.
Duk da haka tana sane da irin rayuwar data baro Innata, a cikin karkara, dai-dai da rana daya bata taBa tunanin ya dace ta nemeta ba, ko bata rabi ni'imar da take ciki ba, taji a wane hali take bayan halin kuncin da ta barota cikin shekaru goma sha takwas!
A tsayin shekarunnan tsammani take Nuratu na wani wuri daban, Nuratu na cikin mummunan yanayi. Nuratu na cike da kewarta. Har ta dangana da kushewarta hakanne a zuciyarta Allah Sarki! A yau ni na gano mata saBani ga tunaninta. Nuratu ‘have already broke a new ground’ ta manta da ita, ta manta da iskar data debota balle Dan tayin shegen data barota da shi; ya rayu ko ya mace? Idan ya rayu wace irin rayuwa yake ciki? Wannan ba damuwarta bane tunda kuwa ita ta tsira da nata mutuncin, tana nan tana zuba mulki su kuwa ko oho…..! Na shiga girgiza kai da karfi, hawaye na fita min tarara. Ta taso a hankali idanunta jike da hawaye, ta karaso gareni, na bata baya ne don haka ta yi amfani da hannunta daya soma kyarma ta juyo da ni gareta, "wanna na nufin… na nufin baki yafe mini ba Zaynabu Abu.
Na rantse da Allah abinda kike tunani ba haka yake ba, labarin mai tsaho ne dana san babu wanda ya taBa gaya miki. Zan kaiki Paris ki sayi duk abinda kike so…. Zan bude miki (account) da duk abinda na mallaka …. Zan cigaba da kula da rayuwarki muddin rayuwata….. zan maido maki farin-cikin da baki samu ba shekaru goma sha takwas a gabadayan tsayin rayuwarki. Zan tsaya tsayin-daka domin inganta rayuwarki da abokin rayuwa nagari… A bayan raina kadai, wani zai kiraki ‘shegiya’ Zaynab…."
Na dago idanuna daketa ambaliyar da hawaye, na yi mata duban tsaf. Mace har mace, data baiwa arba'in baya. Amma tana magana irin ta yaran goye.
“Baki da arzikin da zaki saye dattin ki dake raina.
Ban taso cikin talauci ba, cikin rufin asiri na taso. Ban taBa kwana da yunwa ba, a tun bayan da kika hana mani nononki. Malam Ali yana da shanu, na sha daga nononsu na rayu har na kawo yau. Nayi dogayen kafafun dana zo na nemeki dasu.
Banzo nan don rashin sutura ba, da zaki kaini Paris din ki saya mani. Ko da nazo ba tsumma bane a jikina, kaya ne irin na 'ya'yan gata. Baki da farin-cikin da zaki bani, domin dubun ki sun sadaukar da rayuwarsu domin farin-cikina.
Wa yace dake rayuwa nayi cikin kunci? Saboda kin gudo kin barni domin tsira da siyasar ki? Kina kyashin in sha nononki, sabida ni shegiya ce?
A gidan Ubana na rayu, wanda sanin ta hanyar daya samar dani, bai sa ya guje ni ba, maimakon haka sai ya tsaya tsayin-daka domin ganin hakan bai takaita rayuwata ba.
Ya jani a ciki iyalinsa, duk da dattin dake jikina. Tun ban san kina ba ya mallakamin duk abinda ya mallaka. Ban zo gareki domin raBar inuwar arzikin ki ba, sai don daukar fansa.
To amma zuciyar musulunci da kaunar iyaye, ya canza manufata zuwa ta alkhairi agareki. Tunda kika haifeni kika dire, kin kara waiwayana? Kin kara komawa don ganin wace irin rayuwa nake yi? Sannan yanzu don kinganni rana daya, a matsayin cikakkar mutum kice wai zaki kula da ni? To wace irin kulawa?
Kashi zaki wanke mini ko tumbidi zaki share mini? Maganar zaki tsaya don ganin ba’a kirani shegiya ba, kin taBa jin an sakewa tuwo suna….???”
Kallona kawai take cike da mamaki, dimuwa da ta'ajjibi. Don bata zaci ina magana haka ba. Ta kai dan yatsanta ta saitin kirjinta ta nuna kanta tace “ni kike gayawa haka Zaynab?” Na sunkuyar da kai, ina share hawaye nace "kiyi hakuri, idan maganganuna sun miki ciwo. Ina amayar miki da abinda yake tamkar guba ne a cikin raina. Idan na barshi sai ya kassara ni, in kuma ci gaba da kallonki da shi. Ina kara gaya miki baki da kudin da zaki wanke dattinki da ke raina."
Zuciyarta

24, May 2025
Ibrahim

Thanks alot for the best novel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login