Showing 30001 words to 33000 words out of 45361 words
Chapter 11 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
ba kwanakin baya-bayannan nake ganinta ta kama hannun Faruq sun tafi makarantar firamare ba?” Tace "eh to, gatannan ko yanzu akayi mata aure, gobe zata haihu”. Ya dade yana kallon hoton, cikin wani sabon yanayi atare dashi ya ce "Inna Rabi, Nuratu kyakkyawa ce”. Ta yi murmushi tace “don ma baka ganta tana shekaru biyar ba, sai kace 'yar tsanar roba ce. Da bakin mutane na kama Nuratu, da bata kawo yanzu ba. Hatta kank nin yaro Faruq ya kance Nuratu mai dogon gashi, duk garin nan babu mai kyanta. Da bata fini tsawo ba da na aure ta" suka yi ta dariya. Bai tafi ba sai da ya jona mata kan ‘telephone’ a dakinta domin su rinka gaisawa, ta kuma rika jin halin da yake ciki. Haka ya koma cike da tunanina a ransa.
Da na dawo gida na tarar Ya Rabi tayi kan telephone, na cika da mamaki, kafin na kama tambayar dalilin da zai sa Malam yayi haka, wato ya sanya mata bai sanyawa Inna Dubu ba, ya yi dariya yace “bani bane na sanya mata, danta Sa'idu ne”.
Ba tun yau nake jin sunan Sa'idu a gidan ba, to amma ban zaci yayi girman da har zai sayi telphone ba, a wancan lokacin kam ba karamin mutun ne zai sanya kan telphone a gidansa ba, sai ya zamanto har makotanmu masu mu'amala da birni, kanzo cin aziki dakin mu, har numbar suke badawa a bugo musu, in je in kira su suzo su amsa. To nima sai na sahiga karbar lambar kawayena na makaranta da suke a nesa, muna gaisawa.
Rannan Ya Rabi ta shiga wanka, ni kuma ina sharce kaina dana wanke. (Telfon) ta shiga kira, tayi har ta tsinke ban dauka ba, ina cigaba da abinda nake mai kiran dai bai hakura ba, ya sake kira a karo na biyu, wannan karon ma sai data kusa tsinkewa kamin in aje kum din in amsa da
"sallamu alaikum, mai telphone din ce ta shiga wanka" yayi dariya yace "hala kece Nuratu?” Na cika da mamaki bance komai ba, ya sake cewa "ko ba Nuratu bace, Nuratu mai dogon gashi?” Na yi murmushi nace "hala kaine Sa'idun dake England?”
Ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi yace "na dade da son jin muryar Nuratu, na dade da son ganin Nuratu a zahiri. Ban zaci muryar Nuratu yayi taushin haka ba, ban zaci ajin Nuratu ya kai har haka ba, ashe Nuratun classic babe ne? Irin wannan JAN AJI haka?”
Ban san sanda nayi murmushi mai sauti ba, nace "ina wuni Yaya Sa'idu, yaya sanyin England?” Yace "Sanyin nata har ya kai sanyin muryar Nuratu?” Nikam ban saba jin irin wannan maganganun ba, don haka na ji duk na takura, don ni ban taBa tsayawa wai in saurari wani saurayi ba, tunda nake, ko irin malaman mu na makaranta da ke cewa suna sona, kara nake kaisu a koresu, don a ganina ai iskanci ne ace ana son ka. Don haka da Sa'idu ke min wadannan maganganun da basu dace da wadanda na saba ji a bakin mutane ba, sai naga to me yayi zafi da zan takurawa kaina da cigaba da hira da shi? Na yi hanzarin cewa "ka sake kira in an jima kadan, lokacin ta fito". Ba kuma tare dana bashi damar kara cewa komai ba, na ajiye.
Tun daga ranar ne kuma idan na lura Sa'idu ya kira Ya Rabi, sai in fita daga dakin in Buya a bandaki. Kiran duniyar nan zatayi min ba zan amsa ba, sai sun gama yayi mata sallama sai na shigo, ta ce “Sa'idu yana gaisheni, tayi ta kirana mu gaisa bata ganni ba”. In ce “ina amsawa”. Shi kuma ba yadda za’ai ya kira bai ce ta nemoni mu gaisa ba kamar maye. Kai tun bata ganewa da gangan nake fita, har ta gane, sai ta yi min dabara, ban sani ba.
Da lokacin kiran nata da yake yi yayi, sai tace dani "au dazu kin fita ke da Halima, kawarki 'yar Hadejia ta yi kiranki, nace bakyanan amma bakiyi nisa ba, ta ce zata sake kira nan da rabin awa". Don haka na zauna bakin waya a kalla awa daya zaman jira kiran Maryam Hadejia, calssmate dina. Kiran yana shigowa kuwa na dauka babu ko sallama nace "shegiya Maryam, kina can mukus a Lagos abinki, kin bar mu da zafin Arewa" daga can Bangaren aka ce "ke kuma kina nan mukus a Gwarzo ba, wai Nuratu ashe daman baki da kirki?” Nayi murmushin gane mai Maganar, a shagwBe nace “kai Yaya Sa'id, amma ka shammace ni…” yace "in tambayeki Nuratu, samari nawa kike jawa aji, irin yadda kike ja min?” Na kyalkyace da dariya nace "Allah ni bani da wasu samari, ka tambaya Ya Rabi ma" ya ce “to don Allah, gani, ko nayi maki tsufa ne in aske furfurar?”
Nayi dariya don ni maganarsa a wasa, na dauketa nace "lalle ma Yaya Sa'idu, zolayata kake yi, kai da kake can kana kallon masu jajayen kunnuwa da jan gashi, me zakaci da wata 'yar kuayen Gwarzo?” Yayi murmushi cikin nishadi yace "ai kema jajayen kunnuwan gareki. Allah Nuratu baki san irin aji mai matsayi da muhimmanci da na sakaki bane. A hoto kawai na ganki, kin hana mani barci. A tafe nake, a zaune, a tsaye ko a kwance, tunanin Nuratu nake, mafarkin kasancewarta matar aurena nake kowanne dare. Jiya ma ganinta na yi cikin barci na, rungume da 'yan tagwayena, mace da namiji, tana shayar dasu nono, baki gansu ba jawur dasu kamar Nuratu ………” na katse shi ina dariya da cewa "kai don Allah Yaya Sa'id?” Yace “Allah wallahi da gaske nake Mummy Nuratu" muka yi ta dariya kamar wasu shashashu, ya bini ya maida kansa yaro kamata muka yi tayi. Wallahi tun daga ranar na fara kaunar Sa'idu.
Son sa da kaunarsa ya soma bin jinin jikina, domin yana daga cikin irin mazan da nake burin aure ta kowanne fanni. Ina son na auri namiji mara girman kai, karya da nuna isa, barkwanci da nuna kauna hakanan mai ilimi. To Sa'idu duk ya tattara wannan har ya zarta da wasu.
Ban taBa ganin shi ba, a waya kawai na soma kaunarsa, a waya ya ginawa kansa babban matsayi a zuciyata da ni kaina ban san iyakarsa ba.
A karshen shekarar ya zo hutu, a ranar na samu kaina da yin kwalliya, da ake kira kwalliya, irin wadda ban taBa yi ba. Na yiwa gashina gyara mai suna gyara, irin wanda bai taji ba. Na yiwa kumbana fenti da lalle jawur, kamar wata sabuwar amarya. Yaya Rahi sakin baki tayi galala! Tana kallona kamar a ranar ta fara ganina, ta ce "Nurtu haka kike da kyau kamar aljana? Shin ina zaki ne? Wannan kwalliyar bata dace ki yiwa kowa ba sai mijinki". Domin su kansu kayan jikina masu fidda sura ne, idan a Gwarzo ne ba za'a barni in yi dinkin ba, to Maryam kawata ta kawomin su daga Lagos a dinke, riga da siket ne ‘fitted’, na wani bakin yadi mai santsi da adon jajayen fulawoyi.
Ita bata san don Sa'idu na yi wannan kwalliyar ba, don ko a mafarkinta bata kawo wai soyayya muke a waya ba, abinda ta dauka shine hira ce irin ta wa da kanwa, domin bana fadin abinda har zata digama ayar tambaya, shine dai yake ta aman soyayyarshi kamar wani Romeo, ni kuma ina kasancewa cikin nishadi.
Na tabbatarwa kaina idan na yi sa'ar auren Sa'idu, na yi babbar sa'a, domin namiji ne mai masiffaffar soyayya da zai iya mai da kansa sakarai akan macen da yake so. Na kan kissimawa raina kamanninsa? Ko yaya yake? Dogo, gajere, baki, ko fari? Mai kiba ko siriri? Oho, koma wada ne, nidai ina son kayana haka, zan kuma cigaba da son shi muddin rayuwata.
Sai kawai gashi tsaye tokare da kofar dakinmu, hannun sa daya a jikin kyaure, daya harde a bayansa. Baki ingarman gaske da a turance ake kira 'giant, yafi fadi daga kafadu sannan kafafunsa tsayayyu ne. Baki ne sosai da (weather) din kasar England ya maida ‘cool' kuma bakin shi bai Boye fararen idanunsa ba.
A kiyasce yayi shekaru talatin da takwas, a yayin da ni kuma keda sha bakwai. Kenan tsiran mu ba kadan bane. Gashinan dai fes, kamar wankan inji, ban taBa ganin cikakken namiji mai haibar Sa'idu ba har yau. Dole duk wata lafiyayyar mace, tayiwa kanta sha'awar mallakarsa, ba-katsinen usuli, mai tsaka tsakin kyawun sura.
Ni da shi tsayawa muka yi cirko-cirko, kamar zakaru muna kallon-kallo. Ba sai an gaya mani ba jikina ya bani he is the Sa'id I'm dreaming of. Ya saki kofar yana murmushi yace “idonki kenan Nuratu?”
Na kai yatsuna da suka sha adon lalle, na rufe fuskata ina dariya, cikin wani irin nishadi da soyayya mai tsanani, ya karasa shigowa cikin dakin yayi ido hudu da Yaya Rabi, dake kwance tana sauraron rediyo bata lura da tsayin mintunan daya Bata a tsaye cikin kallon soyayya ba, ta yunkura ta mike ta ce “oyoyo Sa'idu na! Da akwai katon zani da zai goya min katon mutum kamar ka, yau da na goya ka."
Ya shiga sosa keya cikin alamun sarakuta, yau kunya sosai yake nunawa ba kamar da ba, ita bata ma san yana yi ba, ta cigaba da oyoyonta. Inda duk ta mika hannu, sai ta zaro mai abin sawa a baka tana cewa "wannnan ma kai na ajiyewa, kaga gyadar nan yau satin ta guda da soya maka, na san ka da son gyada".
Tana bada baya domin kawo mashi abinci, ya yi tsalle ya dawo gabana, a yayin da ni nake still a tsaye tamkar an kafeni da kusa, yace "this is not the kind of welcome I expect from you…"
Na ja da baya ina dariya, na ce “wacce iri ka tsammana? Duk wannan adon da nayi domin ka?” Ya kuwa bini da ido ‘up to down' ya sauke su a yatsun dana rufe fuska da su, yace "eh, an yi mun kwalliya kam, to amma ai ba'a barni na gani sosai ba an kama an rufe fuskar" ya kai hanu ya sauke hannun daga fuskata, wani irin ‘shock’ daya sameni ya tunasar dani tunda na kawo haka, wani babban namiji bai taBa kama jikina ba. Ya sunkuyo da kuncinsa dai-dai bakina yace "c’mmon! Give me a welcome kiss…." numfashinsa da lallusar kamshin dake tashi jikinsa na dukan hanci na, ya tayar da tsigogin jikina gabadaya, nayi ta maza naja baya da karfi na bugu da bango ina fidda numfashi a wahale. A sannan ne Ya Rabi ta dawo dauke da tray data shako da kayan abinci nau'I-nau'I, yayi hamzarin amsarta yana ta jera mata sannu, nan ya nade hannun riga yana kwasar gara yana zuba santi, tare da gaya mata yadda yayi kewar abincinta. Duk yadda ya so mu keBe a ranar bai samu hakan ba, domin babu hanya. Ya Rabi tana dakin bata je ko'ina ba, to a wanne dalili?
Haka ya wuni kame-kame, Nuratu in ga littafinki na makaranta? Nuratu naji Halima ta tsayar da Malam Harisu, ke kuma wa kike tsayar? Duk rabi Yaya Rabi ke bashi amsa, ni dai iyakata murmushi da daga kai, eh, a'ah.
Tasa wani almajirin Malam ya share mashi daki, na shigar masa da jakunkunansa, da daddare kenan. Ina shirin fitowa ya tare min hanya "wai ni har yanzu ban ji inda kika sa gaba ba" na ce "nasa gaba kamar yaya?” Ya fizgoni jikinsa yace "that’s the kind of welcome I like". Ganin muna neman shiga wani limit, daya wuce tunanina, na kuma san ba dai-dai bane duk da wata irin duniyar dana tsinci kaina, na kwaci kaina da kyar na ce "a’uzubillah da kai Sa'idu. Kana mantawa nan ba Ingila bane, mu musulmi ne diyan musulmi, idan ka manta in tunasar da kai. Ban zanci a duk inda ka samu kanka, duk runtsi zaka yada tarbiyyar Malam ba. I really felt disappointed…" hawaye suka zubo min, na juya na fito na barshi kamar mara lafiya ko magana baya iya yi.
Dana dawo daki na kwanta ina tunani, sai na rinka tambayar kaina anya Sa'idu yana kaunata? He didn’t seem a real lover, but an expert deciever, watau kwararren mayaudari ne kawai. Ban san mecece soyayya ta hakika ba, amma na sha jin kawayena na cewa, duk namijin dake taBa yariya a waje, ba aurenta zai yi ba, kuma ko ya auretan ba zatayi wata daraja a wurinsa sa ba. Na yi kuka na yi kuka amma na kasa yakice Sa'idu a raina, duk yadda na so yin hakan kuwa.
Da safe suna gaisawa da Rabi ni ina shan koko, ko kallo bai isheni ba. Babu ko kunya ya badawa idonsa toka wai "Ya Rabi, me na yiwa yarinyar nan ne take ta hararata?” Ta dubeni na sadda kai ina mamakinsa, da tsinewa bature daya murje wa dan bahaushe kunya. Ta ce "haushi take ji kaki kunce jaka har yanzu ka miko mata tsarabarta”, haushin Ya Rabi ya kamani amma ban tofa masu ba, yayi murmushin daya kara masa kyau yace “ayya Nuratu - hasken al'umma, me kike ci na baka na tsiyaya? Ai ke tsarabarki ‘exraordinary’ ce, ba sai an bude jaka ba, jakarki daban ce, sukutum za’a miko miki ki bude abinki da kanki".
Sa'idu yana da wata tafkekiyar gona, tana can a bayan gidan mu. Yana kiwon fararen dabbobi da shuke-shuken kayan marmari. Duk zuwan da yayi a can yake karar da yawancin lokutansa, haka duk dan abinda ya tara a gyaranta da kara ingantata yake tafiya. To balle yanzun da yaje ya karo ilimi kiwo irin na turawa ai san abin ya kara haBaka.
Kullum zai fita tun safe yana can tare da ma'aikatan suna ta gyara gidan gonar, don haka in ya fita sai yamma lis zai dawo gidan. Don haka Rabi ta dauki nauyin aika masa abincin ranarsa can gidan gonar, kuma wani kuskure da tayi, a wuyana. Ta haka Sa'idu ya samu ya lallasheni da dadadan kalamai na yaudara, tareda yin amfani da masifaffen son da nake mishi ya wanke kansa daga wancan zargin da nayi masa a baya.
Ya ce shi bai yi da wata manufa ba, is just to show me how much he is eager to see me. An ce so hana ganin laifi, tuni na yafe masa muka shimfida soyayyah mai korran ganyayyaki. Haka dana yi la'akari daga kasar da yake rayuwa sai nayi masa uzuri, nasan kuma soyayya ta kansa komai, kuma shi yana kokari ma sosai musaman ta fannin Ibada ina jinjina masa, dole kowanne Dan adam yana da ajizanci, kuma daga ranar koda wasa bai sake kwatawaba.
Mukan wuni sur cikin gonar cikin fararen dabbobin nan, shi yana watsawa tantabaru gero, ni ina tusawa dokin sa abinci a baki, haka muke ta hidima da dabbobi da tsintsayen har sai rana tayi anyi sannan mu koma gida, da yake nima ina cikin hutu ne.
Ya gaya min watanni uku zai yi ya koma amma kafinnan saida wata kwakkwarar magana a tsakanin mu, sai yaje yayi mun shirye-shiryen da suka dace kafin in zana jarrabawar WAEC ya dawo a daura mana aure ya tafi dani. Hakan kuwa aka yi, ya sanar da Malam Ali maganar mu, amma nauyi da jin kunya ya hanashi sanar da Ya Rabi wadda a lokacin ta soma zargin soyayya a tsakanin mu, ko yaro kankani ya dubi kwayar idanun Nuratu da Sa'idu, zaiyi shaidar zuzzurfar soyayya.
Tunda Sa'idu ya tafi, sai na koma wata irin sukuku, gani nan mai lafiya, ba mai lafiya ba. Na koma yin komai ‘slowly’ na zamo ‘calm’, kamar mai ciwon sikila. Hoton Sa'idu cikin ‘snow’ da na sace cikin dakinsa ba tare da sanin sa ba, shine na mayar abokin barci na, kullum yana karkashin pillow, motsi kadan in jawo in kalli abina.
Haka a daddafe na zana WAEC na kammala sakandire, sai zaman jiran dawowar abin kauna. A kullum ranar Allah sai mu share awa gauda muna hira a waya, ko tausayin aljihun sa baya yi shida yake dalibi, saidai ni inji tausayinsa in katse layin yadda ko ya kira ba zai shigo ba.
Watanni suka shude suka zama shekara, na soma kidaya ranar zuwan Sa'idu, domin yace wannan karon bagatatan zai yi min ko ya kamani da saurayi na muna zance. Don haka ne tunda aka shiga watan 'December' na kasa tsaye na kasa zaune, a kullum sai na share dakin Sa’idu sau uku, lalle kuwa da yake yana son ganina da shi, kullum cikin tisawa nake.
A kuma ranar wata laraba ne malam ya yiwa Yaya Rabi maganata da Sa'idu da yace da shi yana dawowa sai a daura auren, domin hatta gidan da zan zauna ya kama mani a can London, da visa ya samar min.
Da daddare inata faman tisa lalle a kumbata, Rabi na zaune a gefena tana kame min kalbar data yi min da robar kyauro don kada ta warware, ta dubi lallena tayi dariya ta ce "su Nuratu manyan duniya, duk wannan lallen na tarbar zuwan maigidan ne?”
Na cusa kaina a cikin rigarta, saboda matsananciyar kunyarta da naji, tace "a’ah ni cikani, kada ki karya ni banga auren naki ba. Amma Nuratu duk kwalisar nan taki, da yangar da kikewa samari, ki rasa inda zaki kare sai a mai mata?”
Na wani irin zaro kaina daga jikinta cikin ‘slow motion’ nace "MATA? Wane ne mai matar?”
Ta yi tsaki tace "kina nufin baki san Sa'idu yana auren Sa'a 'yar kanwar Dubu ba? Tana can Ingilan
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel