Showing 39001 words to 42000 words out of 45361 words
Chapter 14 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
da kaina akan cinyarta nace "Nuratu na kawo miki karar Dan dukusurunki".
Ba ita ba hatta Faruq basu san sanda suka fashe da dariya ba. Ya kuma koma yayi dif, ya dinke, kamar bashi yayi ba, ya ce "ke, wanene Dan dukusurun? Ina wasa dake ne?” Na dube shi cikin kwayar idanunsa, tuni ya koma Ya Faruq dinsa, ya shiga sosa keya da ‘yan mukullayenshi domin bayewa Mamie halin da ya samu zuciyarshi da gangan jikinshi a ciki, yace " Mamie yariyar nan zan soma zane ta, ta fara kawo min wargi” tace "me Dan dukusurun nawa yayi miki, a gaya mun inyi hukunci” na ce "haka kawai yake shareni, ko ya kirani muguwa, sannan bashi da lokaci na".
Ta maida dubanta gareshi, tana murmushi ta ce "to kai Dan dukusuru na kaji laifuffukanka, ko kana da ja?” Yace “eh, ita ce duk ta jawo Mamie” “da ta yi me?” Ta tambaye shi. “Ta taho kan gaban kanta, bada izinina ba, ta tayarwa da Malam da Halima hankali. Inna Dubu har yau bata daina kukan tafiyar Abun ta ba. Har da bar min wata banzar wasika wai wani "DA FATAN WATA RANA ALLAH YA HADA MU CIKIN ALHERINSA". (Sunan littafin Takori mai zuwa).
Mami ta yi murmushi cikin jin dadI, ta jinjina kai tana yiwa Allah godiya, a bisa rahamomin da yake yi mata. Ta ce "to ai gashi a yanzun ya hadaku cikin alherin nasa, sai ku yafi juna.
Ita kanta rayuwar da komai dake cikinta dan afuwa ne. Da Allah baya afuwa a garemu, da dukkan mu bamu kawo yau ba.
Wanda kuma duk yayi afuwa ga dan uwansa musulmi, shima Allah zai masa afuwa. Ba mamaki a lokain tana cikin ‘tension’ ne da har ba zata tsaya yin tunanin abinda ya kamata ba, ka yi hakuri ka yafe mata!".
Kallon da yayi min da wani irin murmushin da bai taba yi ba, kuma bata ganinsa da shi ba. Shi yasa ta tashi ba shiri ta bar mana falon.
Ya taso ya dawo gabana tamkar ya shige cikin jikina, yace "Eye. na'am, maimaita sunan a bakinki Zaynab?” Nayi kasa da murya sosai. Na ce “YA FARUQ" yace “ashe kin gane, to ko kef a? Wancan sunan na Nuratuna ne ita kadai. To yaya? Bani labarin hijirarki dalla-dalla, har na 'yan fashin da suka kusa yi min shigar sauri….” na mike na zaura daki da gudu, babu ko waiwaye, yana kirana amma ban juyo ba.
*** *** ***
Daga Singapore Paris muka wuce, birnin Suisra. Nuratu ta saya min sittiru kamar har abada bazan sake sayen wasu ba, takalma da jaka da kayan kawa na mata, kai ka ce katafaren shago za’a bude. Kayan shafa da turare, wannan ba’a maganarsu. Su kansu su Faruq sun girgiza da dukiyar da take kashewa a kaina. Amma ita din ko a jikinta. Imran tun daga Singapore ya hau jirgin gida Nijeriya ya koma Sokoto.
Muna shirin tahowa ne wani babban al'amari da ya dimautamu ya faru, an yiwa Aunty Hibbani waya daga Chadi, ana gaya mata rasuwar Ahmad Fiance din Haiti a sanadiyyar hatsarin jirgin sama. Jikkunanmu suka yi sanyi kalau. Na daga kai na dubu tsibin kayan auren Haiti, da ake shirin yin lodinsu, amma wai duk sun tashi a banza.
Tausayin 'yar uwata ya kamani. Ni din shaida ce akan matsanancin son da take masa.
A take Mamie ta nemi da a canza mana ‘booking’ zuwa Malaysia domin mu taho da Haiti, wadda a karshen satin dama zata dawo. Aka sanar da ita babu jirgin sai sati mai zuwa, tunda ba passenger. Tayi alkawarin saye sauran kujerun gabadaya, muka daga zuwa Malaysia, inda muka kara hawa wani jirgin muka karasa makarantar su Haiti (University of Malaya) dake a Kuala Lampur.
Allah sarki Haiti! Da gudunta ta taryemu, ta rungume wannan ta koma ta rungume waccan. Daga karshe ta kama ni tamakalkale tana kyalkyatar dariyar farin ciki. Tare da ita muka taho a washegari, babu wanda ya gaya mata sai da muka dawo gida Yamai.
Kwatanta halin da ta samu kanta a dan tsukin ba zai fadu ba, tayi kuka ta yi ciwo daga baya ta dangana. Shi Faruq ya wuce gida Gwarzo domin sanar da Malam halin da ake ciki.
A karshen satin muna cin abinci nida Haiti, misalin karfe hudu na yamma. Muka ji dirin motoci da wani irin cin taya mai nuna anyi doguwar tafiya mai dogon zango.
Mami ta sakko daga bene cikin shiga ta alfarma, rike da falmaran din Alhaji Badeggi zata kai masa dakinsa domin yana shirin fita ne, a cewarsa suna da manyan baki da zasu tara a (Guest House) din su. Kamin in idasa goge bakina da ‘tissue’ in mike don fita ganin su waye? Iftihal da Azizah, sun fado a tsakiyar falon mu, suna kira da babbar murya
"Ina Aunty Abu? Gamu nan mun biyo ki tunda mu, kin guje mu".
Sai kuma ga Inna Dubu, Hajiya Azumi da Inna Rakiya. Na mike jiri na kwasata, kafin in kai ga su Ifitihal, na fadi, na sume. Lallai wani fairin cikin yafi gaban kuka, ko dariya.
Na bude ido a hankali, Imran da Iftihal ne suke min firfita. Na mayar na rufe, a hankali na kamo hannun Ya Em, sannan na Iftihal, Azizah ta dora hannunta akan goshi na tace “haba don Allah Aunty Abu, ki tashi, me yayi zafi har da suma? In baki son ganin mu ai sai ki gaya mana mu koma, ba ki fadi ki suma ki tayar da hankalin masu kaunarki ba. Ke dai ban san yaushe zaki daina yawar nan taki ba!”.
Nayi murmushi, kana na mike na rungume su. Wasu hawayen suka shatato mini, wani na bin wani. A hankali nace “Azeezah, you are always the way you are (kullum kina nan a yadda kike)” ta ce
“naji, ki tashi ni don Allah muje, BABA yana kiran ki”.
Dam! Dam!! Dam!!! Zuciyata ta buga, kirjina ya harba, kwakwalwata ta hautsina kamar ince da ita wane Baban?
To amma wannan tambayar ma ai rainin hankali ce a gareta. Baban guda nawa ne? Banda Babana ABBA BABA SA'IDU? A hankali dai, cikin matsananciyar fargaba, na yunkura na mike muka jero mu uku a tare. Su Mama Hajiya Azumi, suka bimu da kallo cikin kauna da sha'awar da muka basu. Nuratu ta dubi Hajiya Azumi, ta ce
“Allah shine mai GIRMA, amma ba kowa ba!”
Inna Dubu ta ce “wannan haka yake, Allah shine mai GIRMA! Mu duka shirme muke amma shi kadai yasan abinda ya boye a rayuwar bayinsa". Suka girgiza kai cikin karuwar Imani a zuciyoyinsu
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Allah sarki Yaya Rabi, koda hakan ta faru dani bata yi fushi da ni ba. Daga baya ta hakura ta fawwalawa Allah al'amarin. Ta kuma ta dauki dukkan laifin da fushinta mai tsanani ta dora akan Sa'idu. A cewarta ba hali na bane, koma menene shi ya koya mini. In ni yarinya ce ai shi mai hankali ne, da har yake da aure har da Da, anjima kuma sai ta yarfa hannuwa ta ce "wannna rashin tsoron Allah da mai yai kama? Wannan duniya ina zata da mu? Wanda ka amincewa shi yake cutar ka. Wanda ka yiwa alkairi shi yake maka sharri. Idan na cuci Sa'idu a tsayin zamana da shi, da yayi min wannan sakayyar, Allah ka fitar mishi. Nima ka fitar min hakkina akan wannan cuta da cin amana da yayi mini”.
Daga baya har mukan zauna mu koka al'amarin a tsakanin mu. Ina kuka in ce “ni bana tausayin kaina, sai na abinda zan haifa. Me zan gaya masa ya yafe min samar da shi dana yi ta dattin zina? Wallahi ni kaina Ya Rabi, ban san ya akai hakan ta faru da ni ba, ji nake kamar cikin mafarki, sai daga baya na Ankara, na gane ashe ba mafarki nake ba, zahiri ne".
Sai ta share hawayenta ta ce "ni kuma ke nake tausayi. 'Ya mace kike, komi Sa'idu ya yi nasa ado ne, kece keda kaico!
Duk wanda ya aureki nan gaba sai ya goranta miki. Haka dan cikinki da kyar idan zai yafe miki. Ki daina cewa kina jin tausayin sa, muddin ina raye, ba zai taBa sanin cewa bani na haife shi ba".
Na fiddo ido na ce "me kike nufi?” Tace “ina nufin ni zan zamo uwarshi. Malam Ali ya zamo Ubanshi. Idan har su Dubu sun rike wannan amanar. Shi kuwa Sa'idu bar ni da shi, yace ya taba sanina ma balle abinda kika haifa, sai ya gwammace uwarsa bata haife shi ba, sai ya gwammace bai taBa sani na ba. Zan nuna masa bakar Rabi, don farar Rabi ya sani". Anan kuma sai ta koma irin sambatunta na tsinuwa da la'anta Sa'idu, wani zubin kuma sai ta sa kuka.
A lokacin Faruq ya fara hankali, domin ya gama aji uku na sakandire. Ya damu da rashin walwalata da rashin fitowata muje yawo yadda muka saba.
Sai yazo dakin mu ya sani gaba yayi tagumi yace "Nuratu na baki da lafiya ne?” Inyi ta muku-mukun Boye cikina, cikin katon hijabin da nake zurmawa, hawaye ya zubo mani. Yau nice na zama daddawa, daga daki sai daki, ko baki akayi a uwar daki Rabi ke kulleni, idan an tambaya ina Nuratu, tace bata nan. Ba’a gaya masa ba, amma shi da kansa ya fuskanci halin da nake ciki. Jikinsa ya yi sanyi lakwas, ya zama wani zalau, kamar bulala, sai dai ya bude baki yayi magana ya kasa, sai dai ya yi ta bina da ido.
Cikin wannan halin ne a watan July, a wata laraba nakuda ta kamani. Cikin daren nayi ta murkususu ni kadai, kamin asuba na haifeki. Ko irin kukan da jarirai keyi a yayin da suka iso duniya, ke baki yi ba, wanda ya sani tunanin watakila kema kina bakin cikin zuwanki duniyar, kuma har zuwa wannan lokacin babu Sa'idu, babu labarinsa. Sa'a ta janye kayanta tsaf, don ko 'yar wayar da yake yi min fiye da watanni uku ya daina.
Yaya Rabi ta daukeki ta yanke maki cibi, idanunta cike da kwalla da bakin cikin da harshe ba zai iya bayyanawa ba. To amma wata kudura ta Ubangiji, daga ni har ita mun kasa dauke idon mu a kanki. Wata irin kauna irinta da da mahaifi ke ratsa zuciyar kowannen mu, kamar mu dake, har ta Baci, kwata-kwata baki yo komi na Sa'idu ba. Gashi yala-yala har ya rufe idonki, sai da ta dauki sabuwar reza ta rage shi, sannan kika samu kika bude idanunki, farare kal, kika kuwa tsayar da su a kaina.
Hankalina ya tashi, tsoron ranar da zaki sake tsareni da wadannan idanun, ki tambayeni dalilin gurbata maki asali da nayi, shine ya gigita ni, wanda ni kaina ban san amsar da zan baki ba.
Hakannan bana jin zan iya kara hada ido da mutanen dake cikin gidannan, musamman Inna Dubu, Malam Ali da kanina, Faruq. Wace irin tambaya zai min idan ya ganni rungume da jariri, alhalin ya san bani da aure? Me zan yi in wanke bakin cikina da zai sameki, idan kika fara hankali? Tambayoyin suna da yawa, wadanda suka gigitani, har na fara tunanin guduwa, in da ni kaina ban sani ba, ba don komai ba sai don tserar da mutuncina da naki, wanda na tabbata furucin da Yaya Rabi tayi, na maisheki diyar cikin ta, ba zai yiwu bw in har ina nan.
Domin kauna ta da da mahaifi ta wuce misali, ta kuma wuce duk wani bad-da kama da za'a yi a Boyeta, na kuma tabbata Rabi zata kula da ke, fiye da yadda ni zan iya sakin jikina in yi hakan. Uwa-uba ina neman yadda zan yi inyi nisa da Sa'idu, nisan da har abada ba zai taBa sanin in da nake ba.
Ban san dalili ba, amma na tsani Sa'idu, ko sunansa ba na son ji. Ko mai irin kamanninsa bana fatan sake gani a rayuwata, balle wata mu'amala ta hada mu. Ban taba sanin soyayya na komawa kiyayya ba, sai a kaina da Sa'idu. Allah kuma shine masanin wannan sirrin.
Cikin duku-duku asubahin dai Yaya Rabi taje ta taso Dubu, ta zo ta daukeki tana share min hawaye tana istigfari. Ta je ta taso Malam shima ya zo jikinsa babu inda baya rawa, abinda ya fara yi bayan lakanta maki kalmar shahadah, shine ne tofa miki addu'ar kariya daga zina a al'uararki. Ya kuma ce Allah yasa ke cikon addinin musulunci ce. Ya kuma dauke ki a matsayin wata kyauta gareshi daga Allah (S.W.T), saboda duk 'ya'yan da ya haifa mutuwa suke, Faruq kadai ya tsaya. A lokacin ne yayi maki huduba da Nana Zaynab. Ya kuma kiraki ‘Kyauta’.
Dubu ta je ta dora ruwan zafi a murhu don yi min wanka. Malam ya tafi masallaci don bin jam'in sallar asubahi, a daki kuma Rabi ta shiga ban daki domin gabatar da alwalar sallar asubahi. Na daukeki na rungume a jikina tsan-tsan, hawayen dake ambaliya a kuncina na jika taki fuskar, na kuma kura maki ido, kurr! Sai dai a raina nasan ba kallon karshe nake miki ba, ko ba dade ko ba jima nasan zaki bi ni, duk inda nake, in har ni na haife ki, in kuma muna raye.
Maganar kulawa kuma bani da kaico akanki, inada yakinin zaki samu kulawa ta uwa da uba da dan uwa, irin wanda in ina nan, ba zaki sameta ba. Don haka nayi gaggawar ajiyeki, ina da kudi masu yawa ire-iren wadanda Sa'idu ke bani in zai koma, ba kuma abinda nake yi da su, don haka na kwaso su na zuba a jaka. Duk ciwon dake jikina, rashin karfi da jirin dake kwasana, amma a haka na dafa bango na yafa mayafi na fito.
Dubu na daga can madafi, ta durkusa tana ta hura wuta a murhu idanunta sai tsiyaya suke abin tausayi, da gani irin azababben utacennan ne Allah ya hadata da shi, nayi sanda na wuce zaure, malam bai rufe kofar ba bayan fitarsa masallaci, don haka ban wani Bata lokaci ba wajen ficewa.
Almajiran Malam duk suna cikin shagon su, wasu kuma suna kwankwance suna barci a harabar gidan, yayin da masu hankalin sun bi malam masallaci. Sai bayan da na danyi tafiya ne na fuskanci jini yana zuba a jikina. Don haka nasha kwana a wani lungu da babu kowa, na sunto dankwalina nayi kunzugu dashi sannan na cigaba da tafiya ko gani bana yi sosai.
Ban dauki hanyar tasha ba don nasan can ne waje na farko da Malam zai sa a fara bi na. Na rika bin gefen titin fita garin Gwarzo bana ko waiwaye. Na yi tafiya a kalla (kilo mita uku da rabi) kafin in ji wata mota ta makeni akan kwalta. Saboda jinin da ke kwasata, ban san cewa a tsakiyar titi nake tafiya ba.
*** *** ***
Na bude ido ne na ganni kwance a gadon asibiti, ana yi min karin jini. Domin na zubar da jini da yawa. Hannuna na dama daure cikin bandeji, gwiwoyina da wasu bangarori na jikina duk sun kukkuje. Daga baya ne likita ya shigo yake gaya min na samu karaya ne har biyu a hannuna na dama, sai 'yan kujewa da ba'a rasa ba, sannan ya fadi abinda yayi matukar bani mamaki, wai mijina daya kawoni ya tafi gida, yana dawowa zuwa karfe shida na yamma. A lokacin kuma hudu ta yi har da mintuna ashirin.
Ya sake kallona sosai, ya ce ina "Baby din naki? Ai zaki iya zama tare da shi anan gadon asibiti, ko don kada nonon ki yayi ciwo. Idan yazo kice yana iya dauko miki shi" na bishi da “to" kawai.
Na lumshe ido a hankali, in saka wannan in kwance wannan. Ni Nuratu kuma kaddarorin da Allah ya dora min ke nan? Na tabbatarwa kaina ba zan zauna har sai na warke a sibitin nan ba, koma yaya ne, ina bukatar yin nisa da Kano. Nan kuwa nasan ba zai wuce Kano din ba, don kuwa itace mafi kusa da Gwarzo.
Na kai dubana ga mamana da suka cika tam. Suna shirin fara zuba, wani gululu yazo ya tokareni kamin in balle da kuka. Kuka sosai wanda ba zai wanke radadin dake raina ba, ba zai wanke tausayinki da tausayin halin dana baroki ciki ba, ba zai wanke takaicin rabuwata da 'yar uwata ba, da muka taso tare tun zuwana duniya, ba zai wanke tunanin masifar dana jawo mata, na gudu na barta da shi ba, ba zai wanke radadi da kulafucin uwa ga danta, dake narkar da zuciyata ba.
Misalin karfe shidda na yamma, aka turo kofar aka shigo. Wankan tarwada ne makimanci ga shekaru arba'in. Yana da tsagin barebari biyu-biyu a kuncinsa, mutum
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel