Showing 45001 words to 45361 words out of 45361 words

Chapter 16 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt

jihohin mu. Na samu Baffannina muka tattauna, mijina ma ya bani goyon baya dari bisa dari. Ba jimawa na tsaya takara, Kangiwa suka tsaya mini, talakawan garin Damagaram suka yi min alkawarin kuri’unsu, domin Babana.
Ana yin zaBe kuwa na lashe, wannan wani abun tarihi ne da ba’a taba samunshi cikin kasar Nijar ba, wato Gwamantin diya mace. An samu sabanin ra’ayi da yawa, musamman daga Malaman addini da abokan hamayyar zuri’ar mu, inda gari ya rincabe, domin talakawa sun maya sun rantse idan ba ni da suka zaba ba, sai dai a kone garin kowa ya huta, sabida basu ga me mazan suka yi masu ba banda wawashe dan arzikin su, wanda bai kai ya kawo ba, da kyar aka samu aka sulhunta da babbar kotun kasa, wadda ta tabbatar da tsarin mulkin kasar Nijar bai haramtawa mace yin gwamnati ba. Don haka aka rantsar da ni.
Muka tattara muka koma (Govt. House) nida mijina da 'yan uwana masu yawa. Na karBo Haiti da Qassim, da 'ya'yan Baba Shettima uku, da dyar baba Adam wadda kwananan na aurar da ita, da kuma Niyaz diyar Bedeggi, duk na hada na rungume suna karatu a wajena. Haihuwa mun nemeta sama ko kasa Allah bai bayar ba. Likitoci sun tabbaar matsalar daga gareni ce, amma Kabiru yace ko zamu dawwama a haka, ba zai auri kowa ba, na ishe shi rayuwar duniya da lahira.
Ya dade yana yi min zancen mu daukoki a lokacin, ina kin amsawa. Abinda bai sani ba shine na tada dan aike musamman da lambar wayata ya kaiwa Faruq, a lokacin ya fara karatu a Sokoto, yana sanar dani komai kuke ciki. Akwai kakkarfan aminci tasakanina da Faruq dina, daga baya ma na shirya masa tikiti na aika mai don yazo ya same ni, yace mun a’ah suna tare da Imran koyaushe, bazai iya yin tafiya batare da sanin sa ba, sai na aika Qassim ya gano min gidan Sa'idu, ba tare da yasan dalili ba, ba kuma tare da shi kansa Faruq ya sani ba.
Na yi Badda kama nazo Sokoto fiye da sau biyar, har kofar gidan Babanki…..”

24, May 2025
Ibrahim

Thanks alot for the best novel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login