Showing 42001 words to 45000 words out of 45361 words
Chapter 15 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt
ne mai cikar kwarjini da kamala. Akwai alamun tsoron Allah a tare da shi, rashin son wasa ta ko’ina, yanayin sutturarsa, agogon dake daure a hannunsa, da irin takalminsa mai walkiya da sheik, ya nuna ba karamin mutum bane. Wasu mutun biyu ne a bayansa, ga alama daya ‘escourt’ ne dayan kuma direba, rike direban yake da kaya niki-niki cikin kwali, da ledoji abincin (city sweats), ya daura bisa lokar dake jikin gadona, yayin da mai tsaron lafiyar tasa ya ja masa kujerar dake fuskantar gadon da nike kwance, suka juya suka fita.
Yafi mintuna uku bai ce min komai ba, da alamunsa ni yake son in fara yi masa magana. A raina nace amma zaka kwana anan, ka kade ni da mota sannan ka yi min iko?
Ko tunani ya yi bai kyauta ba, sai ya ce "Sannu da jiki ko?” Na amsa da ka, ya sake cewa "Garin yaya kike tafiya a tsakiyar titi, kuma da sanyin asubahi ke kadai, alhalin kina mace, wadda bata yi mun kama da mai taBin kwakwalwa ba?” Nace "Eh, lafiya ta dalau, yanayin rayuwa ne yasa hakan”.
Yayi murmushi, cikin sanyin murya kuma ya ce "kiyi hakuri, Im not here to interfere (bana zo don na inyi miki shishshigi bane), kawai dai nayi mamaki ne. Ko zaki daure ki gaya min wurin aikin mijinki, in je in zo da shi domin anan na yi musu karyar nine mijinki, kuma ni na kadeki a bias rashin sani a kofar gidan mu, don kurum su karBeki ba tare da sun Bata mana lokaci ba. Ba yadda direbana bai yi ba don ya kauce miki, kina kara shan gabansa, karshe dole motar ta shafeki, sun gaya miki kin samu karaya a hannu ko?” Na gyada masa kai, ya ce "to a ina za'a samu mijin naki, ko can kauyen zan koma in bincika?” Ban san sanda na muskuta ba, hannuna ya amsa, azabar har cikin kwakwalwata, har kuma yatsar kafata amma na cije leBBana nace "bani da aure".
Ya zuba min ido curiously (cike da son sanin abubuwa da yawa da suka shafe ni) ya ce “sunana Kabir BADEGGI. Iam politician (watau dan siyasa ne). Ni mutumin Nijar ne, amma na girma a Maiduguri, hannun gyatuma ta, saidai a yanzu haka da girma ya hauni, na koma mahaifata ina tafiyar da harkar siyasata a can. Kina yi min kama da wasu mutane acan na kwarai dana sani, nake kuma tare da su.
Ki daure ki dubi girman Allah, ki gaya min gaskiyar inda kika fito, in sadaki da iyayenki. In ma wata matsala ta fito dake, ni na yi alkawarin zan tsaya maki. Ba zan barki ki fada a lalataccen hannu ba, hannu da hannu zan danka ki ga iyayenki, ki yarda dani".
Na runtse ido cikin tababar in yarda dashi din ne ko a’ah? Bai yi min kama da mutumin banza ba, bai yi min kama da makaryaci ba, haka bai yi min kama da mayaudara irin SA'IDU ba. Magana yake daga fatar bakinsa, har zuciyarsa, haka idanunwasa na tabbatar da abinda ke fita bakinsa. Har da mulmulen sallah a goshinsa, abin nan da ake kira "sujjadah". Shi ba wani kyakkyawa bane, kawai kamili ne, da babu alamun wasa da yaudara cikin al'amarinsa”.
Ta yi murmushi, nima murmushin nayi. Don sanin ko wa take nufi. Amma can a karkashin zuciyata ina KISHI, da nake kalubalantar zuciyata mai cewa BABANA SA'IDU nake tayawa.
"Kabir Badeggi kenan. Wanda zuciyata ta aminta da shi a lokacin daya. Naji ya kwanta min tun bai furta wata kalma mai nufin soyayya a gareni ba. SaBanin Sa'idu da yayi amfani da wayewar shi, wayonshi da kyawun halittarshi ya saye soyayyata. Hakannan na jishi da wani GIRMA a idanuna, ta yadda nake jin har ba zan iya bude su gaba daya in dubeshi ba.
Ban san sanda furucin ya suButo daga bakina ba, na samu kaina da cewa cikin rada, sannan idanuna a rufe "Nima ai asali na 'yar Nijar ce".
Yayi murmushi yace "what a coincedence! Nijer, a wace Jiha?” Na ce "Damagaram" ya yi dan dumm! Yana kallona da dukkan fararen idanunsa, yace "Damagaran, ikon Allah, ina yawan zuwa wajen aminina Shettima, yaya sunan ki?" Na sake runtse ido sosai, saboda yadda sanyin muryarsa ke kassara gabban jikina, na ce cikin rashin kuzari.
"Nuratu Mainasara".
Jawo kujerarshi yayi gabana, yana kallona sosai kamar ya cinye ni, ya kai hannu ya zare hular zanna dake kansa yace "kina nufin ke, jinin KANGIWA ce, kuma kanwa ga Shettima Mainasara?”
Na bude hakorana duka ina dariya, jin wani ya ambato min wani suna daga cikin sunayen da nike matukar girmamawa, dana dade ban ji ba, shekaru masu yawa nace "a’ah Baba Shettima Baba ne a gareni. Shine dan autan su mahaifin mu".
Yace "Nuratu ke kamar kanwace a gareni. Akwai mutunci da harkar neman abinci sosai tsakanina da Babanninki. Don haka ba sai kin warke ba zan sayo mana tikitin Yamai, in danka ki ga Iyayenki duk da ban san abinda ya fito da ke ba, sannna in komo in tafi inda da nayi niyyar zuwa kika hanani.
Amma don Allah kiyi alfarma gareni, ki gaya min me ya kawo ki dajin dana ganki? Me ya kawoki Nijeriya?" Gaba daya fuskata sai ta sauya, da wani irin lulluBaBBen Bacin ran da shi kanshi sai da ya fuskanci hakan. Ya yi saurin gyara zancen sa da cewa "kodayake ‘this may be your personal issue, am sorry, very sorry" na yi murmushi kadan, ganin yadda ya damu sosai da damuwata.
Ban san bayanin da ya yiwa likitocin ba. Washegari ya dawo ya kira Nurse ta taimakamin na shirya, bayan ya bata wani bakar leda shake da kaya. Na sha mamaki da naga har da su (always pad) kodayake hatta gadona Bace yake da jinni, duk da kunzugun dankwalin dake jikina.
Ta hada min ruwan zafi mai matukar zafi ta yi mun wanka, bayan ta zaunar dani sosai a cikin ruwa zafin don ta lura haihuwa nayi, tana yi min tambayoyi game da Babyna nace bakwaini ne, an sanya shi cikin (incubator). Ta hada min shayi mai kauri sosai, ta kuma hadani da gashashshiyar kazar (Capetano) daya kawo cikin plate ta badeshi da yajin daddawa tace in ci sosai, don mijina ya gaya mata doguwar tafiya zamuyi zuwa Jamhuriyyar Nijer.
Cikin kayan daya kawo ta fidda min sabuwar doguwar riga dal daga cikin ledarta, irin wadanda ake kawowa daga Dubai da mayafin su, kalar su toka-toka (ash) har da sabbin (panties) duk sai naji ina jin kunyar hada ido da shi kuma. Ita kuwa ko a jikinta, aikinta kawai take sai cewa take maza sanya mana, yana jiranki a mota. Da ganin irin kulawar da take min na jinjinawa asibitin. Don hakane dana fito na daga kai na ga ‘sign board’ mai dauke da sunan asibitin, an rubuta PREMIER CLINIC. Sai na ce a raina ashe ba'a banza take yi ba.
Haka ta kama hannuna har gaban motar. Direbansa da ‘escourt’ dinsa suna gaba, ni da shi muna baya. A sannan ne wata nutsuwa tazo min, sanyin A/C dana dade ban ji ba ya ratsani. Na lumshe ido na rausayar da kai gefe muna hira jefi- jefi akan su Baba Aliyu, har muka zo Airport din Aminu Kano, inda kai tsaye muka hau jirgin da zai kaimu Niamey.
Zuciyata cunkushe da tunanin fuskar da zan fuskanci dangina da ita, sai da zuciyar ta yi amanna da in fadawa Yadudu gaskiyar abinda ya rabo ni da gidan Ya Rabi. Da kuma dalilinmu na kin neman su alhalin mun san inda suke, wannan kam ni kaina bani da masaniya akai, nasan dai Malam Ali yana addu'a sosai a kanmu, wadda tasa ko sunan dangin mu bama tunawa. Gara ma ni wani lokacin nakan tuno Yadudu, amma Ya Rabi ko zancen kasar Nijer bata son ta ji anyi a gabanta.
Tun a filin jirgi yayi wa Baffa Aliyu waya yace gashi nan tare da diyarsu Nuratu. Baffa ya ce "wace Nuratun? Ba dai 'yar Yaya Sani mai rasuwa ba?” Ya ce ita dai, shima Allah ne ya hadasu, yayi-yayi kuma na ga fada masa daga inda na fito na ki. Don haka kafin minti goma sha biyar filin jirgin saman (Mano-Dayak) ya cika taf, da motocin, iyalin Mainasara. Na hangesu kwansu da kwarkwatarsu KANGIWA FAMILY, maza da mata, tsofaffi da 'yan mata. A tsakiyar su na hango tsohuwa Yadudu, ta kara tsufa kwarai da gaske fiye da yadda na barta. Amma kayan alfarma ne a jikinta. Na karasa da gudu muka rungume juna muna ta kuka. Ta ce "Nuratu ashe Allah yayi zan kara ganinki ina raye? Ina 'yar uwarki, me yasa bata taho tare dake ba?” Nace “labarin mai tsawo ne Yadudu, muje gida tukunna".
A babban falon Baffa Aliyu cikin unguwar nan muka hadu, aka sallami yara-yaran irin su Qassim, lokacin Hibbani tana budurwa kamar ni. Ina kuka na fede musu biri har bindi, tun auren Ya Rabi da mahaifinmu ya bayarwa malam Ali, na ce malam Ali mutumin kirki ne, ba'a rasa ci ba ba’a rasa sha ba cikin gidansa, kuma yana sonta, ku kwantar da hankalinku. Ku barta ta yi zaman aurenta, haka Allah ya tsara mata. In ya so sai a dinga kai mata ziyara akai-akai, abinda har yau Allah bai basu ikon yi ba, kuma da wannan nadamar suke kwana suke tashi a halin yanzu.
Sannan na gangaro ga labarina da Sa'idu, na fada musu komai ban rage ko kalma daya ba, saboda nasan su iyayena ne da bani da kamarsu, hakannan mutane ne masu ilimi, tawakkali da barwa Allah komi. Wannan shine ginshikin rayuwar iyalin Mainasara, wadda ke kara bunkasa su har gobe. Mutanene da suke muhimmanta yarda da kaddara da hukuncin Allah, mai kyau ko mara kyau a gare su. Na kare da cewa duk hukuncin da kuka yanke a gareni dai-dai ne. Ni dai kwanciyar hankalina kadai shine kada yarinyar ta gane ba Ya Rabi ce ta haifeta ba, amma ba don bana son ta. A da, tunanina shine in dauko ta in taho tare da ita, sai nayi tunanin yaya zan dauko 'ya in kawo masu alhalin ban yi aure ba? Mu kuwa 'yan siyasa ne, jinin mu da Bargonmu, masu tarin makiya, amma ba wai don ni in yi siyasa ba kamar yadda tunaninki ya baki. Don a lokacin kwata-kwata ban taBa kawowa raina in cika burin mahaifina ba, wato in zamo makwafinsa. Kawai ina jin su Baba Aliyu ne, da tasu siyasar. Na tabbatarwa kaina zamanki tare da Ya Rabi, shine babban kwanciyar hankalinki, mutuncinki, nasaba da martabarki amma ba wai nawa ba.
Wallahi-wallahi tilas ce ta sani baroki da Ya Rabi, domin abin zai yi mata yawa. Naga yadda kaunarki ta shigeta tun sanda take yanke miki cibi, ko ido bata iya daukewa akanki. Na san in na bar mata ke, kamar na zauna tare da ita ne, ko babu komai zaki debe mata kewar abubuwana da yawa, domin duk wata halittata irin taki ce, hatta sumar kanki, kuma babu maraba da ita, sai ki rantse itace ta haifeki.
Yadudu kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita. Su Baba Aliyu kuwa sun kasa magana. Sun kuma rasa me zasuyi dani su huce. Shettima yafi kowa zuciya cikin danginmu, shine ya fara tamaula da ni a falon, ya rika duka kamar ba zai barni ba. Ganin irin jinni da majinar da ya haDa min ne Yadudu ta mike jikinta na kyarma ta rufu a kaina. Ta ce “ka kashemu mu biyu, mu tadda mahaifinta. Daga nan sai in yi masa bayanin irin rikon da kuka yiwa zuri'arsa a bayan ransa. Shida ya kari rayuwarsa gabadaya cikin hidimar ilmin ku, cikin kyautata muku. Tunda ya rasu cikinku wa ya kara waiwayar 'ya'yan da ya tafi ya bari, alhalin kuna da tabbacin suna raye cikin kasar Nijeriya? Sai yau da ta biyoku da kanta, ta fada maku abinda ba matse bakinta kukayi ta fada maku ba? Da Nuratu lalatacciya ce, tana kuma son lalacewar, da bata dawo cikin ku ba.
Da ta karasa cikin duniya ta cigaba da lalatar ta. Amma dawowa ta yi ta fada maku amanar kanta, wanda daga ita sai Allah sai 'yar uwarta suka sani, sabida tana da yaqinin ku iyayenta ne bazaku taba yanketa ku yar ba, babu abinda zai faru ga dan adam, face ya kasance rubutacce a lauhul mahfuz, don haka ita Nuratu haka Allah ya rubuta mata. Amma dubi kwayar idanunta, ba tayi kama da shaidanun 'ya'ya ba.
Don haka Nuratu ko a yau ki koma kizo da diyarki, ni zan rike maki, kina da dukiyar da zaki rike 'yarki, ba tare da taimakon kowa ba. Babu wanda yake sama da aikata kuskure, sai dai wani yafi na wani, kuma idan kika roki Allah da cika sharuddan tuba, hakika zai yafe maki. Ya yafe wanda yafi wannan.
Ban taBa ganin yarinya mai tsoron Allah irinki ba. Nawa ne suka yi cikin, suka je suka zubar, ko su haife su kashe, ko su yar a bola? Ba tare da iyayen su sun sani ba?
Amma ita tazo ta gaya muku abinda baku sani ba, don tana da tabbacin kune iyayenta, a cikin kowanne hali, ba zaku kita ba. Yau da mahaifinta yana raye ….. Shettima zakayi mata irin wannan dukan fitar ran daka yi mata a gabansa?” Ta kama hannuna ta tayar dani, jinni na bulbula ta hanci ta baka mika ni har gabansu, tace "gata nan ku yankata, sai dai ku sani, in gemun dan uwanka ya kama da wuta, to ka shafawa naka ruwa…..".
Kamilu yace “Yadudu ai baki bari kinji me muka ce akanta ba, shi kuwa Shettima kin san zuciya irin tasa. Me yayi zafi? Me ya kawo wannan maganar? Allah ya huci zuciyar ki.
Nuratu tamu ce, haka ko me tayi ba zamu yada ita ba, amma dole mu ladabtar da ita, don ta kiyayi gaba, da yiwa 'yan bayanta hannunka mai sanda, kuma ko Yaya Sani yana raye, bazai kalubalanci hukuncin da Shettima yayi mata ba.
"Ke Nuratu!”
Ya kira ni da kakkausar murya. Na dago kumburarrun idanuna na dubeshi, amma ban ce komi ba. “Da gaske ne abinda kika gaya mana?” Na daga kai ina hadiyar zuciya "to waye Uban 'yar?” Nace almajirin mijin Ya Rabi ne, sunansa Sa'idu, a yanzu haka yana karatu a Ingila, nasan kuma bada jimawaba zai dawo ya tadda ita.
Wallahi-wallahi Baffa Aliyu, nima ban san ya akai hakan ta faru da ni ba, kawai na bude ido ne na ganni da cikin a jikina, ko shima Sa'idu bai san da zancen cikin ba" yace “to kun shirya yin aure ne idan ya dawo?”
Na share wasu ambaliyar hawaye daga kundukukina, nace “har abada babu zancen aure a tsakaninmu. Ina nufin ba zan iya auren sa ba". Ya ce “zancen banza, to waye zaki aura wanda ya fishi?” Nasa kuka sosai na ce "wane irin aure, GIRMAN JUNA YA FADI? Nidai kuyi hakuri makaranta zan koma".
Dukkan su sai suka yi shiru, aka rasa mai bakin magana.
Daga karshe suka hadu suna yi min nasihohi, kowa da irin tashi, masu ratsa zuciya, at last, suka ce “Allah ya zaBa min abinda yafi alkairi ga ryuwata,” akayi addu'a taron ya tashi.
Bada jimawa ba na bawa Baffa Aliyu takarduna na sakandire ya samo min gurbi a jami'ar Niamey, na soma nazarin kimiyyar siyasa (Polictical Science), sai dai muna yi da harshen faransanci ne. Ina shekara ta biyun karshe Badeggi ya fito gaba-gadi da son aurena, duk da gaskiyar labarina da Shettima ya gaya masa, yace ya ji ya gani.
Ya taBa aure matarshi ta haifa mishi 'ya'ya har biyu, ta rasu a wajen haihuwar na ukun. Biyu maza ne, duk sun girma, AbdulHakim da Abdulsamad, a yanzu haka manyan ma'aikata ne sa'annin Qassim, macen kuma itace Niyaz, wannan 'yar budurwar da nasa ta yi miki magana ranar da Qassim ya kawo ki.
Kai tsaye na nemi alfarmar Kawunnina da suyi min uzuri in kammala karatu na, zanfi samun nutsuwa. Duk da matsananciyar kaunar dake tsakaninmu, maza tsoro suke bani. Na kudurce a raina na daina baiwa soyayya muhimmanci akan ingancin rayuwar diya mace.
Na fito da (First Class Degreee) a shekara ta (1990). Na kuma yi (winning scholarship abroad) daga jami'armu zuwa babbar jami’ar Paris. Daga Baffa Ali, Adam, Shettima Kamilu da Kabiru, babu wanda yayi yunkurin hanani tafiya karatun digiri na biyu na tsayin shekaru biyu kacal, a cewar Baffa Aliyu a kyaleni in je, tunda yanzun ni ba karamar yarinya bace zan iya kula da kaina. Don haka na tafi tsawon shekara daya da rabi kacal na dawo da kwalin digirina na biyu, muka yi aure mai suna aure, wanda yayi tambari cikin kasar Nijar ciki da bai dinta, cike da matsanancin so da kaunar da har yau ba'a taBa samun ma'auratan da suka dade tare da juna, ba tare da wani saBani ya gitta a tsakanin su ba, kamar ni da Badeggi, a gaba dayan Kangiwa family.
A lokacin Kabir ya samu damar darewa shugaban jam'iyyar mu, wadda tafi kowacce jam'iyya karBuwa a kasar Nijar. Haka kawai kamar da wasa rannan na soma tunanin me zai hana in cikawa mahaifinmu burinsa, da ya tafi da shi a zuciyarsa?
Wato tsayawa gwamnatin Damagaram, domin kara fiddo ta da banbantata da sauran
24, May 2025
Ibrahim
Thanks alot for the best novel