Showing 24001 words to 27000 words out of 45361 words

Chapter 9 - GIRMA YA FADI Book 3 End Complete by TAKORI.txt

ta karye, jikinta ya mace murus, “ki saurare ni Zaynab, tsayin mintuna goma sha biyar, in gaya miki gaskiyar abinda kike zargi, wanda ba haka bane…" na girgiza kai da sauri "baki da kalmar da zaki gaya mini in yarda kina kaunar Innata yadda take ka unarki. Da kina kaunarta, wallahi da ba kiyi shekaru goma sha takwas bata san inda kike ba, alhalin kina da masaniyar bazata taBa samun kwanciyar hankali akan hakan ba, da baki bari bakin cikin ki ya kaita kabarinta ba…." cikin shesshekar kuka tace
"Waye ya gaya miki bansan halin da kuke ciki ba? Waye ya gaya miki bansan a gidan Sa'idu kika taso ba? Waye ya gaya miki ban san har soyayya kun yi da Imran ba?"
Nayi hanzarin dagowa na dubeta a rikice, tayi murmushi ta juya min baya tace "Zaynabu ke nan, you are still a baby ina jin sai na sake haifarki. Ina Umar Faruq, ina Imran ina Babanki…..?"
Na bude baki hangangan ina kallonta, ta yi murmushi tace "ki rufe bakin kada kuda ya fada” sai na yi murmushin da ban shirya ba, ta sake mamakantar dani da cewa "ina 'yan uwan ki Iftihal da Azizah?”
Na kai hannuna duka biyu na rufe baki ina dariya "kina yin maganganu wadanda suke bani tsoro". Ta lakuce min baki tare da kama fatan kunnena ta ja ta da karfi kamar zata tsinke min shi, nayi ‘yar kara bata saki ba tace "kamar yadda kudina ba zasu sayi dattin dake ranki ba, haka zasuyi min amfani ta hanyar samomin labarinki keda Ya Rabi. Abinda yasa ba zanyi fushi dake akan maganganun da kika yaBa min ba, don nasa kina a cikin zargi ne. Sannan na gane kina da hankali, kina kuma kaunar mai kaunarki. Wallahi-wallahi Zaynab, baki fini son Ya Rabi ba".
Ta juya da sauri zuwa dakinta, jim kadan ta dawo rike da wata 'yar batta da na soma tunanin ina na san ta? Ta fiddo abinda ke ciki, haskensu ya dallare min ido, na soma kif-kiftawa. Idan har ba gizo idanuwana ke mun ba, sarkar da Baba Sa'idu ya bani ce, shekaru takwas a baya ta dutsen Sapphire, dana baiwa Ya Faruq ajiya. Tana murmushi ta ce “ungo kayanki mai Uban dake sonta. Ba wannan ne abinda ya mallaka mikin ba, tun kina firamare? Ki tambayi wanda kika baiwa ajiyar, kafin ki bashi wannan ajiyar, nawa aka bashi?"
Wannan na nufin; Ya Faruq na tareda mahafiyata a duk tsawon shekarunnan? Ya san inda take, kuma ta hanyarsa ne take samun labarina, kai! Nuratu zata fasa mun kai…. Na kai hannu na dafe kaina da ya soma sarawa tamkar ya rabe gida biyu, ni ban karbi sarkar daga hannunta ba, ita bata fasa mikomin ba, nace idanuna a runtse "idan ba so kike kaina ya tsage ba, ki fidda ni duhun da kike sanya ni". Ta kamo ni ta rungume tana dariya tace "ba ke kikace bazaki saurare ni ba? Zaynab ya zan haifeki, kiyi tunanin bana sonki, alhalin soyayyace mai tsanani ta kaimu ga aikata hakan nida mahaifinki, tunda an hanamu aure karfi da yaji, sai kuma sharrin shaidan da bin son zuciya. Shin ko kin san Sa'a, ina nufin matar Sa'idu?" “Ni kuwa na santa". Ta runtse idonta a hankali cikin tunanin al'amarin daya faru shekaru ishirin da biyar a baya, a yau ya shiga dawo mata tar-tar kamar a majigi. Taja hannuna muka koma bakin gadon muka zauna, ta dubeni tayi murmushi ta dauke siraran hawayen da suka cika mata ido da kyawawan yatsunta, yayin da kaunar Uwata ya cigaba da bunkasa a zuciyata, na kasa cigaba da jurar ganin hawayen da take fitaswa, a hankali na matsa na kwantar da kaina a cinyoyinta. Sai naji tamkar Innata. Tana share min hawayen da yatsunta ta soma……






KAUYEN GWARZO (1970)
LABARIN NURATU.


Kamar yadda kika sani, ko kuma kika fahimta Zaynab mu haifaffun kasar Nijar ne, cikin garin Damagaram. Zaman mu anan Yamai ya samo asali ne tun daga lokacin da Kakana Mainasara Kangiwa ya lashe kujerar shugabancin kasar Nijer. A lokacin su mahaifinmu basu da wayo, su biyar ne 'ya'yansa kuma duk in gansu. Aliyu, Adam, Shettima, Kamilu, da mahaifinmu mai rasuwa. Hajiya Azzo da kika sauka a gurinta kanwarsa ce, cikin su daya, ita ta haifi Hibbani Babar Haiti. Qasim ba danta ba ne, jikanta ne, tunda kuwa da ne ga Baba Aliyu mai bin mahaifinmu.
Zamanta tare dashi ya samo asali ne tun daga wajen haihuwa, da mahaifiyarsa ta mutu ta barshi, ita ta daukeshi ta raine shi, har ya zamo tamkar da a gareta.
Tun Kangiwa yana da rai ya shaci wannan filin wanda daga baya ya zamo anguwar plateux dinnan da muke ciki, ya assasa ginin wannan ‘estate’ yayiwa su mahaifin mu aure a ciki, wanda aka cigaba da canza ginin yadda zai tafi da zamani har kawo na yau da kika gani, wanda duk fadin kasar Nijar, an tabbata babu gini kamar namu, domin duk bayan shekaru uku magina daga kasar China suke kara sabunta ginin da sabon nau'I na zamani. Wannan gidan da nake ciki shine kason mahaifinmu, wanda ya zamo gadon mu ni da Ya Rabi.
Bayan rasuwar Kangiwa, dukkansu sunci gaba da harkar siyasa daban-daban, mahaifinmu ne kadai yafi bada karfi ga kasuwancin fata, wanda ya amshe shi sosai kuma Allah ya sanya mishi Albarka a ciki. Yana fitar da fatar rakuma da sauran dabbobi zuwa masana'antun kasar China da Thailand, daga baya kuma har Nigeria saboda suma akwai sana'ar kayan fata, inda ya san manyan mutane da yawa a Kano ta wannna hanyar.
Duk cikin matan Kakanmu, Yadudu Babar mahaifinmu kadai Allah ya yiwa tsawon rai, tazo nan kin ganta, itace tsohuwar data dake ki da sanda, domin inda akwai wanda tafi so duk cikin zuri'arta to ni ce. Wannan ya samo asali ne da kaunar da take yiwa mahaifinmu. Inada shekaru biyar mahaifiyarmu ta rasu ta bar mahaifinmu ta sanadiyar ciwon kansar nono (breast cancer). An ce mahaifin mu hauka ne kadai bai yi ba, saida 'yan uwanshi suka tafi dashi Saudiyyah suka yi tayi masa addu'a, da taimakon su da taimakon Allah ya koma dai-dai, saboda yadda yake kaunar mahaifiyarmu. To bayan rasuwarta sai ya dauki dukkan kaunar nan ya daura akan mu nida ‘yar uwata. Haka ya shafe shekaru biyar bai kara aure ba yanata harkar fatarsa, mu kuma muna hannun Yadudu a Damagaran, inda a can ne Ya Rabi ta gamu da lalurarta ta shafar aljannu, a lokacin kam mahaifinmu ya bunkasa ya tara arziki sosai. Akwai wata rijiya ta Man fetur da Kangiwa ya gadar masu tun yana raye, tana nan a Damagaram, kinsan yanayin kasar mu (sahara) don haka mallakar rijiyar man fetur a cikin kasar nan ba karamin abu bane. Shi kansa Kangiwa an ce ba'a san ta ina ya hako wannan rijiyar ba, kawai an wayi gari ne an ganshi da ita (just a mirage). Ko da akazo rabon gado bayan rasuwar Kangiwa, mahaifinmu shi ya mallaki wannan rijiyar shi daya, bai karbi ko kwandala na daga dukiyar mahaifin su ba. Banda wannan gidan da muke ciki komi ya tafi ga su Baba Shettima.
[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Kishingide yake a falon alfarma na Baffa Aliyu wanda ke daura da gidan Nuratu. An cika gabanshi da kayan marmari dana ciye-ciye da tsotse-tsotse. A gefe cinyar rakumi ce aka gashe aka kyafe masa ita sai naso take da tashin tiriri. Ga wukar yanka da cokali mai yatsu an soke a jiki, suna hirarsu da Aliyu da Shettima muka yi sallama a tare.
Duk da GIRMA daya soma samunshi, da furfura tsilla-tsilla a cikin kanshi, still yananan a BABA SA'IDUna dana sani; Baki ingarman gaske, ma’abocin gargasa, gagara-gasa a cikin maza. Fi-sauran Babanni ( kamar yadda marigayiya Innata ta rada mishi).
Ya dago fararen idanunsa ya dube ni, sai na fadi ragwaf, akan gwiwoyina domin sun kasa daukata. Saboda wani irin GIRMA da kwarjini da yayi min, koko ince, Allah ya rigaya yayi masa. Baba Sa'idu dashen Allah ne kuma murucin kan dutse, abin nufi, Allah ya rigaya ya tsayar da shi, babu wanda ya isa/ba abinda ya isa ya FADAR dashi, yayi masa haiba da nasibobi da dama. Irin wadannan mutanen tsiraru ne, a cikin al’ummah.
Yayi murmushi yana nunawa Baba Shettima ni da dan alin sa, yace “ZAYNABU kenan, KYAUTAR ALLAH, KYAUTAR INNA RABI, ABUN FARUQ, ABUN BABA SA'ID, BABBAR MACE, MAI BABBAN AL'AMARI!
Suka yi dariya sosai ya ce "Allah ba da wasa ba Shettima, Zaynabu tana da babban al'amari irin na NURATU! Ni na gaya maka nan gaba Zaynab wata ce, sai ta zama ZAYNAB MAINASARA…..!!”

Da gudu na runtuma na rungume Babana, ina kuka yana sharemin hawaye da hannunsa, ni ke neman afuwar, amma maimakon yayi afuwar, sai tawa afuwar yake nema. Su Iftihal sai suka zama 'yan kallon kauna irin ta da da mahaifi. Ashe ‘YAYA DUKA ‘YA’YA NE, amma abin a zuci GIRMA-GIRMA NE……!!!

*** *** ***


A ‘family meeting’ din da aka gabatar, wanda dukkan Kangiwa sun halarta. Malam Ali, Alhaji Sa'idu, Nuratu, Azumi, Alhaji Badeggi, Faruq, Imran da Inna Dubu, gami da Yaya Halima, itace kadai mai kananan shekaru a dakin taron bayan su Ya Im. Bayan tattauna duk abinda ya dace, an nemi afuwar juna. Nuratu da Sa'idu sun yi afuwa ga junansu. Imran ya sunkuyar da kai yace "akwai sako daga mahaifiyata ga Nuratu da Baba Sa'idu”.
Nuratu da Sa'idun ne kuwa suka juyo suka dube shi. Ya lumshe ido ya cije lebbansa masu sulbi, yana mai kawar da dubanshi daga idanun Nuratu masu kaifi kamar reza, ya mayar ga mahaifinsa, ya ce "Hajiya tace ku yafe mata, domin wai itace silar duk abinda ya faru da rayuwarku data Zaynab, amma baku da kaico!”
Falon ya dauki tsit, Inna Dubu tace "ka bude baki kayi magana sosai yadda ta fadi maka”.
Yayi ajiyar zuciya yace
"A cewarta, sanda Baba yazo mata da maganar auren sa da Nuratu, hankalinta ya tashi sosai, saboda ta san Abba baya sonta, saboda darajar malam kawai ya aureta, yake kuma zaune da ita.
A tunaninta muddin ya auri zabin sa, ita kuma tata ta kare, wulakantata zai yi, ko kuma ta kari rayuwarta a zaman boranci, saboda irin tanadin da yake yiwa Nuratu ba kadan bane.
Da farko ta dauki Nuratu yarinya karama kuma 'yar kauye mara wayo, ta dauka idan tayi mata barazana kawai zata hakura ta ji tsoro ta fasa auren Abban, sai taga Nuratu da Inna ko a jikinsu. Shima Abban babu abinda ya fasa na shirye-shiryen aurensa da Nuratu.
Saboda haka ne ta tafi garinsu can Gombe, a wani kauye, Kumo, ta sami wani hatsabibin malami ta yi masa bayanin matsalarta na a lalata maganar auren Nuratu. Malamin yayi duba yayi mata bayanin cewa yayi bincike yaga akwai rantsatstsen rabo a tsakaninsu. Don haka tayi hakuri ayi auren, in yaso sai su san yadda zasu lalata auren daga baya. Ita kuwa tace da ta ga auren Abba da Nuratu, gara taga karshen rayuwarta.
Malamin ya ce to akwai mafita guda daya, zai iya yi musu asirin da zasu haife duk wani rabo dake tsakanin su a titi, daga nan kuma babu maganar aure, zai cusa matsananciyar kiyayyar junansu a zuciyoyinsu.
Bata taba sanin cewa Zaynab diyar Abba bace sai ranar da ya fadi musu da bakin shi dukkansu a asibiti. Lokacin ana cuku-cukun fidda shi kasar Jamus. Tun daga lokacin data yanke jiki ta fadI, ta samu (stroke) wanda har yanzu tana nan a kwance”.
Ya yi shiru yana maida numfashi a hankali, idanunsa sun kada sun yi jawur. Duk cikar falon an ransa mai magana. Ba Nuratun ba, ba Sa'idun ba, kowanne ya fada a tafkin tunanin al'amarin da ya faru dashi, shekaru goma sha takwas a baya.
Sai kuma tausayin junansu ya zo ya lullube su, idanuwan su suka kada suka yi jawur, tsohuwar soyayya ta soma tashi, dama ance wai ita soyayyah, bata tsufa, duk GIRMA, sai dai masoyan su tsufa. Wannan haka yake. Amma Allah bai kaddari suna da rabon aure a tsakanin su ba.
Ko sun yafe din ko basu yafe ba Allah masani.


*** *** ***


A taro na gaba. Nuratu ta mike kokon bararta ga Sa'idu, na nemawa kaninta Faruq auren diyarsa, Aliyu Mainasara ya nemawa nasa dan Qassim auren diyarsa Azeezah, sannan shima Baban ya nemawa Imran dinsa auren Haiti.
Jin haka Badeggi shima yace ba za'a barshi a baya ba. Ya matso ya zauna gaban Sa'idu, yace “BABA SA'IDU nima ina yiwa Abdulhakim, kamun Iftihal, yana Parisa, jibi-jibinnan zai dawo a hada shi". Gabadaya falon aka sa dariyar aminci, yarda da GIRMAMA juna.


*** *** ***



Biki yayi biki! Sha'ani yayi sha'ani!! Ba'a Damagaram ba ba’a Yamai (Niamey) ba, ba Sokoto Birnin Shehu ba, har Gwarzo ta Jihar Kano, inda anan akayi kamun amaren cikin dakin Inna Rabi.
Angwaye da Amare sun gaji tulis, har sun soma tunanin shafe wasu ‘acitvities’ don su samu hutu da amarensu da Nuratu ta babbake ta hana masu ko da jin kamshin su.
Haiti 'yar hutu tuni ta fara ciwon baya. Azeezah kuwa kullum kara fiddo sababbin ‘programmes’ take wanda zai yi dai-dai da irin burinta, ga mijin Allah ya bata a hannu sai yadda tayi da shi, bai san irin wannan hayaniyar ba, sannan an bashi wata irin mata 'yar giggiwa, mai shirin maida shi waina a tanda.
Iftihal da Abdulhakim ko sai shukurah, komai nasu yayi dai-dai. Abdulhakim Kabiru Badeggi (Managin Director na Nuratu's World) watau shagunan Nuratu dake birinin Paris, mutum ne nutsatstse mai sassaukar rayuwa, komai nasa yayi dai-dai da Iftihal wadda dama ita babu karya da nuna isa acikin al'amarinta.
To ga Haiti da Imrananta sai ince kusan burin Imran ya cika, na auren farar mace, ba'abziniyar usli mai jinni a jika wadda tafi Zaynab hasken fata da murjewar jiki, kai kace tocilan ce a cikin duhu, sai dai fa kowanne na jin kansa, ita tana jira a fara neman soyayyarta, shi yana jira azo a tsuguna ana lallashinsa tabdi! Baka san Haiti ba malam, don haka in ma mafarki kake ka farka, ko kuwa a dawwama a hakan.
A Sokoto ne Faruq ya kira wayar Zaynab yace "kina ina ne? Am almost, nearly to die Zaynab, na gaji, na gaji da wannan takunkumin na Mamie, rabon da in ganki fa tun kafin a daura aure, in ba so kike in mutu ba sai ki ta biye mata. Ita Haiti da yake tana da wayo ba gashi nan ba ta san yadda tayi ta fito ba suka fice da Imran, sannan Azizah da Qassim gasu can cikin lambun Abba kin zauna kullum kina biyewa kauyancin Iftihal" murmushi ta yi mai fidda sauti, “kai Ya Faruq, ba mun gaisa ba ranar daurin aure, ni yanzu dilke ake yi min" ya ce “in ma dinke ki ake ki taso kizo nan dakin Imran, I seriously want to tell you something, Allah ko in shigo ciki in jawo ki wallahi” ta dinga dariya ta ce "to bismillah, ai ga Aunty Hibbani nan itace ma take min dilkan, ga kuma Mamie da Mama nan a bakin kofar shigowa" ya dinga jan tsaki, tsut-tsut a kai-akai yayi cilli da wayar. Ya suri hularshi bisa ‘centre-table’ din Imran yayi cikin gidan fuuuu… kamar guguwa.

Da gaske take Mamie da Hajiya Azumi ne a bakin kofar. Don haka daya hango su sai ya rage taku ya koma cikin nutsuwar shi. Ya duka ya kwashi gaisuwa suka bashi hanya ya wuce ba tare da tambayar shi komai ba, hakan ba karamin dadi yayi mishi ba da bai san amsar da zai bayar ba, abinda ya sani kawai shine yan tsananin son ganin matarsa inda hali, har ya ji duminta cikin jikinshi whatever the case! Kai tsaye yasa kai dakin Mama, da gaske dilkan Hibbani ke mata daga ita sai daurin kirji, ya zauna dab da ita yana fuskantar Aunty Hibbani wadda sam bata ji shigowar shi ba ta dukufa tana aikinta tukuru, na lailaya da kalailaitar fatar jikin ‘yarta, sallamar ma a

24, May 2025
Ibrahim

Thanks alot for the best novel

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login