Showing 1 words to 3000 words out of 38754 words
Uwar goyo new book
Chapter1
wajen ya cika da Jama, a maza da Mata babba
da yaro
Kowa harkar gabansa kawai yake ba ruwan kowa
da kowa kasancewar gobe sallane yasa shagon
Mai Suna alfijir Super store cike da Jama, a
baban shagone yanada qofofi har hudu duk wani
nau, in sutura da kayan kyalekyale shagon
nadashi tsayawa fasalta yaddah shagon yakema
bata lokacine
You itace ranan da musulman duniya sukakai
azuminsu na 29 gobe Ko jibi kenan take sallah
Inka dubi fuskokin Jama, ar dake cikin alfijir
Super market din kowannensu cikin farinciki da
annashiwa yake kowa na sayen abinda yakeso
Jama, a sai kashe naira kawai yake a cikin
shagon kaika rantse kace bada guminsu suke
samo kudinba
A wanni vangare kuwa wata matace da yarta da
ba zata wuce year shekara shiddah a duniya ba
Kayane a kusa da Ita masu yawan gaske Wanda
ta saima
Year lelen nata
Kallo daya zakaima Matar Ka gane macece Mai
aji kuma naira ta zauna don alamun Hutu sun
bayyana a jikinta
Daaa ganin yanayin jikinta zaka gane tayi nisa da
talauci
Domin shiga Tai ta kece raini Kaya ta saka masu
tsada Ita da year tatata daga wuyarta zuwa
hannayenta wasu hadaddun danyen gwala
qwalaine a ciki wani siririn gyale ta yafa a
kafadar Tata wacce ake Kira da tayani gantali
Sam batai Kama da Matar aureba kasancewar
yanayin shigar Tata da tayi
Sai baza kamshi kawai take Tana wani hura hanci
irin na masu hannu da shuni
A zaune take a kan wani kujera ba qaramin kudi
ta kashema yar Tata ba duk tsadar Abu bata
shakkar siyama yar Tata inhar ranta naso kuma
Zai sakata cikin walwala
Dukda wannan uwar siyayyar da taima yar Tata a
banza ya tashi domin kuwa ita yar a duk cikin
himilin kayan da aka jibgo Mata din bataga
abinda yai Mata ba
Hasalima Ita wani Riga da siket takeso data Gani
a jikin wata yarinya a lokacin da sukaje Viki a
wani gida tun a lokacin taji kayan sun birgeta don
haka taketa rigima Kan sai momin Nata ta siyo
Mata kalan kayan sai kuma akai rashin sa. A ba,
a samu kalan kayanba don har Dubai abbanta
yaje don kayan Amman Ina Abu yaci Tara saidai
ya samo hadaddu Wanda sukafi wanNan kyau
Amman daya kawo Mata saita dinga ihu da tsalle
akan bataso Dole sai kalan wadancan
Daqar maman Tata ta shawo kanta da yin mata
alqawarin duk indai ake saidawa Ko, a inane indai
har a fadin duniyar nanne wajen yake to sai taje
ta sayo Mata su kuma Ko nawa suke hakan yasa
ta tashi ta nufi gidansu yarinyar da yar Tata taga
kayan a jikinta saidai anyi rashin sa, a domin
kayan ba a naija aka saima yar tasuba Tun daga
Saudi wata yar uwarsu ta kawo ma yar tsaraba
haka ta coma gida cikin sanyin jiki tanata tunanin
ta yaddah zata shawo kan yar Tata ba tare da an
samu matsalaba
Hakan kuwa akai duk wasu kalamai masu taushi
da kwantar da zuciyar da taitama yar tata basuyi
tasiri ba
Don rigima Kala Kala ta dinga tsirowa dAshi
hardasu yajin cin abinci na sati daya
Dadai maman ta fahimci yar Tata Tana cikin wani
haline yasa ta dauketa zuwa alfajir Super market
Wanda Ke cikin Garin Ko allah zaisa taga wasu
kayan wadanda sukafi wadancan Ita a nata
tunanin kantine babba kuma duk abinda kakeso
zaka iya samu a ciki
Don haka yasa ta taho da ita sai kuma akai
rashin sa. A a duk kantin saida suka zagaye ciki
da wajensa Amman Basu samu kalan kayanba
Yarinyace qarama wacce shekarunta Basu taka
sun karyaba Amman sai Dan banzan rigiman
tsiga kodon ita irin yarannanne da babu kwaba
balle harara_tunda Tai wayo komai sai abinda
ranta keso ake Mata komai kuma tsadar abu idan
aka saya Mata ba zatayi amfani dashiba matuqar
bai kwanta mataba
Mahaifinta yana matuqar Jin haushin halayyar yar
tashi saidai ba yadda zaiyi don Bashi da icon
hanawa sbd rayuwar auren nasu ba yaddah aka
sani suke gudanar dashiba Matar tashi Ita keda
icon komai a gidan Sam batason taga bacin ran
yarta shiyasa yar takecin
Karenta babu babbaka shagwaba Kala Kala ta
iyashi Ga qiriniya da rashin Jin magana da kuma
rashin Kunya duk wannan Abu da take a wajen
uwarta duk ado ne domin kuwa batasanma
tanayiba ballentana ta hanata
Duk shirin da kuke da ita kanaqin halayyar yar
tatta to yanxu zaku raba hanya da ita koda kuwa
jikinta nekai
Yarinyar an shagwabata da yawa duk abinda
zatai marar kyau to a wajen uwarta Mai kyau ne
kwarai da gaske Karna cikaku da surutu shin wai
wacece wannan matar
Hajiya fanne Kenan wadanda mutane sukafi sani
da hajia tsigala mafadaciyar matace a zamanin
quruciyarta duk a yarn anguwan nasu babu
Wanda ya kaita masifa
Mummunace sosai baqaqirin da ita babu Ko
alamun fari a jikinta
Yaddah fuskarta take baqa haka zuciyarta take
babu Ko alamun Imani a tattare da ita asalin
mahaifanta mangawane daga qaramar hukumar
nguru ta jahar yobe suka dawo garinda suke a
yanxu idan Suna yarensu kaika rantse kace kanuri
suke mahaifinta talakane Amman yanada Rufin
asiri
Domin kuwa yanada Sana, arsa wacce da ita
yake samun daukar nauyin iyalan Nasa kuma
dattijon arziqine don Jama. A na girmamashi don
halinsa na kirkine ba ruwansa da shiga shirgin da
Bai damesaba
Mahaifin fanne nada ilminsa na addini don da
yawa Jama. A a wajensa suke zuwa daukan
darussa mahaifiyarta da mahaifinta kusan halinsu
dayane don mahaifiyar tatama taso ta kereshi
wajen haquri
Su biyar ne wajen mahaifin nasu uku Mata biyu
Maza saidai duk yayyin Nata an musu auren
dangi Ga Yan uwansu a lokacin da akaxo yin
natanne ta qeqashe qasa akan ita ba zata aure
Wanda akeson a hadata dashiba akai juyin
duniyarnan taqi yarda dukda haquri na mahaifin
fanne Amman saida tasa ya kamata yai Mata
dukan tsiya don da alamun sunansa taqeson
batawa mahaifiyarta kuwa nasiha ta dinga Mata
akan tai haquri ta amince da zabin da mahaifin
Nata yai Mata gamida nasiha Mai ratsa jiki shine
mijin Nata da kalamai harta samu daman shawo
kansa amman da sharadin bata sati biyu tak
inhar sati biyu ya cika bata samo mijin aureba to
zai hadata da Wanda yai niyyah
Nanfa mahaifiyar Tata ta takura Mata akan ta
fitar da mijin da zata aura a cikin gwanon
samarin da suke zuwa wajenta Tun kafin lokacin
da mahaifin Nata ya dibar Mata don tasan halin
mijin Nata akwaishi da haquri amman duk sanda
ya fusata bashi saurin sauka saidai abinda ita
mahaifiyar fannen bata saniba shine duk cikin
samarin Nata babu Mai zuwa wajenta da niyyar
aure duk Yan I love u I love u ne Yan axo axo aji
dadi a Ware ne sai kuma masu nemNta da
fasiqanci Amman Sam bata taba Basu hadin kaiba
Yau itace ran da mahaifin Nata ya dibar Mata
suka cika din haka daya ya kirata domin Jin
Wanda ta tsayar ganin ganin ta faramai hanya
hanyane yasa yace to lallai Da Wanda yai niyyah
Zai hadata Dan Dan uwansa nanfa tai tsalle ta
dire gamida cewa wLlahi inhar aka hadata aure
da Wanda sukeson hadatadin to cikin biyu sai
anyi daya kodai ta kashe kanta Ko kuma tabi
uwa duniya ta salwantar da rayuwR Tata acan
kawai kalaman fannen ba qaramin girgixa
mahaifan Nata yaiba hakan yasa suka qaleta taci
gaba da zama a gabansu har aka dau lokaci mai
tsawo fanne sai qara gansamewa take a gaban
iyayenta don harta wuce minzalin aure don sa,
ointa yanxu wasu nada yaya2 wasu uku
Duk anguwan an santa batada kunya Kona
misqara zarratan ga fada idan Tana fada bakinta
har kumfa ke fita Ga zagi fanne ta iya zagi Lamar
bamagujiya sannan Ga shegen tonon fada Lamar
karya Kai fada koda bada Ita akeba Tana shiga
kullun sai an kawoma iyayenta qararta hakan ba
qaramin qonama mahaifin Nata rai yakeba
Hakan yasa Jama. A ke kiranta da fanne tsigala
fada da gaskia tsorone
Hakan ba qaramin damun mahaifinta yakeba
burinsa daya shine Yaga ya kawar da fanne daga
gabansa koda Zai iya samun kwanciyar hankali ta
wani bangaren
Ana cikin hakane mahaifin Nata ya bada Ita
sadaka Ga wani saurayi Dan anguwan nasu
kyakkyawan saurayine daga gidansu fannen zuwa
gidansu saurayin gidaje ukune kawai a tsakani. A.
Lokacin daya sanar da mahaifiyar fanne matarsa
kenan hukuncin daya yanke akan yar tasa ba
qaramin tashin hankali tashigaba sbd tuna furucin
yar Tata acan baya tashi kuma san mijin Nata
idan yahau baya saurin sauka kuma bai cika
alqawari kuma ya karyaba
Hakan yasa ta shiga wani Hali don Gani take
Kaman lokacin rasa yar tatace taxo gashi kuma
yace Mata karta sake ta fada Mata har sai an
kalmmala komai
Mahaifin fanne shine yadau dawainiyar komai na
game da kayan Viki da kuma Yan abubuwan da
baza. A rasaba Wanda addini ya tanadar a
bangaren mahaifiyar Tata kuwa Sam bata wani
amanna da wannan bikin don Gani take kamar
kashe kan Nata zata kamar yaddah ta fada a
baya shin waye Akabama fanne sadaka
Abubakar sadiq matashin saurayi ajin farko farine
tes dashi ga dan dogon hancinsa yarone Mai
ladabi da biyayyah Da sanin ya kamata ga ganin
Girman na gaba dashi Tun yana qarami
mahaifinsa ya rasu
Don haka Dan uwar mahaifiyarsa ya riqeshi shine
Tun yana aji uku na gaba da firamare mariqin
Nasa ya rasu hakan
Hakan yasa yake zuwa shagon wani a
anguwansu yana masa yan aikace aikace da
koyon Sana. A domin samun na kashewa don
daman abbakar din Mai zuciyar neman na
kansane
Don haka ya tashi tsaye wajen neman na kansa
ganin Hali da dabiun abbakar ne yasa mahaifin
fanne yai sha, awar Bashi yarsa sadaqa a lokacin
da yake fada masa saida ya tsaya sosai ya
tunani kamin ya bashi masa ta bangaren mahaifin
fanne kuwa murnane tattare a tare dashi don
yanada yaqinin abbakar bazai watsa masa qasa a
ido ba sbd dattakon yaron yaroneshi amman halin
manyane dashi
Duk da Bai farin ciki da kyautar da akai masa
kuma baiyi na, am da itaba amman ba zai iyama
tsohon gardamaba don yana ganin girmansa don
daman ance ai shaidanne kawai Ke maida hannun
kyauta baya hakan yasa ya amshi kyautar da
akai masa hannu bibbiyu gamida godiya tareda
wata yar guntuwar murmushin da zamu iya
kiranta da yaqe a ranan da mahaifin fanne ya
sanar da abbakar kyautar da yai masa ranan
wuni yai bashi da kuzari don Ko abinci kasaci yai
ya kasa fita shago mariqiyarsace ta leqo gamida
fadin abbakar lfy you baka fitaba Ko bakajin
dadine yace eh goggo zazzabine Ke damuna tace
to ina zuwa bari na samo maka magani don
nasan ba za, a rasaba nanta barshi ta fice daga
dakin
A daren ranan kasa barci yai ya saqa wannan ya
kwance wancan wai duk dandai ya samu mafita
Amman Ina a haka har gari ya waye abufa yai
qamari don har abbakar ya fara ramewa tunanin
irin zaman da zasuyi shida fanne kawai yake don
tuntuni yasan halin yarinyar ya tsani halayyan
yarinyar da kyamar abubuwan da take aikatawa
Domin shi Ko kadan baison Yaga yaro na Raina
na gaba dashi ita kuwa fanne ba ruwanta tsoho
Ko girman babanta yai idan ya shigo harkarta
yanxu zata yayyafa masa ruwan rashin Kunya kai
Ko kallone kai Mata wanda bai gamshetaba
yanXu saiku Debi Yan kallo kaida ita
fanne ba sa, an abbakar bace don da yayanta na
uku yake abota don akwai wata Rana da abbakar
din ya samu yayan ita fannen akan su dinga
tsawata Mata akan abubuwN da take domin duk
ba masu kyau bane sai ce masa yayi su Gani
suke kamar da shafar aljanu a lamarin fanne don
abubuwan Nata kullun gaba suke mun rasa
yaddah zamuyi da Ita saidai addu, a kawai da
mukasa a gaba kaima Ka tayamu da addu, a
abbakar yace Ina ba wani addu, ai yasin bataji
duka Bane kawai tsagwaron rashinjine Ke
damunta da yarinta kuma wlh Ina tabbatar maka
da duk sanda ta shigo sabgata saina Mata abinda
harta mutu bata Manta dashiba don wlh saina
Mata dukan da sai tayi satittika a kwance abokin
Nasa yai Daria yace abbakar kenan don ba tare
da Ita kakeba shiyasa kake fadin haka abbakar
yace to lallai zakasha mamaki Allah dai yasa tayi
gigin shiga sabgata Ka Gani
ita kanta fannen Tana mamakin yaddah akai take
shakkar abbakar din koda tayi niyyar sauke masa
buhun masifar Tata sai taji ta kasa dukda kuma
irin shishshige matan da yake don Kai tsaye yake
tunkararta ya fada Mata cewa abinda take babu
kyau ta gyra halinta da tayi niyyr mayar masa da
martani Ko zaginsa da zarar ta kalli kwayar
idonta duk saita daburce gaba da gabanta Kenan
wai aljani ya taka wuta
Ita da kanta idan ta zauna saita dinga tunanin
shin wai meye take gani a cikin kwayar idon
abbakar ne wnda Ke firgitata haka Amman har
izuw yanxu bata samu amsar hakan ba abinda
bata saniba kuwa shine akwai wani sirri da Allah
ya boyene Wanda sai shida kansa yasan ko meye
wannan
Jama. A da dama sunyu mamakin wannan Hadi
da akai domin abbakar salihin matashine kuma
natsastse Wanda Ke ganin darajar na gaba dashi
ita kuwa fanne kowa ya Santa batada Kunya
Kona misqara zarratan ballagazaace wacce
qaramin Abu zaisa yanxu Ku dambace kaida ita
bata ganin mutuncin kowa a idonta duk girman
mutun bata shayin angaza masa rashin mutunci
Ko watsa masa ashar hakan yasa Jama. A da
dama Ke zuwa masa jaje na rashin zabama
yayansa uwa ta gari da kuma Yan Bani na iya
dake zugashi akan karya sake ya yarda da
kyautar da akai masa
Mezai faru ta bangaren fanne zata amince Ko a, A
idanma ta amince ya zaman auren nasu Zai
kasance?
Mu hadu a next chapter
Uwar goyo
Chapter2
Jama, a da dama na ganin rashin dacewar tasu
don babu yaddah za, ai tsuntsun dake yawo a
sama yai rayuwa da kifin dake cikin rigiya abinda
Basu saniba shine bakin alqalami ya rigada ya
bushe domin tuntuni ya rigada ya amsawa
mahaifin Nata yanxu kuwa babu ta yaddah za. Ai
ya koma yace masa ya fasa ba, a dau tsawon
lokaciba akasha Viki dukda dai angon ba son
auren yakeba don daqarma ya iya zuwa wajen
saurin auren don daman masu iya magana na
fadin lbrn zuciya a tambayo fuska
Bangaren amarya kuwa abin ba yabo ba fallasa
Don tunda aka fara hidiman bikin batacema kowa
komaiba don koda mahaifin Nata ya kirata
gamida sanar da Ita hukuncin daya yanke a kanta
din na hadata aure da abbakar shirun da tayi ya
nunar masa data amince da zabin da yai Mata din
don haka farincikine fal a tare dashi
Don haka ya tashi gadan gadan wajen ganin anyi
hidiman bikin lfy da kansa ya Kama musu gidan
haya saidai daki dayane kasancewar Mai qaramin
qarfine
Bayan an gamashan Viki yau washe gari amarya
da ago sukaje gaisheda iyaye daman Al, adar
Garin Kenan don haka Suna zuwa mahaifin
fannen ya jashi bangarensa domin su tattauna
ananne yake cema abbakar din abbakar don Allah
inaso kaimin wani Al qawari guda kuma wannan
alqawari ba komai Bane illa so nake Ka riqemin
fanne Amana abbakar duk runtsi karka rabu da Ita
idan har kaimin hada Ka gamamin komai a
rayuwa kaman asirinane Ka Rufe domin manxon
Allah yace duk waNda ya rufama wani asiri to
kuwa Allah Zai nisantar da fuskarsa Ga shiga
wutar jahannama
Nasan bakason fanne kawai girmana da
mutuncina yasa Ka amince akan ta zama
abokiyar rayuwarka domin jama. A da dama na
fadin aurennan nakuba jimawa zaiyiba to inaso
don Allah kabama marada Kunya inhar Kai haka
na tabbata Allah bazai barka hakaba Allah kuma
yasa maka albarka ya kuma saka Maka da gidan
aljannah
Yace Amin baba kuma nai make alqawarin duk
runtsi Zan riqe maka yarka bisa Amana sannan
sukai sallama
Viki ya waste kowa ya Kama gabansa akabar
abbakar dagashi sai amaryarsa sai muyi musu
fatan zama lfy da kuma Bashi icon cika alqawarin
daya daukarma baban nata
A ranan da abbakar ya fara shiga dakin fanne da
dare ya samu har tayi barci abinta tayi daidai
akan gadon basa banban inji bahaushe
Be abinda Ke damunta barcinta kawai take
Sharawa
Daman ba qaramin takaici takejiba idan Tana
kwance akan tabarman Karan dake dakinta
ranaku da yawa Ko runtsawa batayi don Tana
kwanciya ta barman zataita cizonta Kota Ina
Tana sha, awar taje gidan qawarta ta ganta akan
gadonta abin ba qaramin burgeta yakeba kuma
yana daya daga cikin dalilan da yasa bataima
baban Nata musuba alokacin da yace Zai hadata
aure da abbakar ayau ne ta kudiri niyyar fanshe
barcinta data dinga rashinyi a kwanakin baya duk
ta dalilin kwana akan taburman Kara tace in
banda talauuci mai zaisa mutun ya dinga kwana
Akan tabirman Kara duk wani juyi da zakai saita
sokeka
Alokacin data hayekan gadon natane taji wani
sanyin farinciki na ziyartan zuciyarta tace Ashe
daman haka kwanciya akan Gado yake da dadi
Aiko datasan hakane da tuntuni ta amince da
zabin da mahaifin Nata yai Mata na farko kilata
huta da rashin yin barci Amman Ka kwanta kan
tabirman Kara duk inda Ka juya saita sokeka da
wadannan tunanin tunanen har barci ya kwasheta
don batasanma angon Nata ya shgo ba
Dukda abbakar din ba sonta yakeba amman baiqi
shigo Mata da kazar amarciba ganin Tana barci
yasa Bai tashetaba ya aje mata a gafe shikuma
ya fita waje gamida dauro alwala Nan yaxo ya
fara nafiloli Bai tsayaba saida dare ya tsala
Donma wai ya farajin barcine ya dafe Kai shi
kadai yana tunani yace ohni abbakar shin Wai
tayaya zamu fara wannan zaman auren ne oho
Allah kadai shi yabarma kansa sani saida asuba
ya tashi bayan yai Alwala gamida shirin yafiya
masallaci itama ya tasheta don Tai sallah
Amman har yaje ya dawo bata farkaba hannunsa
yasa ya dinga jijiga gadon har saida Yaga ta
bude ido sannan yace Mata to ai saiki tashi kije
kiyi sallah kinga har gari ya soma wayewa ba
yaddah ta iya haka ta tashi gamida zumburo
bakinnan Yayo gaba wai donme Zai Mata
katsalandan alokacin da takejin dadin barcin Nata
harda mafarkai masu dadi
A gurguje taje tayo alwala tai sallan sannan ta
koma kan gadon abbabakar yai mamakin irin
wannan sallah na fanne Bai kamata ace yar
malam Mai farin sani Kaman fanne ace bata iya
sallah ba abinda kuwa bai saniba shine Tun
daman can fanne ba sallah takeba sai an takura
Mata take wani lokacinma idan tayi alwalan
dakinta take guduwa taje ta zauna Ko kuma Tai
kwanciyarta yanxu hakanma tadaiyinne kawai
don karya takura Mata adaidai lokacin da takeson
ta huta
Yace fanne Ga abin kari Nan a cikin ledar can
saiki dauka ki karya da Ita Nina tafi kasuwa
dukda taji abinda ya fadan Aman saitai burus
dashi abin yai masa ciwo Amman saiya nuna Bai
damuba ya kada Kai ya wuce abinsa
Ganin ya fita yasa Tai saurin saukowA tuni
miyonta ya tsinke da abinda ta Gani tace wai
dadi kasheni inji barawon takanta yau itace dacin
kaxa yaushe rabonta da taci kaza don haka nanta
bude ciki taita diban kazarnan har saida taji tayi
qat sannan ta saurara gamida aje saurAn agefe
tace anjima idan ta farka daga barcin ta qarasa
Hakan kuwa akai Tana farkawa misalin qarfe
daya na Rana taqarasa sauran lol
Da farko zaman doya da manja suke kodade daga
wajen abbakar shi bai nemi wani Abu daga
wajentaba baiso ya nema ya janyoma kansa jafa,
I da rashin kunya dukda kuwa iya qoqarinsa da
yake wajen ganin ya kyautata mata inda zasu
shekara a haka babu Mai tankama wani inhar ba
shine yai Mata maganaba to ba zatai masa ba
don wani lokutanma koda yai Mata maganaba
bata cika amsawaba don akwai lokutanda da
zaran taga ya shigo take fita waje ta zauna harna
tsawon wasu lokuta
Har yanxu girman kan fanne da Jiji da kanta babu
Wanda ya daya ballentana axoga yinma Miji
biyayyar aure
Abbakar Dai kallonta kawai yake da kuma jiran
ranan da allah zaisa ta gane gaskia yana qoqari
wajen sauke haqqinta dake kansa kasancewar
har yanxu yana zuwa shagonnan na anguwansu
da yake musu Yan aikace aikace
Ballentanama ganin gaskia da riqon Amana irin
na abbakar yasa Mai gidansa yasa yake shirin
dude masa wani babban shago wanda abbakar
Dinne Zai dinga Kula da komai abbakar wani irin
mutun ne Maison kyautatama iyalansa Kai
hardama Wanda suke tare dashi don baiqi ya
qarar da duk abinda yake dashiba a lokaci daya
don kawai ya biyama kansa buqata daman Ai
masu iya magana sunce biyan buqata yafi