Showing 27001 words to 30000 words out of 64131 words
Chapter 10 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf
har muke aibanta abinda yake mai kyau,wallahi indai yarinya mai addini ce hadisin zadiz
zaujaini kadai ya isa ya sanar da ita ilmin aure dan haka yana da kyau mu tashi mu nemi ilmi,
Wadannan kwanakin kamar yanda nafada miki sunyi yawa maryama musamman ma awurinki
keda kike saka ran cewar zaki auri soja, kin san karfin sha'awar sojoji tafi ta sauran maza
saboda su yanayin motsa jikinsu da shan wahalarsu, idan normal namiji zai bukaceki adare sau
biyu to soja sai dai sau uku ko hudu, kinga kuwa indai hakane bazaku shirya dashi ba mutukar
kina yin period har tsawon kwanaki takwas, wani namijin ma ko kwana hudu kikeyi sai kinga ya
shiga damuwa, yanzu dai nasan bakya gane abinda nake sanar dake sai dai idan lokacin yayi
zaki fahimta"
Mikewa maryama tayi cikeda jin kunyar anty maijidda ta nufi bedroom taje ta dauko pad din ta
shiga dakinta,
Wanka tayi ta shirya cikin wasu pink din riga da wando masu laushi ta koma falo inda anty
maijidda ke zaune tana kallon _Dhoom_ a tashar mbc Bollywood,
Zama tayi ta dauki robar dambun nama ta bude tafara tsakura tana ci,
"Maryama mai zaki dan dafa mana muci?"
"Duk abinda kikace anty"
"To dafa mana taliya sai ki danyi mana sos da kifi.."
"To anty.."
Tashi tayi ta ajiye dambun naman da take ci ta nufi cikin kitchen, tana ji wayarta na kara amma
ko ta kula saboda tasan samarin dake damunta kullum ne,
Binta da kallo anty maijidda tayi fuskarta dauke da murmushi saboda da saninta take saka
maryama aiki kamar su girki da sauransu saboda tana son kiwar dake tattare da ita ta ragu
sannan idan tana yawan yin girki akai akai to hakan zai sata ta goge ta kware afannin girkin
shiyasa yanzu yawancin girkin ita take barwa tayi musu kuma alhamdulillah tun ba ayi nisa ba
har maryaman tafara kwarewa sabanin da wanda babu abinda ta iya ko dafa ruwan zafi ma
wahala yake mata saboda ita tunda ta taso agidansu kuku ne yake dafa musu duk abinda zasu
ci,
Jin karar wayar maryama yayi yawa ya cikawa anty maijidda kunne yasata dauka ta kaimata
kitchen din,
"Ungo phone dinki samarinki sai cika min kunne suke da kira.."
Hannunta ta tsame daga robar da take wanke kifi sukumbiya da ruwan kal saboda magance
karninsa,
Daga wayar tayi tana murmushi saboda ganin dr fahad ne wanda ke kiranta,
Makale wayar tayi akafadarta tafara amsawa yayinda anty maijidda ta juya ta fita daga cikin
kitchen din,
"Hello fahad...." Tafada tareda jan sunan,
"Hy maryama ta, yakike?"
Murmushi tayi "lafiya lau fahad ya aiki?"
"Alhamdulillah maryama, ya lagos"
"Lfy, ni ina abuja ma nazo hutu"
"Ahh daidai kenan, zanzo miki mu gaisa sai mu gama maganar bikinmu ko, saboda nidai na
kosa.."
Tana jin haka ta bata fuska kamar yana ganinta saboda ita ta tsani taji anyi mata zancen aure
mutukar ba za a danganta maganar auren da shaddad ba,
"Ok, to kabari zan kiraka yanzu ina kitchen ne"
"Me ake dafa mana sarauniya?"
"Cikin kosawa da maganar ta amsa masa, "ina wanke kifine so we will talk later.."
"Ok queen bye"
Ajiye wayar tayi tana tsaki, "yara kanana basu taka kara sun karya ba suce wai kaine Sa,an
aurensu saboda tsabar rashin kunya, ko idan sun aureni ina zasu kaini oho.."
Da haka ta samu ta kammala girkin tana yi tana ta korafi ita kadai,
A babban farantin tangaran ta zuba musu abincin itada anty maijidda ta fita,
A inda ta tafi tabar ta anan ta sameta tana rikeda remote tana rage volume din tv,
Ajiye abincin tayi wanda yaketa faman kamshi domin sos din tasha curry kala kala,
Fara cin abincin sukayi, girkin ya danyi sai dai kuma akwai yan kura kurai wanda ba arasa ba
nan anty maijidda ta danyi mata gyaran da yadace saboda gaba....
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/15, 10:04 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_Fatan alkairi ga duk masoyan littafin maryama sarauniya, masoya ina ganin sakonnninku
kuma ina godiya, bazan iya zayyano sunayenku bane saboda yawanku amma sai dai duk
wacce ta turo sakonta agareni mutukar ya riskeni to tana nan acikin zuciyata..._
*_24_*
~~~Cikin lokaci kankani anty maijidda tasaka maryama awata islamiyya ta kudi wacce ake
zuwa kullum da misalin karfe 10 nasafe a taso karfe 1 na rana,
Registration anty maijidda tayi mata har na naira dubu talatin sannan duk karshen term ana
biyan dubu goma sha biyar amma kuma makarantar taci kudinta saboda akwai mazakuraren
malamai masana wadanda suke koyarwa sannan duk dakikancin mutum cikin lokaci kadan zai
kai matakin da akeso,
Dogon hijab har kasa ash colour shine uniform din makarantar dolen maryama haka ta
burmashi ta tafi,
Tunda tafara zuwa makarantar kuma sai tazama busy koda yaushe bata da lokacin kanta gashi
tana dawowa gida kuma anty maijidda zata fara dora mata wani sabon karatun, dan haka ba
adauki wani dogon lokaci ba maryama tafara haddace azkar da hadisai marassa tsawo,
Yauma kamar kullum ta taso daga makaranta tana rikeda alqur'aninta tana kokarin karasawa
wurin da ta ajiye motar da tazo da ita,
"Malama maryama..."
Juyawa tayi anan taga ya sayyadi dinsu ne malamin dake koyar dasu darasin alqur'ani,
"Ohh ni maryama nikuma da haka Allah ya jarrabeni wasu na sona nikuma ina son wani.."
"Ya sayyadi" tafada fuskarta babu yabo babu fallasa,
"Malama maryama kenan, wato nidai tun ranar da nafara tozali dake na yaba da kyakkyawar
surar da Allah madaukakin sarki yayi miki..., ataikace dai maryama..., atakaice gaskiya kin
kwanta min arai"
Murmushi tayi ta bude motar, "to ya sayyadi nagode madalla, yanzu sauri nake yi dan haka
gobe ma karasa maganar"
"Ato a sauka lafiya malama maryama, Allah ya tsare"
Shiga motar tayi ta dauki hanyar gida tana yi tana tsaki saboda ita kullum burinta da addu'arta
shine Allah ya hadata da shaddad amma maimakon su hadu sai haduwa take da wasu daban,
Kamar zata fashe da kuka haka ta shiga cikin gidan tana rikeda kayan karatunta, a falo ta zube
kayan sannan ta nemi wurin zama saboda yunwa takeji gashi ta gaji lis,
Anty maijidda ce ta fito daga cikin kitchen inda take shirya abincin rana,
"Yata andawo ne?"
Hamma tayi ta rufe bakinta sannan tayi magana "nadawo anty...."
"Angaji ko?"
Kai tadagawa anty maijidda tana jingina da jikin kujerar da take zaune,
"Ai naga alama tunda gashi nan ko magana bakya iyawa,bari nakawo mana abinci tunda na
kammala.."
"Yawwa anty"
Cikin kitchen anty maijidda takoma taje ta zubo musu abincin data shirya jalop din shinkafa da
taliya sai hadadden salad agefe da lemon kwakwa mai sanyi,
Tunda maryama ta zauna tafara cin abincin bata yi maganaba har saida tagama saboda yanzu
tana dan iya cin abinci ba kamar da ba da sai ta wuni bata ci komaiba sai zallar tea empty,
Tashi tayi ta shiga daki tayi wanka tayi salla ta kwanta domin yin baccin rana amma kuma sai
hakan ya gagareta maimakon ta runtsa ma sai tunanin abin sonta tafara yi dole babu yanda ta
iya ta hakura ta tashi ta koma falo ta kunna kallo ta dauki wayarta ta kira Dada.
Yau tunda taje islamiyya taga wata bakuwar fuska a ajinsu wanda bata santa ba, yarinyar
kyakkyawa da ita ya sayyadi yana yimata dori idan yafada itama ta fada ba karamin burgeta
yarinyar tayiba saboda jin yanda take rero karatunta cikin kwarewa da iyawa gashi tsakiyar
kur'ani ake biya mata kasancewar kowa dorinsa ake masa daban,
Sai da aka gama dorawa yarinyar sannan maryama taji ya sayyadi yace,
"Yawwa malama khairat Allah yabada Sa,a"
Juyawa yayi ga maryama "malama Maryam bismillah ko.."
Ita maryama ma sai taji kunya ta kamata saboda ganin ita ba wani nisa tayi acikin alkur'ani ba
amma ga yarinya karama wacce bata wuce shekaru 25 ba ta kusa sauke alkur'ani,
Ahaka dai ta daure taje aka dora mata ta taso ta dawo ta zauna dama ita bata fiya shiga cikin
yan ajinba saboda taga duk yarane ta girmesu ba sa'anninta bane,
Tana zaune ita kadai tana amsa wayar dr yazeed wannan yarinyar da aka kira da suna khairat
tazo kusa da ita ta zauna tana murmushi,
Sallama tayi da dr yazeed ta juya wurin yarinyar,
"Adda maryam ina wuni..?"
Murmushin yake maryama tayi kafin ta amsa,
"Lafiya lau yagida"
"Lafiya lau, amma baki dade da fara zuwa makarantar nan ba ko saboda naga ban sanki ba,
nima gida natafi shiyasa bana zuwa sai jiya nadawo, yan gidanmu duk suna Kaduna nan awurin
yayata nake to shine last week muka tafi gida nida ita.."
Maryama dai sakin baki tayi tana ganin ikon Allah azuciyarta kuwa cewa take,
"Wannan yarinyar amma kinada surutu.."
"Kefa kema yar nan garince?"
Ta sake jiyo muryar khairat tana tambayarta,
"A,a nima zuwa nayi, a Lagos nake"
"Ohh Allah sarki nima kuwa ina son zuwa Lagos wallahi, amma dai ba canne asalin garinku
ba?"
"Uhm.." Maryama tabata amsa a takaice saboda ita bata son yawan magana"
"Inane asalinku?"
"Jimeta.." Maryama tabata amsa cikeda kosawa,
"Ashe shiyasa naganki haka tubarkalla, Allah sarki"
Ita dai maryama shiru tayi mata tana binta da ido domin ita dai tunda tafara zuwa makarantar
nan babu abinda yake hadata da yan ajin sai gaisuwa daga nan kuma bata shiga harkarsu
saboda tana son taja girmanta..
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/15, 10:04 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: _®HASKE WRITERS ASSOC.(HWA)_
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_*25*_
aishaummi.blogspot.com
~~~Zubawa yarinyar ido kawai maryama tayi tana ganin kokarinta yanda ta dage take tayi
mata surutu kamar ba yaune ranar farko data fara ganinta ba, ita idan itace tayi wannan surutun
ai sai kanta yayi ciwo,
"Adda maryam wacce makarantar kikeyi?"
Murmushine ya subucewa maryama saboda ita rabonta da makaranta ai tafi shekara biyar
saboda tun tana 25 years tazama kwararriya kuma cikakkiyar likita,
"Ni ai najima da gamawa, yanzu bana zuwa school"
"Ohh Allah sarki nikam iya diploma nayi amma ana nema min admission a federal university
dake Kaduna da zarar nasamu zan bar abuja nakoma can nafara zuwa makaranta"
"To Allah ya bada sa,a"
Ita dai yarinyar nan khairat haka kawai taji maryama ta burgeta saboda yanda take yin komai
nata a nutse babu hayaniya gata yar gayu kyakkyawa fes da ita komai nata cikin jan aji,
Yayinda ita kuma maryama ta kosa da maganganun da khairat keyi mata saboda ita bata son
hayaniya,alla alla take atashi ta tafi gida domin taji kanta yana neman ciwo,
Koda aka tashin ma biyota khairat din tayi har wurin motarta tana yimata zance,
"Adda maryam kibani phone number dinki mana saboda wani lokacin ko bazan samu damar
zuwa ba sai in sanar dake"
Bata phone number din maryama tayi ta shiga mota ta wuce, tun daga kofar gida tasan yan
makaranta sun dawo saboda yanda take jiwo hayaniyarsu,
Tana shiga kuwa ta gansu barbaje a falo suna ta faman cin abinci,
Yaran anty maijidda biyar duk maza dayace mace yar autar wadda yanzu take jss 1 a Nigerian
Turkish school dake nan cikin birnin abuja,
"Ahh anty dama yau yan makaranta zasu dawo shine baki fada min ba?"
"Ina sone in baki surprise dama tun safe driver yatafi debosu"
Tasowa sukayi yaran dukansu suka rungumeta, itama rungumesu tayi saboda tana jin sonsu
kamar ciki daya suka fito, zama tayi tana binsu da kallo daya bayan daya domin har yanayi
suke yi da ita afusge, nan anty maijidda tafara tuna mata sunayensu domin duk sun giggirma
shiyasa ma takasa banbancesu,
"Kinga sadiq nan ga faruk, ga haydar, ga usy nan ga kuma yanmata na nan aysha autata, ko
autan mama" anty maijidda tafada tana dariya,
"Anty ai ke duk sunayen iyayena kika hada hadda fa sunan surikina baban shaddad"
"Shi din ya sunan baban nashi?"
"Sadiq wallahi"
"Ahh to kai sadiq kazama surikin adda maryama dan haka sai tafara girmamaka tun daga
yanzu.."
Dariya maryama tayi tace "ai ko baki fada ba anty.."
Haka suka cigaba da barkwancinsu da raha itama ta shiga ta zauna suka fara cin abincin tare
da ita domin ita bata san dadin yan uwaba tunda ta taso ita kadai take rayuwarta babu yaya
babu kani, koda yamma tayi ma kwasarsu tayi suka fita yawo har anty maijidda basu suka
dawoba sai daf da sallar magrib,
Agajiye suka dawo tana bawa anty maijidda labarin khairat yar islamiyarsu mai surutu, sai
dariya suke anty maijidda nacewa,
"Kin hadu da aku kenan gashi ke kuma bakya son surutu"
"Ai anty wannan yarinyar tafi parrot..".
Haka rayuwar maryama taci gaba da kasancewa kullum bata fashin zuwa makaranta shiyasa
sannu ahankali har tayi nisa a karatu, khairat kuwa koda yaushe a makaranta tana kusa da ita
tana yimata zance shiyasa yanzu itama har ta saki jiki da ita tana biyeta suna hira, yauma
kamar kullum bayan angama yimusu dorin karatu malamin ya fita maryama take cewa khairat,
"Khairat ina gayyatarki birthday dina gobe, ko baza abarki agida ba?"
"Za abarni mana anty, shekaru nawa zaki yi? Ko 26?"
Murmushi maryama tayi, "26 khairat ai sai dai yata kuma na 30 years zanyi"
Kwalalo ido khairat tayi amma bawai dan tayarda ba duk a zatonta maryama bata kai haka ba,
"To Allah ya kara nisan kwana zanzo"
Washe gari da yamma akayiwa gidan anty maijidda decoration aka shirya abubuwa duk da
cewar ba wasu mutane akayi inviting ba iya maryama ne kawai sai yaran gidan sai ko khairat da
tazo,ko ina maryama tayi binta take da kallo saboda yanda tayi kyau cikin blue din gown mai
tsada wacce tasha stones ajiki,
Sosai suka taya maryama celebrating akaci aka sha sannan aka yanka cake, sai mangariba
sannan khairat tatafi gida,wannan dalilin ne yasa washe gari itama maryama tace da anty
maijidda zataje ta ziyarci khairat din ta kaimata ziyara tareda yimata bangajiya saboda zuwan
da tayi mata jiya, duk da cewar yarinyar ba sa'arta bace amma tana son yin zumunci da ita,
Shiryawa sukayi ita da A'isha suka tafi, sai da ta biya ta wani store tayiwa khairat yar siyayya na
kayan kwalliya da turare sannan suka je gidan wanda ke cikin unguwar mai tama,
Murnar da khairat tayi kamar zata yi hauka,cikin rawar jiki ta kaisu falon baki taje ta fara kokarin
kawo musu kayan motsa baki, sai murna take ta kawo musu ruwa da lemo suka sha,
"Kuzo muje ku gaisa da antyn nawa to"
Fita sukayi zuwa wani falo inda matar ke zaune tana rubutu acikin wani littafi,da fara'arta ta
karbesu suka gaisa suka tashi zasu fita, har sunkai bakin kofa kamar wadda aka cewa
maryama juya sai ta jiyo nan idonta suka sauka kan hotonshi kato wanda ke manne ajikin
bangon falon yana sanye cikin uniform dinshi na sojoji yayi kyau har ya gaji...
*_Ummi Shatu_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/16, 8:01 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_*Gaisuwa mai dumbin yawa ga duk members na haske writers association, ina alfahari daku
Allah yaci gaba da hada kanmu,wannan shafin nakune domin jin dadinku.*_
*_26_*
~~~Jiki asanyaye maryama ta dauke idonta daga kan hoton tafita zuciyarta sai ambulo mata
tarin tambayoyi take wanda bata da amsarsu, gashi lokaci guda kirjinta ya hau harbawa da
sauri da sauri banda bugun da zuciyarta take dum dum saboda duk atunaninta nan gidan
shaddad ne,
"To kodai shaddad yayi aure ne? Innalillahi amma da na shiga uku.."
Komawa falon baki suka yi suka zauna amma ita maryama duk ji take zaman ya gundureta
babu abinda take kauna irin taganta agida,
"Khairat bari muje mu tafi ga wannan babu yawa.."
Mikewa tayi takama hannun A'isha idanuwanta har sunyi jajur,
"Kai adda Maryam daga zuwa sai tafiya?"
"Ehh khairat bana jin dadin jikina ne shiyasa"
"Ayya to Allah yabaki lafiya ashe gobe ma ba lallai kizo makaranta ba"
"Ehh sai yanda ta yiyu dai"
Daukar ledar kayan khairat tayi tanufi falon antynta tana kwalla mata kira,
"Anty zo ki tayani godiya kinga kayan da adda maryam ta kawo min.."
Fitowa matar tayi fuskarta dauke da murmushi,lokacin itama maryama har sun fito zasu tafi,
"Ahh duk wannan, maryama harda wahala haka? To angode madalla Allah yabar zumunci"
Ita dai maryama yaken dole kawai take tana amsawa daga nan suka fice daga gidan,
Har kofar gida antyn khairat tabisu tana yiwa maryama godiya,
"Adda Maryam angode madalla"
"Babu komai khairat"
Shine kawai abinda maryama tace ta tashi motar da suka zo da ita ta dauki titin da zai mayar
dasu gida,
Ko kadan bata jin surutun da Aisha take yimata tana bata labari saboda gaba daya hankalinta
ba ajikinta yake ba,
Koda sukaje gidama dakin