Showing 24001 words to 27000 words out of 64131 words

Chapter 9 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5650


aike sai nadade zan dawo amma bata taba damuwa ba, ko mahaifiyata ce tazo ta tambayeta ko
da wani abu sai tace babu.."
Shafa kan maryama yayi yana kokarin boye yar kwallar da ta taru a gefen idonsa,

"Ke kadaice yar da ta haifa a duniya kuma ta mutu wurin kawoki duniya dan haka kema kiyi koyi
da ita ko kinyi aure kiyi kokarin rufe sirrin mijinki kinji mamana..."


D'aga kai maryama tayi tana murmushi, "insha Allah Dada nayi maka alkawarin zanyi irin
abinda mahaifiyata tayi, bazaka taba jin na kawo maka karar mijina ba.."

"Allah yayi miki albarka mai sunan mama.."

"Amin father"

Tashi tayi taje ta hau kan exercise machine ta kunna tafara yi domin tana son ta warware ta
rabu da damuwar dake damunta ko dan lafiyar Dada,

Tana daga kan exercise machine din shikuma Dada yana zaune a falo yana bata labarin
kuruciyarta, murmushi tayi saboda jin yace tun tana rarrafe take kaunar butterfly shiyasa ma
kusan duk kayan wasanta masu adon butterfly yake siyo mata,

Dawowa kusa dashi tayi ta zauna hannunta rikeda battle water mai sanyi,

"Father ashe na dade ina son butterfly.."

"Zan fito miki da wasu hotuna wanda aka yimiki kina karama lokacin hatta rigarki zanen butterfly
ne ajiki"

Dariya tayi ta jingina ajikinsa, ko babu komai labaran da yabata yasata jin damuwarta ta ragu,
sun raba dare suna hira da Dada kafin daga bisani ta shiga dakinta ta kwanta,

Kamar kowanne dare yauma kasa bacci tayi sai tsananin tunanin shaddad da yake addabar
zuciyarta.

Haka taci gaba da kasancewa kullum cikin bege da kaunar shaddad amma har yau babu
alamun sake ganinshi atare da ita,

Kullum cikin damuwa take sanin idan ta zauna agida damuwa ce zata yimata yawa yasata take
fita aiki amma kowa yasanta da yaganta yanzu yasan akwai abinda yake damunta, akwana
atashi har saida akayi shekara daya da yan watanni amma kullum son shaddad sake shiga
zuciyarta yake, sam takasa cire tunaninsa aranta, wani lokacin ma idan ta zauna tana tunaninsa
sai ta ringa cewa kila ma yanzu haka shi har yayi aure,

Samari bawai ta rasasu bane kawai har yanzu shaddad zuciyarta ke muradi,

Yauma kamar kullum cikin bacci shaddad yazo mata har yana cemata zata ganshi sannan zata
hadu dashi amma sai taje wani gari,

"Wanne garinne shaddad?"Kafada min ko inane zanzo.."

Yabude baki kenan zai fada mata tayi firgigit ta tashi....





*_Ummi A'isha_*👌🏻
[5/13, 7:16 AM] Ummi Shatu👌🏻: _®MANAZARTA ONLINE WRITERS (MOW)_



*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_




_Dedicated to Maryam Qaumi_💕


_Anty maijidda musa your page done start...._



*_21_*


aishaummi.blogspot.com




~~~Shiru tayi tana bin jikinta da kallo yanda duk tabi ta hada gumi, tagumi tayi tana son tuna
inda ya dace tatafi neman shaddad ko Allah zaisa ta dace ta hadu dashi, amma zuciyarta taji
ciwon rashin fada matan da baiyi ba, shekara daya kenan harda yan watanni tana fama da
radadin soyayyarsa acikin ranta amma bata san inda zata sameshi ba,
Tashi tayi ta shiga bathroom tayi wanka ta fito, blessing tagani tana kokarin fito mata da kayan
da zata sa,

"Blessing ki fito min da kayana ki dauko babbab akwati ki shirya min su saboda gobe zanyi
tafiya.."

"To anty.." Blessing ta amsa mata,

Shiryawa tayi tafito das da ita domin dama maryama badai kyau ba,komai tasa yimata kyau
yake yi musamman ma bakaken kaya,

Falon Dada ta shiga ta zauna tana jiranshi yafito, bata jima da zama ba sai gashi ya fito cikin
shirin fita wurin aiki,

"Father... Ina kwana"

"Lafiya lau mai sunan mama, har anfito?"

"Wallahi nafito Dada, zanje asibiti ne saboda ina son na rubuta leave with out pay..."

"Saboda me?" Yayi mata tambayar yana kallonta,

"Dada ina son zuwa wurin yan uwan mahaifiyata ne kuma zan dan jima acan.."

Ajiyar zuciya ya sauke yayi dan murmushi,

"Za kije zumunci kenan,dama ai rabonki da can tun farkon dawowarki daga Malaysia, yakamata
kije kam"

"Insha Allah gobe zan tafi"

"Da wuri haka? Har kin gama shiryawa?"

Kai ta daga masa,"nagama father.."

"To Allah ya kaiki lafiya"

"Amin dada"

Tare suka fita ita ta dauki motarta ta nufi asibiti shikuma driver yajashi suka tafi office dinshi.

Tana zuwa agurguje ta dudduba marassa lafiya taje round ta fito, wasikar daukar hutun ta
rubuta ta dauka da kanta ta nufi office din shugaban asibitin,

Kasancewar shima yana sonta sannan ya dade yana bibiyarta kan ta bashi dama ya aureta
yasa atake awurin yayi approving yabata, babu wanda ta fadawa ta kwaso duk wasu kayanta
dake cikin office din ta koma gida,

Akwatuna biyu manya manya sai da aka cika su da kayanta ahakanma dayawa barinsu zatayi
bazata tafi dasu ba,

Tunda ta dawo shirya kayan suke itada blessing har magrib tayi a lokacin dada ya dawo,

Wurinshi taje ta zauna suka fara hira anan yake sanar da ita cewar yasa an yanko mata ticket
din jirgi, zata bi jirgin karfe 9 nasafe,

Murnar da tayi gani take kamar ma har ta mallaki shaddad din, daren ranar tsananin murna bai
barta tayi bacci ba.


Washe gari misalin karfe 8:30 tabar gida su dada suka rakata airport harda su blessing, wata
kwalla ce ta siraro ta gefen idonta lokacin da suke yin sallama da dada domin idan ba dole ba
bata son yin nesa dashi, sakin hannunshi tayi taje ta shiga cikin jirgin suna tsaye suna kallonta,

"Mamana kenan duk lokacin da za ayi tafiya sai anyi kuka, haka ma lokacin da tana karatu duk
hutun da take zuwa idan zata koma to da kuka take komawa..."

Dada yace dasu blessing yana murmushin karfin hali domin shima zuciyar tasa a karye take.

K'arfe tara da rabi su maryama suka sauka a birnin abuja,

Taxi ta samu ta hau aka kaita har kofar gidan kanwar mahaifiyarta wanda ke cikin unguwar Yar
adu'a housing estate, tana gaba mai gadi yana binta da kayanta har cikin gidan,

Tana kitchen tana hada abincin karyawa taga shigowar maryama, cikin sauri ta fito tana fadin,

"Oyoyo maryama.."

Rungume juna suka yi cikin farin ciki, har suka shiga cikin falon basu iya sakin juna ba,

"Anty maijidda yau kin ganni nasamu zuwa.."

"Naganki maryama ai gara da kikazo amma kya yi shiru ki kyalemu bakya ziyartar mu?"

Murmushi maryama tayi tana kallonta saboda bata da maraba da mahaifiyarta kamarsu daya
sak,

"Anty maijidda ina yaran naji gidan shiru.."

"Maryama ai babu kowa agidan nan sai ko ke yanzu da kikazo duk sun tafi boarding school"

"Lallai anty kinyi kokari.."

"To bari na karasa shirya mana abincin nakawo dama oga baya nan bai kwana agari ba.."

Tashi tayi ta shiga kitchen ta karasa hada musu abinci ta fito dashi,

Dumamen tuwon shinkafa miyar agushi da tea sannan ga soyayyen dankali da miyar hanta,

"Kai anty duk wadannan kayan kuma a ina zamu durasu?"

Dariya anty maijidda tayi tana kallonta "maryama kenan ai dan oga baya nanne da yana nan to
da sai nayi masa girkinshi daban"

"Lallai kina kokari gashi bakida yar aiki.."

"Ai shi baya son yar aiki maryama sannan nima nafi son nayi komai da kaina.."

Murmushi maryama tayi domin dama can tasan anty maijidda kwararriya ce wurin iya tarairayar
miji da bashi kulawa shiyasa har yau mijinta ya kasa karo mata abokiyar zama,

"Yanzu maryama wa kika tsayar a matsayin mijin da zaki aura? Ina nufin waye proposed dinki
domin yanzu ya kamata ki fara maganar aure tunda kin kammala karatu har kina yin aiki duk
wata kina karbar salary, to yakamata kuma yanzu kifara shirin tunkarar shiga gidan miji domin
yanzu shekarunki 30 babu watanni, dan haka ki nutsu ki zabo nagari mai kyawawan halaye
wanda zakiji dadin zama dashi..."

Shiru maryama tayi sai dai maganar da anty maijidda tayi ya soso mata wurin da yake yi mata
kekayi nan tafara shawara da zuciyarta kan shin ta sanar da anty maijidda abinda ya fito da ita
daga gida ko kuma tayi shiru??

*_Ummi Shatu_*👌🏻


[5/14, 4:31 PM] Ummi Shatu👌🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*




*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to Maryam Qaumi_💕



_Wannan Shafin nakine yar uwa rabin jiki Khairat Dandawakee keda duk k'awayenki.._

*_22_*




~~~Ganin tayi shiru ta shiga duniyar tunani yasa anty maijidda fahimtar cewa akwai wani abu
dake damunta,


"Maryama meyake damunki ne? Ki fada min mana, nifa mamanki ce haifarki ne kawai banyi ba,
wallahi dake da dan da nahaifa acikina duk daya nake ganinku babu banbanci..."

"Anty maijidda wallahi nima ina son nayi auren to amma wanda nake son aurar ne shikuma bani
yake soba asalima ya tsaneni, rabona dashi anfi shekara daya da rabi..." Nan ta kwashe labarin
komai ta sanar da anty maijidda,

Zuba mata ido anty maijidda tayi tana kallonta cikin tausayawa amma sai ta dake domin tana
son karfafa mata gwiwa har ta samu wanda take so ta aura,

Dan haka cikin sigar lallashi anty maijidda tace,

"Haba maryama to kuma menene na daga hankali? Ki kalli fa irin baiwar kyau da Allah yayi
miki, wallahi babu wani d'a namiji da zai ce bakiyi masa ba sai dai idan har yasan bazai sameki
ba,

Kina da baiwar da kowanne namiji zai so ya mallakeki dan haka ko kaffara bazanyi ba idan na
rantse miki kan shima shaddad din yana sonki, yatafi da tabon sonki acikin zuciyarsa, son da
yake miki ma koke bakya yi masa, kuma koda bai fito ya furta miki ba afili to azuciyarsa hakane,

Dan haka ki kwantar da hankalinki ki nutsu Ki saurareni domin zan doraki akan hanya wacce
zata kaiki ga muradinki har burinki ya cika,

Nafarko dai sai kin zama mai hakuri da juriya domin hakuri shine matakin da yake kai bawa ga
kowanne irin nasara, idan kika kasance mai hakuri da juriya to wallahi zaki kai ga nasara, ba
yanzu ba ko bayan aurenku da shaddad to sai kin zama mai hakuri da juriya, bari nabaki misali,
zakiga akwai matan da suke zaune lafiya agidan mazajensu ko kansu ba aji amma idan zama
ya hadaku dasu zaka fahimci tsananin hakurinsu ne yakaisu ga wannan matsayin wanda har
ake yimusu kallon marassa matsala agidan aure, dan haka samun nasararki yanada alaka ga
hakurinki da kuma juriyarki,

Abu nagaba kuma shine ki zama mai zurfin ciki marar tona sirrinta ko kuma matsalarta, dayawa
daga cikin mata zaki samu bamuda sirri idan abu yana damun mu to sai kowa yaji bama iya rike

abin acikin ranmu, to ki zama mai rike sirrinki duk abinda ya dameki Allah zaki fadawa sannan
awurinsa zaki nemi sauki,

Wadannan abubuwan guda biyu sune masomin samuwar nasararki, sannan insha Allah a
wannan zaman da zamuyi dake zan koyar dake abubuwa da dama kama tun daga kan girki,
kula da maigida,gyaran jiki da sauransu, sai abu na karshe shine ilmin addini, ya zama dole
maryama ki shiga makarantar islamiyya har yanzu baki makaraba,idan kika shiga makaranta
zaki karu da abubuwa da dama kafin kibar garinnan, kin san kowanne namiji baya son jahilar
mace domin tarbiyar yaransa zata samu nakasu,ita mace duk kyanta duk arzikinta duk kyawun
nasabarta to mutukar bata da ilmin addini to wallahi ansamu matsala..."

Ajiyar zuciya maryama tayi sannan ta bude bakinta dakyar tayi magana,

"Nagode anty maijidda sannan insha Allah zanyi yadda kikace.."

"Yawwa 'yata, insha Allah sai kin mallaki abinda kike so"

Murmushi maryama tayi acikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya amsa,

"Yawwa tunda kinzo sai ki rubuta min maganin ciwon baya wallahi bayana ciwo yake, baby
likita.."

Murmushi maryama tayi saboda jin yanda anty maijidda tayi maganar cikin barkwanci.

Tunda maryama tazo gidan anty maijidda tare suke shiga kitchen kullum su shirya abinci
banda drinks kala kala da take koya mata gashi babu kunya ko wani abun ta hadawa mijinta da
ita kanta sai tafito ta fada mata amfaninsa da kuma dalilin yinsa,

Satinta biyu da zuwa suka fara fita ganin gari, sune wurin shakatawa da super market da duk
wani wuri wanda masu son bude ido suke ziyarta,gashi duk lokacin da suka fita to maryama
bata dawowa sai da sabon saurayi,

Yauma kamar kullum agajiye suka dawo daf da sallar magrib, hannun maryama dauke suke da
ledojin ice cream da cake ga wata ledar kuma mai dauke da dambun nama dan gaske,

Tunda suka fito daga exclusive supermarket wani guy yake faman binta ganin taki kulashi
yasashi shiga motarshi kirar Lexus ya biyosu, har gida ya bisu amma ita sam bai burgeta ba,
dakyar anty maijidda ta lallabata taje ta saurareshi nan dinma duk fuskarta babu walwala,

Bayanin kanshi yayi mata yace sunanshi mufid kallonshi kawai take kyakkyawa ne kuma daga
gani dan manyan mutane ne amma bata jin zata iya amincewa ta aureshi, nan yabata phone
number dinshi ta karba tana yatsina fuska, ganin kamar atakure take yasashi yi mata sallama
ya tafi,

Tafiya take tana tsaki har ta shiga falon inda anty maijidda ke zaune tana cin dambun naman da
suka shigo dashi,


"Yata mai farin jini wannan kuma waye? Ni ai da shi dinma kika aura.."

"Tab haba anty maijidda ni wallahi sai navy.."

Dariya anty maijidda tayi ta bugeta akafada cikin wasa,

"To shima ai naga dan gayune kakkarfa.."

"Kinga anty ni idan kina da pad kibani kawai uzuri gareni.."

"Kashhh ai kuwa saura kwaya daya kuma ina jin guda bakwai ne aciki da kamar tun dazu muka
yi maganar ai da mun siyo wani, koda yake dayanma ai zai isheki.."

"Anty wallahi yayi min kadan"

"Kai maryama har kwana nawa kikeyi?"

"Kwana takwas anty"

Ido anty maijidda ta zaro tana kallonta,

"Kwana takwas? Amma idan kinyi aure zaki rinka shan maganin da zai rage miki kwanakin ko?
Ai wannan kwanakin yayi yawa maryama gashi maza basa so saboda takura suke.."

Sunkuyar da kanta tayi saboda kunya ita kuma anty maijidda sam babu boye boye komai fada
take yi afili baro baro....





*_Ummi Shatu_*👌🏻
[5/14, 4:31 PM] Ummi Shatu👌🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_




_Dedicated to Maryam Qaumi_💕


_*23*_


aishaummi.blogspot.com



~~~Jin tayi shiru yasa anty maijidda taci gaba da fadin,

"Kidaina wani kunya da nuku nuku maryama, ba abin kunya bane dan kin san wadannan
abubuwan,

Ni kinganni nan tun kafin nayi aure lokacin ina budurwa nasan abubuwa da yawa wadanda suka
shafi al'amuran aure wallahi, ba laifi bane dan budurwa ta samu ilmi na rayuwar aure amma sai
kiji wasu suna cewa wai yan matan yanzu menene basu saniba ai practical ne kawai basu yiba
amma sun san komai, to wannan din shine daidai domin yanada kyau budurwa tasan hakan tun
kafin tayi aure ba wai sai lokacin da tayi auren sannan zata fara tunanin tayaya zan zauna da
mijina ko kuma me mijina ya kamata inyi masa ba,

Wallahi maryama nasan abubuwa da dama ina budurwa wanda wasu matan auren da yawa
basu saniba kuma zurfi acikin karatun addini shine yakaini ga wannan matakin, saboda alokacin
nakasance ma'abociyar karance karancen littattafan addini da sauraren wa'azozi wadanda
malaman addini sukayi akan rayuwar aure, amma mu yanzu sai muke ganin abin banbarakwai
idan budurwa tasan abubuwan da suka shafi, sai mu rinka yi mata kallon yar duniya ko kuma ai
yar iskace, to wallahi ba iskanci bane kuma ba mummunar wayewa bace asalima wannan itace
wayewa irin wacce musulunci ya tanada mutukar ba ta mummunar hanya tasan hakanba,
shiyasa nake cewa zaki shiga islamiyya domin ina son ki kara samun gogewa da wasu tarin
ilmin wanda ya shafi lamarin aure duk da nasan kin san dayawa daga cikinsu tunda ke likita ce
amma wannan wanda zaki samu a makaranta daban yake,

Kuma nasan zakiyi alfahari dani koba yanzu ba saboda zaki gane cewar nayi miki babban gata
wurin doraki akan turba mai kyau, sannan ko bayan kinyi aure zaki ji dadin zama da mijinki
batare da matsala ba,

Shiyasa kika ga tunda nake babu wurin wacce nake zuwa neman shawarar wai ya zan yi

inbawa mijina kulawa, domin nadade da sanin abubuwan da maza keso da wanda bakya so,
shiyasa nazama star mai haskawa awurin mijina"

Dafa kafadar maryama anty maijidda tayi sannan taci gaba,

"Yanda nasamu fada awurin mijina kema haka nake miki fata yata, amma sai kin nutsu sannan
kuma kin jajurce, akwai wa'azi dayawa da malamai suka yi akan yammata da masu shirin shiga
dakin miji musamman dan abasu wani ilimi na yanda zasu kula da mazajensu ya kamata ki
nemesu ki adana kuma ki rinka saurara sannan kinga idan har hakan ba abune mai kyau ba to
da malamai basu bata lokacin su sun zauna sun rubuta ba, kamar yadda nafada miki ba iskanci
bane kuma ba abin kunya bane saboda acikin magabata ma ansamu matar da tayiwa yarta
nasiha tabata shawarwari lokacin da zata kaita dakin miji, hatta yanda yadace ta kula da mijinta
da irin yanda zata faranta ran mijinta da abinda zata yimasa lokacin rayuwar auratayyarsu duk
sai da wannan matar ta koyar da yarta,kuma hakanne ya kamata ko wacce uwa ta zama, mu
rashin zurfafa awurin karance karancen addini da sauraren malamai duk shine ya mayar damu
baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login