Showing 45001 words to 48000 words out of 64131 words

Chapter 16 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5656

motsinshi ba,

tashi tayi taje tayi dressing din wurin ta dauko wata rigar baccin ta saka saboda waccan
shaddad ya gama illatata, kwanciya tayi amma fur ta kasa bacci sai tunanin wulakancin da
shaddad yake yi mata take, har asuba tayi bata iya yin bacci ba, gari yana wayewa bayan ta
idar da salla haka ta lallaba tayi aikin gidan sannan tayi wanka ta shirya ta fita tana dingisawa,
ta riga shaddad fita domin lokacin da tafito ta jiyo motsinshi acikin kitchen yana yin girki.


Tun daga wannan ranar bai sake yunkurin zuwa dakinta ba har akayi sati daya, ranar talata da
safe khairat kanwar shaddad tazo, ganinta ne ma ya hana maryama fita aiki, nan ta tsaya ta
karbeta sai kuma tafara tunanin abinda zata dafawa khairat din,

"Khairat me zakici inje in siyo miki?"

"Adda maryam wanne irin siya kuma? Ni da kin kyaleni ma kinyi tafiyarki office dinki kafin ki
dawo na yi mana girkin"

Ita dai maryama bata son khairat tagane cewar iya tuwone abincinta amma khairat sai da ta
dage maryama ta tafi tabarta agidan, kitchen ta shiga nan taga iya garin tuwo ne kadai store
kuma arufe ruf,

Waya tayiwa hajiya, hajiya na dauka tafada mata abinda tagani harda su karawa da karya, suna
gama wayar hajiya ta kira shaddad domin shi baima san zuwan khairat ba saboda tun asuba ya
fita,

"To dan masu gida mai cikakken iko, sai kaje ka budewa yar uwarka store saboda ita tace
bazata iya cin tuwo ba kamar matarka.."

Shiru shaddad yayi yakasa magana, "bakaji abinda nafada bane?"

"Hajiya naji.."

"Mazaje wato dai ni ban isa dakaiba ko? Ban isa kayi min abinda zanji dadiba ko? Yayi daidai"

K'it yaji hajiya ta kashe wayar, babu shiri ya koma gida yana zuwa yaga khairat a falo tana yin
mopping, "Yaya Navy ina kwana?"

"Lafiya, ashe kece munafukar ko? Wallahi idan kina zuwa kina yimin munafurci agidana kina
hadani da hajiyata sai na ballaki.."

"Oho dai nidai nafadawa hajiya yaushe zaka bar baiwar Allah da iya gayan tuwo bayan
agidansu ba haka ta saba ba, kai in banda ma so me zatayi dakai, wallahi maryama kalar abuja
ce senator ya kamata ta aura ko minister amma kai baka da ko sisi kama samu tana sonka
shine zaka rinka wulakantata.." Khairat tafada acikin zuciyarta,

Dakinshi yaje ya dauko key din store din yaje ya bude ya sake fita, yana fita ya kira hajiya yayita
bata hakuri dakyar ya samu ta saurareshi tace ta hakura,

Maryama kuwa dawuri ta dawo gida tana gama ganin patients tadawo gida lokacin ko karfe
daya na rana bata yiba, lokacin data dawo tasamu har khairat ta gama shirya musu lafiyayyen
girki, jalop din shinkafa da farfesun kifi, da salad,nan khairat ta kwashe yanda akayi har
shaddad yazo ya bude store din ta fadawa maryama,
Gidan ba karamin dadi yayiwa maryama ba saboda zuwan khairat, sunata hirarsu gwanin dadi
sai da dare sannan shaddad ya dawo, duk khairat tana lura dashi dama daukarwa hajiya rahoto
tazo yi, tana ganinsa baici abincin da aka girka ba,

"Daya.." Tafada acikin zuciyarta,dama kuma tazo ta samu store a kulle, koda sukayi shirin bacci
dakin maryama taje,

Suna hirarsu har tafara gyangyadi,

"Adda Maryam bari natafi na kwanta"

"Ke kiyi zamanki mu kwana anan"

"Adda Maryam ance babu kyau kwanciya akan gadon matar da mijinta yake kwana akai"

"To ai ke yayanki bai taba kwana akai ba dan haka zaki iya kwana"

"Bai taba kwana ba? Biyu" khairat tafada acikin zuciyarta, nan suka yi kwanciyarsu suka kwana
tare, washe gari maryama ta tafi aiki tabarta amma da wuri take dawowa bata kaiwa yamma,

Kwanan khairat uku da zuwa gidan cikin dare ta fara jiyo maganganu, tashi zaune tayi ta duba,
nan taga maryama bata nan, fita tayi taje ta tsaya a kofar dakin shaddad tana jin abinda yake
faruwa,

"Wallahi baka isa ka kusanceni da condom ba sai dai mu shekara ahaka"

"Dole na kusance saboda bazan bari ki rinka bin maza awaje kina jawo min bala'i ba, kuma
wallahi duk namijin da kika kula awaje Allah ya isa.."

"Naji nayarda amma nidai kam bazaka zomin da condom ba"

"To fice min adaki kar kiyi min rashin kunya"

"Zan fita saboda dama kaine kaje ka daukoni bani na kawo kaina ba"

Fuhhhh maryama ta fito daga cikin dakin, dagudu khairat taje ta kwanta saboda bata son susan
cewar taji abinda yafaru domin sirrinsu ne...





*_Ummi A'isha_*👌🏻
[5/20, 8:11 PM] Ummi Shatu👌🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



_*NA*_


*_UMMI A'ISHA_*





_Dedicated to Maryam Qaumi_💕



_Gaisuwa mai yawa ga Maryam Abdul, Maryam s Bello, Queen Mimi & Khadija candy_




*_41_*




~~~Tana ji maryama tazo ta kwanta tana ta faman jan tsaki, yanda maryama bata iya yin
bacciba haka itama bata yi bacciba saboda tsananin tausayin maryama,

Abin mamaki dasafe ko ta nunawa khairat cewar wani abu ya faru, sam bata nunaba haka ta
tashi fuskarta asake ta shirya ta tafi office karfe daya ta dawo sai da ta biya ta gidan Dada ta
gaidashi sannan takoma gida,

Kwanan khairat bakwai a Lagos ta shirya zata koma gida,

Wata hadaddiyar super wacce kudinta zai kai 25,000 maryama ta bata banda kayan kwalliya
cikin wata leda sannan ta bada atamfa kala biyu da leshi shima guda biyu tace akaiwa
hajiya,sannan ta karawa khairat da kudi dubu goma,

Murna sosai khairat ta shiga yi saboda ita harga Allah tana jin maryama kamar yayarta wacce
suka fito ciki daya, karfe goma da rabi nasafe ta tafi itada shaddad wanda ya tafi rakata,

Tunda khairat taje gida ta shiga bawa hajiya labarin duk abinda tagani babu Wanda ta boye,

"Hajiya ko abincinta baya ci sannan ya rufe store ya boye key din iya tuwo kawai yake bata,
sannan bai taba kwana a dakinta ba, har yau babu abinda ya hadasu da ita wai shi tsoron
daukar cuta yake dan haka bazai kulata ba sai yayi amfani da condom, shine ita kuma taki, ina
jinsu suna fada da daddare akan taki, gashi kullum cikin yimata gori yake yana cewa wai ta
dade batayi aure ba har takai shekara talatin shi yar shekara 18 zai aura,

Banda zarginta da yakeyi babu dama yaga ta dan gota lokacin dawowarta bata dawo ba sai
yace wai yawon bin maza ta tafi.."

Tunda hajiya taji wadannan maganganun ta cika tayi fam,

"Ai wannan ba maganar waya bace, zuwa ya kamata yayi ya sameni, kiduba kiga yarinya yar
arziki amma kullum cikin wulakantata yake, zai zo ya hadu dani"

Waya hajiya tayi masa tace lallai lallai yazo tana son ganinsa, dayake suna cikin wasu ayyuka
bai samu damar zuwaba har sai da akayi sati uku da maganar,

Maryama dai abubuwan gabanta kawai take yi bata sakawa ranta damuwa ba domin tasan idan
tasa bacin ran shaddad a zuciyarta to BP dintane zaita hawa, tana office tana aiki khairat tayi
mata waya tace tafadawa shaddad zatayi registration yabata kudi dubu 30 Yaya Yusuf ma zai
bata rabi, ko fada masa maryama batayi ba ta turawa khairat dubu 50 tace gashi nan harda na
siyan lecture notes, ai hajiya da sauran yan uwan shaddad wannan abu ba karamin dadi yayi
musu ba, anty babba cewa take,

"Haka muke son surika yar arziki ba yar tsiya mai bakar rowa ba"

Acikin sati na hudu da kiran da hajiya tayi masa ya shirya ya tafi, lokacin da yafito zai tafi ya
leka dakin maryama,

"Idan kin tashi daga aiki kije gidanku ki kwana ni zanje Kaduna hajiya na nemana kuma bazai
yiyu indawo ayau ba sai gobe, idan kuma kika kawo min namiji gidana ko ke kikaje wurin wani

kika kwana Allah ya isa.." Abinda yafada kenan yawuce ya tafi,

Shiryawa tayi ta tafi office daga can tawuce gidan Dada zata kwana, itafa gaba daya yanzu ma
maganganun shaddad sun daina yimata zafi saboda inda sabo har tasaba dasu,

Tunda shaddad yaje hajiya tasashi agaba da fada, ta inda take shiga bata nan take fitaba sai da
tayi masa tatas sannan tace kuma lallai lallai daga ya koma ya bawa maryama hakkinta sannan
maganar condon idanma yasake yi bata yafeba,sannan idan tayi abinci baiciba nanma bata
yafeba,
Kwananshi daya ya juya ya koma Lagos, kai tsaye asibitin su maryama yawuce yayi mata
zuwan bazata, bai sameta a office ba dan haka ya nufi dakin yara, can ya hangota tana yiwa
wani yaro wasa wanda ta duba,

Juyawa yayi ya fita yatafi gidansu maryama, yasamu Dada agida bai fita ko inaba nan suka
gaggaisa Dada yake cemasa ai maryama jiya tazo agidan ma ta kwana tace yayi tafiya zuwa
Kaduna,

Ajiyar zuciya ya saki saboda dama abinda yazo ji kenan, ya dan jima agidan kafin yatafi zuwa
gidansu,

Maryama bata dawoba sai karfe 5 na yamma, tana dawowa ta shiga kitchen ta dora girki, jalop
din taliya da macaroni tayi ta dafa kwai,

Ita bata ma san shaddad yana dakiba, akan table ta zauna taci ta shiga daki domin yin wanka,
fitowa shaddad yayi ya hau table din shima ya dan zuba abincin nata yaci sai dai bai taba
tunanin ta dan iya girki kamar haka ba saboda yaga agidansu bayi takeba,

Fita yayi sai bayan sallar isha ya dawo, duk ya damu saboda Allah ya isan da hajiya tayi masa
idan bai bawa maryama hakkinta na aureba, shiryawa yayi ya nufi dakinta tana zaune da rigar
bacci ajikinta da laptop akan cinyarta tana wani aiki,

Zama yayi agefen gadon, "kibar wannan aikin kizo muje nabaki hakkinki tunda har kin fara kai
karata akai, amma kisani idan har na dauki wata cuta ajikinki to bazan taba yafe miki ba kuma
sai Allah ya saka min domin ni ban taba aikata zinaba, kaddarace kawai Allah ya jarrabeni da
mata mazinaciya.."
"Kabarshi hakkin nayafe"

"Idan tun farko kin san kin yafe meye naki na zuwa ki fada kice tunda muka yi aure ban baki
hakkinki ba? Ki tashi ni kina bata min lokaci.."

Bai jira amsarta ba ya fincike laptop din ya je ya dorata akan bedside drewar, ya nufeta,

"Kisani kawai zan kusanceki ne dan yiwa mahaifiyata biyayya amma ba wai dan ina sonki ba,
bana sonki kuma bazan taba sonki ba har abada.."

Sam yau bata son kokawa dashi saboda tasan itace zata ji jiki amma bakaken maganganun da
ya yaba mata sune suka sakata kasa jurewa, nan ta shiga tureshi tana dukanshi,

Sai da suka dambatu sosai sannan yasamu nasarar rabata da komai na jikinta, saddakarwa
kawai maryama tayi saboda jin irin muguntar da shaddad ke yimata,

Wahala sosai ya bata dan sam bai tausaya mata yabita ahankali ba saboda ya rigada ya gama
sakawa zuciyarsa cewar tasaba bibiyar maza, amma kuma sai yaji abinda yake zargi ba haka
bane,

Wahalar da maryama tasha sai da taji kamar mutuwa zatayi shikuwa shaddad baima san a
duniyar da yake ba, gaba daya baya cikin hankalinsa dan haka raga raga yayi mata,

Dakyar ya iya kyaleta ya tattara ya koma dakinsa yayi kwanciyarsa, yabarta tana numfashi
dakyar,

Sai da asuba tayi sannan ya tashi ya shiga bathroom ya gyara jikinsa ya fito ya tafi masallaci,
lokacin da ya dawo ya dan leka dakin, har lokacin bata tashi ba tana kwance kamar yadda ya
tafi yabarta, shi kansa yasan wahalar da yabata ba kadan bace sannan gajiyar da tara mata
itama mai yawace, haka kuma yanzu yagane shine namiji nafarko da yafara saninta sannan
komai na jikinta sabone fil kamar na budurwa yar 16,dadewar da tayi babu aure baisa ta rasa
wani abu ajikinta ba,

Wucewa yayi zuwa dakinsa yana zama aka kirashi awaya daga office suzo zasu fita operation,

Wanka kawai yayi ya zira uniform ya fita, dakin maryama ya leka nan yaganta kwance cikin jini
duk bedsheet din dake kan gadon yayi face face da jini, ganin har lokacin bata tashiba yasashi
fita yatafi.


Sai da misalin karfe 8 nasafe maryama ta iya tashi, da rarrafe ta shiga bathroom ta gasa jikinta
tayi wanka amma yanda takejin radadi yasata fahimtar cewar shaddad yaji mata rauni ba
kadanba dan haka sai anyi mata dinki,

Salla tayi ta hada tea tasha ta dauki key din motarta ta rufe gidan ta fita.

Wani asibiti mai zaman kansa tanufa asibitin wata kwararriyar likitan mata,tana zuwa ta samu
ganin likitar suka shiga cikin office dinta dayake sun san juna suna haduwa awurin taron likitoci,

Bayanin matsalarta tayiwa likitar nan ta fara dubata daga karshe tace zata yimata dinki, runtse
ido maryama tayi saboda dama tasan haka zata faru, kan wani dan karamin gado ta hau dr
munnira tazo tafara kokarin yimata dinkin,

"Amma dai dr wannan mijin naki yarone ko?"

"Wallahi dr ba yaro bane kawai dai bai taba aureba sannan soja ne"

"Ah shiyasa, karfi kawai ya nuna miki bai san fatar wurin bata cika kwari ba"

Maryama tasha wahala sakamakon dinkin nan da akayi mata sai da tasamu gado ta kwanta
domin hutawa saboda wani irin jirine yake daukarta dan haka dole saida ta huta sannan tatafi
gida.


Shaddad kuwa karfe goma sha daya ya koma gida amma sai ya tarar maryama bata nan, fita
yayi yatafi gidansu yagani ko can tatafi amma koda yaje can dinma shiru bata nan, asibiti
yawuce canma bata nan, Gida ya sake komawa yana tunanin ina tatafi?

Yana zuwa gida sai gata itama ta dawo, ahankali take tafiya tana runtse idonta saboda radadin
dinkin da akayi mata,

Bude gidan yayi ya shiga itama ta shiga,afalo ta tsaya ta cire hijab dinta ta kwanta akan
doguwar kujera,

"Daga ina kike?"

"Asibiti naje"

"Wanne asibitin?"

"Karama clinic"

"Me kikaje yi? Dama namanta ban fada miki ba wallahi muddin kikasha kwayoyin hana daukar
ciki ko kikayi allura ko duk wani abu da yake hana daukar ciki sai ranki ya baci kuma koda
aboye kikayi to Allah ya isa ban yafeba"

Kallonshi tayi idonta jajur saboda ita kadai tasan irin wahalar da take sha,

"Ciwon da kaji min naje aka dinke..." Shine kawai amsar data bashi ta sake gyara kwanciyarta
tana tsotsar vitamin c,

Jin abinda tace yasashi yin shiru bai kara magana ba yawuce dakinshi, wani baccine ya kwashe

maryama ba ita ta tashiba sai da azahar, dakinta ta shiga domin yin wanka anan taga shaddad
ya cire bedsheet din dake kan gadonta, baki ta tab'e ta shiga toilet tayi wanka tafito danma
zazzabin daketa son rufeta bai rufeta ba saboda magungunan da tasha,

Zama tayi ta danyi kwalliya sama sama ta saka doguwar riga marar nauyi mai siririn hannu,
sallar azahar tayi sannan ta shiga kitchen ta dafa indomie ta debi kadan taci, takoma falo ta
kwanta,

Tana kwance tana kallo taji shigowar shaddad daga masallaci, indomie din data dafa ya debo
ya zauna akan dining yana ci, tana jinshi yana waya da wani wanda bata san ko wayeba yana
cewa wai ai yakusa ya auro karamar yarinya yar 18 years,

Yunkurawa tayi dakyar ta tashi tana kallonsa saboda yau ranace ta mayar masa da martanin
gorin budurcin da yadade yana yimata,

"Dan Allah idan katashi k'ara auren tsabar kankanta ka auro yar datake cikin cikin uwarta wacce
bata fito duniya ba,duk tsiya dai da yarinya yar shekara 14 wacce ta lalata rayuwarta gara
tsohuwa yar shekara 35 wacce ta rike mutuncinta.."

Tana kaiwa nan takoma ta kwanta, shaddad najinta sarai yaji abinda ta fada amma yayi mata
shiru bai tanka ba....

_Fatan alkairi ga Khadija maikano,Hafsatu Alkasim, jannart & Saudat yerima.._

*_Ummi A'isha_*👌🏻


[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatu👌🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_




*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*




_*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

_Dedicated to Maryam Qaumi_💕


_Gaisuwarku ta dabance, Benaxir Omar,Lubabatu m/tafsir,Khaleesat Hydar,Hafsat
Bunza,Teemah cool & A'isha (maman Khadija)_




*_42_*



aishaummi.blogspot.com


~~~Komawa tayi tai kwanciyarta saboda yau ta fadawa shaddad abinda ke cikinta, wunin ranar
akwance tayi shi babu abinda ta iya tashi tayi har dare yayi, shirin bacci tayi ta sakawa kofarta
key ta kwanta,

Kwananta uku agida bata fita ko ina har saida taji tafiyarta tafara komawa normal sannan ta fara
zuwa aiki, ai shaddad kuwa na ganin haka yafara kaiwa dakinta ziyara duk daren duniya kullum
cikin kokawa suke dakyar ya hakura ya rabuda ita ta huta na tsawon sati biyu, aranar da ta cika
sati biyun aranar ya ritsata a daki,
Tana daure da towel ta gama shan tea kenan ya shigo,

"Lafiya?"

"Kinfi kowa sanin in lafiyarce ta kawoni ko kuma sabanin haka, zan cikawa mahaifiyata umarni
ne"

"Kar kayiwa hajiya karya.."

"Nine makaryacin?" Ya tambayeta yana dosota, kafin tayi yunkurin tashi har ya take kafarta da
tashi,

Daukarta yayi zuwa saman gadon, sanin irin bakar azabar da tasha rannan yasa yau bata bawa
kanta wahala wajen biye masa suyi kokawa ba, rabuwa tayi dashi ya karaci sha'aninsa yayi
abinda yake so sai dai kuma yau sai taji har tafi rannan shan wahala saboda dinkin dake jikinta,
ji take kamar ana bin jikin dinkin ana farkewa,
Tana son tayi kuka amma bata son yaji ya samu damar rainata, sai da tasha mutukar wahala

kafin ya kyaleta ashe barinta yayi ta huta,

"Yau na hadu da jarababben miji ni maryama nashiga uku, wannan gayen kasheni yake son
yayi ne?" Ta fadi hakan acikin zuciyarta, juya kanta kawai take yi saboda azaba,

K'ankameshi tayi sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login