Showing 60001 words to 63000 words out of 64131 words

Chapter 21 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5647

mallakeshi,
shiyasa babu ruwana da sha'awar na matan waje saboda nasan nima ina dashi agida na"

Murmushi maryama tayi ta mayar da dan kwalinta ta daura ta lulluba hijab dinta ajikinta,

"Banda zuga dai navy.."

"Ba zuga bace baby gaskiya ne, wallahi kina da duk wani abu wanda yake sakani farin ciki
shiyasa lokacin da na tafi burtaniya idan kewarki ta dameni surarki kawai nake tunowa sai naji
hankalina ya kwanta nasamu nutsuwa, gashi awurin akwai mata kala kala dayake wurin boda
ne amma ni ko kadan basu taba burgeni ba saboda nasan inada wacce tafisu acan gida tana
jirana ni kadai"

Murmushi maryama tayi ta shafi kumatunsa, "Allah sarki navy ashe dai kaima kayi missing dina

wannan lokacin duk da baka sona sannan kana zargina da kula wasu maza awaje"

"Nifa dama najima ina sonki baby, kawai zafin kishine yake damuna idan natuno yanda naganku
keda wannan yaron naziru a office dinki yana gyara belt din wandonshi, da yanda kike zuwa
guest house wurin manyan mutane sai naga kamar ko akwai abinda suka taba amfana dashi
daga jikinki amma ni bana zarginki ko kodan shiyasa ma da nayi tafiyar nan hankalina bai
tashiba saboda nasan zaki kula min da kanki.."

"Lokacin da kaga naz yana gyara belt din wandonshi wallahi nice nayi masa fada saboda sai
kaga bai daura belt ba kawai yabarta haka wandonshi yana faman sabulewa shine nayi masa
magana to yana cikin gyarawa kai kuma ka leko, alh bashir kuma da nake zuwa wurinshi shine
yayi min cuku cukun siyan wannan filin da nake gina asibiti na.."
Rungumeta shaddad yayi yana shinshina kanta yana shakar kamshin saloon din da akayi mata,

"Shiyasa annabi (S.A.W) acikin wani hadisi yace kabar abinda kake kokwantonsa izuwa ga
wanda baka kokwantonsa, duk yanda ka kai ga ganin mutum mai laifine awurin Allah to karka
kuskura ka yanke masa hukunci har sai ka ganshi ido da ido yana aikata laifin, nidai dama
nadade da sanin cewar matata tawace ni daya.."
Kwace jikinta tayi tana murmushin dole amma azuciyarta tausayinshi take ji sannan dama tun
jimawa ta fahimci cewar yanada tsananin kishi akanta saboda lokacin da basa shiri ya taba
ganin text massage awayarta wanda dr fahad ya turo mata cewar yana nan yana jiranta bazaiyi
aure ba har ranar da boko haram zasu kashe sojan mijinta sai ya aureta, masifar da shaddad
yayi lokacin ba kadan bace har fahad din ya kira awaya agabanta yace masa to ko ya mutu shi
bai isa ya auri matarsa ba,koda ma ya aureta to shi bai taka matsayin da ya takaba domin a
bazawara ya aureta shikuwa tun tana budurwa yayi rayuwa da ita,

"Wai tunanin me kike yi?" Maganar shaddad ta dawo da ita cikin hayyacinta,

"Tunani nake nabar jaririna agida"

Murmushi yayi yafara driving, "naga alama dai kina ji da wannan jaririn"

"Yana kama da kaine shiyasa naji yafi shiga raina akan nu'aima"

"Nikuma kinga nafi son nu'aima saboda komai nata irin nakine sannan bata wahalar min dake
kinyi dogon suma har ana tunanin kin mutu ba.."

Dariya maryama tayi tana kallonsa, cikeda farin ciki suka koma gida.....

*_Ummi Shatu_*👌🏻

[5/25, 9:20 PM] Ummi Shatu👌🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_



*_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to Maryam Qaumi_💕


_Gaisuwa ga yan haske writers association, Afra bhai,Asmy b Aliyu, Ayusher mohd,Billy
galadanchi,faxy fation, Phertymah Xarah,Hajja ce,Kausar luv, Khaleesat hydar,Lilmeerah
cute,miss Xoxo,miss billy,Maman Shakur,maman Khadija,Nana diso,Nuceey love, Queen Mimi,
Rash kardam and rest....,Allah yakara hada kanmu ina alfahari daku..._


_*51*_


aishaummi.blogspot.com



~~~Ahaka ranar suna tazo aka gudanar dashi cikin farin ciki da nishadi, yaro yaci suna
Muhammad amma zasu kirash da nu'aim,

Aranar da akayi sunan mutane suka fara bajewa basu zauna ba kamar lokacin sunan nu'aima,
iya hajiya da anty maijidda ne kawai suka zauna sai anty babba da khairat saboda yan aikace
aikacen da za ayi washe garin suna amma su dinma aranar suka ce zasu tafi da zarar sun
gama aikin saboda shaddad kiri kiri yanzu yake nuna musu so yake su tafi subarshi daga shi sai
matarshi da yaranshi,

Hakance kuwa ta faru washe gari tunda asussuba su anty maijidda suka tashi suka gama soye
soyen nama suka gyara gidan sannan suka yi girki, karfe goma na safe har sun gama dukkan

abubuwan da zasuyi,

Waya shaddad yayiwa maryama yace yana kiranta, tashi tayi ta fita nan anty maijidda tabita da
kallo tace,

"Idanma kunyi hakuri yanzu zamu tafi mu bar muku gidanku"

Dariya anty babba tayi, "ai yaron nan jarababbe ne wallahi daga gani baya barinta ta huta"

"Itama ai dama ta dade da sanin irin mijin data aura dan tun kafin ayi bikin na kora mata jawabi"

Dariya anty babba tasake yi, "to mudai ai yau zamu basu sarari suga filin gidansu"


Maryama na shiga dakin shaddad ta sameshi kishingide agefen gado nu'aima kuma tana
jikinsa tana bacci,

"Baby kin san meye? Har baba lami karta zauna tabi su hajiya su tafi Kaduna idan da yiyuwar ta
dawo zanje na dawo da ita"

"Haba mazaje har baba lamin ma tafiya zata yi? Aikin zai yimin yawa fa ga yara ga kula dakai
sannan ga hidimar gida..."

Mika hannu yayi ya kamota zuwa jikinsa,

"Kema mazajen zaki kirani dashi kamar hajiya?"

Murmushi tayi, tafara wasa da zobunan gold din dake sanye a yan yatsun hannunta,nu'aima ya
gyarawa kwanciyarta ya tashi zaune yana kallon fuskarta, ba karamin kyau tayi ba sannan ga
barima ta gold akan hancinta,

Hannunshi yakai kan barimar yafara juyata acikin kofar bular dake kan hancinta, ba karamin
kyau hudar hancin tayi mata ba saboda komai tayi yimata kyau yake,

"Idan baba lami tatafi ai gani, zan rinka yimiki duk aikin da kika sani.."

Murmushi tayi ta kalleshii, "karfa ka sake magana daga baya"

"Bazan sakeba.."

Yafada tareda kai bakinshi kan nata,kallonshi tayi tana kokarin tashi, "ka fito fa saboda may be
sun gama shiryawa"

Fita tayi ta koma wurinsu anty maijidda wadanda suka kammala shirin tafiya,

"Uhm hajiya dadyn nu'aima yace baba lami ma basai ta zauna ba.."

Kallon anty babba anty maijidda tayi suka hada ido tareda saka dariya a lokaci guda,

"Danme zata tafi, idan ta tafi waye zai rinka tayaki sauran ayyukan gidan?"

Hajiya tafada cikin fada,

"Hajiya babu komai nima zanyi ai"

Fadin haka da maryama tayi yasa hajiya fahimtar cewar itama maryaman tafi son baba lami din
tatafi,

"To shikenan sai mu tafi ai inyaso duk lokacin da kuka bukaci yar aikin na samo muku wata"

Shaddad ne ya shigo cikin dakin yana kallon su hajiya, "hajiya idan kun shirya muje na kaiku
tasha.."

"Ah mun shirya, ku tashi mu tafi"

Kallon maryama khairat tayi, "adda maryama sai mun sake dawowa suna next year tunda na
nu'aima ma last year muka zo gashi yanzu this year mun zo na nu'aim"

Dariya anty babba tayi, "ai kuwa dai wata shekarar ma muna tafe"

Ita dai maryama bata cemusu komai ba saboda hajiya na wurin, drewar din gadonta taje ta
dauko kudi sabbi yan 200 rafa guda ta bawa shaddad, "gashi idan ka kaisu kabasu susha ruwa
ahanya"

"Ke babu kudin da zamu sake karba duk, wannan hidimar da kikayi mana har sai kin kara da
kudi?"

Hajiya tafada bayan ta tashi tana yafa mayafinta,

"Hajiya danma ban nuna miki kayan data baniba masu kyau wallahi har kala biyar kuma duk
bata sakasu sosai ba sai munje gida zaki gani.." Khairat tafada tana murna,

"To angode Allah dai yasaka da alkairi yayi miki albarka maryama, Allah ya raya miki yaranki"

Tafiya suka yi bayan ta rakasu waje, sai da taga tafiyarsu sannan ta koma cikin gidan,wanka ta
shiga tayi ta fito ta shirya ta tsuke sosai cikin riga da wando English wears, rigar pink colour ce

mai budadden kirji agaban rigar an rubuta, _love makes heart to beat sweeter.._,sai matsattsen
bakin wando wanda ya bayyanar da hips dinta sosai,

Tana tsaye gaban mirror tana taje gashin kanta shaddad ya shigo, tsayawa yayi yana kallonta ta
jikin mudubin domin indai ba sani kayiba to idan kaga maryama bazaka taba zaton ta haihu ba,

Zuwa yayi ya rungumeta ya dora kansa akan kafadarta yana kallonta ta jikin mudubin,

"Kinyi kyau sosai.."

Kiss yayi mata a kumatu ya karbi pink colour ribom din hannunta ya daure mata gashin nata
yajata suka fita zuwa falo, kwanciya sukayi acikin kujera suka fara yiwa junansu hira irin ta
masoya, har shi kanshi shaddad sai da yayi mamakin maryama saboda yanda ta dage tana ta
yimasa labarai kala kala wanda ta sani,
Sai da suka fara jiyo kukan nu'aim sannan suka bazama sukaje kai masa agaji.

Cikin farin ciki da kaunar juna sukayi wunin wannan ranar shaddad kuwa yana gida babu inda
yaje, har 12 suka kai suna kallon wani American film a tashar MBC action,

Kashe komai shaddad yayi suka nufi dakinsa, wanka maryama ta shiga yabita cikin toilet din
dole sai tare suka yi suka fito suka shirya cikin kayan bacci suka kwanta bayan sun saka nu'aim
da nu'aima a tsakiya.

Karfe 9 nasafe maryama ta tashi nan taga kan gadon babu kowa sai ita kadai, fita tayi nan ta
ga ko ina na gidan agyare tsaf anshare anyi mopping dinshi ga turaren wuta yana tashi, hatta
nu'aima da nu'aim shaddad yayi musu wanka ya hadawa nu'aima tea tana sha, shi kuma yana
kitchen yana soya chips da kwai,
Dakinta ta fada nan dinma ashare agoge sai kamshi yake, hatta toilet din an wankeshi sannan
ya tara mata ruwan da zatayi wanka dashi, wanka tayi tana cikeda farin ciki ta fito ta shirya cikin
wata hadaddiyar doguwar riga ja mai dan karamin hannu, gashinta kawai ta daure ta fita
saboda yunwar da take ji,
Shaddad yana shirya table ta karasa wurinsa,

"Sannu navy gaskiya kasha aiki"

Murmushi yayi, "karki damu baby ai kinfi haka agareni, ni bawanki ne saboda kasancewarki
SARAUNIYA,zanyi dukkanin iyawata saboda ganin na hutar dake baki wahala ba"

Kujera ya ja mata ta zauna ya zuba mata breakfast din, tare suka ci suna ciyar da junansu har
suka kammala.

Tun daga ranar kullum kafin maryama ta tashi daga bacci shaddad ya tashi ya gyara gidan
sannan ya shirya musu breakfast yayiwa su nu'aima wanka.

Yau ma tun kafin ta tashi ya gyara gidan yayiwa su nu'aima wanka yana tsaka da shiryata
yana yimata kwalliya maryama ta fito ta shiga wanka har ta fito su shaddad basu gama kwalliyar
ba, kwalliya tayi ta shirya ta saka wani blue din materia riga da skirt sun kamata sosai saboda
yar kibar data kara yi,
"Sweetheart kinyi kyau.." Haka shaddad yaketa fadawa nu'aima bayan ya gama yimata
kwalliyar yasaka mata riga yar kanti baka doguwa,

Fushi maryama tayi ta fita tabarsu a dakin ta koma falo ta fara karyawa tana rikeda nu'aim,
binta falon shaddad yayi yana murmushi yaje ya rungumeta,

"Menene abin fushin saboda nacewa daughter dina tayi kyau ke ban fada miki ba? Ai ke ba
fada zanyi da bakiba nuna miki zanyi ki gani"

Kafin tayi magana ya kama lips dinta sun jima ahaka yana nuna mata yanda tayi kyau din sai da
kyar tasamu ta kwace bakinta,

"Gaskiya kadaina wannan aikin gidan, ai idan wani yazo yagani sai ace na mallakewa hajiya d'a
na mayar dashi mijin tace.."

Hancinta ya dan ja yafara shafa barimar dake kai, "nifa kafin kice kika mayar dani ba mijin tace
ba, kafin kice na aikata duk abinda kike so.."

Kullum da safe sai shaddad yayi mata komai sannan yake tafiya office, haka suka kasance
kullum, gashi idan yadawo gida sai yayi ado yasha turare ya tura nu'aima ta kirata wai yazo
hira, kamar wasu saurayi da budurwa haka zata shirya ta fito falo hirar,

Yauma da misalin karfe 8 nadare hirar yazo ya tura nu'aima ta kirata,

"Kije kice bana nan.."

Dariya yayi ya kirata awaya, "yau kuma har dasu karyar ba anan?"

Kwantar da nu'aima tayi akusa da nu'aim ta fita, yana zaune yana kallo a tv sai kamshin turaren
precious yake yi yana sanye da wandon sojoji da wata t shirt tasu,

Akusa dashi ta zauna ta kwantar da kanta kan kafadarshi ta rikeshi,

"Yau fa ni bacci nake ji"

Kanta ya fara shafawa daga karshe ya dawo da ita kan cinyarshi ya rungumeta,

"To muyi hirar ahaka har kiyi baccin"

Hira yake yi mata tun tana cemasa "uhm" har yaji shiru, sai da yagama kallonshi sannan ya
dauketa a kafadarshi ya kaita daki, dakinshi ya koma yasaka kayan bacci ya dawo dakinta ya
kwanta ajikinta ya rungumeta.

Rayuwa mai dadi suke yi har ranar da su maryama suka cika kwana 40 cif da haihuwa, ai
ranar taga hidima awurin shaddad, sallah sukayi raka'a biyu ya dauketa zuwa toilet suka yi
wanka, wata kyakkyawar night gown mai zanen butterfly ajiki ya saka mata ya dauketa zuwa
dakinshi wanda ya gyarashi ya shimfida wani bedsheet pink and blue colour tsakiyarshi kuma
zanen wani katon butterfly ne,

Shafa hoton butterfly din tafara tana murmushi, wani farantin silver shaddad ya hawo mata
dashi kan gadon wanda yake dauke da gasasshiyar kaza da fresh milk da fruits,

Tashi zaune tayi tana kallonsa tana jin soyayyarshi tana karuwa acikin zuciyarta, fresh milk din
kawai ta dauka tasha sai fruit din shima ba kowanne ba apple da water milon kawai tasha ta
tashi zataje wanke bakinta, riketa yayi bayan ya ajiye farantin a kasa,

"Kibarni nima nasamu sauran dake bakinki mana.." Bai barta tayi magana ba yafara tsotsar
bakinta, wata soyayya mai sanyi yafara nuna mata cikin nutsuwa da so,

Yau kam maryama ta yarda cewar shaddad yana sonta dari bisa dari kuma natane ita kadai,
soyayyar da ya nuna mata bazata misaltu ba amma karshen kauna ya nuna mata tamkar zai
hadiyeta dan so, wani bacci mai dadi mai cikeda nutsuwa tayi bata iya tashi ba sai 7 nasafe,
tana bude idonta taga shaddad agaban mudubi yana shiryawa da alama fita zaiyi saboda
umifom ne ajikinsa, ta cikin mudubi ya hangota ya sakar mata murmushi, juyawa yayi yana
kallonta,

"Makararriya..."

Murmushi tayi ta tashi yayi saurin zuwa ya dauketa kamar wata jaririya, jikin maryama mai
kyaune babu wanda zai kalleta ya tsammaci tafi shekara 22 shiyasa shaddad baya jin wahalar
daukarta, cikin toilet ya kaita,

"Sorry baby, nine ko? Gashi zan fita yanzun nan.."

"Kaje babu komai sai kadawo"

Kissing dinta yayi agoshi ya fita, wanka maryama tayi ta fito tayi salla ta fita, yau ma babu inda

bai gyaraba hatta su nu'aima ya shiryasu tana zaune a falo tana kallon carton,

Satinsu biyu suna shan soyayya suka shirya suka tafi kaduna sukayi kwana uku daga can
suka wuce abuja suka yi kwana biyu, kayan gyaran jiki anty maijidda ta tattarawa maryama ta
bata tana cewa "naga wannan mijin naki bita zaizai ne"

Dariya maryama tayi, "ni anty ai wadannan kayan basu dameni ba well women kawai nakesha
kuma shima har gyara mace yake shiyasa yawancin matan manya shi suke sha"

"To koma dai menene idan kana da kyau ka kara da wanka dan haka dole ki kara da
wadannan".

Kwana biyu sukayi suka koma Lagos, washe gari maryama ta koma office ta fara zuwa aiki,
gidan Dada takai nu'aima da nu'aim ta ajiyesu saboda yanzu dada babu inda yake zuwa yana
gida.





_*Ummi A'isha*_
[5/25, 9:20 PM] Ummi Shatu👌🏻: _®HWA_


*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to Maryam Qaumi_💕



_Wannan Shafin nakune Besty phertymah Xarah keda Cwt Kausar luv (aminiya ta kwarai)_



_*52*_

~~~Tunda taje asibitin suke waya da shaddad tana waya tana duba patients dinta, duk wanda
ya shiga office din zaiji tana magana kasa kasa ga earpiece makale akunnenta, har tagama
duba patients din ta nufi round har lokacin suna tare awaya itada shaddad tana fada masa
dakin yara zataje round,
Su Kansu basu san tsawon lokacin da suka dauka tare awayar ba, kullum haka suke shafe
lokuta masu tsawo suna waya idan suna gida kuwa suna manne da junansu,

Akwana atashi babu wuya har an kammala ginin asibitin maryama furnitures ne kawai ba azuba
ba aciki, daukar shaddad tayi ta kaishi yaga asibitin, ya sanya mata albarka suka dawo gida,

Kwana biyu baya Dada yayi mata waya yasanar mata ya siyo mata furnitures din daga kasar
India shine gudun mawarsa, lokaci kankani aka yiwa asibitin fenti aka zuba masa komai da
komai aka rubuta suna asama MARSHANN HOSPITAL,wato Maryam, shaddad, nu'aima &
nu,aim,
Cikin yan kwanakin aka shirya walimar bude asibitin, duk yan uwa da abokan arziki sun halarci
walimar, sannan ga wani babban gida kato da yake cikin asibitin wanda yasha kayan alatun
more rayuwa aciki shikuma gidan maryama ne wanda ta gina musu zasu koma idan har
shaddad ya yarda, lokacin data fada masa murmushi yayi yace,
"Shikenan nayarda tunda dan kwali yaja hula.." Murmushi maryama tayi ta manna masa kiss a
gefen kumatunsa, nan da nan suka yi packing din kayansu suka koma sabon gidan, maryama
ta debi ma'aikata da yawa kowacce lalura ta yara akwai likitanta, sannan duk da haka tana
zuwa asibitin da take aiki tana ganin patients gashi kuma state university suma sunyi inviting
dinta kan taje ta rinka yin lecturing acan a matsayin contract,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login