Showing 63001 words to 64131 words out of 64131 words

Chapter 22 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5611

nan abubuwa suka taru suka
cakude mata danma dai business dinsu itada anty maijidda ba komai take yiba anty maijidda
dince take fita dubai ta shigo musu da kaya,

Duk wannan ayyukan basu hana maryama kulawa da mijinta ba, bashi kulawa take yi sosai
sannan har lokacin bata da mai aiki balle mai raino, ita dashi ne suke yin komai na aikin gidan,
sai idan zata fita office ne take daukar su nu'aima ta kaisu gidan Dada kafin shekara ta zagayo
su saka nu'aima a makaranta,
Agajiye lis ta dawo Gida saboda sai da tafara zuwa office tayi aiki sannan ta wuce university
tayi lectures har guda biyu daga nan ta dawo asibitinta taga patients sannan taje gidan Dada ta
dauko yara ta nufi gidanta,

Wanka tayiwa yaran ta shiryasu ta dora girki tabasu suka ci suka kwanta bacci har lokacin bata

yaye nu'aim ba domin watanshi goma sha daya,

Wanka da ruwa mai zafi itama tayi ta fito nan taga shaddad kwance agefen gadonta,

"Yaushe ka shigo mijina? Allah sarki daga gani kaima ka gaji"

Janta jikinsa yayi ya rungumeta,

"To ya zanyi tunda na zama mijin hajiya.."

Murmushi tayi tana kallonsa tana ji yana shirin rabata da towel din dake daure ajikinta,

"Kayi hakuri idan har nagaza a kulawar da nake baka, yanzu fada min awurin da na gaza sai na
rage ayyukana ko nadaina zuwa office ko nadaina lecturing na zauna na baka kulawa"

"Ni baki gaza ba ako ina baby, aikin mace ko kasuwanci dama bashine abin kyamatar ba abin
kyamatar shine ta fifita aikinta ko kasuwancinta fiyeda kulawa da mijinta nidai ni kika fi fifitawa
akan komai kuma nasan baki gaza ta ko ina ba sai dai har yau kin kasa bawa nu'aim kani"

Rungumeshi tayi tana murmushi, "wai ai bari nayi idan ka auro yar 18 years sai ta basu kanin.."

Rufe mata baki yayi, "ai ni yanzu babu wacce zan sake aurowa domin ke Allah ne ya zaba min
ke yabani, da atunanina bazaki soniba bazaki girmamani ba bazaki girmama yan uwana ba,
nazata karamar yarinya ita zan iya juyawa ita zata fi bani girma, ashe abin ba haka yakeba ke
din duk da tsananin kyawunki da ilminki da dukiyarki da shekarunki hakan bai hanaki girmamani
da yimin biyayya ba, lallai Allah shine tsarkakken sarki, hakika Maryam ke wata sashe ce babba
na rayuwata, kuma naji dadi da rayuwarki tayi kamantacceniya da wani hadisi na manzon Allah
wanda yace ka bibiyarwa mummuna da kyakkyawa sai kyakkyawan ya shafe mummunan daka
aikata a baya, tabbas wannan magana haka take idan mutum yayi abu marar kyau to ya
kamata ya aikata abu mai kyau agaba to sai yasamu kyakkyawan sakamako,

Godiya ga Allah wanda ya kyautata rayauwarki da halittarki sannan ya mallaka min ke a lokacin
da ban zata ba"

Soyayya ya shiga gwada mata bai bari ta sake yin magana ba.

Cikin satin shaddad yazowa maryama da labarin cewar anturasu kasar Canada zasu tafi ta
ruwa, ganin maryama kawai yayi idonta fal da kwalla,

"Navy yanzu irin tafiyar nan da ka taba yi zaka sakeyi ka tafi kabarni?"

Rungumeta yayi yana dariya, "wasa fa nake yi miki, wasu aka tura amma banda ni aciki"

Rungumeshi tayi cikeda farin ciki, acikin kwanaki biyu kacal ta biya musu kudin ziyartar kasashe
biyu, zasuje India medical check up domin kafarta tana dan ciwo kuma tana son aduba musu
lafiyar yaransu daga nan sai su wuce madina umarah,

Shi shaddad ma bai san ta biya musu ba sai da visa din ta fito nan suka tattara suka tafi yana
mai cikeda farin ciki da saka mata albarka saboda kudinta sam bai rufe mata ido ba, duk abinda
ya kamata na harkokin gida da dangi yimasa take babu rowa bare kyashi,

Rayuwa mai dadi suka gudanar awadannan kasashen tun a india ta yaye nu'aim daga can suka
wuce umarah, sati uku a kasa mai tsarki suka yi suka dawo Nigeria, suna dawowa aka kawo
kayan auren khairat kanwar shaddad nan maryama ta zage tayi mata kayan kitchen hadaddu
duk wani abu na amfanin kitchen babu wanda bata siyaba takanas tayi order aka kawo mata
daga kasar waje,

Sai da ta kashe kudi sama da dubu dari biyar a siyayyar kayan khairat, tun ana saura sati shida
bikin sukaje suka kai kayan Kaduna itada shaddad, lokacin da sukaje tana cewa hjiya shaddad
ne ya siyi kayan shikuma yana cewa itace daga karshe dai har hajiya tagane itace ta siya taita
sanya mata albarka.
Lokacin bikin ma itace ta zama amara kirjin biki idan ba sani kayiba zaka zaci kanwarta uwa
daya uba daya ake aure saboda duk abinda aka nema zata cire kudi ta siyo daga ance babu
kaza zata dauki kudi ta siyo, _(chaii Mata mu tashi mu nemi kudi kodan taimakon mazajenmu,
arzikin mace yana sawa asamu zaman lafiya saboda rokon miji bani kaza bani kaza zai ragu
kuma in mun samu kudin banda yiwa miji rowa dan Allah, kar muce yaci kudinsa muci namu,
ahadu aci gaba daya shine zaman tare..)_

Rayuwarsu maryama da yan yaransu guda biyu haka taci gaba da tafiya cikin farin ciki har
yaran sun fara zuwa makaranta, amma daga su maryama bata sake samun wani cikin ba,
shaddad ya samu karin girma yazama canal, muna yimusu fatan cigaba arayuwarsu....



Alhamdulillah!!

Anan littafin maryama ya kammala bawai dan ya kare ba sai dai kawai gajiya da nayi sannan
kuma masu karatu nasan kun kosa kuga an kammala maryama queen, Allah ya yafe mana
kuskuren dake ciki ya tara mu acikin ladan tare.



*SADAUKRWA*

Sadaukarwar littafin gaba daya takice kawata kuma aminiya ta jini, MARYAMA QAUMI

GAIDAM, ina alfahari dake Allah yabarmu tare har abada.


*TUKWICI*
Tukiwcine agareku,

ANTY MAIJIDDA MUSA

AUTAR HAJIYA

ANTY ZAINABU (Anty sis)

KHAIRAT DANDAWAKI

Da dukkan masoyan Ummi Shatu.

Fatan alkairi ga yarana masu albarka MUHAMMAD (Sultan) &NANA A'ISHA,Allah ya raya
minku cikin imani da aminci.


Jinjina ga dunbin masoya na wadanda suke kaunata suna bibiyar rubutuna sannan suna yimin
fatan alkairi akoda yaushe, nima ina alfahari daku sannan banida kamarku saboda kun zama ni
nima na zama ku da bazarku nake dancing, ina yimana addu'ar yin ibada cikin koshin lafiya da
kwanciyar hankali, Allah ya karbi ibadunmu ya amsa mana addu'o'inmu sannan ya biya mana
bukatunmu, sai mun hadu acikin littafi nagaba mai suna MIJINA SIRRINA, wanda zaizo muku
bayan salla da yardar Allah, Ummi Shatu ta gaisheku kyauta,duk wani masoyin Ummi Shatu to
itama tana kaunarshi.



*_Ummi Shatu_*👌🏻




Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login