Showing 18001 words to 21000 words out of 64131 words

Chapter 7 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5619



_Dedicated to Maryam Qaumi_💕




*_15_*



~~~ Ji take kamar ta fashe da kuka sai dai kuma ta dauki alwashin bazata taba yiwa wannan
yaron kuka ba kome zaiyi mata,

Kallon fuskarta taci gaba dayi wanda take a kumbure sannan ga shatin yan yatsun shaddad nan
sun fito rado rado ajiki,

Girgiza kai tayi ta Shiga bathroom tayi wanka tafito, rigar baccinta ta zira ta fiddo kwalabin
benalin guda hudu ta shanye saboda jin ranta take yana sake dagule mata,

Babu bata lokaci bacci yayi gaba da ita, da safe kuwa da wani irin zazzabi ta tashi ajikinta
wanda tasan marin da shaddad yayi matane sanadinshi,

Ko tashi kasawa tayi har saida blessing ta shigo ta taimaka mata ta rakata toilet tayi wanka
tafito, har lokacin fuskarta tana nan a kumbure,

Komawa tayi ta sake lwanciya ta lulluba tana mai jin tsanar shaddad acikin ranta,

Wuni guda tana kwance bata ci komai ba dakyar ta iya tashi tasha ruwan tea ta kwanta, koda
shaddad yazo kaita office blessing cemasa tayi bata da lafiya, kafada kawai ya daga alamun ko
oho yayi tafiyarsa.

Da yamma misalin karfe 5 dr naz yazo gidan duba maryaman, har dakinta ya shiga shida
blessing domin ganin jikin nata, blessing ya tambaya ko tasha magani tace a'a nan yafara
yimata magana,

"Haba dr ya za ace bakida lafiya amma bakisha maganiba? Meyasa?"

Dakyar ta bude idonta wadanda suke jajur ta kalleshi,


"Zansha dr so nake sai natashi lokacin naji karfin jikina.."

"To bari nayi miki allura inyaso idan kika tashi sai kisha magani.."

Dakyar ta yarda dr naz yayi mata allurar a hannu saboda tana tsananin tsoron allura ko kadan
bata sonta,

Murmushi dr naz yayi yana kallonta bayan ya zare allurar daga jikinta,

"Ke baki son allura amma kuma kinfi kowa yiwa mutane allura,koda yake ashe fa ance doctors
sunfi tsoron allura.."

Kwanciya tayi tasake lulluba, "nagode likita"

Sallama yayi mata yatafi, ahaka tasake kwana da zazzabin gashi jini har yataru a idonta guda
daya wanda shaddad ya mareta, washe gari ma sai da dr naz yasake dawowa yayi mata allurar.

Sai da ta kwana uku tana zazzabi kafin ta dan warware,akwana na hudune ta shirya fita office,
koda shaddad yazo kaita bata musaba ta shiga suka tafi yakaita ya sauketa sai dai amma ko
k'ala bata shiga tsakaninsu ba, lokacin da ta tashi ma haka ya koma ya daukota,

Kullum haka yake kaita ya daukota sai dai babu kalmar dake hadasu,shi dai yanzu yagama

sanin wacece maryama, kaf halayenta babu wanda bai saniba hatta shaye shayen datake
yasani

Ranar juma'a da daddare mahaifinta yadawo daga tafiyar da yayi zuwa saudiyya, shaddad yayi
mutukar mamaki jin bata sanar da Dada cewar ya mareta ba, harkarta kawai taci gaba dayi,

Tana zaune afalon dada da medical glass a idonta gabanta kuma laptop dintace ajiye tana
kallon wani american film _iron man_,sanye take da pink colour din doguwar riga mai hannun
shimi kanta babu dan kwali, gefenta kuma Dada ne zaune yana cin tuwon alkama miyar
kubewa danya, hira suke yi ita tana kallon film din data kunna shikuma Dada yana kallon tv,
"Father zan samu rancen kudi.."

Kafin yabata amsa shaddad yaturo kofa ya shigo hannunsa rikeda envelope babba,

Zama yayi suka gaisa da dada ya mika masa envelope din,

"Mai sunan mama me zakiyi da kudi idan nabaki rence?" Dada yafada yana bude envelope din
da shaddad yabashi,

"Dada ginin asibitina da aka fara yifa ya tsaya gashi ko rabi ba ayiba kuma wallahi banida kudi,
shine nake son ka ara min 3 millions adan kara tsayin ginin.."

Dariya dada ya danyi yaciro zungureriyar takardar dake nade cikin envelope din yafara dubawa,

"Daughter dama shi gini ai sai da kudi, shiyasa nace miki kibari sai kin tara kudi sosai sai kiyi
ginin amma haka kawai kika tsiri gini ba kadanba bayan baki tara kudiba.."

Juyawa yayi ga shaddad ya kalleshi,

"Masu tafiya Niger delta dinnan aka turo, jiyama munyi meeting kan cewa za atura sojoji ta ruwa
zuwa Benin to amma bana jin za atura dakai.."

"Ah ranka yadade ai da antura ni nima ina son zuwa kawai dai matsalar banida lafiya ne dan
zazzabi ne ke damuna"

Shaddad yafada yana murmushi,

"Allah yabada lafiya, ga maryama nan ai sai tayi maka allura ko?"

Girgiza kai yayi "nasha magani ai Yallabai"

Tashi Dada yayi ya shiga cikin bedroom dinshi,

"Nima dama ba yimaka allurar zanyi ba, maza nawa nagani irinka atube..?" Yajiyo muryar
maryama tana yimasa gatsali,

Ko saurarenta baiyiba yamaida hankalinsa kan tv,amma aranshi cewa yake,

"Dama nasan ai kin ga maza irina dayawa tsirara koda baki fada ba.."

Bai sake kallon inda take ba har dada yafito suka gama abinda zasuyi yayi masa sallama yatafi.

Yau kimanin sati uku kenan da marin maryama da shaddad yayi,

Yana kwance adakinsa yana bacci yaji karar wayarshi, hannu ya mika ya katse kiran, nan aka
sake kira, sai da aka kira wurin sau biyar sannan yatashi yana dubawa, bakuwar number yagani
nan ya kalli agogo,karfe 2 nadare,

Kara wayar yayi a kunnenshi nan yaji muryar mace tana kuka,

"Shaddad ka taimaka min Dada babu lafiya kazo mu kaishi asibiti, dan Allah kayi sauri ko motsi
bayayi gashi acikin dakina, wayyo nashiga uku..."

Ko ba afada masa ba yasan maryama ce saboda ya gane muryarta,dagashi sai dogon wando
da singileti ta maza ko neman riga bai tsaya yiba ya fita da sauri, tsabar gaggawa ma agida
yabar wayar tashi,

Yana zuwa gidan ana dauke wuta, acikin duhun yasamu ya kutsa ya tasamma dakin maryama,
yana shiga yafara jiyo shesshekar kukanta,

"Maryam, kunna fitila mana, ina Yallabai din yake, maryam kunna haske.."

Yana wadannan maganganun yana tafiya domin karasawa gadonta, caraf yaji an makaleshi
tareda jefashi kan gadon, nan ta haye jikinsa ta kwalla kara mai mutukar karfi,

Kansa ne ya daure gaba daya yana tunanin to meye yake shirin faruwa, makalkaleshi yaji ta
sakeyi tana ihu, kafin yayi wani yunkuri har dada ya shigo cikin dakin kuma daidai lokacin NEPA
suka dawo da wuta mai karfin gaske, mirginawa tayi karkashinsa ya zama shine asamanta,

Duk gashin kanta ya tarwatse, rigarta anfara yagata,tana rungume dashi sai ihu take kwallawa,

Tsayawa dada yayi yana kallon shaddad fuskarsa a daure, kafin wani lokaci har gidan yacika da
mazauna barikin wadanda suka shigo domin bayar da taimako saboda sun jiyo karar maryama,

Tashi tayi dagudu taje ta tsaya a bayan dada tana kuka,

"Wayyo dada nashiga uku.."

Shikam shaddad yama kasa motsi yana zaune akan gadon kansa a daure,

Wata tsawa dada ya daka masa mai sa firgici,

"Kai shaddad ashe bakada mutunci ban saniba? Yar tawa kwaya daya zaka lalatawa rayuwa
kayi mata fyade? Na daukeka kamar dan da nahaifa acikina shine zaka yimin mummunar
sakayya? To daga yau sai yau karka sake shigo min cikin gidana sannan babu kai babu yata,
kuma sai kabar garin nan agobe ba jibiba, sannan sai na dauki mummunan mataki akanka...,
get out!"

Tashi shaddad yayi batare da yayi magana ba sai dai idanuwansa sun kada sunyi jajur, ko musu
baiyiba domin yasan zaiyi wahala a yarda dashi kasancewar ankamashi red handed, wato
dumu dumu,

Daga idanuwansa yayi ya kalli maryama wadda ke tsaye tana yimasa murmushin mugunta sai
yanzu yagane ashe makirci ta shirya masa,

Fita yayi daga gidan cikeda kunya da takaici domin yasan yanzu duk jama'ar wurin zasu daina
ganin kimarshi sannan sun gama yadda cewar kwadayine yakaishi dakin maryama har yaso
yimata fyade,

Gida yakoma yanemi wuri ya zauna yana kukan zuci, ji yake kamar ya kira mahaifiyarshi ya
sanar da ita halin da ya shiga sai dai kuma baya son ya daga mata hankali, wayarshi ce tadauki
ruri yadaga batare da yayi magana ba,

"Hello, yanzu nasan kagama tabbatar da cewa maryama cikakkiyar karuwace kamar yadda ka
fada....."


Kit ya katse wayar yana rike da kanshi, har gari yawaye idonshi biyu, shiryawa yayi ya tattara
kayansa domin yasan yau zai bar garin Lagos koda baya so saboda zai bi sahun wadanda za
atura Benin,

Fita yayi zuwa headquarter amma duk inda ya gifta maganarshi akeyi cewar yaje yiwa maryama
fyade, abokinshi Abbas ne kawai ya tareshi da maganar yace yasan bazai aikata hakaba, nan
ya kwashe duk abinda yafaru ya fadawa Abbas,

Posting letter dinshi yaje ya karba saboda dama an rigada an buga sai dai kawai arubuta sunan
mutum abashi yayi signing,

Barikin yakoma ya tattara komai nasa ya fito yana mai yiwa barikin kallon karshe saboda yasan
shida sake dawowa ciki har abada...

*_Ummi A'isha_*👌🏻


*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*





*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*




_Dedicated to Maryam Qaumi_💕

*_Gaisuwa mai tarin yawa ga Maryam s Bello da Aysha garkuwa, tabbas ku masoyana ne na
hak'ik'a dan haka wannan shafin na badashi tukwici agareku daku da duk wani wanda yake jin
yana son ummi Shatu_*



aishaummi.blogspot.com



_*16*_



~~~Tagaban gidansu maryama yawuce yana jin wani bacin rai yana ziyartar zuciyarshi,ko daga
ido bai yi y kalli gidanba har yayi nisa dashi amma acikin zuciyarsa damuwace kwance saboda
yasan mahaifin maryama ya kullace shi acikin ransa domin yana tsananin son yar tashi sannan
ya daukeshi kamar dan cikinsa yabashi dukkan yarda sai dai kuma daga karshe yaci amana,
Tamkar marar jini ajiki haka yake takawa har ya karasa fita daga cikin barikin, taxi ya tara ya
shiga ya tasamma tashar mota.

***

Tsalle ta doka ta fad'a kan gado ta kwanta tana shakar daddadar iskar air condition din dake
ratsata, yanzu kam ranta yayi mata fari kuma hankalinta ya kwanta sakamakon mayarwa da
shaddad martanin abinda yayi mata da tayi,

Bargo ta jawo ta rufe jikinta ta lumshe idanuwanta tana jin wani irin farin ciki yana ziyartar
zuciyarta,

Rungume daya daga cikin manyan teddy din dake kan gadon nata tayi tana murmushi,

"Wai har ni wannan yaron zai daga hannu ya mara sannan ya kirani da karuwa..., sannan kuma
har ya tsammaci zama lafiya, wallahi bazai yiyuba, yanzu nasan na tabbatar masa da cewa ni
karuwar ce kamar yadda yace.."

Duk wadannan maganganun tana yinsu ne acikin zuciyarta fuskarta kunshe da fara'a, ranta fari
tas bacci ya kwasheta.

Washe gari kamar kullum haka ta tashi tana zuba mulki tayi wanka ta shirya kuku ya hada
mata abincinta kamar yadda ya saba, wata red din gown tasaka mai adon duwatsu ta yafa dan
siririn mayafin rigar tana ta faman zuba kamshi,ga yar siririyar barimar gold tasaka acikin hudar
hancinta domin tana tsananin son kwalliyar hanci,
Falon Dada ta nufa tana tafe tana taunar chewing gum, zaune ta iskeshi ya kammala breakfast
yana jiran driver yazo ya kaishi office, zama tayi agefenshi tana dan murmushi,

"Good morning father.."

"Morning daughter, har anfito?"

"Nafito Dada.."

"Gashi kuma babu mai kaiki office, koda yake kibari idan driver na yazo sai mu fita tare muyi
dropping dinki"

"Babu komai dada kabarshi ma zanyi driving da kaina yau..."

"To shikenan dama ina son kifara driving din saboda bana son nasake baki wani drivern asamu
wata matsalar"

"To Dada, insha Allah ma daga yau ni zan rinka kai kaina office ina dawowa.."

"Idan kikayi hakan nima hankalina zai fi kwanciya"

Murmushi tayi ta mike tsaye, "Dada bari naje natafi.."

"To mai sunan mama sai kin dawo sannan daga yanzu zuwa yamma zan turo miki kudin da kika
nema harda kari.."

"Dada rencen kabani?" Ta tambaya tana dariya wanda har saida kyawawan fararen hakoranta
suka fito waje,

"Kyauta nabaki daughter saboda ina son ki samu ki kammala ginin asibitin naki.."

"Ai dada akwai saura sosai yau idan natashi daga office zan biya nadubo ginin, nagode sosai
dada Allah ya kara girma da lafiya.."

"Amin mai sunan mama"

Fita tayi fuskarta kunshe da murmushi, har cikin motarta blessing ta rakata tana dauke da hang
bag dinta da sauran kayan tarkacenta nazuwa office,

Bakin glass tasaka ta daura belt ta tashi motar, sosai motar tayi mata kyau kuma ta karbeta,
ahankali tafara driving tabar harabar wurin ta nufi asibiti.

Tunda shaddad yabar Lagos bai ko je gidaba ya tafi Benin domin abubuwan dasu gudanar
awurin masu muhimmanci ne, dadin dadawa kuma za abasu training na sati biyu shiyasa ma
baiyi yunkurin zuwa gidaba, kullum da haushin abinda maryama tayi masa yake kwana yake
tashi gaba daya yakasa mantawa da ita balle ya manta da abinda tayi masa, zuciyarsa duk
lokacin da ta tuno masa da abin sai yaji kamar zata hudo kirjinsa tafito waje, ahaka ya daure ya
kammala wannan training din ya nemi izinin zuwa gida kuma cikin sa'a ya samu, shiryawa yayi
ya hari gida saboda yanada abu mai muhimmnanci da yake son aiwatarwa.


K'arfe Biyar daidai maryama ta fito daga cikin office dinta ta nufi packing space domin daukar
motarta, dr sameer ne ya biyota a baya yana tsayar da ita,

"Ranki ya dade har zaki fita..?"

Murmushi tayi ta bude motarta ta dafa murfin kofar motar ta dage glass dinta dake sanye
afuskarta ta mayar dashi kan goshinta,

"Wallahi har zan fita dr, ina sone nafara zuwa wurin ginin hospital dina da akeyi acan agege"

"To Allah yabada nasara, dama kawai zuwa nayi nace miki wani abu idan kin bani dama sai na

fada.."

"Nabaka dama dr kafadi ko menene.."

Sai da ya danyi murmushi sannan yace, "kinyi kyau yau, sannan da ace zaki bani dama to da
na aureki na kasance dake har abada.."

Murmushi tayi ta shiga cikin motar ta zauna, tana kokarin daura belt ta kalleshi,

"Dr kenan zandai baka damar nan in gani.."

"Amma kuwa da kin gama yimin komai"

Rufe kofar tayi tana murmushi ta tashi motarta ta fita tana yi masa bye bye, can agege ta nufa
wani katon daji inda ake gina mata asibitin yara wanda yake mai girman gaske, kasancewar
ginin katone yasa ko rabi ba ayiba, fita tayi ta dan dudduba takoma cikin mota ta nufi gida, tana
zuwa gida ta sake yin wanka ta tsuke tafito domin zuwa stadium,
Kullum haka take bata da lokacin hutu sai week end sai dai tunda samari suka yi yunkurin keta
mata mutuncinta har yau bata sake komawa club ba.

Lamurranta kawai take aiwatarwa hankali kwance kuma yanzu tafara ji a zuciyarta cewar zata
zabi daya daga cikin samarinta dr sameer ko da yazeed ta aura saboda shi dr naz da fahad duk
yara ne amma har yanzu zuciyarta ta gaza tantance mata wanda ya dace ta aura, batun
shaddad kuwa tuni har ta mance dashi saboda yanzu a kalla za ayi kimanin watanni biyu da
tafiyarsa daga gidansu.

Fitowarta kenan daga wanka ta danyi abubuwan da zatayi ta fesa turare ta saka rigar bacci
pink colour light, rigar bata da nauyi sannan iyakacinta gwiwarta,

Kwanciya tayi ta kunna air condition ta kashe wuta, babu bata lokaci bacci yace muje zuwa, can
cikin dare tana tsaka da bacci taji kamar motsin ana daure mata hannu ta baya, sake gyara
kwanciyarta tayi, abu sai kara gaba yake sai jin kafafunta tayi suma a daure, kafin ta iya saita
tunaninta har andaure mata baki, a lokacin tsoro da razani suka dirar mata, ihu take son yi
amma babu hali, tana ji aka dauketa aka dorata akafada akayi waje da ita cikin sand'a,

Hankalinta idan yayi dubu to duk yagama tashi sannan gashi garin bakikkirin yake da duhu
kasancewar anyi ruwan sama gashi babu wuta kuma ankashe injin da aka kunna tun karfe 1,

Wani lallausan hannune ke rikeda ita sannan ga wani kamshi mai dadi da sanyi da take shaka,
zuciyarta sai harbawa take a tamanin musamman ma dataga an nufi dajin kare kukanka da ita
wanda ke cikin barikin daga can karshe gashi yayi nisa da gidajen cikin barikin ko kashe mutum
za a iya yi batare da an saniba,

Kan wani yayi taji an jefata tareda take kafafuwanta, idanuwanta ta runtse dan tsananin azaba,
ahankali taji an matso saitin fuskarta, fitila ya kunna ya haska mata fuskarsa take taji tana shirin
sakin fitsari a wando saboda ganinshi, idanuwanta ta zazzaro saboda tsananin firgici,

Daurin da yayiwa hannunta da kafarta ya kunce yasake saka kafarshi ya take kafarta, kyallen
da ya daure bakinta yakunce mata ya kura mata ido,

Ita dinma kallonshi take fuskarta cikeda tsoro tana kokarin ja da baya sai dai amma takasa
saboda ya take mata kafafu wanda take ji kamar ya karya mata su, cikin rawar jiki take kallonshi
tana rufe bakinta, ba kowa bane illa shaddad, yana sanye da bakin wando da bakar riga ajiki an
rubuta Nigerian Navy,
"Kinyi min sharrin fyade ko? To yau zanyi miki na gaske in yaso sai mahaifinki yasa aharbeni,
yau zanyi miki abinda baki taba ji ba ko acikin tarihi so kishirya..."

D'aga mata kafarta yayi daga takewar da yayi take tafara jada baya tana girgiza masa kai cikin
rawar murya mai hadeda tsoro tareda firgici tafara magana,

"Dan Allah dan annabi kayi hakuri, dan Allah karka keta min alfarmata...."

"Shhhhhh...." Yadora hannunshi akan bakinsa,

"Karki kuskura ki hadani da Allah saboda yau sai na nuna miki cewar ke karamar karuwa ce,
zan nuna miki ke ba kowa bace.."

Ganin yafara kokarin kunce belt din wandonshi yasata cigaba da matsawa baya tana runtse
idonta gashi duk tabi ta kukkuje jikinta sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login