Showing 51001 words to 54000 words out of 64131 words
Chapter 18 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf
haka acikin zuciyarsa yace, "keda kika tsani tuwo yanzu kuma shi kike so?"
Tun daga ranar kullum babu abinda take son ci sai tuwo, abubuwan da ada take son ci yanzu
duk ta tsanesu musamman ma masu madara irinsu cornflakes, golden morn, viju milk, ziza, duk
yanzu bata sha saboda amai suke sata.
Tana tsaka da wannan laulayin su anty maijidda suka zo itada anty zainab saboda rabonsu da
ita tun bikinta watanni biyar da suka wuce,
Tana kwance adakinta tana faman shan farar kasa suka zo dama ranar shaddad baya nan sun
tafi Ilorin duk tanata missing dinshi kuma bazai dawo ba sai wani satin,
Tashi tayi cikeda murna taje ta rungume anty maijidda, amma cikin hanzari ta saketa saboda
kamshin humarar da tasaka ta tayar mata da zuciya, bathroom ta shiga tayi amai ta fito,
Anty zainab kallon anty maijidda tayi ta kuma kalli robar da maryama take tara yawu ga kuma
farar kasanan cikin wata farar leda,
"Anty maijidda kin kusa samun jika sai kifara tanadin kayan baby"
Dariya anty maijidda tayi, "nima ai na fahimci hakan zainabu, Allah ya rabasu lafiya"
Fitowa maryama tayi daga cikin bathroom bayan ta gama aman,
"Wai anty maijidda wannan humrar taki amma da karfi take, koda yake nima tawa haka nake
jinta yanzu shiyasa ma na daina shafawa ciwon kai take sakani da amai"
Murmushi anty maijidda tayi suka karasa bakin gadon suka zazzauna,
"Yata kenan ashe andace har an samu rabo"
Dauke kai maryama tayi cikin jin kunya, "anty ina daddy? Inasu haydar?"
Dariya anty zainab tayi "kinji yarinya taki zancen.."
Nan suka gaggaisa suka shiga hira, da Kansu su anty maijidda suka shiga kitchen suka yi girki
sannan suka tukawa maryama tuwon shinkafa miyar agushi, ba karamin dadin zuwansu tajiba
domin sun dauke mata kewar mijinta,
Kwanansu biyar saboda shaddad baya nan amma da ace yana nan da kwana biyu zasuyi, ana
igobe zai dawo su anty maijidda suka tafi bayan sun zaunar da maryama sun yimata jawabai
kala kala kan yanda ya kamata ta kula da mijinta yanzu Sannan kar ta rinka gudunshi,
Sai karfe 8 nadare su shaddad suka sauka, dayake garin garine na damina tuni har anfara
ruwan sama, dan haka ajike ya dawo gidan yasa key ya bude ya shiga, ganin maryama tayi
bacci ya kyaleta bai tasheta ba sai da asuba ya shiga dakinta, sai lokacin ma ita tasan ya dawo,
Tari tafara yi sosai saboda har ya goga mata murar da yazo da ita jiya, haka ta fito da safe
hancinta yana yoyo ga uban tari da take, shi kanshi yasan shine silar wannan murar tata,
Kullum maryama tana gida bata fita aiki saboda laulayin dake damunta ko gidan Dada bata iya
zuwa sai shine yake zuwa ya dubata duk bayan kwana biyu, sai da cikin ya danyi kwari ya shiga
wata na shida sannan tafara fita,acikin wannan lokacin su shaddad aka turasu kasar burtaniya
kuma ta ruwa zasu tafi, hankalin maryama ba karamin tashi yayiba, sallama shaddad yayi mata
ya tafi,
Aranar da ya tafi kasa bacci tayi tanata sakar zuci wani lokacin har tunani take cewar kila fa
sallamar kenan tsakaninta da shaddad ba lallai ya dawo ba, kuka tayi sosai wanda ta dade bata
yi irinshi ba,
Kullum idan ta tashi daga aiki sai taje gidan dada shine yake kwantar mata da hankali yace
karta damu ai babu wani abu shaddad zai dawo,
"Dada wata da watanni fa zasuyi acikin ruwa, tayaya zasuci abinci? Tayaya zasu sha ruwa?
Tayaya zasuyi ibada?", haka take fada kullum tana kwalla,
"Kibar damun kanki daughter, insha Allah babu komai"
Kullum haka sukeyi da dada yayita rarrashinta yana nuna mata cewar shaddad zai dawo mata
lafiya da yardar Allah.
Haka ta hakura taci gaba da gudanar da al'amuranta amma kuma duk ranar da tunanin
shaddad ya tunkudo ta to kwana take bata runtsaba gashi dama tunda ya tafi ko sau daya
basuyi waya ba saboda babu dama tunda shi yana cikin ruwa,
Ita tausayinsa ma takeyi kullum tunaninta tayaya zaici abinci,tayaya zai sha ruwa alhalin yana
cikin ruwa?.
Akwana atashi babu wuya har shaddad yayi wata biyu da tafiya kullum cikin zuba idon
dawowarshi take amma shiru, har suka kusa shiga wata na uku, nan hankalin maryama ya
tashi,
Watansu uku cif ranar talata da daddare sai gashi ya dawo, nan maryama ta shiga hidima dashi
masu karatu karfa kuga laifin maryama kun san shi so hana ganin laifine indai kana son mutum
to kullum son dadada masa kake,
Duk inda ta wulga binta da kallo shaddad yake saboda cikinta ya tsufa saura yan kwanaki ya
rage ya shiga wata na tara,
Duk da yaga yanda take takawa dakyar amma sai yakasa hakuri saboda sun jima basa tare,
maryama baiwar Allah haka da tsohon cikin da komai tabashi hadin kai bata k'i ba domin ita
aduniya duk abinda shaddad yake so zata iya bashi mutukar baifi karfinta ba,kwana biyu ya
dauka kullum yana gida yana yimata naci baya fita ko ina,masu karatu duk fa wannan abun da
yake faruwa har yau shaddad bai taba nunawa maryama cewar ya kamu da sonta ba bare ya
furta mata,kwanansa biyar da dawowa ya shirya ya tafi Kaduna amma aranar ya dawo.
Sati biyu da dawowar shaddad maryama tafara nakuda, karama clinic suka tafi nan dr muneerat
tace operation za ayi mata saboda kamar haihuwar zata yimata wahala sosai, babu bata lokaci
aka shiga da ita aka yi mata aiki aka ciro baby girl katuwa mai kamar maryama sak,
Sai da maryama ta farfado sannan aka gyara babyn wata nurse taje ta Kira shaddad da Dada
wadanda ke waje suna jira.....
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_*45*_
~~~Zubawa shaddad ido maryama tayi tana son taga da wanne irin yanayi zai karbi babyn
lokacin da suka shiga cikin dakin, fuskarshi da fara'a taga ya karasa gadon da babyn take ya
dauketa yana ta kallonta, ita kuwa ko wurinda take bai kalla ba balle ta saka ran zaiyi mata
sannu,
Wannan abu yayi mutukar bawa maryama haushi ganin ya nuna halin ko in kula akanta sai ta
babyn sa yake,
"A tsaga jikin nawa afito maka da yar amma banida darajar da zaka cemin koda sannu?" Tafada
acikin zuciyarta,
Ta wuri daya taji dadi taji bacin ranta ya tafi shine lokacin da Dada ya shigo shima bai nufi wurin
kowa ba sai wurinta yaje yana ta yimata sannu yana tambayar ko da akwai wurinda yake yi
mata ciwo?
Dadi taji azuciyarta tace "dadinta dai nima nawa uban yadamu dani.." Tafadi acikin zuciyarta,
Sai da Dada yaji cewar lafiya lau take sannan ya matsa wurin shaddad ya karbi babyn ya sanya
mata albarka ya fita, zuba ido maryama tayi tana ta kallon shaddad yana kai kawo da yarshi
akan kafadarshi,
Waya yayi kaduna ya sanarwa da hajiya haihuwar sannan ya kikkira yan uwa ya fada musu,
murna hajiya ta shiga yi sosai kamar wannan ne karo na farko data fara samun jika nan tace
khairat ta shirya ta tafi tunda dama acikin hutun semester take,
Ita kuwa maryama wayarta tasa blessing ta dauko mata ta kira anty maijidda ta fada mata ajiyar
zuciya anty maijidda tayi ta shiga hamdala domin tunda cikin maryama ya shiga watan haihuwa
bata iya bacci saboda fargaba,
Kashe wayar tayi ta kira anty zainab itama ta fada mata,
Har bacci ya kwasheta bata san lokacin da shaddad ya ajiye babyn daga hannunshi ba,
Sai yamma lis ta farka lokacin har khairat tazo daga kaduna sunje gida itada blessing sun hado
mata kayan tea sun dawo,
Tashi tayi ta zauna aka miko mata babyn ta karbeta zata shayar da ita, kurawa kirjinta ido
shaddad yayi yana kallonta har lokacin kamar bata haihuba kirjinta yake sai dai cika da ya kara
amma babu alamun zubewa atare dasu,
Haka aka yita faman kaiwa da komowa a asibitin har aka sallamesu suka koma gida, aranar su
anty maijidda suka zo lokacin kwanan maryama uku da haihuwa, tunda suka koma gida kuma
dangi da yan uwa suke ta zuwa ganin jaririya, kwanansu hudu su hajiya suka zo ita da anty
karama da matar yaya Yusuf hadiza,
Dan murna hajiya ji take kamar zata hadiye jaririyar, kiran shaddad tayi tace wanne suna za
asawa jaririyar? Nan yace sunanta zai saka,
"Ita kuma maryaman fa? Kamata yayi asa sunan mahaifiyarta tunda ni ai kaga yan uwanka sun
sassaka sunana dayawa"
"Hajiya ai sunanku daya da babartata itama.."
Fara'a hajiya tayi ta gutsiri goro,
"Ashe kai maryaman naka suna da yawa, to Allah ya rayata"
Tashi yayi ya fita a kitchen ya hango su khairat suna aiki ita ya kira yace taje ta turo masa
maryama saboda yaga dakin acike yake, dakinsa ya wuce ya tsaya yana jiranta,
Tana sanye cikin doguwar riga na atamfa ta shigo dakin, sai da yaji wani kamshi ya gauraye
dakin lokacin data shigo kamar ba maijego ba,
"Gani.." Tafada saboda dama har lokacin a kule take dashi na rashin sannun da baiyi mata ba
lokacin data haihu,
Zama tayi agefen gadonshi bata ko kalleshi ba, tunda yaga haka yasan fushi take dashi,
"Munyi magana da hajiyane akan sunan da za asawa jaririyar, sunanta maryama"
"Allah ya rayata.." Shine kawai abinda tace ta tashi zata tafi,
"To babu wani abu da kuke bukata?"
"Babu" tafada tareda karasa ficewa, tun daga nan take shareshi taci gaba da hidimarta, har gida
mai saloon tazo tayi mata ta gyara mata yalo yalon gashinta sannan aka yi mata jan lalle
wannan kam khairat ce tayi mata saboda dama ta iya sosai,
Kyawun da maryama tayi kai idan ka ganta ba zakace itace ta haihu ba shiyasa duk inda tayi
idon shaddad akanta yana lasar lebe, shaddad yayi kokari sosai wurin yi mata kayan kece raini
ita da jaririyar,
Manyan raguna guda biyu ya siyo ma jaririyar, ranar suna aka yankasu aka radawa jaririya suna
MARYAMA zasu rinka kiranta da Nu'aima,
Anyi hidima iya hidima awannan sunan, Dada mahaifin maryama gida guda ya mallakawa
jaririyar, su hajiya da sauran dangi duk basu tafiba sai bayan suna da kwana biyu,
Yanzu gidan daga anty maijidda sai khairat ne kadai sai ko blessing da take zaune agidan tana
tayasu ayyuka,
Tun maryama na share shaddad har ta dawo ta hakura ta rabu dashi amma bawai dan ta manta
abinda yayi mata ba, ita kuwa anty maijidda maida hankali tayi wurin gyara maryama
sosai,daga maryaman har nu'aima sunyi bulbul sunyi kiba sunyi kyau abinsu, ana igobe zasu
cika kwana arba'in anty maijidda ta tattara ta tafi abuja gidanta tabar khairat awurin maryama
saboda ta rinka tayata rainon nu'aima, ranar da suka cika 40 shaddad bai daga kafa ba dama
tunda ya kyalla ido yaga khairat adakin maryama take kwana ya kira maryaman yace khairat ta
koma daya dakin da kwana,
Yar gidan jiya suka koma koda yaushe baya barinta ta huta daga dare har asuba samun hutunta
da ranane kadai, yanzun ma kuma sai da ya sake maimaita mata cewar indai tayi planing a
boye Allah ya isanshi bai yafeba,
Haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu har sukayi wata biyu lokacin khairat ta koma
Kaduna saboda school, sha tara ta arziki maryama ta hada mata sannan tabada sako mai
girma tace akaiwa hajiya,
Khairat bata jima da tafiya ba shaddad ya shirya ya tafi Kaduna ashe zance yatafi wurin
budurwarshi Amira saboda yanzu tayi candy, sai da yagama zancenshi sannan ya tafi gidan
hajiya, tsabar zance yayi dadi wai har number din maryama ya bawa yarinya akan zata kirata su
gaisa,
Duk lokaci zuwa lokaci yake zuwa Kaduna yanzu saboda Amira, ita maryama bata saniba, idan
yana gida kullum yana makale da yarshi nu'aima hatta bacci tare suke yi, bikin blessing ne ya
taso nan maryama ta hada mata sha tara ta arziki ta sallameta ta tafi garinsu, yanzu gidan
yadawo sai su uku kacal, kullum da nu'aima maryama take zuwa aiki idan taje da ita kuwa bata
sake ganinta sai idan tatashi zata dawo gida sannan ne zataje ta nemota su koma gida,
Tana tsaka da aiki acikin kitchen taji an kirata awaya, bakuwar number tagani ana kiranta
awaya,
Dagawa tayi tun kafin tayi magana taji ance,
"Sannu amarya yar shekara 30 yanzu ke ko kunya bakiji ba kika dage kika auri yaro sa'anki,
bayan kin san yadade yana sona tun ina jss 3 yake sona kuma har yanzu bai daina sona ba..."
Kashe wayar maryama tayi saboda ita bata iya fada ba, duk da ta kashe wayar Amira bata
hakura ba sai da ta sake turo mata da text massage,
Haushi iya haushi maryama tajishi amma bata ko nunawa shaddad ba duk da tasan shine zai
fadawa budurwar tasa cewar shekarunta 30 lokacin da ya aureta,
Cikin satin suka shirya suka tafi Kaduna gaida hajiya, ina ka saka ina ka ajiye haka hajiya
tayiwa su maryama, shi kuma shaddad ya tafi wurin Amira saboda yana son ya turo ayi
maganar aurensu da ita....
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
*_46_*
~~~Amma koda yaje yayiwa Amira maganar sai tace masa ita makaranta zatayi ba yanzu zata
yi aure ba,
"Amira kin san dai na dade ina sonki kuma hajiya ta matsa akan ayi ayi maza ai auren nan.."
Budar bakin Amira sai cewa tayi, "kuma ni ina ruwana da wata hajiya, ai ba itace zata yimaka
auren ba da zata bi ta uzzura maka.."
Tunda tafadi haka yaji ransa yabaci sannan yaji yarinyar tafara fice masa arai saboda sam bata
da kunya gata dai yarinya karama dan ko khairat da take kanwarsa ta biyu ta girme mata nesa
ba kusa ba amma sai ta rinka fada masa bakar magana, duk da yasan harda yarinta acikin
tsarin nata amma harda rashin kunya da rashin ganin girman nagaba, ta inda yake sarawa
maryama kenan sam bata son bacin ranshi gashi tana mutukar kaunar mahaifiyarshi da yan
uwanshi sannan duk abinda ya fada mata bata iya yimasa musu kuma duk tsanani baya
magana ta mayar masa ko lokacin da yake yimata wulakancin nan farkon aurensu shiru take yi
bata ramawa gashi dai ahaife ba girmanta yayiba amma tana bashi girma da daraja a
matsayinshi na mijinta,
Cikeda bacin rai yabar wurin Amira ya koma gidan hajiya, kwanansu biyu suka koma Lagos
bayan hajiya ta samowa maryama wata yar dattijuwa mai suna baba lami wacce zata zauna da
maryama ta rinka tayata yan aikace aikacen gida saboda yanzu bata da mai aiki ita kuma hajiya
ko kadan bata son taga maryama na shan wahala,
Komawa Kaduna suka yi suka cigaba da gudanar da rayuwarsu, nu'aima babu laifi ta girma tayi
wayo sosai, shi kuwa shaddad dole yanzu ya hakura da maganar Amira musamman ma da
yaga text massage din data turowa maryama awayar maryaman nan yasake jinjinawa maryama
wurin hakuri da dauriya domin ba duk macece zata iya wannan ba da wata matarce Allah ne
kadai yasan tashin hankalin da zasuyi da ita amma ita maryama ko nuna masa bata yiba,
sannan baya ga haka ma tunda tafara jami'a ta hadu da wani guy ya ke hure mata kunne,
yanzu kwata kwata ta juyawa shaddad baya, ganin haka yasa shaddad hakura ya kyaleta
saboda dama hajiyarsu da sauran yan uwanshi ba son aurensa da Amira suke ba.
Watan nu'aima tara maryama ta fara laulayin wani cikin danma nu'aiman mai saurin girma ce
sannan tunda maryama likitan yarace tana taimaka mata da wasu sinadirai masu gina jikin yara
shiyasa ta taso cikin koshin lafiya dama kuma ba damuwa tayi da shan mama ba shiyasa
maryama ta yayeta,
"Zo Mamana, ummice ta yaye ki ko ta hanaki shan abincinki, yi hakuri zamuje in siyo miki
bobo.."
Tana ganin shaddad ya dauketa suka fita yawo, haka tayita laulayinta wannan karonma kamar
lokacin da tayi na nu'aima, amma yanzu tunda bana farko bane ta ji dan dama dama, shiyasa
ma ko hutu bata dauka ba a office har saida azumi yazo lokacin cikinta yana wata bakwai shine
ta dauki hutu saboda tana son su tafi umarah itada nu'aima,
Shaddad bai hanata ba tunda da kudinta ta biya, nan aka gama musu dukkan shirye shiryen da
ya kamata suka tafi,
Kullum suna waya da shaddad, satinsu uku acan suka dawo, nan shaddad ya karbesu da farin
ciki domin yayi missing din matarshi sosai,
Gidan Dada maryama takai nu'aima saboda kullum sai ta rinka cemata zataje wurin dada tunda
ta kaita bata daukota ba sai da zasu tafi Kaduna salla,
Kamar koda yaushe wannan zuwanma taji dadin yanda su hajiya suka karbeta kowa kamar zai
hadiyeta dan so, sai da akayi salla da sati daya sannan suka koma Lagos,
Kwanci tashi da haka har watan haihuwar maryama ya cika, ranar da edd dinta ya cika aranar
ta tashi da nakuda,shaddad ne ya dawo daga office ya kaita asibitin, wannan karon ma cs din
za ayi mata, yana ganin lokacin da aka zo za awuce da ita nu'aima taje gaban gadon tana kuka,
"Ummi zaki dawo ko? Dan Allah Ummi karki tafi"
Jin abinda nu'aima take fada ne ya karyarwa da maryama zuciya har taji kwalla tana kokarin
sauko mata batare da ta shirya ba,
Shi kansa shaddad sai yaji jikinsa yayi sanyi sosai, zuwa yayi ya kamo hannun nu'aima batare
da ya iya kallon wurinda maryama take