Showing 33001 words to 36000 words out of 64131 words

Chapter 12 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5652

PM] Ummi Shatu👌🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*




*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to Maryam Qaumi_💕



_Ina jida ku Nana Hafsat (miss Xoxo),Zainab Y Hussain (autar hajiya), Allah ya k'ara raya
minku yan matan kirki.._




_*29*_



~~~Rawa jikin anty maijidda yafara take ta saki kara ta tashi aguje tafita,

Mintuna kadan sai gata da wani saurayi dan makotansu, kinkimar maryama akayi aka sa a
mota suka nufi daula clinic, suna zuwa aka bata gado,

Tsabar tausayi anty maijidda harda kwallarta,

"Dan Allah maryama kar kema ki tafi kibarmu kamar yadda mahaifiyarki ta tafi tabarmu domin
ke kadai muke gani a madadinta muji dadi.."

Haka anty maijidda taketa furtawa tana kuka,

Kanwarta zainab ta kira dama su ukune daga marigayiya mahaifiyar maryama sai ita sai mai
binta zainab wacce take aure a Kaduna,

Tana dauka ta fada mata rashin lafiyar maryama, nan zainab din tace tana nan zuwa,

Maryama kuwa tunda tayi wannan dogon suman bata farfadoba sai da yamma tayi,

Bude idonta tayi taf da hawaye ta rike hannun anty maijidda,

"Anty mutuwa zanyi, wallahi ina son shaddad shikuma baya sona, ya tsaneni anty"

Rufe mata baki anty maijidda tayi itama idonta dauke da k'wallar,

"Ya isa kiyi shiru maryama insha Allah bakida miji sai shaddad.."

Haka anty maijidda tayita fada mata kalamai masu dadi dan kwantar mata da hankali,

Ba asallamesu ba sai bayan sallar isha kasancewar clinic din basa barin patients su kwana,

Suna isa gida anty zainab na isowa, kamar dama tare suke,

Murmushin yake kawai maryama keyi saboda ita kadai tasan irin radadin da zuciyarta keyi,

Ciki suka shiga ta kwanta akan doguwar kujera tana sauraren zancen dasu anty maijidda sukeyi
itada anty zainab sunata jajanta abin,

Tashi tayi dakyar ta nufi cikin dakinta, wayarta ta dauka ta fara kiran khairat kanwar shaddad,
cikin yanayin bacci ta dauka,

"Adda Maryam"

"Khairat ki taimakeni dan Allah, ina daf da rasa yayanki kuma wallahi idan har ban sameshi ba
mutuwa zanyi.."

Zunbur khairat tayi ta tashi daga kwanciyar da take babu shiri taji baccin idonta ya wartsake,

"Adda Maryam kin sani aduhu meke faruwa?"

"Khairat son shaddad nake tun ba yauba, na dauki tsawon shekara biyu ina fama da ciwon
sonshi, amma shi ya tsaneni"

"Kiyi hakuri adda Maryam gobe zanzo yanzun ma saboda dare yayine da sai nazo amma gobe
zaki ganni"

Kashe wayar maryama tayi tasake fashewa da kuka, tana cikin yin kukan ne su anty maijidda
suka shigo nan suka shiga rarrashinta har tasamu ta yi shiru, wanka ta shiga tayi da ruwa mai

dumi ta fito, dakyar anty maijidda tasamu ta bata abinci ta dan ci ta kwanta.


Washe gari kamar yadda khairat ta alkawarta sai gata da misalin karfe tara nasafe, adaki ta
samu maryama tana kwance ana yi mata karin ruwa,

"Sannu adda Maryam..."


"Yawwa khairat sannu"

"Adda Maryam wai meya farune haka...?"

Labarin abinda yafaru maryama tabata tun daga kan farkon haduwarta da shaddad har kawo
yanzu babu abinda ta rufe mata komai saida ta fayyace mata,

Kama hannunta khairat tayi tana zubar da hawayen tausayinta,

"Yanzu adda Maryam akan son yaya shaddad kike kwance bakida lafiya? To ki kwantar da
hankalinki nayi miki alkawari zanyi iya kokarina naganin kin mallaki Yaya shaddad, insha Allah
sai kin aureshi, nidama tun farkon ganina dake naji kin shiga raina, yanzu gida zanje in fadawa
anty dama gobe zamu tafi kaduna saboda yayarmu ta haihu jiya da daddare"
"Nagode khairat, nagode.."

"Kibar godiya anty dama yarinyar da yake son ya aura ma hajiya ba son auren takeba shine
yake so, duk yanda ake ciki dai zakiji daga gareni"

Sallama khairat tayi mata tatafi, tana zuwa gida ta kwashe zance tas ta fadawa antyn ta, nan
itama antyn ta hau fadin,

"Ai kuwa wallahi wannan yarinyar ni banga laifinta ba da zai wulakantata,yarinya kyakkyawa da
ita, dama wannan yarinyar da yake jiran tagama makaranta ya aureta ma ba lallai ne abashi ba,
Allah yakaimu gobe muje gida wallahi hajiya zataji komai, kuma muddin hajiya taji to dolensa
sai ya aureta, haba zamanshi haka babu aure ai ya isa kidubi sulaiman fa har yayi yara biyu shi
yana nan yanata jiran gawon shanu..."

Haka antyn khairat wacce ake kira da anty babba tayita bambami tana fad'a da alama itama ta
goyi bayan sai shaddad ya auri maryaman, dan haka washe gari da sassafe suka dauki hanyar
Kaduna garin governor.....

*_Ummi A'isha_*👌🏻
[5/17, 4:31 PM] Ummi Shatu👌🏻: _®HWA_




_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*




_Dedicated to Maryam Qaumi_💕



_Gaisuwa ta musamman ga masoyan maryama sarauniya musamman ma ke k'awata
Halima Lawan Bala, and babbar Yaya Anty Sis (Maman sultan)_




_*30*_



~~~Koda su khairat suka je gida samun hajiya mahaifiyarsu suka yi suka kora mata jawabin
abinda ya faru tsakanin maryama da shaddad nan anty babba takara da cewa,

"Ni hajiya abinda nake gujewa wannan yaronma shine wallahi indai bai auri yarinyar nan ba to
ya tafka babbar asara saboda baki ganta ba, yarinya yar mutunci mai nutsuwa,mace iya mace.."

"Wallahi anty gata da hakuri babu ruwanta da hayaniya" Khairat tafada cikin zuga,

"To ai ko baku fadi haka bama anty yazama dole ya aureta tunda tana sonsa, kinga sansdiyyar
son da take yimasa bazata saba masa ba kullum cikin faranta masa zata kasance"

"Ku kyaleni dashi zai zo ya sameni ai yazo tun jiya yana nan agari..."

Hajiya tafada tana gyara zamanta daga zaune zuwa kishingide, cikeda murna khairat tace,

"Yawwa hajiya wallahi har rashin lafiya takeyi akanshi".


Abangaren maryama kuwa yanzu ta dan fara warwarewa saboda nasihar da anty maijidda da
anty zainab keyi mata, babu laifi yanzu ta danji sauki sai uwar ramar da tayi.

A Kaduna kuwa shaddad hankalinsa kwance ya shiga falon mahaifiyar tashi bai san akwai
wata a kasa ba saboda tun ranar da yabar abuja ya rufe shafin maryama rufewa ta har abada,

"Kai shaddad wai yaushe zakayi hankali ne? Saboda kaga yarinya na sonka shine zaka rinka
wulakantata? To bari kaji kar kaji da wai wallahi sai ka auri wannan yarinyar saboda nagaji da
zamanka ahaka kanata sauraren wata yarinya wacce ba asan ranar aurenku ba.."

Ido ya kwalalo jin abinda hajiya tace,

"Hajiya wai akanwa kike magana ne?"

"Akan wannan yarinyar maryama ta abuja"


Gabansa ne ya fadi to taya akayi hajiya tasan maganar,

"Hajiya wa zan aura? Wannan yarinyar yar shekara 30? Sa'ata cefa, bayan haka kuma ni
wallahi bata yimin ba saboda batada tarbiyya gata marar kamun kai kullum cikin zuwa wurin
maza take ga shaye shaye.."

"Kai ka rufe min baki, wannan sharrin da kake kagowa kana fada bashi zai hana auren nan ba
wallahi, aure sai anyishi ko baka so, tashi kabani wuri"

Tashi yayi fuskarsa a hade ransa abace saboda shi aganinsa yanzu ai andaina auren dole, ko
mata andaina yimusu auren dole balle shi namiji,yana fita ya iske Suleiman abokinsa a kofar
gida yana jiransa,.


"Sulaiman kaji abinda hajiya ta tsiro dashi kuma yanzu? Wai sai na auri wata yarinya sa'ata"

"Ah to meye aciki? Nifa age mate dinama naso aura Allah ne baiyi ba"

"Kajika da wani zance kuma, ana ga gabas kana ga yamma mtswww"

Shaddad yafada cikeda jin haushi yatafi yabar sulaiman awurin bai ko kara bi ta kansa ba,

Ran shaddad idan yayi dubu to yagama baci aranar musamman ma da ya sake shiga wurin
hajiya yaji tana waya da baba Ahmadu kanin mahaifinsu kan cewa suzo ranar asabar shida
kawu auwalu zasuje nemarwa shaddad auren maryama,kasancewar mahaifin su shaddad din
yajima da rasuwa,
Zama yayi yana jiran tagama wayar idonshi jajur,

"Yanzu hajiya idan aka yimin haka anyi min adalci kenan, taya za adage kan lallai sai na auri
matar da bana so, yarinyar nan wallahi hajiya bata da tarbiyya ko kadan gata da bin maz.."

Dakatar dashi hajiya tayi, "wai kai ban hanaka wadannan maganganun bane? Kar nakara jin
wannan maganar a bakinka koma yaya take to itace matar aurenka.."

Shiru yayi bai sake magana ba har babban yayansu ya shigo wato yaya Yusuf, yana jinsu shida
hajiya suka fara maganar yanda za aje neman auren,

"Ai ni hajiya ina ganin ma kawai da munje to agama magana har rana asaka mutaho da
ranarmu.."

Yajiyo yaya Yusuf yana fada,


"Ehh nima dama nayi wannan tunanin Yusuf, kamar ka shiga zuciyata wallahi, ni amma bana
son asa doguwar rana idan har son samu ne karshen wata mai zuwa ayi bikin nan kowa ya
huta, kaga yau 20 ga wata amma ya kagani?"

"Hajiya hakanma yayi daidai tunda kinga ai dama nan din muma ashirye muke kuma insha Allah
suma gidansu yarinyar nasan ashirye suke.."

"Yawwa Yusuf Allah yayi maka albarka zan fadawa baffan nakuma dan Allah duk yadda zakuyi
to kuyi abar ranar auren nan akarshen wata mai zuwa.."

"To hajiya insha Allah za ayi yanda kikace"

"Yawwa nima yanzu kiran yaran nan zanyi ana gama hidimar sunan nan su shiga kasuwa su
fara hado kayan lefe muyi muyi mu kai musu can mu huta inyaso sai mu jira ranar biki"

"To Allah ya sanya alkairi hajiya" Yaya Yusuf yafada yana kokarin mikewa, Yaya Yusuf shine
babba agidan shima soja ne sai dai shi ba Navy bane army ne dagashi sai anty babba wacce

ke aure a abuja sannan sai shaddad sai anty karama wacce ta haihu yanzu sai yar autarsu
khairat,

Da harara shaddad ya raka yaya Yusuf sannan shima ya mike zai fita,

"Zo nan mazaje" wannan shine sunan da hajiya take kiransa dashi tun lokacin da yana karami
yana burin zama soja,

"Ai ba tafiya zakayi ba ban gama dakai ba"

Komawa yayi ya zauna yana kallonta, shi bakin cikinsa ma tayanda akayi wannan maganar har
tazo kunnen hajiya,

"Kaima idan Allah ya kaimu wani satin bayan anje an tambayo maka auren zaka shirya kaida
sulaiman kuje ya rakaka ku gaishe da mahaifin yarinyar sannan ku tattauna da ita kana ji?"

"Naji hajiya"

"To tashi kaje Allah yabada sa'a"


Mikewa yayi ya fita fuskarsa adaure, ko su khairat bai kulaba wadanda ke zaune atsakar gida
suna gyaran kayan miya wasu kuma na yin wanke wanke, kamar zai fashe da kuka haka yasa
kai yafice daga gidan....




*_Ummi A'isha_*👌🏻
[5/17, 4:31 PM] Ummi Shatu👌🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*




_Dedicated to Maryam Qaumi_💕

_*31*_

aishaummi.blogspot.com



~~~Ita maryama tana can abuja bata san abinda ake ciki ba, duk tabi ta rame ta kanjale tayi
kashin wuya,

Dakyar anty maijidda da anty zainab suka samu suka rabata da damuwar datake addabarta,
anty zainab bata bar gidan ba saida taga maryama ta dan murmure,

Nasihar da anty maijidda keyi mata yasata ta dangana ta cire damuwa daga cikin ranta domin
kullum anty maijidda cemata take,

"Maryama idan har shaddad mijinki ne to zaki sameshi ta inda baki zataba idan kuma ba shine
mijinki ba to da yardar Allah wanda yafishi zaki aura"

Wannan maganganun na anty maijidda suke sa zuciyarta ta yi sanyi dan haka yanzu ta cirewa
ranta damuwa har tafara maida jikinta sabanin da datayi rama,

Komawa tayi taci gaba da al'amuranta tacigaba da zuwa makarantar islamiyyarta, kusan kullum
sai sunyi waya da khairat amma bata taba fadawa maryama abinda ke faruwa ba,

Ranar asabar da yamma Dada yakirata awaya yace mata bakinta sun zo kuma ya yaba dasu
harma an tsayar da ranar aure karshen wata mai kamawa dan haka tayi kokari ta dawo gida,

Mamakine ya kamata nan tafara tunanin to ko fahad ne ya tura iyayensa ko kuma dr naz?
Amma tafi zaton fahad ne saboda kwana biyu ya matsa da kiranta awaya,

Tabe baki tayi "koma waye damuwarsa ce, naji zan aureshi ahaka" tafada acikin zuciyarta,

"Shiyasa maryama nadade ina yimiki nasiha akan karki damu kanki akan maganar aure domin
komai da kika gani na rayuwa to da lokacin sa yanzu gashi kina zaune Allah ya kawo miki
lokacin, nasan babu surutun da bamu sha ba nidake akan naki aurar dake to yau gashi Allah zai
nuna min wannan lokacin, Allah yasa ayi a sa'a mai sunan mama.."
"Amin Dada, insha Allah zan sa rana nadawo gida"

"Yawwa mai sunan mama Allah yadawo dake lafiya, kigaida antyn naki"

Katse wayar tayi bata sake bi takan zancen ba har saida tayi baccinta ta gama sannan ta tashi
taje tana fadawa anty maijidda abinda Dada ya fada,

"Koma waye maryama kiyi hakuri ki aureshi kinji tunda har ya aika gidanku to yana sonki da
gaske, ki cire batun shaddad dinnan aranki"

"Dama haka zanyi anty, insha Allah zan manta dashi har abada"

Tun daga wannan lokacin ta cire batun shaddad acikin rayuwarta bawai ta daina sonshi bane
a'a har lokacin tana kaunarsa kawai karfin halin rabuwa dashi tayi bata san shi dinne yake shirin
zama mijinta ba.

A can Kaduna kuwa ana can ana shirye shiryen hada lefen shaddad wanda za akaiwa
maryama, ranar lahadi hajiya tasa ya shirya shida sulaiman suka nufi lagos kai gaisuwar
surukai,

Lokacin da Dada yaga shaddad ba karamin mamaki abin yabashi ba amma sai bai nuna komai
ba haka ya karbesu hannu bibbiyu saboda duk atunaninsa maryaman ce tabashi damayazo
neman aurenta dan haka cikin sakin fuska ya gaisa dash, kuku ya shirya musu table,

Karfe biyar na yamma suka jiyo kasancewar ajirgi sukaje kuma ajirgin zasu dawo, duk wannan
aikin hajiya ne kasancewar mai kudin gaske ce dama can ita mai tarin dukiyace saboda tana yin
kasuwanci sosai, plaza plaza da take da ita acikin central market na Kaduna sunfi talatin,

"Shaddad ka kwantar da hankalinka zakaji dadin zama da wannan yarinyar"

"Ba wani dadin zama da zanji da ita, bafa yarinya bace, shekararta 30 me zan samu awurinta?"

"Duk wani abu da zaka samu awurin wata mace itama zaka samu awurinta wallahi domin duk
mace macece"

"Banda wannan saboda sam bata da tarbiya ga bin maz.."

Shiru yayi saboda sai yaji kunyar fadawa sulaiman munanan halayenta tunda ko babu komai
dai yanzu tana shirin zama matarsa,

Haka sulaiman yayita bashi baki daga karshe ya b'ige da tsokanarsa,

"Yo kai in ba yar shekara talatin din ba wacece zata iya daukar dawainiyarka, ai kafi karfin yar
sha takwas"

"Kuma sai na auri yar sha takwas dinba, me zanyi da tsohuwa yar shekara 30,ni wallahi yarinya
nake so karama"

Shi dai sulaiman cigaba da tsokanarshi yayi har suka sauka.

Sati biyu da saka ranar auren maryama ta shirya ta koma Lagos, kukan da tayi lokacin da zata
tafi ba kadan bane, ita tana kuka anty maijidda na kuka har suka rabu,

Karfe shida na yamma ta sauka Dada sukaje suka dauko ta, daren ranar kusan kwana suka yi
suna hira da Dada,wani ikon Allah kuma har suka kammala hirar bata iya tambayar Dada waye
yake shirin zama mijinta ba.

Kwana biyu da dawowarta takoma office taci gaba da zuwa aikinta sai dai yanzu sam bata
sakarwa su dr sameer fuska kamar da saboda tace musu aure zatayi nanda karshen wata,

"Wannan sojan ne ya kadamu ko?"

Dr sameer yafada yana dariya,

"Ehh shine" tafada cikin gatse,

"Yawwa nidama nasan sai dai shi"

Shiru tayi taki zancen taci gaba da aikin da takeyi saboda bata son afama mata ciwon son
shaddad dake cikin zuciyarta.


Gidansu shaddad sun gama hada lefe, akwatina goma sha biyar hajiya ta hada da
kudinta,blue and pink shine colour din akwatinan, komai naciki mai tsadane domin khairat
tacewa hajiya itama maryaman Yar gayuce bata saka kaya sai masu tsada saboda kwararriyar
likitace duk wata albashi take dauka,
Anty babba da kanta tasaka khairat agaba sukaje gidan anty maijidda sanar mata zasu kawo
lefe gidanta jibi, tsabar murna anty maijidda dai gud'a ta shiga yi saboda tsabar murnar jin
shaddad ne zai auri maryama, saida ta gama gud'a sannan tafara yiwa annabi salati,

Ki'n fadawa maryama tayi amma ta kikkira danginsu da kanwarta anty zainab ta fada mata, nan
tazo suka hau shirin tarbar bakinsu, sai da suka soya kaji cikin katuwar bakar roba ta zuba
ruwa, banda cake da meat fie wanda suka yi order dasu donotes,spring rolls da sauran kayan
makulashe,
Ranar juma'a kamar yadda sukace aranar suka kawo lefen maryama murnar da anty maijidda
da anty zainab sukayi ko ranar aurensu basuyi haka ba,

Jan anty maijidda anty zainab tayi zuwa cikin daki, suna shiga ta rike haba tace,

"Anty Maijidda nawa zamu bawa mutanen nan kudin tukwici kiduba kiga uban kayan da suka
kawo mana fa"

"Dubu dari cif zamu basu zainab, dama dadyn su Faruk yabayar yace gashi nan abasu, ai
batayi kadan ba ko?"

"A,a baiyi kadan ba hakanma yayi"

Komawa falo sukayi suka bada tukwici da sauran kayan dadin da suka tanadar musu, yan kawo
kayan basu wani jimaba suka tafi saboda kaduna zasu juya a lokacin,

"Har yaufa yar taki bata san waye mijin nataba, bata san wanda takeso zata auraba, amma
karki fada mata fa"

Anty Maijidda tace da anty zainab

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login