Showing 57001 words to 60000 words out of 64131 words
Chapter 20 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf
yimin koda na bacin raine
to ki dauka raina bai baciba domin ina maraba da duk wani abu da zai zo gareni mutukar daga
gareki yake"
Bude idanuwanta tayi akan kyakkyawar fuskarshi tana jin wani irin farin ciki yana ziyartar
zuciyarta...
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/25, 9:20 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_*49*_
~~~Hannunta tasa ta shafi gefen fuskarshi tana murmushi,
"Nagode navy, Allah ya barni dakai har ranar da zan daina numfash..."
Rufe mata baki yayi da hannunsa guda daya,
"Ki daina ambatar wannan kalmar saboda bana son jinta, tana hanani sukuni sannan tana
rabani da nutsuwata, bana fatan mu rabu har abada.."
Murmushi tayi idonta cikeda kwalla duk kalaman da yake fada mata ji take kamar a mafarki ne
ba agaske ba,
Girgiza mata kai yayi yafara goge mata kwallar da ke kokarin sauka daga idonta,
"To kuma menene zakiyi kuka..?"
Murmushi tayi ta lumshe masa idonta, nan shaddad yaci gaba da zama atare da ita har dare
yayi, koda daddaren ma da anty maijidda tazo tace zata kwana awurin su maryaman shaddad
cewa yayi a,a shine zai kwana awurinta, sai dakyar anty maijidda ta samu ta shawo kansa ya
hakura,
Mannawa maryama kiss a kan goshinta yayi sannan yafita ita dai anty maijidda binsu da ido
kawai take yi,
Washe gari kuwa da sassafe sai gashi dauke da kayan breakfast shi ko karyawar ma bai yiba
haka ya taho, azaune ya samu maryama kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta,
"Baby sannu ya jikin naki?"
Kallonshi tayi tai murmushi, "Navy kenan, ina kwana?"
Kashe mata ido guda daya yayi, "kema dai daga ganina kin san ba lafiya na kwana ba saboda
rashinki.."
"Bani tea din.."
Sauka yayi daga kan gadon ya hada mata tea ya fara bata da haka har anty maijidda tazo ta
iskesu ta dawo daga karbowa maryama magani,
Gaisheta shaddad yayi nan tafice ta basu wuri saboda yanzu taga tashen rashin kunya suke,
sai da yagama bawa maryama tea din sannan yatafi gida domin yin wanka,
Haka shaddad yayita zirga zirga har aka sallami su maryama daga asibitin lokacin kwanansu
hudu saura kwana uku suna,
Suna zuwa Gida suka tarar su hajiya dasu anty zainab da sauran dangi, an gyarewa maryama
dakinta tsaf komai fes sai kamshin turaren wutar da aka kunna ne yake ta faman tashi agidan,
Dan zama maryama tayi ta shayar da jaririn sannan ta barwa su anty maijidda shi ta shiga daki
saboda wanka take son tayi,
Tana shiga wankan shaddad ya shigo cikin bedroom din, motsinta da yaji acikin toilet ne ya
fahimtar dashi cewar wanka take yi,
Kofar dakin ya sawa key yabita cikin toilet din, maryama sai ganinshi kawai tayi ya shigo yana
balle botir din gaban rigarshi,
"Shaddad ya haka? Wanka fa nake yi"
"Nima wankan zanyi shine nazo muyi tare"
"Kai shaddad ka fiya rigima, nifa jego nake"
"Nasani ai, wankan kawai nake so muyi tare.."
"To idan su anty maijidda suka shigo fa"
"Babu mai shigowa ai na rufe kofar"
Tare suka yi wankan anty maijidda sai bugun kofar dakin takeyi saboda jaririn maryama yanata
kuka, maryama ce taje ta bude kofar shikuma shaddad yana tsaye yana saka rigarshi, batare
da anty maijidda ta shiga dakin ba tabawa maryama jaririn ta fita, wurin anty babba ta koma a
inda suke zaune suna hirarsu,
"Nifa ana yin suna nima washe gari zan bar gidan nan.."
Anty maijidda tafada, "au wannan karon ba zaki taya yar taki zama ba?"
Inji anty babba,
"A'a wannan yaran ai yanzu sunfi karfina, tare suka yi wanka fa yanzu, ina zuwa suna fitowa
shikuma gogan ko kunya ina ganinshi yana saka riga shiyasa ma ko dakin ban shiga ba"
Dariya anty babba tayi, "ashe baya yin surukar dake"
"Ai shiyasa zan tafi tun kafin yafito kiri kiri yace in tattara kayana in tafi"
Sai da shaddad ya rikewa maryama jaririn ta shirya sannan ya bata shi ya fita, yana fita
nu'aima ta shigo taje jikin maryama ta kwanta, shafa kanta maryama tafara yi tana jin tausayin
yarinyar saboda yanda tayi ranar da zata haihu ba karamin tayar mata da hankali tayi ba,
Shaddad dakinsa yaje ya shirya yafita, tunda ya fita kuma bai dawo gidan ba sai da daddare,
wasu na falo wasu kuma na dakin maryama yayinda wasu na daya dakin dake kusa da na
maryama,
Ita maryama tana dakinta ita da khairat da anty maijidda da anty babba,
"Ni kam maryama nu'aima tayi shekara biyu ne?" Anty babba ta tambayi maryama,
"A'a Anty bata yi shekara biyu ba"
"Ni ai ban taba ganin likitar da tayi kunika ba sai maryama" anty maijidda taceda maryama tana
dariya,
"To anty yaya zanyi ya hanani inyi planning yace ko aboye nayi bai saniba Allah ya isanshi.."
"Nima ai da wasa nake yimiki, kiyi haihuwarki wallahi muma ai duk kunikar muka yi shiyasa su
hydar gasu nan duk Kansu daya"
Kafin maryama tayi magana shaddad ya shigo, anty babba ce ta tashi khairat tace taje ta kawo
masa abinci, fita yayi yanata kallon maryama saboda yafi son ita takawo masa abincin ba
khairat ba,
Koda khairat ta kai mishi abincin cewa yayi taje ta turo masa maryama, lokacin da khairat tazo
ta fadi sakon anty babba cewa tayi maryama ba zataje ba sai anty maijidda tace abarta taje suje
can su karata,
Tashi maryama tayi ta fita taje dakin shaddad, yana kwance akan gadonshi, agefenshi ta zauna
tana kallonsa,
"Navy tashi kaci abincin mana"
Hannunta ya rike nan taji zazzabi ne ajikin nashi, zirga zirgar da yayita yine yanzu kuma take
tambayarshi ga ciwon kai dake damunsa,
"Ya naji jikinka da zafi? Zazzabi kake yi?"
tashi zaune yayi ya kama hannayenta ya rike,
"Bani abincin naci sai ki bani magani nasha"
Murmushi tayi, "allura zanyi maka sai kafi jin dadi"
Bashi abincin tayi yaci tabashi ruwa yasha ya koma ya kwanta, tasan yana jin jiki amma sam
baya son tagane saboda kar hankalinta ya tashi,
Fita tayi ta koma dakinta ta dauko allura da sirinji ta dawo, rub da ciki ta sameshi yayi ahankali
tayi masa allurar,
"Washh.." Ya fada lokacin da yaji ta shigar da allurar cikin jikinshi,
"Da zafi ne?"
"Da zafi mana"
Zare allurar tayi tasa dan yatsanta tafara shafa wurin da tayi masa allurar,
Hannu yasa ya kwanto da ita jikinsa ya rungumeta,
"Dan Allah ki zauna mu kwana anan karki tafi"
"To kuma jaririn fa?"
"Zamuje mu daukoshi"
Murmushi tayi ta fara shafa kumatunsa, tana kallonshi idanuwanshi har sunyi ja saboda ciwon
kai da zazzabin dake damunshi,
"Kayi hakuri dai ka kwanta kayi bacci saboda kaga akwai sirikai agidan namu su hajiya suna
nan ga su anty babba da anty maijidda"
Hannunta ya rike sannan ya rike kanshi da daya hannun,
"Sannu Navy.." Tafada cikeda da tausayinsa saboda tun da taga yana yin haka to tasan yana jin
jiki, tashi tayi ta shiga toilet dinshi ta debo ruwa a dan karamin baho tazo ta zauna abayanshi,
rigarshi ta cire masa ta tsoma dan kwalinta aruwa ta fara matsewa tana goge masa goshinsa da
jikinsa,
Ta jima tana yimasa haka har bacci ya daukeshi, sai da taga yayi nisa da bacci sannan ta fara
kokarin tafiya, bakinshi ta yiwa kiss ta tashi zata tafi, hannunta taji ya rike ahankali kuma ya
bude idonsa,
"Tafiya zakiyi ki barni baby?"
"A'a zuwa zanyi nadawo" sakinta yayi yana murmushi saboda bai san cewar wayo zata yi masa
ba,
Sakin hannunta yayi ta tafi, yanda tabar su anty babba da anty maijidda haka tazo ta samesu
suna hira khairat ce kawai tayi bacci,
Rigar bacci ta saka ta kwanta, har bacci yafara daukarta taji wayarta tana ruri, shaddad tagani
mai kiran,
Tana dagawa taji yace, "baby najiki shiru.."
"Ya jikin naka navy?"
Lumshe idanuwanshi yayi yana jin dadin muryarta mai sanyi wacce take kara rura wutar sonta
acikin zuciyarshi,
"Kinga ma wani zazzabin ne ya sake rufeni, zo kiyi min wata allurar"
Jin ya fadi haka yasata tashi da sauri ta fita tana rikeda wayar a kunnenta, a falo ta samu su
anty maijidda sun maida dabar hirar tasu can sudai Allah ne kadai yasan lokacin baccinsu
amma kowa sai yayi bacci ya barsu,
Dakin shaddad ta hara, tana yi masa magana a waya,
"Harda ciwon kan bai daina ba?"
"Shima bai daina ba.. Ba kiji ba kamar zai fita daga jikin.."
Daidai lokacin ta bude kofar dakin nashi ta shiga, a kwance ta sameshi yayi rub da ciki,
Zama tayi ta kwanta a bayanshi tana shafashi ahankali amma kuma sai taji jikin nasa sanyi
kalau alamar babu zazzabin,
"Navy ai naji jikin naka babu zafi"
Murmushi kawai yayi baiyi magana ba ya mika hannunshi kan bed side drewar ya ajiye
wayarshi ya kashe bedside lamp,
"Navy magana fa nake yi maka wallahi bacci nake ji"
"To kiyi baccinki mana"
Tashi tayi yayi saurin riketa,
"Dan Allah karki tafi"
"Nabar jariri adaki kar ya tashi yazo yana kuka"
Dakyar ta samu ta kwace ta koma dakinta taje ta kwanta saboda wani irin bacci take ji gashi ta
gaji mutuka....
_*Ummi Shatu*_í ½í±Œí ¼í¿»
[5/25, 9:20 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: _*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_Sako ga autar hajiya, in banda abinki auta ai ni ban hanaki mijina ba,matsalar kawai yace
daga ni babu k'ari.._
_*50*_
~~~Ko minti biyu batayi da kwanciya ba taji shigowarshi, tsugunnawa yayi a saitin kanta ya
dafata yana bin kyakkyawar rigar baccinta da kallo,
"Bacci zakiyi?"
Kai ta daga masa saboda idanuwanta har rufewa suke yi saboda tsabar bacci, "to yi addu'a"
"Nayi" ta bashi amsa batare data bude idonta ba,yana tsugunnen har bacci yayi gaba da
maryama,ya jima yana tsugunne yana kallonta yana ta faman shafa kyakkyawan sajen dake
fuskarta wanda ya tafi ya lullube goshinta, ya jima ahaka kafin ya tashi ya fita, lokacin da ya fita
har su anty maijidda sunyi bacci itada anty babba.
Washe gari ya kama saura kwana biyu suna, tun sassafe maryama tayi wanka ta shirya
saboda yau za ayi mata kunshi da saloon, wani leshi ta saka baki mai adon ja ajiki, kyawun da
tayi ba kadan bane, gashi tako ina kamshi ne yake fita daga jikinta,
Tana rikeda jaririnta a hannu tace da anty maijidda,
"Anty bari nakai boy ya duba dadynshi yayi masa sannu bashida lafiya"
"Sai kun dawo"
Anty maijidda tafada tana kallon anty babba domin jiya da daddare sunga lokacin da taje dakin
shaddad sannan shima sunga lokacin da yasake binta dakinta,
Fita tayi da jaririn akan kafadarta ta shiga dakin shaddad, yana tsaye agaban mirriro yana zira
rigarshi, bakar t shirt mai dogon hannu, jaririn ta kwantar taje gaban shaddad ta tsaya tafara
balle mishi botir din jikin rigar tana murmushi,
"Ya jikin?"
Hannuwanshi yasaka gaba daya ya zagayeta ya rungumeta,
"Da sauki,ina nu'aima?"
"Tana can tanata bacci bata tashi ba"
"Da ace ta tashi da ta rakani kasuwa, ina son inje in siyo muku duk abubuwan da suka kamata,
gashi ma dai banida kudi wallahi.."
Jan hancinshi maryama tayi, "nima kuma ina son zaka kaini saloon anjima idan khairat ta gama
yimin kunshi kuma dole zaka biya kudin kunshi da na saloon"
Fuskarshi ya hada da tata yana murmushi,tareda jan hancinta, "ai ko baki fada ba ma dole na
nabiya domin matata aka gyara min tasake yin kyau"
Murmushi tayi taja shi suka karasa bakin gado ta dauki jaririn ta dorashi akan cinyarshi, "gashi
dama gaisheka yazo yayi"
Tana bashi jaririn ta fita zuwa dakinta bata jima ba sai gata ta dawo rikeda ATM card dinta a
hannu, zama tayi a kusa dashi ta mika mishi ATM card din,
"Naji kana cewa baka da kudi, gashi kaje ka ciri duk yanda zaiyi maka.."
Kallonta yayi sai kuma yayi murmushi ya jijjiga kansa,
"Bazan karbi kudinki ba baby, kudin wurina zai isa na siyo muku komai da komai"
Fuska ta bata ta mika masa hannu alamar ya bata jaririn, hanata jaririn yayi ya kwantar dashi
agefe yana cewa,
"Muhammad kwanta anan inje in rarrashi mamanka mai daru.."
Sai lokacin tasan Muhammad zai radawa jaririn domin har yau basuyi maganar sunan da zai
sakawa yaron ba.
Kusa da ita ya matsa yasa hannuwanshi guda biyu ya tallafe kumatunta,
"Baby menene nayin fushin? Kin san dai bana son bacin ranki.."
Sake daure fuska tayi, "ai dama nadade da sanin baka daukeni a matsayin abokiyar zama ba,
baka daukeni a matsayin sirrinka ba, sannan ni ka daina kirana da wani baby, budurwarka da
kakeso yar 18 years wacce har kabata number ta dan ta kirani tayi min rashin kunya ita ya
kamata ka kira da baby"
Murmushi yayi sai kawai taji ya rungumeta,
"Allah yabaki hakuri, wallahi ke sirrina ce saboda akwai sirrin dake tsakaninmu wanda duk
duniya babu wanda ya sanshi sai ubangijin da ya haliccemu, kuma ni ban bawa Amira number
ki dan ta kiraki taci miki mutunci ba.."
"To ya akayi tasan shekarata 30 lokacin da ka aureni indai ba kaine ka fada mata ba.."
"Ni nafada mata amma bawai da wani abu nafada ba, haba baby tayaya zanje naci mutuncin
iyalina awurin wacce ba iyalina ba? Nifa kawai cewa tayi tana so ku gaisa shine nabata number
ki, anan take tambayata wai ta girmeki ko kin girmeta shine nace kin girmeta shekarunmu daya
dake... Dan Allah kiyi hakuri"
Shiru tayi domin dama ta dade da hakura amma mamaki takeyi sosai wai yau itace shaddad
yake bawa hakuri,
"Kin hakura? Uhm baby nah..?"
Dagowa da kanta tayi tana kallonshi shima itan yake kallo,
"Na hakura amma sai ka tafi da ATM card din nan ka ciri kudin siyayyar da zaka iyo mana"
"Baby bana son in rinka taba miki kudinki.."
"To ai ba tambayata kayiba, nice nayi niyya na baka, haba shaddad nifa kafi haka awurina
wallahi duk abinda nake dashi zan iya mallaka maka, nasan abinda kake jin tsoro baka son inyi
maka gori watarana, to ka kwantar da hankalinka bazan taba goranta maka ba domin mun
zama daya, account dinma da babu wani kudi mai yawa aciki duk ginin asibiti ya lashe kudin..."
Sake rungumeta yayi cikeda kauna, "gashi kuma mijinki talaka ne balle ya kara miki wasu kudin
ki karasa ginin.."
Dariya tayi tana shakar kamshin turaren active man dake fita daga jikinshi,
"Ina son mijina ahaka komai babunshi, da mai kudi da talaka duk daga Allah suke"
"Nagode baby Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwarki data yaranki"
Dadine ya ratsata sakamakon addu'ar da taji yayi mata, sakinshi tayi tana kallonsa,
"Zanje saloon saboda wacce take zuwa tayi min agida tatafi garinsu"
"To idan kin shirya sai ki fada min in kaiki"
"Tom, bari nakawo maka breakfast.."
Daukar jaririnta tayi ta fita shaddad yabita da kallo cikeda so da tausayawa irin na masoya,tana
fita suka yi kicibus da anty maijidda,
"Nazata ai acan zaku zauna keda jaririn" anty maijidda ta fada tareda karbar jaririn tayi gaba
saboda tun dazu yan barka suka zo, kitchen maryama ta wuce ta karbowa shaddad breakfast
takoma takai masa,
Zama tayi tafara bashi shima yana bata har suka koshi, tare suka fito tana rikeda farantin
kwanukan da suka ci abincin, a falo yasamu su hajiya ya gaisheta sannan ya dauki nu'aima
wadda ke zaune tana shan tea.
Zama maryama tayi khairat ta zana mata jan lalle mai kyau, sai da yayi jajur sannan aka cire,
nan ta je ta sake yin wanka tana jiran shaddad ya dawo ya kaita wurin saloon domin ya fita da
motar tata,
Shaddad bai dawo gidanba sai da mangariba, siyayya ce ya iyo mai yawan gaske duk abinda
za a bukata saboda shagalin suna ya siyo shi sannan ya siyo raguna biyu manya,
Shigar musu da kayayyakin da ya siyo yayi cikin kitchen ya wuce dakinsa, mintuna kadan ya fito
ya shiga dakin maryama yace ta fito ya kaita saloon din,
Anty maijidda sai fada take tana cewa ahakura da wannan saloon din, ko kwana 7 da haihuwa
bata yiba amma har zata fita, hajiya ce tace abarta taje ai yanzu zasu dawo, nan maryama ta
dauki hijab ta fita tana tafiya ahankali saboda har lokacin bata gama warwarewa ba,
A mota ta samu shaddad ta shiga,kallonta ya tsaya yi kafin yakamo hannayenta masu taushi
wadanda suka sha jan lalle yafara gani,kissing din tafin hannunta yashiga yi dakyar ya saketa
ya tashi motar suka tafi cikin gari,
Wani shagon saloon ya kaita ta shiga tabarshi acikin mota yana jiranta,
Tafi minti 40 kafin ta fito bayan angama yi mata gyaran gashin, zama tayi tana kallon shaddad,
"Allah sarki mijina yi hakuri yau sai wahalar dakai nake yi naki barinka ka huta"
Haske ya kunna acikin motar yana kallonta,
"Karki damu baby ai kinfi haka, muga gyaran kan da akayi miki"
Bude mishi tayi yagani maryama badai gashi ba, domin gashinta har kafadarta yake bakikkirin
mai laushi,shafa gashin yayi,
"Nidai nayi dace duk wani abu mai kyau wanda ake bukata awurin mace matata ta