Showing 54001 words to 57000 words out of 64131 words
Chapter 19 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf
ba,
Yana nan atsaye har nu'aima tayi bacci akan kafadarsa, gida ya koma ya mayar da ita wurin
baba lami ya sake dawowa asibitin,
Shida dadane a reception suna jira, can nurse tazo tace anciro jaririn suzo su ganshi, duk
murnar da shaddad yake yi na zai samu karuwa amma sai yaji wannan lokacin ya nemi farin
cikin ya rasa,
Wurin jaririn sukaje suka ganshi tubarakalla kato dashi mai kama da shaddad fitik, nan aka
shirya yaron aka ajiyeshi acikin gadonshi,
Maryama kam awa da awanni bata farfado ba dan haka hankalin doctors din ya tashi sosai nan
suka rufu akanta domin ceto numfashinta sai dai amma ina basu da wannan ikon daga karshe
dai dole suka hakura domin tuni rai yayi halinsa maryama ta rigamu gidan gaskiya,
Dr muneerat ce ta fito jikinta yana rawa taje wajen su Dada amma sai ta kasa fada musu
rasuwar maryama,
"Dr ta farfado ne?" Dada ya tambaya, girgiza kai dr muneera tayi,
"Yallabai sai dai muyi hakuri mu karbi kaddarar da Allah ya aiko mana.."
Hawaye suna bin kuncinta ta mikawa shaddad wata farar takarda,
"Gashi itace ta rubuta kafin ayi mata aikin.."
Karba yayi hannunsa yana rawa ji yake kamar mafarki yake yi, cikin rawar jiki ya warware
takardar yafara karantawa,
"Mijina dan Allah idan nayi maka laifi ka yafe min, Allah ya hadamu a aljanna sannan dan Allah
ka taimaka ko gawata ne ka fada mata Kalmar so duk da nasan ba ka sona, amma ka sani ni
ina tsananin sonka son da ban san adadinsa ba, Allah ya raya mana yaranmu..."
Ai shaddad yana gama karantawa yaji kamar zai zube awurin saboda hajijiyar data fara
daukarshi idanuwanshi suka rufe baya ganin komai sai duhu....
_Gaisuwa ga masoyana masu sona, ina mai baku hakuri sakamakon bana baku amsa da wuri
idan kun yimin magana wallahi abinne yafi karfina shiyasa, sakonninku da yawa bazai yiyu in
amsa a lokaci guda ba,nagode da kaunarku gareni, ummi shatu luvs u too.._
_*Ummi A'isha*_í ½í±Œí ¼í¿»
_®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_
_*NA*_
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_*Gaisuwa mai dunbin yawa gareku masoyan maryama sarauniya ina jida ku sannan ina
alfahari daku....*_
*_47_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Duk karfin hali irin na shaddad wannan lokacin ji yayi ya kasa controlig din kanshi, idonshi
cikeda wani irin duhu wanda ya hanashi ganin komai ya dubi dr muneerat,
"Tana ina?"
"Tana ciki.."
Bin bayanta yayi yana jan kafarsa domin bazai iya dagata ba, shi kuwa Dada yana nan tsaye
awurin kamar an kafashi ya kasa koda motsi,
Tiryan tiryan shaddad yake biye da dr muneerat har zuwa dakin da maryama take lokacin har
doctors din sunja farin kyalle sun lullubeta har fuska,
Jikinsa yana rawa hannunshi yana wani irin karkarwa ya yaye kyallen daga fuskarta,
idanuwanta a lumshe amma kuma fuskarta dauke da murmushi kamar lokacin da tana raye,
fadawa jikinta yayi ya fashe da kuka kamar ba namiji ba namijin ma soja,
"Dan Allah karki mutu maryama, kiyi hakuri kidawo muci gaba da rayuwarmu..."
Wani jirine ya debeshi daga nan ya zube awurin shikenan ya rasa hankalinsa bai sake sanin
abinda yake faruwa ba, yana damke da takardar da maryama ta rubuta masa kam kam ya kasa
sakinta ta fadi,
Kinkimarsa akayi akan wani gado aka nufi emergency dashi, koda Dada yaga haka sai ya kira
driver yace yazo su dauki gawar su tafi da ita gida,
Haka kuwa akayi nan da nan aka fito musu da gawar maryama aka saka musu a mota suka nufi
gidan Dada da ita, ahanya dada ya kirasu anty maijidda ya sanar musu, ai anty maijidda naji ta
hau salati tana cewa,
"Wacce maryaman? Dazu fa ta kirani tace za ashiga dakin haihuwa da ita..". Nan ta kashe
wayar jikinta yana rawa, tama rasa me zatayi dole sai samun wuri tayi ta zauna hawaye nabin
kuncinta.
Koda Dada suka je gida kafin wani dogon lokaci har gidan ya fara dinkewa da jama'a, su anty
maijidda da anty zainab sunzo sannan su hajiya ma da yan uwan shaddad su anty babba
sunzo, in banda koke koke babu abinda akeyi, babu mai rarrashin wani, wani karin abin
tausayin ma sai da su baba ladi suka karaso itada nu'ayma nan nu'ayman ta rinka neman
umminta tana kuka,
Cikin lokaci kankani aka yiwa maryama wanka aka shiryata, mutane sai zuwa suke daya bayan
daya suna yi mata addu'a,
Shaddad kuwa sai da ya dauki fiyeda awa daya kafin hankalinsa ya dawo jikinsa, bude idonshi
yayi nan take mutuwar maryama ta dawo masa cikin kwakwalwarsa ai zunbur ya mike ya fincike
karin ruwan da ake yimasa ya fita jiri na daukarsa ba tare da ya saurari kiran da nurses din dake
cikin emergency din suke yi masa ba,
Motar maryama da suka zo da ita ya shiga yafita daga asibitin aguje, yana driving yana kuka
sannan har lokacin yana damke da wasikar da maryama ta rubuta masa,
Gidan Dada yaje anan yaga mutane sun fara taruwa wadanda zasu yimata salla,
"Me kuke yi anan? Maryama fa bata mutu ba, wallahi bata mutu ba, ku tafi, ku tafi, maryama
tana raye..." Tamkar mahaukaci haka yake ta fada yana kuka hawaye nabin kumatunsa, cikin
gidan ya shiga, yana shiga nu'ayma taso tazo ta rungumeshi tana kuka,
"Dady ka kaini wurin Ummi.."
"Mamana umminki tana raye bata mutuba, wallahi bata mutuba..,maryama ba zata taba mutuwa
tabarni ba, waye ma yace ta mutu? Bata mutuba.."
Kowa binsa yake da kallon tausayi saboda ya zauce hankalinsa baya tare dashi,
Sakin nu'ayma yayi ya nufi falon Dada inda gawar maryama take, yana zuwa ya yaye lullubin da
akayi mata ya dauketa gaba daya ya rungumeta ajikinsa yana kuka, takardar data rubuta masa
ya warware yana sake karantawa rubutunta gashi nan mai kyau irin na likitoci kamar da
computer aka rubuta bada hannu ba,
Sake damke takardar yayi yana wani irin kuka kamar ba soja ba,
"Maryama wallahi ina sonki, dan Allah kiyi hakuri ki dawo zan nuna miki irin soyayyar da nake
yimiki, wallahi maryama ina sonki tun ranar farko dana fara ganinki, kiyi hakuri maryama nauyin
baki nayi ban taba furta miki ba amma da ace zaki iya bude zuciyata to da kinga sonki mamaye
acikinta,
Kiyi hakuri maryama, ina sonki, ina sonki, wallahi ina sonki, maryama ina sonki.."
Kamar a mafarki yaji taja wata irin doguwar ajiyar zuciya,nan zuciyarta taci gaba da aiki
numfashinta ya dawo,
"Yawwa maryama dama nasan ba zaki mutu ki barni ba, sai da nafada musu baki mutuba
amma suka ki yarda... Ni dama nasan ba zaki mutu yanzu ki barni ba.."
Ahankali take bude idonta tana kallonsa hawayen dake fita daga idonsa suna sauka akan
fuskarta,
"Maryama wallahi ina sonki, ina sonki maryama, waye yace miki bana sonki, wallahi ina sonki..."
Fashewa yayi da kuka ya rungumeta,
Su hajiya dake babban falo suna jin duk abinda yake faruwa su duk a tunaninsu shaddad
zaucewa yayi dan haka hajiya ta mike ta nufi falon domin bashi baki da yimasa nasiha kan yayi
hakuri ya karbi kaddara domin dukkan mai rai mamaci ne,
Tana shiga ta ganshi rungume da maryama ita kuma maryaman idonta a bude tana jijjiga masa
kai alamun yabar kuka, ai hajiya komawa tayi da baya har tana yin tuntube,
"Bata mutu ba, wallahi ashe bata mutu ba" hajiya ta fada cikin razani,
Nan itama aka fara yi mata kallon ko tabi sahun shaddad dinne basu gama mamaki ba sai da
suka ga shaddad ya fito dauke da maryama a hannunsa kamar wata jaririya zai mayar da ita
asibiti saboda tanata yimasa nuni da cewar cikinta ciwo yake yi mata,
Mimmikewa tsaye sukai suna kallonsu saboda ganin maryaman idanuwanta a bude sannan
tanata rirrike shaddad,
Nan kuma kowa ya shiga murna anty maijidda harda tsalle, taya juna murna aka shiga yi, shidai
shaddad fita yayi da ita, su Dada na zaune suna jiran afito da ita ayi mata salla aje akaita
makwancinta sai ga shaddad ya fito dauke da ita idanuwanta a bude tana kallon kowa,
"Dama nafada muku maryama bata mutu ba, wallahi bata mutu ba"
Sakata yayi a mota ya zagaya da gudu shima ya shiga ya finciki motar aguje ya koma asibiti da
ita, kamar mahaukaci haka ya dawo, daukarta ya sakeyi bayan sunje asibitin ya nufi ciki da ita
yana shiga yayi kicibus da dr muneerat nan ta nuna masa dakin da zai kaita, tare suka shiga ya
kwantar da ita akan gado, yana makale da hannunta acikin nashi dr tafara dubata daga karshe
tayi mata wata allura sannan ta daura mata drip,
Kafin wani lokaci har asibitin ya cika da yan uwa duk sun baro gida sun taho nan, shaddad yana
zaune agefen gadon yana rikeda hannun maryama ahaka duk yan uwa suka shisshigo suka
dubata suka fita,
Juyo da kanta tayi ta kalli shaddad saboda yanzu ta dawo cikin nutsuwarta sosai,
Cikin sauri ya daga kanshi yaje saitin fuskarta,tareda sake damke hannunta,
"Maryama kiyi hakuri wallahi ina sonki, idan bana sonki ai bazan zauna dake ba, tunda kika ga
na zauna dake ai dan ina sonki ne...
Kiyi hakuri maryama dan Allah karki tafi ki barni ni kadai, wallahi idan babu ke nima bazan iya
rayuwa ba,
Kiyi hakuri muci gaba da zama tare nikuma nayi alkawarin zan soki zan nuna miki soyayya
fiyeda irin wacce kike nuna min.." Yana maganar ne hawaye yana bin kuncinsa,
"Kadaina kuka please.." Tafada ahankali,
Kifa kanshi yayi a kirjinta ya rungumeta, ita dinma rungumeshi tayi tana shafa sumar kanshi,
"Ina abinda muka haifa?"
Sai a lokacin shaddad ya tuna da batun jaririn domin shi tun lokacin da yaji mutuwar maryama
bai kara bi takansa ba,
"Bari nasa akawo manashi ki ganshi.."
Fita yayi ya samu nurses din da ke zaune awaje yace akawo musu jaririnsu,
Komawa wurin maryama yayi ya zauna yakama hannunta ya rike cikin nashi,
Har aka kawo jaririn yana makale da ita, "ni babu ruwana dashi tunda ya wahalar min da matata
har tayi dogon suma akace min ta mutu.."
Murmushi maryama tayi ta leka fuskar jaririn ta gani,
"Masha Allah, yaro mai kamada babanshi sak" tafada bayan ta koma ta kwanta,
"Nima ramawa nayi ai, last time mai kamada ke kika haifa shiyasa nima this time around na
dage na samu mai kama dani"
Murmushi maryama tayi tana kallon shaddad wanda idanuwansa suke jajur har lokacin,
"Maryama kiyi min uzuri kibani dama irin damar da phertymah xarah tabawa jawad lokacin da
ya rusa mata MARTABARTA,nikuma nayi miki alkawarin zan zama tafida bazan manta alkairinki
agareni ba domin shi AlHERI DANKO NE, zaman da nayi dake na fuskanci kinada hakuri da
juriya da kawaici fiyeda Aishan Abdulhakeem wadanda suka yi rayuwarsu karkashin inuwar
BIYAYYAR IYAYE, kiyi min alfarma irin alfarmar da Ikhlas ta yiwa Lamido lokacin da yayi amfani
da kalmar hausawa ta cewa RUWAN KASHE GOBARA basai mai kyau ba, idan kika bani dama
zan yi amfani da SANADIN GATA na mayar dake WANI HASKE acikin rayuwarmu data
yayanmu irin yadda jabir ya mayar da bahijja, sai na mayar dake tauraruwa fiyeda yanda
Awwab ya mayar da nihal acikin KWARYA TABI KWARYA, insha Allah zaki kasance MACE
GUDA DAYA TILO acikin birnin zuciyata tunda kin dade da daukar AURE a matsayin YAKIN
MATA.."
"Kana sona..?"
Rufe mata baki yayi da hannunsa guda daya, "kidaina wannan tambayar, da bana sonki da
bazan taba zama dake ba"
Matsawa yayi saitin kunnenta, "akwai wani lokaci guda daya wanda shi kadai ya isa ya sanar
dake dunbin kaunar da nake yi miki..."
Murmushi maryama tayi ta lumshe idanuwanta tana mai sake jin wata irin zazzafar kaunar
shaddad tana kwaranya acikin zuciyarta....
_masoya kuyi hakuri da wannan, gani nayi hankalinku ya tashi ne shiyasa na samu nayi muku
wannan..._
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/25, 9:20 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
_Wannan shafin nakune masoyan maryama sarauniya daku da takwarorinta gaba daya._
*_48_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Shaddad yana rike da hannun maryama gefe daya kuma jaririn sune kwance agefen
maryaman, gaba daya shaddad ya kasa tashi ya matsa ko nan da can saboda gani yake yi idan
ya fita kafin ya dawo maryama ta mutu,
Ko sallah ya kasa zuwa yayi yana nan zaune kusa da ita kwakume da hannunta, tun suna yin
hira tare har ta dan fara yin bacci, zuruf ya mike yaje ya kara kunnensa ajikin kirjinta nan yajiyo
bugun da zuciyarta take yi, duk da haka hankalinsa bai kwanta ba har sai da ya kai hannunshi
saitin kofofin hancinta yaji numfashinta yan sauka akan hannun nashi sannan yakoma ya zauna
ya zuba mata ido kamar lokacin ne yafara ganinta, hakurinta da juriyarta yake tunawa da irin
soyayyar da take yi masa koda wasa bata son taga yayi fushi ransa ya baci, dai dai da rana
daya bata taba fada masa kalmar da zata bata masa rai ba, sannan duk tawon lokacin da suka
dauka tare bai taba shakar wani abu atareda ita sabanin kamshi ba,
Bude idanuwanta tayi tana yi masa murmushi,
"Navy baka tafi gida kayi wanka ba?"
"Jira nake naga kin bude idonki kin gama baccin tukunna..."
Murmushi ta sake yi ta runtse hannunshi cikin nata,
"Tunda natashi to kaje ka tafi"
Hannunta yakai kan bakinshi yayi kissing dinshi tukunna ya mike zai tafi,
Bude kofa akayi khairat ne da anty maijidda suka shigo hannunsu rikeda dan karamin basket
wanda suka hadowa maryama kayan tea aciki,
Komawa shaddad yayi ya zauna,
"Yaya Navy bakayi salla ba fa.."
Khairat tace tana dariya, "navy ai yau yazama baby.."
Anty maijidda tafada itama tana dariya,
Karbar kayan yayi yana murmushi ya hadawa maryama tea rabin cup ya koma bakin gadon ya
tadata zaune ya jinginata da jikin pillow yafara diba a spoon yana bata,
"Navy baka fifita ba da zafi tea din..."
"Yi hakuri bari na fifita miki"
Wani cup din ya sake dauka ya fifita mata tea din sannan yaci gaba da bata su anty maijidda da
khairat suna tsaye suna kallon ikon Allah,
Daf da zata kammala shanyewa ta kauda kanta tea din ya zuba ajikin habarta,
"Barshi haka ya isheni.."
Babu kunya shaddad yasa harshensa ya lashe wanda ya zuba akan habar tata, anty maijidda
da khairat sai ficewa suka yi daga cikin dakin,
"Zanje gida nayi wanka nayi salla sai in dawo..."
"Abinci fa? Kaci abinci kafin ka dawo dan Allah"
Kiss yayi mata akan lebenta, "to sai nadawo"
Fita yayi tabishi da kallo, ta glass din window din dakin take hangoshi har ya bacewa ganinta,
Murmushi tayi ta janyo jaririnsu tana kare masa kallo komai na yaron irin na shaddad ne sak
babu banbanci,
Fitar shaddad ce tasa wadanda ke zaune awaje suka shisshigo cikin dakin suna yiwa maryama
sannu,
Shaddad na fita gidanshi ya wuce acan ya iske su hajiya da su anty karama da anty zainab
suna kitchen suna girke girke,
Ganinshi yasa Nu'aima zuwa ta rungumeshi tana murna,
"Dady wai Ummi ta siyo mana sabon baby boy?"
Dariya maganar nu'aima tabishi, riketa yayi yana dariya, "ehh mamana umminki ta yimiki kani,
zamuje ki ganshi ko?"
Kaita wurin hajiya yayi ya juya zai tafi,
"Kai shaddad sai ka nemo wani sunan da zan rinka fada maka saboda bazan kara kiranka da
mazaje ba.."
Dariya yayi saboda jin abinda hajiya tafada yasan tafadi hakane saboda ta ga irin kukan da yayi
dazu,
Dakinsa ya shiga yaje yayi wanka yayi salla ya shirya cikin blue din jeans da jar riga mai
gajeren hannu,
Yana kokarin fitowane suka yi kicibus da anty karama zata kawo masa abinci, kamar ba zai
zauna yaci abincin ba sai ya zauna saboda rokon da maryama tayi masa dazu kafin ya bar
wajenta, yanzu so yake shima ya nuna mata so da kauna irin wacce ba ataba nunawa wata ya
mace ba,
Cokali uku yayi a abincin ya fita ya dauki nu'aima suka tafi asibitin, lokacin da yaje ya samu
maryama azaune tana rike da jaririn akan cinyarta sai khairat kuma dake zaune akan wata farar
kujera tana yiwa maryama hira,
"Ummi ina babyn da kika siyo mana?" Nu'aima ta fada tareda kokarin hawa kan gadon,
shaddad ne ya dagata ya dorata akan gadon shima ya zauna akusa da maryama,
"Gashi mamana, kaga yaya nu'aima.."
Maryama tace tareda dora jaririn akan cinyar nu'aima,
"Yarinya karama sai manyance" khairat ta fada tana dariya,
"Bawani manyance itama ai yanmata ce yanzu da me kika fita?"
Maryama tafada tana dariya, kallon shaddad tayi wanda ya maida hankalinsa akan wayarshi
dake hannunshi,
"Kaci abincin kuwa..?"
Gira ya daga mata yana murmushi,
"Ban yadda ba Navy"
Bakinshi ya kai kusa da hancinta,
"Shinshina kiji zakiji kamshin curry"
Maimakon ta shinshina din kamar yadda yace sai kawai ta cijeshi, tashi khairat tayi ta fita ta
basu waje,
Riketa yayi yana kallonta ido cikin ido fuskarshi kumshe da murmushi,
"Kika cijeni?"
Lumshe masa idanuwanta tayi tana yi masa murmushi,
"Tsautsayi ne.." Tace dashi tana wasa da hannunshi,
"Idanma bada tsautayin kika yi ba nayi miki uzuri, ni duk abinda kika