Showing 36001 words to 39000 words out of 64131 words

Chapter 13 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5648

bayan yarage su biyu acikin falon suna sake ganin kayan,

"Allah Sarki maryama, jinkiri alkairi ne yau dai kiga yarinyar nan shekararta talatin kamar bazata
yi aureba yau kiga irin uban kayan da aka kawo mata, wallahi duk wata wacce ta jima batayi
aureba sai kiga idan Allah yatashi bata yabata mai nagarta kuma son kowa kin wanda ya rasa"

"Ah tun yaushe ai mai hakuri mai komai ne zainab yanzu dai duba kiga wannan uban kaya wai
na maryama ne ita kadai"

Anty Maijidda tace tana rufe akwatin dake gabanta,

"Allah dai yasa rabonta ne"

"Amin zainab jibi sai muje mukai musu can Lagos din ko idan makota da yan uwa sunzo sun
gama gani"

"Ehh sai mukai"

Haka suka yita murna suna maganar kayan har zuwa wani lokaci.

Abangaren shaddad kuwa takaici goma da ishirin ne yake ciciyarshi saboda anturo masa
posting letter cewar an sake turashi aiki Lagos sai dai wannan karon ba barikin su maryama
bane wani barikin ne daban dake can gaba da nasu maryama amma shi dinma acikin Victoria
island dinne,
Kamar zaiyi kuka haka ya shirya yatafi kai repot gashi yau aurensu shida maryama saura
kwana goma cif...

*_Ummi A'isha_*👌🏻


[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu👌🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_




_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*





_Dedicated to Maryam Qaumi_💕


_Kuna ina? Aminiyata ta k'warai cwt Kausar luv, and my besty Pherty Xarah, idan kuna kusa to
ga shafinku ummi shatunku ta baku domin jin dadinku..._





*_32_*


aishaummi.blogspot.com




~~~Haka Shaddad ya shirya ya tafi cikin bacin rai, aranar da yaje aranar yagama komai
yawuce masaukinsa, yana kwanciya ko gama hutawa baiyi ba hajiya ta kirashi awaya,

Yana dauka yaji tafara fadin,

"Lallai lallai kaje wajen amaryarka ku gaisa kafin kadawo, kajini ko mazaje?"

"Ehhh hajiya naji.." Yafada yana jin wani irin kunci yana shiga zuciyarsa,

"Yawwa idan kaje kace ina gaisheta"

"To zataji"

Daga haka ya kashe wayar cikeda bacin rai saboda shi sam baya son wannan auren na
maryama domin yana ganin kamar wata wahala ce zai tsunduma kansa aciki,

"Nidai kawai sangartacciya zan aura, yarinyar da babu abinda ta iya sai shan cyrup da zuwa
club da bibiyar maza wai kuma yanzu azo ace itace matata, kai gaskiya nidai wallahi ba akyauta
min ba,yarinyar nan babu abinda ta iya, ko shara bata iyaba bare girki"

Yafada afili yana cizon leb'e amma yasawa ransa cewar shi babu wani gidansu maryama dai
zaije kawai dama ya amsawa hajiya da to ne saboda gudun bacin ranta.


Abangaren maryama kuwa tana can sun fara tunkurar shirin biki itada Dada domin har Dada
yayi order akawo furnitures din da za akaiwa maryama gidanta daga kasar Italy,

Ranar alhamis da safe su anty maijidda da anty zainab suka zo gidan dauke da kaya niki niki
wanda sai sojoji ne ma suke binsu da akwatunan,

Maryama tana zaune afalo da filet a hannunta tana cin soyeyyen plantain ga waya makale a
kunnenta suna hira da dr fahad sai ga su anty maijidda sun shigo, ajiye wayar tayi ko tsayawa
kashewa batayi ba ta tafi da gudu ta rungumesu,

"Yata kayanki muka zo kawo miki"

Anty zainab tace tana ajiye kit din dake hannunta,

"To anty zainab kuma baku barinshi anan idan nazo sai nagani"

"To uwar yan hankali ai akawowa dadan naki yagani ko?"

Anty maijidda tafada tana yaye mayafin dake kanta saboda zafi,

"To anty ai mantawa nayi"

Tafada tana bin akwatinan da kallo saboda sunyi mutukar daukar hankalinta gashi best colour

dinta aka samu wato pink and blue,

Gaban akwatin ta karasa tana shafashi saboda ganin hoton butterfly ajikin mirfin daga sama,

"Wowwww,anty wadannan akwatinan sun yimin kyau"

"To ai dama nakine" inji anty zainab,

"Yata albishirinki"

Anty maijidda tafada tana murmushi,

"Goro anty.."

"Me zaki bani tukwici"

"Idan labarin mai dadine anty zan baki salaryna na 1 month"

"Nawa kike karba per month?"

"Anty dubu dari bakwai da hamsin ne kacal"

"Ke yar nan ashe kudi kika tara bamu saniba, wannan uban kudin ya kike yi dashi?"

Anty zainab tafada tana zazzare ido dan tsananin mamaki,

"Wallahi anty ginin asibiti ake yimin, so nake nagina asibitin yara nawa na kaina, kuma inada
gidan gona.."

"Ato kinyi dabara ai hakan yayi kyau"

Anty zainab tafada tana murmushi,

"Albashinki na wata yayi min yawa maryama amma dai dole kibani tukwici tunda har nakawo
miki kayan lefen shaddad gidan nan.."

Mikewa tsaye maryama tayi, "anty wanne shaddad kuma?"

"Wanda dai kika sani, shaddad dinki, Navy.."


"Wayyo anty maijidda tsokanar har takai haka"

"Ke idan zaki ware ki ware babu wani tsokana wallahi dagaske ne shaddad shi zaki aura shine
ya kawo miki wannan kayan"

"Alhamdulillah.." Shine kawai abinda maryama tafada ta fadi tayi sujjada tana murmushi, kallon
kayan jikinta anty maijidda tayi daga ita sai farar body hug da jeans ta tattare kafar wandon sai
kace wata yar kokawa,

"To yanzu dai ciwo ya kare, ankusa aje gidan shaddad ayita tsukewa da kananan kaya tunda
kedai bakya kaunar kayan hausawa"

"Ai anty ni wallahi bana jin dadin kaya indai ba doguwar rigane ko riga da wando ba, ni kwata
kwata ma bana son wasu kaya inba english wears ba.."

"Zaki saka da kyau ai" anty zainab tace da ita,

Blessing ce tafito hannunta rikeda faranti takawo gabansu ta dire,

"Woww anty kayan aurenki ne? Ni inama in samu quarter din wannan da naji dadi.."

"Kayanta ne blessing zauna kigani"

Anty maijidda tafada tana tsiyayar juice acikin cup,

"Kema kije kiga kayan lefenki yarinya"

Anty zainab tace da maryama.

Matsawa gaban kayan maryama tayi suka fara kallo itada blessing,duk abinda blessing ta daga
sai kaji tana cewa,

"Woww anty wannan zai yi miki kyau.."

"Kema za akawo miki irinshi wata rana blessing ai tunda zanyi aure to kowa ma zaiyi.."
Maryama tafada tana murmushi,


Da haka suka gama kallon uban tulin kayan wanda sai hakura ma sukayi basu iya kallo gaba
daya ba, ko tashi daga wurin basuyi ba Dada ya shigo yana rikeda sandar da yake dan
dogarawa da ita duk lokacin da ciwon kafarshi ya tashi,

"A'a kayan maman nawane suka sauka.."

Dada yace yana murmushi,

"Ga kaya nan kam mun kawo" inji anty maijidda,

Zama shima dadan yayi blessing tafara daga masa kayan yana gani sai sanya albarka yake,ita
dai maryama tashi tayi ta shiga kitchen ta dorawa su anty maijidda abinci, zuciyarta tana cikeda
tarin farin ciki wanda ba zata iya kwatantashi ba sai dai kuma tana jimamin irin zaman da zatayi
da shaddad kafin ta samu hankalinsa ya dawo gareta ya fara kaunarta...


*_Ummi A'isha_*👌🏻
[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu👌🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*




_Dedicated to Maryam Qaumi_💕


_Gaisuwa mai yawa ga antyn amarya, antyn ummi Shatu wato anty maijidda musa.._




*_33_*



~~~Kwanan shaddad 5 a Lagos bai tafi Kaduna ba har sai da yagama dukkan abubuwan da
suka kamata sannan ya nemi hutun sati biyu saboda bikinsa,hatta mukullin gidan da zai zauna
sai da ya karba, wasu sabbin gidajene masu dakunan bacci guda uku da babban falo guda
daya sai kitchen da store, a unguwar Victoria island yake shima na sojoji ne aka gina musu
musamman,

Aranar da yagama komai yayi tafiyarsa Kaduna bai ko nemi ganin maryama ba balle yaje inda
take,

Lokacin da yaje gida tisashi da tambaya hajiya tayi kan ya yabaro maryama, shikuwa kawai
amsawa yake da tana nan lafiya, saboda yasan idan tagane baijeba zai sha fada.

Maryama kuwa daren ranar da su anty maijidda suka zo kasa bacci tayi dan tsananin murna
nan ta kira khairat tana yi mata godiyar ceton rayuwarta da tayi,

Kusan kwanan zaune suka yi dasu anty maijidda suna hira,kwanansu biyar agidan suka tattara
har maryaman suka nufi abuja saboda suna son suje su gyarata, za ayi mata gyaran jiki da
sauran abubuwan da suka kamata, sallama tayiwa dada da sauran mutanen dake gidan domin
idan tatafi bazata sake dawowa gidanba sai ranar da za akaita gidan mijinta aranar ne za
akawota dan tayiwa dada sallama,

Tattarawa sukayi suka tafi ita dasu anty maijidda zuwa abuja, suna zuwa kuma ta shiga busy
domin bikin saura kwana biyar kacal, shagunan dinki sukaje takai dunkunanta sannan suka
shiga kasuwa suka dan iyo siyayyar da baza arasa domin ashe gaba daya anty maijidda
tagama siya mata kayan kitchen da sauran kayan kwalliyar falo zuwa bedroom da sauransu,
Suna komawa gida anty maijidda ta kira hajiya fiddausi Sodangi kwararriya wurin gyara amare
tazo takanas tun daga garin borno domin gyara maryama,tana zuwa tafara tsumata da kayan
gyara sahihi dan borno,

Nan aka fara dirjar fatarta ana shafeta da kayan hadin gyaran fata, cikin kwana biyu kacal
maryama ta juye ta zama balarabiya,sai dai tulin abubuwan dasu anty maijidda da hajiya
sodangi suke dura mata amai yake sata, daga tasha sai amai gashi sam bata iya cin abinci
kwata kwata,
Kallon anty maijidda tayi sannan ta kalli cup din dake hannunta cikeda wani abu mai kamada
madara,take tafara jin zuciyarta tana tashi,

"Anty dan Allah kiyi hakuri kibar abin nan wallahi amai karninsa yake sani.."

"Sai fa kinsha garama ki daina hadani da Allah, ko kin amayar ai dole wani zai zauna acikinki.."

Anty maijidda tafada tana mika mata cup din,

"Anty zainab,anty zainab.." Maryama tafara kwalawa anty zee kira wai ko zatazo ta ceceta,
amma koda anty zainab din ta shigo itama rike take da farfesun yan shila acikin plate ta kawo
mata, haka suka tisata agaba sai da ta cinye sannan ta shanye wannan abun, kullum haka suke
yimata tun tana yin amai har ta daina.
A bangaren shaddad kuwa shi babu wani shiri da yake yi, su hajiya ne kawai ke yin shirinsu sai
sauran jama'ar gidan amma shi sam babu abinda ya d'ad'a shi da k'asa da wannan bikin,

Ita kuwa hajiya tsabar soyayya cewa tayi bayan an daura aure akawo mata maryama tayi
kwana biyu sannan su tafi Lagos itada shaddad din.

Tun ranar laraba gidan anty maijidda ya dinke da dangi da yan uwa harda abokan arziki,
maryama tasha kunshi da gyaran gashi tafito tayi kyau sosai,fatar nan tata kamar ta jarirai
domin ta yan hutuce gashi kuma ta had'u da gyara na musamman,

Aranar sulaiman abokin shaddad yazo kawo mata kudaden da zata yi hidima dasu kamar yadda
ake bawa kowacce amarya da kawayenta, to ita bata da kawayen ma, bata da wata kawa ko
daya komai nata ita kadai take yi,

Lokacin data fita sulaiman yaganta sakin baki yayi ya tsaya yana kallonta, shi mamaki yake da
ganin wautar shaddad da yaketa ikirarin baya sonta, shikuwa sulaiman sam baiga laifinta ba
asalima babu wanda zai ganta yace takai wadannan shekarun gata kyakkyawar gaske,

Gaisawa suka yi yabata kudin ya tafi, itama cikin gida ta koma tana cike da murnar ashe dai
shaddad yana sane da ita.

Ranar alhamis da yamma aka yi kamun maryama awani babban hall dake cikin Real Hotel,
kamun yayi kyau sosai kuma ya kayatar, karfe shida aka gama aka watse kowa ya koma
gidansa, anty babba yayar shaddad suma sun halarci wurin itada sauran dangi,

Washe gari ranar juma'a aka daura auren SHADDAD A SADIQ da DR MARYAMA FARUQ
BELLO akan sadaki naira dubu hamsin agarin jimeta, kuma aranar su anty maijidda suka shirya
suka tafi Kaduna tareda amarya,

Suna zuwa aka karbesu cikin mutunci da girmamawa, hajiya kuwa kamar zata karawa maryama
numfashi dan tsananin so, jin anty maijidda ma tace bata ci abinci ba haka ta zauna ta bata
abincin tanayi tana lallabata da haka har sai da ta koshi,


Sosai itama maryaman taji tana kaunar mahaifiyar shaddad domin itama tana tsananin sonta
gashi dadin dadawa ma ashe sunansu daya itama hajiyan sunanta hajiya maryam,


Dare yanayi misalin karfe 8 aka fara shirin tafiya dinner wacce sisters din shaddad suka shirya,
nan aka rangadawa amarya kwalliya aka shiryata tafito cikin doguwar wedding gown pink and
blue colour, tasha head shima pink, komai dai pink,

Gabanta ne ya fadi lokacin da anty babba ta kaita gaban motar da shaddad ke ciki yana zaune
agidan baya saboda rabonta dashi tun ranar da yaje abuja, shikuwa shaddad ta cikin glass din
window din motar ya zuba mata ido yana kallonta dan kyau kam tayi kyau shi kawai matsalar

baya sonta ne bata cikin irin tsarin matan da yake son aura,

Bude mata kofar motar anty babba tayi ta shiga ta zauna, yana zaune yasha farar shadda sai
kyalli da maiko take daga gani an kashe naira wurin siyanta...



*_Ummi Shatu_*👌🏻
[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu👌🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*




*_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_



_Dedicated to Maryam Qaumi_💕




*_34_*



aishaummi.blogspot.com




~~~Shima shaddad din kallonta yake yi ta gefen idonshi yana ganin irin dukiyar da aka kashe
ajikinta domin bayaga tsadadden materia din da tasa wasu gwala gwalai ne aka zuba mata
ajikinta tun daga kan sarkar da ke wuyanta wanda Allah ne kadai yasan adadin kudinta zuwa
kan abubuwan hannunta da agogo da zobbuna sannan ga wata yar karamar barima akan
hancinta barimar tayi mata mutukar kyau kamar indiya haka ta fito, ko yaya ta juya kyalli da
walwali take yi wal wal,

"Ina yini..." Yaji ta gaisheshi mamaikon ya amsa sai ya matsa kusa da ita nan kamshin turaren
da yake addabarshi ya sake karuwa,

Bakinshi yakai saitin kunnenta saboda baya son sulaiman ya jiyo abinda zai fada,

"Congratulations, ina tayaki murnar zama matata tafarko da kiyi, sannan kinyi namijin kokari
wajen shiga da fita har kika mallakeni, to ina son nasanar dake abu guda daya,

Kisani kamar yadda kika yi kokarin auren yaro sa'anki to da fatan zaki yi hakurin zama da shi,
zama da yaro sa'anki sai kin jure sannan sai kin daure, saboda zanyi mutukar kuntatawa
rayuwarki ,zan tsananta miki ko kadan ba zakiji dadin zama daniba saboda dama sai da nafada
miki bana sonki bana kaunar zama dake, ke ba irin matan da nakeso bace amma sai da kika
nace kika mayance har nakai ga aurenki,

To kinyi nasara kuma kinyi sa'a sannan zakara yabaki sa'a kin aureni sai dai kuma ina mai
shawartarki da ki shirya zama dani zama na raba raini, ki shirya zama da sa'anki a matsayin
mijinki..."

Shiru yayi sakamakon jin motar ta tsaya har sunzo wurin da za a gudanar da shagalin,

Ita kam maryama duk murnar da take ciki yau sai da gabanta ya fadi hankalinta ya tashi saboda
jin kalaman shaddad, banda cin fuskar da yayi mata harda bakaken maganganu ya fada mata,

Bude kofar barin da take akayi domin ta fito har ta zira kafarta daya zata fita idonshi ya hango
masa sarkar gold din dake daure akafarta ta hagu,

Rikota yayi ya dawo da ita cikin motar ya janyo kofa ya rufe,

"Cire wannan sarkar ta kafarki, ko baki daura ba dama nasan kina hulda da mata kamar yadda
kike yi da maza, basai kin nunawa nawaje koke wacece ba.."

Sunkuyawa kawai maryama tayi batace dashi ko uffan ba ta fara kokarin cire sarkar da take
daure a kafarta, tajima a sunkuye amma ta kasa cirewa,

"Kaga taki ciruwa, nakasa.."

Ta dago tana yimishi magana cikin maganarta mai sanyi hadeda shagwaba shagwaba saboda
ita tsabar gayu da gatan da ta taso aciki maganarta ma gaba daya ta shagwababbu ce,


A zuciye ya kwaye rigar tata wanda ba kwaurinta kadai ba hatta cinyarta sai da ta bayyana jan
kafar yayi wacce ke sanye cikin wani dogon high hill pink colour,yafara kokarin kunce sarkar
amma shi dinma dakyar ya iya kuncewa dan sai da sarkar ta wahalar dashi, nan ya dago da
sarkar a hannunshi yana dubawa,
Inbanda kyalli babu abinda takeyi domin ta gold ce, akan cinyarta ya cilla mata, nan ta dauka ta

saka acikin jakar hannun dake rike a hannunta,

Anty babba ce ta bude kofar motar suka firfito nan tabi shaddad da kallon tuhuma,kasancewar
su sun rigasu tahowa sannan tun dazu itama ta karaso tana jiran su fito amma taga shiru har
sai yanzu da tayi kundunbala ta bude su,

"Kai shaddad meye hakan? Idan kayi hakurima gobe za akawo maka ita amma nan wurin
mutane kazo ka makaleta ka hanata fitowa bayan ga mutane nan sunata faman jiranku"

Shiru shaddad yayi cikeda bacin rai wato ita anty ta zargi ko wani abu ya rike maryama yake
yimata kenan, dan karamin tsaki yaja,

"Inma yanzu daga nan can zaku wuce ku kaita ni babu abinda ya dameni" yafadi acikin
zuciyarsa,

Ganin maryama nagaba yana baya yasa anty babba dakatar dasu,

"Haba haba ai ba haka akeyi ba"

Janyo shaddad tayi zuwa wurin maryama ta sakala hannunta cikin nashi ta rab'ata da gefen
kirjinshi,

"Yawwa kunga yanda akeyi,ai haka ya kamata kuyi tunda an rigada an daura muku aure da ba
adaura bane shine, kai shaddad ka ruketa fa sosai saboda wannan dogon takalmin nata
wahalar tafiyane dashi idanma tazo da tsautsayi zata iya faduwa.."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login