Showing 9001 words to 12000 words out of 64131 words

Chapter 4 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf

12 Mar 2025

5620

azaune ta cika tayi fam sai ga Joseph yashigo yace ta fito anzo daukarta, hada
mata kayanta yayi ya fita, sai da ta gama bata lokacin ta son ranta sannan tafita ta na aikin
yatsina fuska,

Yana zaune da farar riga mai gajeren hannu da wandon sojoji ya kunna radio yana sauraren
wani programme na ban dariya,tafito kenan sai ga dr naz shima yana fitowa zai wuce zuwa
theatre, kallonta yayi yana karasawa kusa da ita,

"Sai yanzu?" Yafada cikin tsokana,

"Wallahi tun dazu nake jiran driver amma wai bai zoba sai yanzu"

"Hakuri zakiyi maryama sarauniya.." Yafada yana kokarin gyara mata barimar gold din dake kan
hancinta saboda yaga ta dan zamo kamar zata fadi, duk abinda ke faruwa akan idon shaddad
ne dama tuni zuciyarsa tafara zargin cewar maryama tana bin maza ko kuma tana
lesbian,wucewa tayi bayan dr naz ya gama gyara mata barimar wacce ta kasance mai kirar star
sai walwali take,

Bude gaban motar tayi ta shiga ta zauna batare data kalleshi ba, shima tun kallon farko da yayi
mata lokacin da zata shigo bai sake kallonta ba,

Shi Kadai yake murmushi yana driving saboda abin dariyar da yakeji, hannu maryama tasa ta
kashe radion saboda har kanta yafara ciwo, sam bata son radio domin bata kaunar hayaniya a
lamuranta,

Sake kunnawa yayi ta sake kashewa domin aganinta wannan ma ai rainin wayone, ita da
motarta har ya tsaya yana yimata abinda yake so,

"Kai Malam bafa motarka bace tawace so baka da hujjar da zaka takura min..." Tafada akufule
domin dama can ranta abace yake sai gashi kuma yasake kunnota,

"Tabbas nasan ba mota ta bace amma ya zama tilas nayi abinda nakeso da ita ahalin yanzu
tunda a hannuna take.."

Tsaki taja ta juyar da kanta tana jin haushin sa saboda ya takurawa rayuwarta da yawa,

"Karki sake yimin tsaki dan ba ayimin tsaki kin gane? So respect your self..."

Rabuwa tayi dashi ta zaro iPhone dinta daga cikin hanbag dinta ta jona earpiece tasaka acikin
kunnuwanta ta toshe, tana jinsa yasake kunna radion,

Sai da tabari sun kusa zuwa barikinsu sannan ta sake bata fuska tace,

"Namanta ina son shiga kasuwa zan yi siyayya.."

K'uluwa shaddad yayi saboda wannan rainin hankalin nata yayi yawa, yarinyar da batafi sa'ar
kanwarshi ba itace zata rinka kokarin dole sai ta juyashi kamar wani waina acikin tanda,

"Hello father, ina son zuwa kasuwa, ka fadawa driver ya kaini"

Yajiyota tana magana da alama mahaifinta ta kira,

Tun kafin Dada ya kirashi yayi ribos ya juya ya nufi yoroba market domin itace tafi kusa
dasu,kiran mahaifinta ne ya shigo cikin wayar shaddad,

Yana dauka yaji yafara rokonsa akan ya yi hakuri yakai maryama kasuwa,amsawa yayi da
cewar ai sunma kusa zuwa kasuwar, katse wayar yayi ya mayar da ita cikin aljihun wandonshi,

"Bana zuwa wannan kasuwar domin abinda nake nema ba asayarwa anan.." Tafada fuskarta
atamke ranta ahade,

"Ke ni ba sa'anki bane kuma ba drivern ki bane, kar ki rainamin hankali" yace da ita cikin zafin
rai,

Fusgar motar yayi suka koma baya ya nufi wata kasuwar daban ransa abace,

Handbag dinta ta balle ta ciro wani chewing gum kato ta bare ta jefa cikin bakinta tafara tauna
ahankali babu abinda kakeji sai k'as k'as,

Agefen titi yaja yayi packing saboda babu hanyar da mota zata shiga, bude motar tayi ta fita
tana rike da handbag dinta earpiece makale a kunnenta, farin medical glass dinta ta ciro tasaka
duk yana kallonta ta glass, sai taunar chewing gum take tana yin k'wai sai kuma ta fasashi tush
taci gaba da taunar chewing gum din, titi ta tsallaka tana rike da high waist dinta data dage
gudun kada ta kwashi datti dan haka duk k'waurinta awaje suke ga wani dogon takalmi dake
kafarta amma kasancewar tasaba tafiya dashi takunta take yanda take so....


*_Ummi Shatu_*👌🏻
*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*




*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



_Dedicated to Maryam Qaumi_💕


_*9*_


aishaummi.blogspot.com

~~~~D'an karamin tsaki shaddad yayi lokacin da yaga shigewarta cikin kasuwar,

"Yarinya kamar karuwa, komai nata irin na yan tasha, in banda tsabar duniyanci menene nata
na shiga kasuwa tana taunar chewing gum?" Yayi wannan maganar acikin zuciyarshi,

Tunda ta shiga kasuwar bata fitoba sai da ta shafe fiyeda mintuna 20,duk yagama kosawa da
jiranta sai faman tsaki yake yana bin hanyar da kallo domin ganin kota taho sai yaga shiru, yana
nan zaune ya hangota ta fito tana ta faman taunar chewing gum dinta tana yin k'wai amma
taunar chewing gum dinma cikin yanga da kinibibi take yi,k'ura mata ido yayi yanda take tafiya
tamkar bazata taka k'asa ba saboda tsananin yanga, gashin kanta duk awaje kasancewar
mayafin data yafa akanta bai gama isarshi ba,

D'auke idonshi yayi daga kanta aranshi yana jaddada tabbas mace mai kyau fitinace a duniya,
yanzu kamar maryama yanda take da wannan tsananin kyau din da rashin kamun kai ai Allah
ne kadai yasan yawan adadin mazan dake kwadayin kasancewa da ita,

Bude gaban motar tayi ta shiga ta zauna ta rufe tana mai cigaba da taunar chewing gum dinta,
kallon ledar dake hannunta shaddad yayi saboda yana son ganin abinda ta siyo wanda har ta
dade haka, sugar cane yagani acikin ledar an daddatsashi, mamakine da haushi suka kamashi
saboda ganin yanda ta b'ata masa lokaci ta zaunar dashi gashi har lokaci ya kure yasan bazai
samu salla a jam'i ba domin kafin su koma har an idar,

Cikin bacin rai ya yiwa motar key yahau titi, ita kuwa sarauniyar sai aikin latsa iPhone dinta take
tana taunar chewing gum, chaten take da dr naz wanda har yanzu yana asibiti bai tasoba amma
yace yau zai zo hira wurinta,

Har suka shiga barek din shaddad bai ko kalleta ba domin haushi take bashi tunda yazo garin
nan bai taba rasa salla a jam'i ba sai yau ta dalilinta,

Bude murfin motar tayi zata fita, juyowa tayi ta kalleshi,

"Kajira blessing tazo ta daukar min kayana sai kaje kasaka motar cikin garage.."

Sake harzuka yayi ya kashe motar ya fito ya rufeta yace da ita,

"Ungo key dinki.." Bai jira amsarta ba ya wulla mata mukullin yayi gaba ranshi abace,kallo
tabishi dashi ganin komai nasa yana yinsane cikin zafi zafi da zafin nama,

Bata damuba tawuce ciki tana yatsina fuska,

Blessing ce ta sauko da sauri tana rikeda duster a hannunta wacce ta kammala goge glasses
din dake jikin window din dakin maryaman,

"Karbi key dinnan kije cikin motata ki dauko min kayana, akwai sugar cane idan kin kawo kisa
minshi cikin fridge" abinda tafada kenan ta wuce sama, tana zuwa ta shiga wanka duk ranta
abace yake saboda gadarar da shaddad yake nuna mata gamida wulakancin da yake son rinka
yimata ako yaushe,
Ruwa ta sakarwa kanta tayi wanka mai kyau tafito, wasu kananan kaya ta tarar blessing tafito
mata dashi,farar riga yar karama body hug da farin wando three quarter, pant kadai tasaka ta
zira kayan tafesa turare ta fita bayan ta saka silifas dinta,

Fridge taje ta buda ta ciro robar coke guda daya ta nufi bedroom dinta, drewar din jikin gadonta
ta bude ta ciro takardar wasu kwayoyi ta debi guda biyu ta jefa cikin coke din sannan ta sauka
kasa da robar coke din a hannunta tana sha,

kan dining taje ta zauna domin ganin abinda kuku ya girka musu yau, white rice & stew tagani
sai ko hadadden salad da aka hada agefe sannan ga dafaffen kwai nan agefe, shinkafar ta dan
diba spoon uku tasaka miya amma ta zuba salad din da yawa sai dafaffen kwai data saka guda
biyu, fara ci tayi sai dai kuma dakyar ta iya cinyewa abincin data hada,
Coke dinta ta shanye ta tashi takoma sama ta kwanta sai a lokacin ma ta tuna da cewar ashefa
batayi sallar azahar ba bare la'asar kuma gashi yanzu har ankusa yin isha, kwanciyarta tayi ta
mike ta lumshe idanunta.

Tunda ta kwanta ta dan samu bacci ba ita ta tashiba sai karfe 8,dan siririn gyale ta dauka irin
wanda tasaba yafawa tafita zuwa falon Dada,

Zaune ta sameshi kafarshi dore kan wani tumtum saboda ciwon kafar dake damunshi,

"Sannu dada, ciwon kafarne?" Tafada tana karasawa inda yake,

"Yawwa sannu mai sunan mama..." Dada ya amsa mata yana kallonta,

Agigice ta zauna akusa dashi tana kallonsa saboda yanada ciwon sugar sannan wannan ciwon
kafar ma yadade yana fama dashi, itama kusan tayi gadon ciwon saboda tana fama dashi lokaci
zuwa lokaci,

"Dada kodai sugar dinka ya hau ne?"

"A'a daughter lafiya lau fa nake"

Tashi tayi ta nufi dakinsa domin dauko na'urar gwaji wadda ta tanada musamman domin gwada
mahaifin nata,

Tana fitowa taganshi zaune shida shaddad yana duba wasu takardu,

Agaban dada taje ta zauna ta ciro na'urar ta fara gwadashi, ajiyar zuciya ta sauke ganin sugar
din bai hauba hakama jininsa shima bai hauba kawai dai ciwon kafarne ya tashi,

Mikewa tayi taje ta mayar da na'urar sannan ta dauko masa maganin da yake shafawa a
kafarshi ta dawo falon ta zauna ta bude maganin tafara shafa masa a kafafunshi, shaddad yana
kallonta ko kunyar fitowa ahaka bata ji,

Cigaba da Shafa maganin tayi tana ma mahaifinta magana ahankali,

"Father tunda kafar nan ta matsa kawai kaje saudiyya this time kar kaje chairo"

Murmushi Dada yayi yasake gyara zamansa,

"To daughter yanda kikace ai haka za ayi, insha Allah nanda 3 weeks zan nemi visa sai intafi"


Ahankali take murza masa maganin akan yan yatsunshi tana jijjiga kai cikin kulawa,

"Dada dan Allah ka rage cin tuwon semo dinnan, kaga yanzu sugar dinka normal yake Bai hau
ba bai sauka ba"

"To mai sunan mama insha Allah za arage"

Mikewa tsaye tayi tana cewa, "yawwa father, ni shiyasa kullum cikin exercise nake saboda ban
son nayi gadon wannan ciwon sugar din naka..."

Fita tayi daga cikin falon taje bedroom dinta ta dauko key din motar ta, falon ta koma ta mikawa
shaddad key din,

"Am gashi ka saka min motar acikin garage.."

Kamar bazai karba ba sai kuma ya karba saboda nauyin idon mahaifinta da yakeji domin
yajashi ajiki koda yaushe nunawa yake shi danshi ne ba bare ba,

Juyawa tayi ta fita aranta tana cewa "kai din dai kaine zaka dauke motar daga inda ka ajiyeta"

Bedroom dinta ta koma ta sake gyara fuskarta ta feshe jikinta da turare saboda dr naz yazo,
ayanda take dinnan ahaka ta fito zata fita wurinshi babu abinda ta kara, daga ita sai body hug
din jikinta da wando three quarter iya gwiwarta sai dan siririn karamin gyalen data warware ta
dora akanta sabanin da dayake adaure akanta ga wani sanyayyen kamshi dake fita daga jikinta,

Afalon kasa suka hadu da shaddad shima da alamar fitar zaiyi, batare da ya kalleta ba yawuce
abinshi bin bayanshi tayi tana latsa wayarta amma kafin taje waje har ya dade awurin shi,

Ya bude kofar motar kenan yaganta ta fito ahaka ta nufi wata mota dake fake a gaba kadan da
wurinda ya ajiye mata motarta, mamaki ne yaketa dawainiya dashi tun lokacin da yafara ganinta
saboda dabi'unta mabanbanta ne da sauran matan da ya saba gani, in banda rashin tarbiya
yaushe mace zata iya fita ahaka?
Motar ya shiga ya tadata ahankali ya nufi cikin garage din domin adanata lokacin tuni har
maryama ta bude gaban motar dr naz ta shiga ta rufe ruf......




_Gaisuwa mai tarin yawa ga baby Lilmeerahcute..!!_


*_Ummi A'isha_*👌🏻

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_
💕
*_10_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Ahankali ya fito daga cikin
motar ya rufeta zuciyarsa na tir da
halaye irin na maryama domin tun
lokacin da yafara ganinta babu
wani abu guda daya da zai iya
tunawa wanda ya kasance mai kyau
data aikata sai dai sabanin haka,
Motar dr naz ya nufa yana zuwa
yafara knocking din glass din saitin
da take amma shiru sai da yayi
kusan sau biyar sannan ahankali
yaga glass din yana yin kasa,
Hangota yayi jingine jikin kujera
tana kallonshi amma ta kasa
magana, cilla mata key din yayi
cikin motar ya juya ya tafi batare da
yace komai ba saboda ko ba afada

masa ba yasan yanayin da ta shiga
wanda har yasa ta kasa yimasa
magana,
Tsaki yayi ya waiwaya domin yajiyo
karar tashin motar dr naz din, su
dinne shida ita suka fita a mota da
alama wani wurin zasuje,
Wani dogon tsaki yaja yana mai
kara jin tsanarta acikin ranshi,
"To yanzu ina zasuje acikin wannan
daren?" Ya tambayi kanshi,
"Yawon shedancinsu mana" wata
zuciyar tasake bashi amsa,
Hannayenshi duka ya zira cikin
aljihunshi ya nufi gida yanata
faman tunanin irin rayuwar da
maryama ta zabarwa kanta indai
kuwa hakane to tayi kyan banza,
tayi kyan dan maciji, da wannan
tunanin yaje gida ya bude ya shiga.
***
K'arfe 11:30 daidai maryama ta
sauko cikin shirinta na fita office,
wata kyakkyawar hadaddiyar
doguwar riga Arabian gown ce
ajikinta, coffee colour mai adon
stones ajiki ta dan dora dan siririn
mayafinta akanta, wani cover shoe
mai mutukar tsini ta saka coffee
colour, babu abinda kakeji sai
kamshin tuarukan data bulbulawa
jikinta wanda ya gauraya yabada
wani daddadan kamshi na
musamman,
Tana tafe tana gyara barimar kan
hancinta harta ida saukowa,
shaddad yana tsaye shida kukunta
wanda yake rike da lunch box dinda
ya hada mata abincinta kamar
yadda ya saba,
Fuska ta dan yamutsa ta dubi kuku,
"Me ka dafa min yau?"
"Tea na dafa miki sannan kuma na

soya miki chips.."
Girgiza kai tayi, "yau bazan ci chips
ba, plantain nake son ci dan haka
kasan yanda zakayi da wannan
chips din ka koma kitchen ka soya
min plantain anjima driver zai dawo
ya karba after yayi dropping
nawa..."
Daga ido tayi ta kalli shaddad
bayan kukun yabar wurin, fuskar
nan tashi ko alamun murmushi
babu tana nan awani murtuke
ahade kamar wanda aka aikowa da
sakon mutuwa,
"Idan kafito da motar muje ko.."
Tace dashi bayan tafara tafiya,
"Idan natafi to kisani bawani
dawowa da zanyi na karbar miki
abinci kwara ma ki tsaya ki tafi da
abinki saboda ni ba bawanki bane"
Tsayawa tayi cak saboda jin abinda
shaddad yafada, juyawa tayi da
niyyar ta mayar masa da martani
amma sai ta kasa saboda
kwarjininsa da ya cika mata ido,
dole ta koma falon ta nemi kujera
ta zauna ta dauki wayarta tana
latsawa tana jan dan siririn tsaki,
Tana nan azaune shikuma yana can
tsaye har kukun ya fito da alamu ya
kammala, tashi tayi ta fara tafiya
batare da ta jira abinda kukun zaice
ba,
Kusa da motar taje tana jiran
karasowar shaddad, tun daga nesa
ya kamata ya bude mata amma
baiyi hakan ba har saida ya zo
gaban motar, lokacin ne ya bude ya
shiga, itama shigar tayi fuskarta
babu walwala ko kadan saboda
wannan guy din ya gama rainata
tarasa dalili,
Fisgar motar taji yayi bayan kuku

yagama zuba mata kayanta abaya,
babu shiri taja belt ta daura domin
ta fahimci zata iya buguwa da
gaban motar mutukar bata daura
belt ba,
Yauma radio ya kunna yana sauraro
yayinda ita kuma taji ta takura, kai
alla alla ma take yaje ya sauketa
yakama gabansa domin yagama
takurata,
Wurin wasu sojoji suka tsaya
wanda ke tsaye agefen titi suna dan
yin checking, I d card dinshi ya ciro
ya nuna musu ya ajiye agefenshi
bai mayar aljihu ba, bude motar
yayi ya fita bayan yayi packing
agefen titi,
Haushine yakama ta saboda ganin
sai bata mata lokaci yake yi alhalin
ita kuma tanada abinyi, tsaki taja ta
juyar da kanta tana tunanin to ina
yaje yabarta acikin wannan zafin
haka?
A.c ta kunna sai kuma idonta ya
sauka akan id card dinshi, dauka
tayi tafara dubawa,
SHADDAD A SADIQ shine cikakken
sunansa,
Date of birth dinshi ta kalla bakinta
abude saboda tsananin mamaki,
"28 years? Dama duk wannan rainin
wayon nasa 28 years yake shine
zai rinka yin abu kamar wani ubana,
mtswwww ashema age mate
dinane, to daga yanzu nadaina jin
tsoronka wallahi.."
Ta mirror ta hangoshi yana tahowa
dan haka tayi gaggawar ajiye I d
card din tasake daure fuska taci
magani ta ciro medical glass dinta
ta sa tadauki phone dinta tasoma
latsawa,
Bude kofar mortar yayi ya shiga ya

zauna ya figeta, ko dagowa batayi
ta kalleshi ba wayarta kawai take
latsawa jin ya kunna radio yasata
kashewa,
Bai ko bita kanta ba yaci gaba da
driving dinshi har suka shiga
asibitin, yana packing ta sake bata
fuska,
"Ka tabbatar kadawo daukana da
wuri saboda akwai inda zanje da
yamma bayan natashi daga aiki"
Ko kulata ma yayi balle tasa ran
samun amsa daga gareshi, hakan
da yayi yasake sata jin haushi,
"Kai dakai fa nake magana",
Mamaki abin yabashi jin ta kirashi
da kai sai kace wata uwarsa lallai
yarinyar nan bata da kunya,
Da karfi ta rufe kofar ji kake
gummm ta nufi office dinta bayan
Joseph ya taho dibar mata kayanta,
"Na hadu da shu'umin driver ni
maryama" tafadi hakan acikin
zuciyarta,
Ranta abace fuskarta babu walwala
ahaka ta kammala duba patients ta
nufi round, kasancewar ma yau
bata samu patients da yawaba da
wuri tagama,
Tana fitowa sukayi kicibus da dr
Sameer dama wurinta ya doso,
"Maryama sarauniya azo atayani
aiki mana..!" Yafada tareda
langabar da kansa,
Dan murmushi tayi ta kalli
fuskarshi,
"Baka gama ganin patients din
bane?"
"Ai maimakon raguwa karuwa ma
suke yi wallahi gashi yau dinnan
natashi da ciwon jiki"
"Ayya sorry, to muje"
Jerawa suka yi zuwa office dinshi

suka shiga kowannensu yaja kujera
ya zauna patients suka fara
shigowa suna dubasu, suna yi suna
hirarsu har patients din suka kare,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login