Showing 15001 words to 18000 words out of 64131 words
Chapter 6 - Maryama Sarauniya Book Complete by Ummi Aisha .pdf
Lallai yarinyar nan yar duniyace ta karshe, ko kunya bataji take
fadin cewa ta zauna daki daya da namiji,namijin da mijinta ba sannan ba muharraminta ba"
shaddad yafada acikin zuciyarsa, nan yasoma hango irin dukan da zaiyi mata da ace kanwarsa
ce ita,
Jijjiga kai yayi yaci gaba da tukinshi baima san lokacin data gama wayarba, har sukaje asibitin
bai kalli saitin datake ba saboda yaki jinin kallon fuskarta,
Bude motar tayi tafita tana takawa cikeda rangwada, yana zaune yana jiran azo a daukar mata
kayanta har Joseph yazo ya kwashi kayan ya tafi,
Fisgar motar shaddad yayi ya tasamma head quarter dinsu ta sojoji yana zuwa yasamu Abbas
wanda aka daukesu tare kuma tare sukayi passing out dashi,
"Abbas nifa nakusa barin garin nan, gaskiya dole nanemi canji saboda zaman garin nan bai
dace daniba"
Dariya Abbas yayi ya kama hannun shaddad,
"Haba Navy, wai Kai sai yaushe idonka zai bude ne? Kai da yakamata kayi murna saboda
ankawoka nan babu wanda kasani babu wanda ya sanka kaci karenka babu babbaka"
"Wallahi bazan iyaba, nidai kawai burina nasamu transfer domin rayuwar mutanen nan kwata
kwata bata dace daniba"
Matsawa abbas yayi kusa dashi yafara magana ahankali,
"Naga wata sarauniyar kyawawan mata agidan oga ance yarshi ce, meyasa bazaka shigar da
kanka wurinta ba kasamu ka kwashi rabonka.."
"Allah ya sawwaka wallahi, me zanyi da ita? Yarinyar da bata da maraba da karuwa.."
"Ai wayewar kenan Navy, kaine bazaka ganeba"
Shaddad bai sake magana ba yabar wurin domin yasan idan zancen yayi nisa to ranshi ne zai
baci a banza.
K'arfe biyar daidai yaje dauko maryama, yanata zaune zaman jiranta ga kayanta Joseph ya
kawo amma ita din kuma taki fitowa, fitowa yayi a fusace ya nufi office din nata saboda yafi minti
goma sha biyar yana zaman jiranta,
Ko izini bai nemaba ya bunka kai cikin office din, tsaye yaganta tana gyara rigar jikinta gefe
kuma dr naz ne yake tsaye yana gyara belt din wandonshi,
Hada ido sukayi shida ita ya sakar mata wata muguwar harara sannan yaja kofar da karfi jikake
gammm ya rufe ya tafi,
Cikin halin ko in kula suka fito itada dr naz yana mai gyara necktie din dake daure a wuyanshi,
Ko a kasan takalminta babu kunya ta bude motar ta shiga kafin ta rufe kofar tuni har shaddad
ya figi motar yayi gaba, sake jin kyamarta yayi saboda abinda idanuwanshi suka gane masa
yanzu,
Suna zuwa gida yasake ganin wani ikon Allah domin fahad ne yazo wanda take kira da room
partner dinta, hannunta cikin nashi suka shiga cikin gidan, wanka kawai tayi ta shirya cikin riga
da wando tafito zasu fita club ita da fahad din,coke mai sanyi ta dauko ta ciro wasu kwayoyi
guda biyu ta jefa aciki tareda ballo wasu manyan tablet guda biyu ta afa abakinta ta korasu da
coke,
"Kefa yar kwayace har yanzu ashe kina sha.." Fahad yace da ita yana murmushi,
"Ai dole sai da tsaro room partner, yaushe zan daina? Ai na kariyane ko ka manta"
Dariya suka saka dukkaninsu harda tafawa taja hannunshi domin tafiya, duk wadannan
maganganun a kunnen shaddad suka yisu nan yabisu da kallon takaici.......
_*Ummi Shatu*_í ½í±Œí ¼í¿»
[5/7, 8:20 PM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
*_13_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Bin bayansu da kallo shaddad yayi cikeda tsana da kyamatar hali irin nasu,
Janye jikinsa yayi yakoma ya nufi gida batare da ya shiga koda gidansu maryaman ba.
Abangaren maryama kuwa tunda suka fita cinema suka fara zuwa itada fahad suka yi kallo na
dan wani lokaci daga nan kuma suka fito suka tasamma club nan suka dade suna hirarsu
sannan suna ganin abubuwan dake faruwa awurin,
Sai da misalin karfe 12 nadare harda yan mintuna sannan suka nufo gida, suna tafe suna
hirarsu itada fahad wani lokacin idan hira tayi dadi har tafawa suke yi,
Gida ya kawota ya sauketa sannan yakoma domin zuwa masaukinsa wato murna hotel.
Washe gari da safe maryama ta sauko kasa ta shiga kitchen tana tsarawa kuku irin abubuwan
da take son ya shiryawa fahad na karyawa,
Daki ta koma ta shiga wanka tafito tasoma shiryawa, fahad ne yayi mata waya cewar ya karaso
gidan dan haka tabashi izinin ya karasa dakin ya sameta,
Kayanta ta saka green din t shirt da skirt high waist ja,
Tana kokarin daura sarka a kafarta fahad ya turo kofar dakin ya shigo,
Murmushi ya aika mata dashi itama ta mayar masa da martani,
"Kinyi kyau sannan kinyi min laifi fa maryama.."
"Nagode fahad, laifin me kuma nayi maka?"
"Tunda nazo gidan nan baki hadani da dady dinki ba why?"
Murmushi tayi ta dauki dan karamin gyalenta ta yane kanta dashi ta juya tana kallonshi,
"Haba fahad kai ai ba bako bane agidan nan kazama dan gida, jiya lokacin da kazo dada baya
nan yaje abuja sai asuba suka dawo, so yanzu after kayi breakfast zamuje ku gaisa.."
"Yawwa ko kefa sarauniyar mata, nagode da wannan damar da kika bani"
Murmushi ta saki na kasaita takama hannunshi suka fara saukowa daga kan matattakalar bene
suna gangarowa kasa, daidai lokacin kuma shaddad shima yasako kai ya shigo cikin falon,
Dauke kai maryama tayi tasake makale hannun fahad acikin nata tana murmushi,
"Fahad kafata ciwo take wallahi.." Tafada cikin yatsina fuska,
Kan dining table suka karasa yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna kusa da ita,
"Maryama ciwon kafar nan nakifa akwai matsala, tun jimawa nafada miki"
Kallonshi tayi tana tsiyayar tea acikin wani dan karamin glass cup,
"Kai ai fahad maganarka bata da alaka da ciwon dake damuna, nafada maka dada ma haka
yake fama dashi shiyasa last time nace mishi yaje saudiyya yaga dr.."
"Ayya to Allah yabashi lafiya, amma ke din dai yakamata nayi checking dinki before natafi"
Yace da ita yana dan murmushi kasancewar shima likitan matane, jin tayi shiru yasashi soko
wani zancen,
"Maryama wai sai yaushe kika shirya aurata ne? Nafada miki dad dina ya matsa min da
maganar aure nikuma kece macen da nake son mallaka a matsayin mata..."
Shiru tayi ta kura masa ido tana kallonshi yayinda shi dinma itan yake kallo, dan kyau fahad
kyakkyawa ne sannan ga aji gashi dan masu kudi, to ita matsalar shine yayi mata yaro dayawa
domin shi dinma irinsu dr naz ne yara, ita kuma a burinda take dashi tafi son auren namiji dan
shekar 35 zuwa 40 aganinta kuma a ra'ayinta shine daidai da ita amma wadannan mitsi mitsin
yaran ina zasu kaita?,
Pork ta dauka ta cakulo dankali takai bakinta tana kallonshi,
"Haba maryama say something please..."
Batare data zare cokalin daga bakinta ba ta langwabar da kanta gefe tana yimasa murmushi,
Ita gaba daya ma bata san auren namijin da yake yawan mu'amala da mata shiyasa duk taki
auren doctors din asibitin su dake tururuwar sonta, shi kansa fahad din bata da sha'awar
aurenshi saboda likitane yana mu'amula da mata sosai.
Hannunshi yakai ya rike pork din ya cireshi daga cikin bakinta,
"Nadai fahimci kawai ni dinne baki so ko maryam?"
Girgiza masa kai tayi tana murmushi,
"Ba haka bane fahad, yanzu dai kaci abinci idan kakoma gida zamuyi magana through call.."
"Hmm kullum dai haka kike cemin gaskiya nafara kosawa da wannan jan ran da kike yimin.."
"Haba fahad nace zamuyi magana, yanzu kaci abinci kawai.."
Badan yasoba haka ya hakura yaci gaba da cin abincin har suka kammala tayi masa jagora
wurin dada suka gaisa lokacin shaddad yana zaune suna yin brreakfast in banda harara babu
abinda ke hadashi da maryama har shi fahad dinma ji yake ya tsaneshi, fahad ne yatashi zai fita
domin tafiya nan maryama tabishi ta rakashi,
Hannunta ya kama yana kallonta,
"Wancan guy din waye shi?"
Tab'e baki tayi, "driver nane.."
"Wai dagaske?"
"Dagaske mana, wani abune yafaru?"
"A,a babu komai"
"Shikenan tunda babu komai, sai munyi waya.."
Sakin hannunta yayi ya wuce ya nufi motarshi, tana tsaye awurin har saida taga fitarshi sannan
ta koma cikin gida,
Takalmi tasaka tafita da wayarta a hannu ta shiga falon Dada tana yiwa shaddad kallon tara
saura kwata,
"Father bari naje asibiti.."
Cikin fara'a da kulawa ya kalleta, "adawo lafiya mai sunan mama, Allah yabada sa'a"
"Amin father, thank you" tafada tareda mikewa tana kallon shaddad,
"Am muje ko"
Bai ko kalleta ba ya mike yayi gaba ta mara masa baya, so take ta kamoshi amma takasa
domin kafin tayi taku daya shi yayi biyar, babu shiri ta hakura domin har tafara yin haki,
Motar ta shiga ta zauna tana dan daddanna kafafunta dake yimata ciwo,blessing nagama ajiye
kayan shaddad ya fisgi motar, idanuwanta ne suka sauka akan hannuwanshi dake rike da
sitiyarin motar,fatarshi luwai luwai take gwanin kyau ga gashi kwance ajiki, dauke idonta tayi
daga kallonshi, har sukaje asibitin bai kalleta ba asalima lokacin da yayi packing kawar da
kanshi gefe yayi har saida ta fice.
Da daddare misalin karfe 7 tace tana son zuwa stadium kallon ball, wata harara ya cilla mata
sannan yayi magana,
"Ke nifa ba dan iska bane kin gane? Ki nemi mai kaiki stadium amma baniba.."
Dada tayiwa waya ta fada masa shikuma ya kira shaddad yace ya kaita, bama stadium ba duk
wurinda take so ya rinka kaita,
Matsu tasha cikin jeans da t shirt da bakar hula facing cap,tasha bakin combos tafito, yana
kallonta ta mirror din jikin motar lokacin da take tahowa,
"Karuwar banza karuwar wofi, Allah ya wadaran halinki" yafadi hakan acikin zuciyarshi,
Shiga tayi ta zauna tana faman taunar chewing gum, ko kallonshi ita dinma batayi ba ta dauke
kanta tana kallon mirror,
Kaita stadium din yayi ya zauna acikin mota yana jiranta, sai wurin karfe 8 sannan aka gama
wasan ya dauketa zasu koma gida,
"Ina son zan sai plate din wrestling" tace dashi tana tauna chewing gum din dake bakinta, bai
bata amsaba amma ya nufi wurinda zasu iya samun Kaset din sai dai mamaki ya kamashi
mutuka, shin ita wannan yarinyar wai duk dabi'unta irin na mazane? Itace kallon kwallo itace
hawa bike itace kallon wrestling to ko shi da yake namiji ma wadannan abubuwan basu
dameshi ba amma ita tana mace tana abubuwa irin na maza, da kanta tafita ta siyo Kaset din ta
dawo cikin motar ya maida ita gida.
Haka rayuwar taci gaba da tafiya atsakaninsu kullum shaddad ne ke kaita office ya daukota
sannan wani lokacin kuma har club yake kaita, yau ma akan hanyarsu ta dawowa daga asibiti ta
yamitsa fuska tana yi masa magana,
"Anjima zaka kaini stadium da karfe 6"
Bai amsa ba dama tasan ba amsawar zaiyi ba, tana komawa gida ta shirya tana jiransa bai
zoba gashi dada baya nan yatafi saudiyya ganin likita,
Cika tayi fam saboda tasan tayi missing din wannan wasan, karfe 8 shaddad din yazo ganin
haka yasata fita tace yakaita club saboda bata son ta kyaleshi haka bai wahala ba duk tsiya dai
sai ta fitar dashi awannan daren koda baya so,
Baiyi musuba ya dauketa suka fita zuwa club din, sanye take da wani damammen wando da
riga body hug ita dinma ta kamata sosai, dan karamin gyale ta dora akanta kawai daga nan
bata kara komai ba,
Lokacin da sukaje club din packing yayi tafita ta shiga ciki shikuma ya zauna acikin motar ya
kunna radio yana sauraren wa'azi.
Maryama na shiga cikin club din taganshi cikeda maza da yanmata ashe wasu students ne yan
university suke party awurin, tunda ta shigo samari ke kallonta domin ta hadu tayi awon gaba da
imaninsu,
Can tasamu wuri ta zauna, diffff aka dauke wuta kafin tayi wani motsi tuni har an toshe mata
baki anyi sama da ita, kokawa take iya karfinta domin kwatar kanta amma takasa kasancewar
mazan da suka rufu akanta sunfi biyar,
Can bayan club din suka kaita suka ajiye sannan suka fara kokarin aiwatar da mummunan
kudirinsu akanta....
_Wayyo maryama maza zasuyi mata aika aika.._
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/9, 9:42 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*
_Dedicated to Maryam Qaumi_í ½í²•
*_14_*
aishaummi.blogspot.com
~~~Rufuwa samarin suka yi akanta suna kokarin rabata da sutturar dake jikinta, jin idan batayi
dagaske ba zasu cimma manufarsu akanta yasata dagewa ta ciji hannun wanda ya toshe mata
bakin babu shiri yayi azamar sakinta, wata kara mai karfi ta k'walla tareda kiran sunan shaddad
akaro nafarko acikin rayuwarta,
"Shaddad...." Tafada cikin karaji,
Shaddad yana cikin mota zaune sai kunnensa yajiyo karar da maryama ta kwalla, bai gasgata
cewar itace ba har sai da yaji ta ambaci sunanshi, cikin azama ya fito daga motar ko kulleta bai
tsaya yiba ya nufi inda yake jiyo sautin muryarta, gashi ko ina na club din duhune dim babu
haske ko kadan sai ko na farin wata,
Bayan club din ya nufa jikinsa har wani rawa yake saboda tsananin gigita, yana zuwa ya iske
samari fal sunyi mata runfa har sun kusa rabata da sutturar dake jikinta, bindigarsa ya ciro ya
harbi sama ji kake, tauuuu...!!
Babu bata lokaci samarin suka baje kowa yayi ta kansa, maryama dake kwance sai faman
kankame jikinta take yi ta samu ta mike da kyar sai layi take tana tangadi kamar wacce tasha
kayan maye,
Ko kallonta baiyiba ya juya yafara tafiya, da saurinta tabi bayanshi batare data tsaya daukar
gyalenta ba wanda yafadi awurin,
Jikake garammm lokacin da ya shiga motar ya rufeta,
"Washhhh...!" Tafada tana runtse idonta bayan ta danna kafafunta domin dama can ciwo suke
yimata kuma gashi yanzu an tattaka mata su,
Kallonta yayi zuciyarsa na radadi da tafarfasa wanda bai san dalili ba,
"Sunyi miki wani abune?" Ya tambayeta yana kallonta cikeda tsana,
Kai ta girgiza masa alamun a'a, bai sake magana ba ya kunna motar suka bar wurin,
Tsaki yaja mai karfin gaske sannan yafara magana cikin zafin rai,
"Ni ban taba ganin mahaukaciya, marar tunani, jahila, marar kamun kai irinki ba, kowacce mace
tana adana halittar da Allah yayi mata, tana kare mutuncinta amma banda ke, ke kullum burinki
shine ki bayyanar da surar da Allah yayi miki..."
Dauke kanta tayi alamun maganganun nashi basu shigeta ba, nan yaci gaba,
"In banda iskanci da rashin ilmi da rashin sanin yakamata ina macen kirki da zuwa club, mace
indai ta arziki ce babu abinda ya danganta ta da club, idan kina ganin hakan kamar wayewa ne
ko kuma wata burgewa ce to wallahi kinyi kuskure domin ba hali ne mai kyau ba, duk macen
dake zuwa wannan wurin karuwa ce..."
Cikin razani ta juyo tana kallonsa lokaci guda fuskarta ta sauya,
"Wacece karuwan??"
Ta fada cikin bacin rai da masifa,
"Ke mana, keda mecece idan ba karuwa ba, bakida maraba da karuwai..."
Nunashi tayi da yatsa, "karka kara kirana da karuwa.."
Packing din motar yayi agefen titi ya juya yana kallonta cikin bacin rai,
"Idan ankiraki da karuwan me kika isa kiyi? Kinada wani sunan ne bayada wannan? Ke
karuwace cikakkiya..."
"Naji ni karuwace amma da kanwarka ko yayarka muke karuwancin tare..."
Tun kafin ta karasa rufe bakinta ya dauketa da wani gigitaccen mari wanda yayi barazanar
makantar da ita domin lokaci guda ta nemi ganinta ta rasa sannan taji kanta ya dauki ciwo yana
barazanar barin jikinta ga wani jiri da yafara daukarta,
Nunata yayi da dan yatsa,
"Ki iya bakinki, ni duk dangina babu yan iska sannan babu karuwai aciki..."
Dakyar ta iya bude idonta ta kalleshi tana mai jin wani bakin ciki yana shigarta sanadiyyar marin
da yayi mata domin tunda take a duniya babu namijin da yataba gigin kai hannunsa fuskarta da
sunan mari amma yau wannan yaron da baifi Sa,anta ba wai shine ya mareta,
"Ka mareni..?"
"An mareki din ko zaki ramane?" Yabata amsa yana huci,
"Wallahi sai na rama, bazaka taba marina kuma ka zauna lafiya ba, kamar yadda kace ni
karuwace to zan nuna maka cewar ni din karuwarce cikakkiya kamar yadda kafada, wallahi
bazan yarda ba..."
Tafada idanuwanta sun kada sunyi jajur, fuskarta kuwa har ta kumbura musamman barin da ya
mareta, hatta hakorinta dake barin sun kumbura sun fara yimata ciwo,
"Karki fasa ki rama idan baki ramaba ke ba yar halak bace.." Yafada yana huci,
Murmushin takaici tayi ta gyara zamanta tana shafa kuncinta da ya Mara,
"Sai na nuna maka kai yarone karami, wallahi sai na koyar dakai babban darasi.."
"Karki fasa.."
Bata kara magana ba shima bai sake koda kallonta ba ya figi motar, suna zuwa gida yayi
packing ya cilla mata key din motar kan cinyarta ya fita yayi gaba ransa yana wani irin zafi,
Har lokacin maryama na dafe da kuncinta tana kallonsa zuciyarta tana yimata wani irin kuna
sakamakon marin da shaddad yayi mata gashi wai ita ya kalla ya kira da karuwa,
Fita tayi ta rufe motar tabarta anan ta shiga cikin gida, bedroom dinta ta shiga ta kunna wuta ta
karasa gaban mudubi tana bin fuskarta da kallo....
*_Ummi A'isha_*í ½í±Œí ¼í¿»
[5/9, 9:42 AM] Ummi Shatuí ½í±Œí ¼í¿»: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*
*_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*