Showing 30001 words to 33000 words out of 64509 words
Chapter 11 - YARINYAR CE TAYI MIN FYADE By miss untichlobanty.pdf
na duka.
Tunani na ya datse sanda tace ta fasa auren kuma zata bawa me gadi dama a raina nace
masha Allah dama nasan yarinta ke damunta.... amma dakata! Ta fasa aure na saboda me
gadi? Me take nufi wato ya fini ko me ? Toh dukda banason ta saina AURETA ba ita uwar taurin
kai ba? Ko me akayi in bataso ta tada bori? Toh AI in tasan wata batasan wata ba zan AURETA
dan in kure taurin kan muga abinda zatayi.
Kiran wayar nayi taki ta daga daga baya ma naji switched off. Gida na shiga abina ina shirya
bomb din da zan Mata Dan jira zanyi ladidi ta Dan shekara sai nasa luba ma daga ciki.
Ya Allah ka jarabce ni da rasa Mata na nayi kuma karbi kaddarata ya Allah na rokeka saboda
tawakkalin da nayi kar ka kashemin wadannan kar ka rabani dasu. Shafawa nayi kamin nabar
kofan masallatin.
LUBA'S POV
Ummi na samu nace Mata ummi nifa wallahi azo a sake zama na fasa auren uncle aliyu bige
min baki tayi tace sannu shashasha kawai Dan yabaki haushi sai akace ki fasa aure? Haka
zakiyi bayan auren da an bata miki rai kice sake ki? Zama nayi a kasa Wanda ummi tasan
abinda zai biyo shine bori tace toh karma ki fara kinga yanzu SS3 kike ki rufe ido kiyi karatu kina
gamawa lokacin kin kusa shekaru 17 ayi miki aurenki.
Bori na fara nifa Allah in aliyu za a aurenin yasin ko karatun bazaiyi ba. Ummi tace subhanallah
yau ko uncle din babu ? Kuma da kike batun bazakiyi karatu ba wa jahilci zai kashe ? Ki auri
aliyun ki a gidansa sai kiyi university ko ya kikace. Mikewa nayi nace toh ai sai muga yadda zan
aureshi ni dama can nasan ba sona ake a gidannan ba. A fito a fadamin ko tsintata akayi yasa
za'amin auren dole.
Bulala ummi ta dauko ta biyoni zonan yar banza in dauki cikinki wata 9 harda sati 2 awanni 13
nayi ina nakudar ki shine zakice tsintar ki akayi toh sai kin auri aliyun tukunna ma in baki
aureshi ba wa zaki aura? Manna Mata nayi ta bankado labulen dakina ta shigo.... Luna wai
meke damunki ne? meyasa kikeson bamu ciwon kai? Me yasa kikeson maida daddynki karamin
mutum?
Maganarnan an gamata ke da kanki kikace a aura miki aliyu yanzu kice kin fasa? Ki bari idan
kin huce ki sake tunani... turo baki nayi nace nide acewa abba na na fasa. Toh ai shikenan.
Abinda ta fada kenan kamin ta sauke ajiyar zuciya ta fice.
Da daddare ummi ta samu daddy ta fada masa kamin ta karashe ya daga Mata hannu yace
kiramin yarinyar. Kwala min Kira tayi na shigo parlourn ina wani mika da hamma daddy yace in
baki warware ba zan ware ki da Mari tsam na mutsu na zauna yace wani shiririta nakeji wai kin
fasa aure?
Nace nifa daddy ba aure na fasa ba uncle aliyun ne banaso! Ke dalla rufemin baki lokacin da
mukayi justin duniya ki hakura burus kikayi mana kikace sai shi yanzu kuma kina wani magana
da batada kan gado? Toh bari kiji gara ki sani aure ba fashi. Kuma in bakida hankali ki kawomin
kasa da credit shida gidannan saina ballaki.
Mikewa nayi na koma daki ina fadin zakusha mamaki, sannan na fada kan gado na sai bacci.
Washe gari da asuba ummi ta tashi zata tasheni sallar asuba taga empty! Ban daki ko ina ta
duba babu ni babu alamata sai ta dauka ko zuciya nayi na tafi gidan aunty maryam toh amma
da asuba kuma? Daddy na ta fadawa aka Kira su aunty maryam sukace banzo ba.
Uncle Aliyu aka kira shima yace bai ganni ba nan cikinsu ya duri ruwa aka fara cigiya ta a
unguwa amma babu alamata.
Abinda ya faru kuwa shine tun da magrib ina waya da nana nake fada Mata nifa idan aka ki
yarda guduwa zanyi tace yayi mutuniyata toh amma in kin gudu ina zakije? Nace nima ban sani
ba. Maama tace toh me zai hana tazo nan ba tare da sanin kowa ba sai musa ta a BQ ko ya
kukace mu dinga bata su abinci daga nan.
Nace toh amma masu gadi zasu fada ai nana tace karki damu zan rufe musu baki aiko tunda
daddyna bai yadda ba karfe uku nayi sneaking dama already nana ta sanar da masu gadi zuwa
na Dan haka suka budemin kofa.
Inaji da safe anata cigiya na dan video call muke da su nana ina ganin komai.
Zama aka Kira da azahar na yadda za'a soma nemana Allah sarki har sun bani tausayi amma
nasha alwashin idan ba auren aka fasa ba bazan fito ba. Gidajen radio da talabijin duk an watsa
amma shiru babu labarina. Ladidi ko abin ya Mata dadi amma sai ta nuna tafi kowa damuwa.
Harkuka tayi anata bata hakuri ummi ma tasha kuka tace ma daddy na asanar cewa an fasa
auren kila na dawo.
Yace Sam ba'ayi haka ba idan naji ba haza San dawo gida shirme nake yunwa ma kadai ya
isheni ummi tace toh AI garin neman kudin abinci in na fada wani hali fa gashi dama ba hankali
gareni ba? Yace a bari nan da sati sai ayi sanarwan.
Su nana kullum tsakar dare suke kawomin ziyara musha hira kuma Allah cikin ikonsa babu
wadda ya taba tsammanin ina gidan kamar wasa har sati daya yayi Dan haka yau abbana suka
shirya suka tafi gidan yasa labarai... basusha wahala ba aka basu Dama domin yin magana.
Daddy na yace assalamu alaikum! Nine mahaifin yarinyar nan lubabatu da akayi sanarwa satin
daya gaba ta cewa ta bata... luba diyar albarka idan kina jin mu yanzu haka ki dawo gida mun
janye batunnan mun fasa. Aliyu ma ya bada nasa jawabin cewa ya fasa Niko tabe baki nayi
nace sai bayan kwana biyu zan fito.
Haka sukayi ta zuba ido suna neman ranta inda zan billo amm shiru. Washe gari ma haka abin
ya fara daga musu hankali sosai toh kode na mutu ne? Da daddare ne su nana suka hadani da
Allah cewa na fito kullum sai ummi tayi kuka kawai sai na yanke shawarar zan fito gobe.
Washe gari ummi na rashi da safe ta leka daki na yadda ta Saba dukda bata tsammaci gani na
ba ta ganni nayi wannan wawar kwanciyan nawa a da kullum make ni take amma yau cikin jin
dadi ta rungume ni tana sumbatar goshina. Allah sarki diyata ta dawo lubabatu na uwata in kika
shiga umminki tayi kewarki.
Kureta nayi da ido Dan ta bani tausayi har ta rame nace ummi na kiyi hakuri na saki damuwa
amma babu yadda na iya ne sanda nace muku banason auren kuka dage sai anyi. Tace karki
damu an fasa kiyi karatun ki kinji? Toh nace mika sha kuka.
Aka fada wa su aunty maryam an sameni aiko shikenan ban karajin anyi batun auren ba har
lokacin WAEC dinmu yayi. A dakin jarabawa ne naji wasu dalibai na hira ta fari tace nifa wallahi
ko da aunty kaltume ta rasu naso ni aka aura wa mijin ta gaskiya aliyun nan ya hadu. Ta biyu ne
tace nikam kullum sai kin mana zancen aliyunnan amma ko saninshi bamuyi ba ta fari tace aliyu
mukhtar fa! Ta uku tace wanne shi kenan? Ta biyu tace me me Ablimuk plaza ? Ta farin tace
shidai.
Ta biyun tace wow gaskiya nima naji ance gayen ya hadu ta ukun tace nikam ban sanshi ba. Ta
biyun tace dama ance miki shugaban kasa ne da kowa sai ya sanshi? Mtsww ta ukun tace
kanku akeji toh dukda ban sanshi ba toh yamin kuma zan Nemo bayani akansa. Ta farkon tace
sannu Sara me bakar tak*shi Sato dan ubanki ya fi namu kudi shine zaki wani ce ya miki zaki
kwata? Ta biyun tace ku da kuke hauka bakusan matansa 2 ba ? AI daddy naji yana cewa
matansa biyu amma dayan na sirri ne. Kinsan daddy na aminin yayansa ne.
Ta farkon tace ince wancan lubar ance ta sansa? Yayar mamanta ke auren yayansa? Ta biyun
tace kwarai nima naji hakan toh mu tambayeta mana. Ta uku tace yarinyar dake da shegen fi'ili
ga reni cab a dawo lafiya. Wajena suka zo suka ce sannunki luba.... take na musu nace
sannunku. Sukace wai da gaske kinsan Aliyu mukhtar? Nace na sanshi amma munyi fada ban
kulashi Dan haka inma sako me daku bazan iya kaiwa ba.
Sukace haba yar uwa toh ko numbarshi kya bamu AI ko hannu na mika alamun abani littafi
suka miko min hannunsu Niko na rubuta na cire numbar karshe nace su nemi wannan da
kansu. Daidai lokacin aka kawo papers Dan haka babu halin magana.
ALIYU'S POV
Ya ABBA ne ya tisa ni a gaba yace toh aliyu ga luba fa kaga yadda ta kafe yanzu ya kake
tunanin za'ayi? Kaga de har gida ta bari akan kar ta aureka an tambayeta inda ta zauna ma
tace bazata fada ba kar a kuma cewa za'ayi auren ta rasa wajen buya wadda ke nuna in aka
sake takura Mata zata gudu kuma dai kasan matsayinta.
Ajiyan zuciya na sauke nace AI ya ABBA kuma kunyi gaggawa bai dace sanda takai shekara
goma tace ta yarda ayi auren kuka daura a lokacin ba da kun bari ko zuwa yanzu kunga ko ta
fasa ba matsala. Uncle ABBA yace toh ka saketa mana tunda bata ma San da auren ba! Nace
kai gaskiya bazan iya ba ni bansan yadda zanyi da ita in tazo gidan sai in sanar da ita. Ya
ABBA yace toh kadai yi a hankali kasan kamar me aljanu kar mu sake nemanta mu rasa!
í ½í¸³TOH FA NAJI WANI LABARI KO KUNNE NA NE?í ½í²ƒí ¼í¿»í ½í²ƒí ¼í¿» TOH BARI NA TAKA RAWA ASHE
LUBAR MU MATAR ALIYUN CE MA TOH YANZU DE YA ZA AYI TA YARDA TAJE GIDAN?
KU BIYONI A NEXT CHAPTER DANJIN YADDA ZA'A KAI LUBA A DABARA, SHI IN ANKAITA
ZATA ZAUNA KO ZATA ARCE?
IN KUNYI COMMENTS DAYAWA IN BAKU UPDATE IN NAJI SHIRU KUWA TOH SHIKENAN
NIMA ZAKUJI SHIRUí ½í¸‰
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty í ½í²•
23rd June,2020.
[6/23, 3:18 PM] Miss Untichlobantyí ½í²•: DAN ALLAH YAN UWA IDAN AKWAI WACCE TAYI
COMMENT BAN MATA REPLY KUYI HAKURI BA SHAREKU NAYI BA WASU MESSAGES DIN
WAITING SUKE SAKAMIN
[6/24, 6:31 PM] My Samsung: *í ¼í¿†í ¼í¿†YARINYAR CE TAYI MIN FYADEí ¼í¿†í ¼í¿†*
í ¾íµ‡ *20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY* í ¾íµ‡
í ¼í¼¹by miss untichlobanty í ¼í¼¹
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
í ¼í½€ *CHAPTER 21*í ¼í½€
AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....
*Not edited*
*MaryamyakuraMuhammad,husnalhakeem, aisha_gidalle da Usumaima3315 wannan shafin
naku ne Allah yabar kauna.*
LUBA'S POV
Har yau ba'a sake yi min zancen uncle aliyu kuma nima ban koma gidan aunty maryam ba Dan
nayi zuciya da gaske gashi har mun gama su WAEC da NECO har JAMB mun yi kuma nayi
Dan kokari dukda nana ta fini a JAMB tanada 218 ni kuma 210 Dan haka ummi tace zanje
gidan aunty maryam celebration.
Nace babu Inda zani ta buga ta raya nace bazan fa je ko ina ba tace toh AI shikenan kinyi wa
kanki dama wata gagarumar kyauta za'ayi miki wadda zai MATUKAR baki mamaki amma tunda
bakyaso shikenan da sauri nace bari na shirya ina mikewa rikeni tayi tace ai ba yau bane sai
ranan asabar yanzu dai gyara zamuyi. Nace gyara kuma sai kace me shirin yin aure ?
Tace banda abinki keda za'ayi taro ayi su hotuna ai kune idon kowa zai zama akai Dan Haka
dole ayi gyara. Nace kuma haka ne. Aiko ummi kullum sai tayi min gyara ga bakin shayi da take
bani wai na kara kwarjini ne bansan tsimi take tace min ba!
Nide cikin jin dadi da kaguwa nake cewa ummi kidan fada min menene kyautar tace wannan
kyautar zai canja rayuwar ki baki daya. Tsalle na soma Dan ni na dauka burina na hada kayan
gyaran jiki ne zai cika ashe de akwai lauje cikin nadi.
Ranar juma'a ne aka Nemo mai lalle da kitso suka baza min abina sai walwala nake ina tunanin
yadda hankalin kowa zai dawo kaina Dan nasan zanfi nana hadewa. Dukda bawai kyashi make
Mata ko wani Abu ba.
Aiko washe gari gidan mu da gidan aunty maryam an cika anata San barka da sa alkhairi gefe
naja ummi nace wai ya naji ana Allah yasa alkhairi yasa a dore.
Tace Allah yasa ALKHAIRI wa sakamakonki mana sannan yasa iliminki da kwazo ya dore nace
aiho masu cewa Allah yasa gidan ta ne fa? Tace ah ah ke bakyaso alkhairi ya zama
gidanki?Nace inaso mana yadda sukeyi ne kamar aure akayi min.
Dariya tayi tace sai kace yar tsana ki shirya maza daddynki zaiyi magana dake. Dakinsa na
wuce yayinda ummi ta sake jaddada wa matan kar a kuskura a kirani amarya Dan surprise
akeso Amin suka amsa da ba matsala.
Daddy na yamin wa'azi sosai akan rayuwa har na danyi kuka nace daddy wai ya kake magana
kamar zamu rabu ne yace ai zaki tafi jami'a ki hadu da mutane iri iri kuma kinga yanzu kin girma
kinyi shekaru 16 sure ko wani lokaci Dan haka ki natsu kinji diyar albarka ? Toh nace na
rungumeshi daga nan muka wuce gidan aunty maryam.
Hotuna mukasha dukda matan basuda yawa duka da na gidan mu da gidan aunty maryam
basufi su 100 ba ai kuwa ba'a damu da yi. Hoto da nana ba kamar itama ba graduation tayi ba
har naji ba dadi.
Har na gaji Dan inata tsimayin sanda za'a bani kyauta ta na aunty maryam da iya hajjo ne kawai
suka riko hannuna sukace muje nace ba tare da ummi za'a nuna min kyautar ba? Aunty
maryam tace ai ita tana can ta rigamu zuwa ashe duk sani ake a kwano ummi tana gida babu
inda taje.
Daure min ido akayi da muka shiga mota sukace so suke ayi min surprise da yake nasan aunty
maryam wayaiyace shiyasa ban daura ayan tambaya ba ni duk na kagu naga menene ake ja
min rai.
Tsayawa akayi na washe baki Dan nasan an iso kofofi naji ana shiga dani har AC mai dadi ya
dakeni. Zaunar dani akayi na bude idon nagan my a wani daki dai dai misali mai mugun kyau
komai na dakin blue ne yadda nakeso.
Dukda ban gane ba neme neme na fara da ido ina neman kyautar amma na tsaya sanda naga
katan leda a gefena. Budewa nayi naga katan ciye ciye ne. Aunty maryam tace maza kici abinki
kinji yanzu zamuje mu dauko kyautar. Ina lashe hannu nace uhm Dan magana bazai samu ba.
Fita sukayi nikam naci gaba da ciye ciye da hannu bibbiyu ina jinjina kai kamar wata
kadangaruwa.
ALIYU'S POV
Tunda na fadi plan din kowa ya yarda amma toh yadda zan zaunar da luba bayan an kaita shine
matsalar. Sanda su aunty maryam suka fito daga side dinta kuma side Dina na da.
Sukace toh aliyu mu mun gama namu ga luba de an kawo ma ka rike amana kaji ko? Sannan
ka bita a hankali don Allah. Aunty maryam tace kai hajjo kiji da wani zance yarinyar ko tsarki ma
batada shi. Hajjo tace AI zata samu... ratan dai kaji ni ko?
Sosa kai nayi a raina nace ni dama babu abinda zanyi Mata kawai so nake na nuna Mata batafi
karfinmu ba yayinda a zahiri nace insha Allah.
Suna fita na kafta Mata sakata na wuce dakin ladidi abina Dan nasan yanzu haka luban tayi
bacci Dan kayan ciye ciyen nan ba haka kawai nabar su kazar ba. Kuma kan ta tashi sai an
jima.
A gida kuwa duk an watse su ABBA ana fatan zaman ya dore Dan sun tsorata da luba zuwa
yanzu saide addu'a.
Washe gari da safe ba duba ta aiko ta bingire hannunta dama dama da abinci. Karba nayi na
ajiye na cire alewar dake bakinta na gyara Mata kwanciya ina ja Mata kumatu kamin na fita
abina.
LUBA'S POV
Ina tashi naji kaina na ciwo sosai nayi mika har zan sauko ba tuna banyi addu'a ba nayi kamin
na sauka sai lokacin na fara tunanin ina kyauta ta kuma me yasa na kwana anan ? Fita nayi
nagan ni a parlour komai fari kalle kalle nayi kamin na bude wata kofa kitchen ne turo baki nayi
Dan kofar fita nake nema.
Sunan aunty maryam na fara Kira ina bude wata kofa ban daki ne sai wani daki daya.... kofar da
nake tunanin na fita ne toh shi a kulle Kira nayi amma kowa wayar sa a kashe. Na uncle aliyu
na Kira Dan zuwa yanzu na fara tunanin ko saida ni akayi.
Dagawa yayi yana fadin wow I am honored yau her royal highness luba da kanta ke kirana. Toh
sarauniya me zan miki? Cikin Muryan kuka nace uncle aliyu an sace ni kazo ka taimake ni yace
yimin bayanin me ya faru...
Nace kawai ni da su aunty maryam munzo wani gida na fara ciye ciye su kuma suka tafi dauko
min kyauta ta daga nan basu dawo ba kuma nima ban sake sanin komai ba sai yanzu na tashi.
Kode bigesu akayi aka dauresu? Yace karki damu your savior is here kawai sai aka bude kofar.
ALIYU'S POV
Ina zaune muna cin abinci ni da ladidi wacce itama batasan