Showing 63001 words to 64509 words out of 64509 words
Chapter 22 - YARINYAR CE TAYI MIN FYADE By miss untichlobanty.pdf
ya jona yaki da jahilai kuma yana skill
acquisition na computer so yana sa rai yayi using certificate dinsa ya shiga jami'a nan da
watanni 7.
Mika Mata kunun ladidi tayi tace toh maman yan uku mijinki ya dawo nima najiyo Muryan future
hubby na bari nabi bayan labule na wuce ko? Dariya Luba tayi ta zamo dakyar sanadiyyar
nauyin da cikin ya fara saboda ya shiga wata na bakwai.
Bin bayan ladidi luba tayi da kallo tana mai tausaya Mata yadda ta rabu da mijinta kuma bata
hassada ma matarsa.
Fitowa parlour tayi musa wato mus yace a ah auntyn mu ashe kece a kitchen din tace wallahi
kuwa yaya mus ina wuni? Yace lafiya mun sameku lafiya ko? Tace Alhamdulillah dan kyakkyalla
ido yake ko zakiga ladidi amma bai ganta ba.
Luba da ta gano sa tace aiko yanzunnan aunty ladidi ta shige daki nasan zata fito diba maka
abinci da wannan ta shige dakinta aliyu yabi bayanta bayan ya dauko ludayi a kitchen. Bata
ankare ba kawai taji ya tsindumo Ma ta ludayi a cikin kunu turo baki tayi tace wai kai wani irin
baba ne kullum kana cikin shanye ma yaranka kunu ? Gwaliyo ya Mata yana dariya ta matsar
da kunun tace kasha rabonka.
Yace haba maman babies kar muyi haka dake please kinji kunun ne dadi dukda cewa na jiya
yafi dadi tace Allah ya soka ni nayi na ajiyan bani ludayin in diba maka rabi.
Yace uhm uhm kishi na damun wata ko? Ya fada yana dauke kai tace a bakin kunun ka yace
tuba nake sarauniya yana miko Ma ta ludayin Suka kyalkyale da dariya.
Ladidi kuwa tana shiga daki ta goge hawayenta ta fada kan gado tana cire hijab din dake jikinta
tace ya Allah ka yaye min kashin dake damuna Allah ka gani bawai Dan inason musa nabar
aliyu ba na barshi ne saboda ina tsoro. Bazan iya zama da kishiya ba kar na cutar da luba Allah
ko digon son musa ne kasa min Allah indai na taba yin wani aiki na ALKHAIRI ina tawassali
dashi ka zaba min mafi alkhairi.
Mayar da hijab dinta tayi ta fita ba kowa a parlourn ta dauki abincin mus ta nufi dakinsa dake
bayan gidan tu da saura satu a gama gyaran gidan da aliyu ya basu. Kwankwasawa tayi ya
bude yana Mata murmushi ta tsuguna ta gaisheshi yana fadin nagode sosai ladidi aci gaba da
hakuri dani tace ba komai ni zan koma yace toh anjima zanzo inji me da me kike bukata na
auren dukda cewa kinsan har yanzu abubuwan basu bude ba.
Tace ai ba komai kasan ba wani shagali za'ayi bama nagode. Tana kaiwa nan ta Mike ta shige
gida abinta. Ita fa har ga Allah a wani sako na zuciyar ta haushin mus takeji.
Bayan Sati biyu aka daura auren musa da ladidi saide luba abin bai Mata dadi ba saboda bata
iya tafiya Dan yara 3 sunyi Mata nauyi idan ba ya zama dole kamar zuwa bandaki ba toh bata
tashi yaso ayi auren bayan ta haihu musa yace AI bazai hana ladidin zuwa Gidan ba.
Su aunty maryam da makota kadan ne kawai suka kaita ba wani taro Dan ma kwana 3 kamin
biki aunty maryam uwar gyara ta dauketa akayi Mata gyara Wanda ko aurensa na farko ba'ayi
Mata ba.
Bayan sun tafi tana zaune a dakinta taji shigowan su mus kukanta ya tsananta shi da aliyu ne
kadai nan de aliyu yayi musu nasha da fata na gari ya gudu Dan shi kanshi kishi ke taso masa
wai matarsa ce ke daukan sunan matan wani.
Koda ya koma gida ya samu luba ma an zuba tagumi ga rid'ed'en ciki taga ya shigo jiki a
sanyaye. Zama yayi a gefenta baice komai ba sai hawayen da yake gogewa. Bata ce masa
komai ba Dan itama tayi missing ladidi amma tana jin kishin yadda yake ma wata kuka ganin zai
fashe da kuka yasa ta rungumo shi a kirjinta tana shafa kanshi ya gama kukansa harda
shessheka ita kam mamaki ma ya bata a haka har yayi bacci.
Zata kwantar dashi a gefe saboda yadda bayanta ya rike ya kankameta yana fadin lubabatu
Karki barni ke daya ce gareni Dan Allah. Shafa kanshi tayi a hankali tace bazan barka ba tana
kwantar dashi kamin ta shige ban daki Dan fitsari take ji.
Dakin su mus kuwa tsoro yakeji kar ladidi tace baikai aliyu ba gashi shi ba gwani bane a fannin
Dan bai taba sanin mace ba. Yace toh ladidi godiya ta tabbata ga Allah..... haka dai ya gama
Mata jawaban shi ya ce su tashi suyi sallah. Shi yajasu domin kuwa cikin watannin nan ya zage
ya koyi karatu sosai.
Riko hannunta tayi yace zo muci abinci kinji ? Kawai sai ta fashe masa da kuka shi rikecewa
yayi dama haka amaren keyi ko ladidin ne? Da kyar ya lallabata ta bada hadin kai badan taso
ba.
Bayan wata daya da sati uku ladidi tana bakin gadon luba tana zaune luba tace aunty ladidi
Anya kuwa kinajin dadin zamanki da mus? Naga sai ramewa kike kina baki. Ladidi tace banida
lafiya ne nace ma a kawo min sakamakon zasu iya zuwa ko wani lokaci. Nan take cewa kema
haihuwa yau ko gobe gara na karasa hada miki jakan nan.
Baifi minti 5 da hiran ba akace Mata an kawo result din karbowa tayi ta bude taga maleria and
typhoid report ne kuma negative dayan ta bude taga....
PREGNANCY REPORT ne kuma positive wani ihu ta buga tayi zaman daba tana fadin na shiga
uku lubabatu innalillah wa inna ilaihi raji'un. Zabura luba tayi ganin yadda ta rude tace aunty
karde kice min HIV gareki? Ladidi tace HIV din banza lubabatu ciki gareni na shiga uku na.
Luba tace kamar yaya aunty ladidi ? Cikin ne masifa ko me? Ladidi tace wallahi Allah banason
mus kawai zama nake dashi yanzu kuma saina Haifa masa da? Aliyu ne ya shigo da gudu
hannu a ka yana fadin innalillah wa inna ilaihi raji'un ladidi ashe har kinji sakon saide hakuri
Allah yayinwa musa rasuwa. Dam! dam !! Kukeji take labour ya rike luba Wanda bata shirya ba
ladidi ko shako aliyu tayi tace kaji maganar banza, kai ka kasheshi? Yace hakuri zakiyi ladidi.
Tace karya ne wallahi karyane musa na bai mutu ba ko a Nemo min shi ko nayi tashin hankali
kace masa ya tashi, bai isa ya mutu ya barni ba. Aliyu yace haba ladidi karkiyi sabo mana.
Bayan kin gama takaba sai na aureki ko?
Atake fire din luba ya fashe amma basu ma lura da ita ba ladidi tace bani SONKA wallahi yanzu
shi nake so!
Murmushi yayi yace zo muje. Suna fita suka ga mus yana musu murmushi da gudu ta rungume
shi tana fadin mus mus Dina shine zaka bari a bani tsoro ace min ka mutu ? Ta fadi haka tana
dukan kirjinsa.
Dariya take yace laifinki ne AI muna dawowa muka jiki kina ihu wai baki sona zaki haifamin da
shine oga aliyu yace zai gwadaki ashe de kina so na? Tace bana son tsokanan nan Dan Allah
karka barni kneeldown yayi ya rungume jikinta yana dariya yace kai Dan samari kace daddy.
Dariya aliyu yayi daidai lokacin luba ta kwalla kara nan akayi hospital da ita bayan awanni 6 ta
haifo yaranta maza 3 cas.

Bayan an gyarasu ne su ladidi suka shigo kowa yadau daya sai lokacin aka tuno da wasu aunty
maryam aka sanar musu luba tace kai gaskiya nan gaba Allah yasa na haifi mace. Ladidi ta
dungure mata kai tace oh su luba ande ji kunya..
Kwaikwayanta ta soma yi tana fadin waiyo Allah na aliyu ka cuceni bazan sake haihuwa ba
wallahi ko yatsa na ka sake rikewa saina yanke ma hannu... yanzu kuma fadi take Allah yasa ta
haifi mace.
Da shike a jingina luban take tayi Muryan ladidi tace "na shiga uku lubabatu innalillah wa inna
ilaihi raji'un wallahi Allah banason mus kawai zama nake dashi yanzu kuma saina Haifa masa
da?"
Sai kuma muka ga mutuniyar na fadin "karya ne wallahi karyane musa na bai mutu ba ko a
Nemo min shi ko nayi tashin hankali kace masa ya tashi, bai isa ya mutu ya barni ba."
Dariya suka kyalkyale dashi dukansu aliyu yace toh ku jera muyi selfie! Yace cheese! Take da
daukan hoton CLICK!
bayan wani lokaci kauna ta barke tsakanin nana da samir harde takai ga aure inda suka ci gaba
da karatu luba ta karamci law yayinda nana ta karanci chemistry mama kuma ta karanci mass
com.
ALHAMDULILLAH! ALLAH YAYI KAMAR YADDA NA FARA A SA'A GASHI NA KARKARE
MUKU WANNAN LABARI NAWA. INA MATUKAR GODIYA GAREKU MASOYA NA INSHA
ALLAH ZAN SAKI MUKU CIRCULAR NA SABON LABARI NA MAI SUNA (YAJI TA MATA) SAI
KUN JINIí ½í²‹
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty í ½í²•
17th July,2020.