Showing 24001 words to 27000 words out of 64509 words
Chapter 9 - YARINYAR CE TAYI MIN FYADE By miss untichlobanty.pdf
a rufe Dan idan ba haka ba wannan Terere da ya faru in anzo
aurensa sai ya taso kasan jama'a da kara gishiri wa zance Dan tayi manda.
Dafe kirji aliyu yayi yace ya ABBA aure fa kace? Ya ABBA yace kwarai kuwa zaka AURETA!
♀️♀️♀️OH NI UNTO NA BANU YANZU KUMA WANNAN JAGWAL DIN DAGA INA TA
BALLO? KAI JAMA'A
SHIN KUNA GANIN YA DACE DA SUKA YARDA DA SHIRIRITAR LUBA? KUNSAN FA BA
HANKALI GARETA BA ITA A GAME MA TA DAUKI ABUN AMMA KARKU MANTA TAKI
KARATU YASA SUKA YARDA.
KUNA HANGO JAGWAL A GABA KO BAKU HANGOWA. SHIN ZATA YARDA KO KUWA ZATA
FASA IN TAKAI SHEKARA 10 ?
KU BIYONI DAN JIN YADDA ZA'A WARWARE WANNAN CAKWAKIYAR. AMMA DAI LUBA
TANA RUWA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty
16th June,2020.
4 -
[6/18, 7:30 PM] My Samsung: *YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY*
by miss untichlobanty
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*JANNAT,SUMAYYA YARIMA, SA'ADATU TIJJANI, ZAKIYYA and MATAR MANYA wannan
shafin naku ne* Allah yabar kauna
*CHAPTER 16*
AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....
Not edited
ALIYU'S POV
Wannan wace irin magana ce ake min ace in aureta? Taya ma zasu biye shiriritar yarinya ?
Ajiyar zuciya na sauke. Dadin abin ma ance in takai shekara 10 za'a sake tambayar ta. Toh ni
ince wa nafeesa me? Dukda Cewa tana da hakuri amma ace tun kamin ayi aure a fada ma
kishiyar ka? Lamarin nan da sake.
Kallon ya Abba Nayi nace Toh Allah ya kaimu nan da shekara 4 Daga nan aka Shiga sabgar
biki na.
Akwana a tashi har Anyi aure na nida nafeesa Muna zaman lafiya mata me hankali da biyaiya
samun irinta Nada mugun wahala. Tasha wahala sosai saboda 'bari da tayi yafi sai 4 Daga nan
tahau jinya har Allah ya amshi ranta.
Daga nan na auri salma itama a hatsarin mota ta rasu. Kamin kace me na auri mata 6 amma
duk babu mai tsawan rai kuma duk na kwarai ne saide abinda baza'a rasa ba.
Lokacin da luba tayi shekara Goma muna zaune mu mun mance da zancen ma Dan gani ake
shirman ta ne ta manta kawai muka jiyota tana fadin indai zaman nan na batun aurena da uncle
Ali ne toh ban fasa ba. Kallonta muka tsaya yi iko sai Allah yarinyar nada abin mamaki.
Yaune aka daura aurena na 7 da ladidi a yanzu shekarun luba 12 itane kirjin biki anata rawar
kai. Inda Allah ya taimaka bata iya rawa ba Dan haka da akace za'a yi party tace baza ayi ba
dama nima banaso ladidi ce ta dage.
Luba ko tace indai akayi dinner sai ta bata sauran ba'ayi ba wannan ms baza ayi ba. Dan haka
aka fasa akayi Karin ango kawai aka kawo min amarya ta.
LUBA'S POV
Uncle aliyu kamar me aljanu da yayi aure se matar ta mutu ni da fari na dauka wasar buya suke
mana ashe tafiya yama sunan wajen ? Yauwa ashe tafiya barzahu sukeyi duk sanda yayi aure
toh gidansa nake weekend an hanani an hanani amma naki ji har an gaji. Aunty maryam tace AI
idan ina zuwa ko wani lokaci bazaiyi dauki na ba amma nayi biris. Ba lura so suke na manta da
zancen Niko kullum da na tashi daga bacci abinda nake tunawa kenan Dan bazan taba yarda
suyi winning ba. Kenan fa na zama loser.
Matan sa nada kirki duk sanda naje suyita bani labari muna hira tun ina kankanuwa ta. Har
goyona suke aunty nafeesa kam har cemin take idan na auri uncle aliyu ni zan dinga tayata
wanke wanke. Niko sai na kyalkyale da dariya Dan abin birgeni take ashe de baza tayi Nisan
kwana ba nati kewarta.
Wasu idan aka fada musu cewa zai aureni da fari basa yarda amma idan suka ga banida
matsala shikenan sai mu dinke Dan ni inason aiki sosai komai na gani sai na taba ko anyi shara
sai nayi nima. Gani da surutu ba comma bare full stop.
Satin bikin uncle aliyu da aunty ladidi na shigowa na soma dauki, nayi can nayi can dukda
yanzu shekarata 12 na soma game kishi amma ban damu saboda na Saba ganinshi da Mata.
Bari na Baku labari in kuka ganni zakuce nakai shekaru 15 Dan mugun girma nayi.
Dinki naje karbowa dukda anyi anyi na bari a karbo naki Dan nasan telan Dan jagwal ne. Aiko
koda naje ya yanka be dinka ba. Tada ma yan shagon hankali nayi sanda akayi a take aka bani
ba zuburo Bali da yasha Jan baki sosai na dau ledar kayana na bashi 1500 nace yasin Rabin
kudin zan biya saboda an bata min rai.
Kamar uwarsa jiki na ruwa yace jeki ba matsala kai ilu tara Mata me adaidaita sahu. Jiki na
rawa kuwa ya tara mini ina tafiya suka Nemo ruwa da sobo suka kora Dan na caja musu kai ba
kadan ba.
Ina dawowa naji ana wani batu wai za'a yi party nace in anyi shegiya nake. AI da gangan ake
cewa za'ayi bayan ansan cewa ban iya rawa ba. Amma usilin zance babu rawar da ban iya ba
tunba na bazo bazo ba. Kawai banish ayi party ne Dan a islamiya ance mana babu kyau amma
nasan da na fadi wannan za'a kafa mini hujja da abinda nayi ina yarinya Wanda nasan abin ya
faru amma na mance da abubuwa sosai bazan iya hada labarin ba saide a takaice.
Aiko da alamu uncle aliyun ma bayaso Dan babu wasting time yace angama uwani AI abinda
kike so shi za'ayi. Nasan gatse yayi min a wasa mikewa nayi ina tsalle zan fice nace haka
nakeson ji ubale na. BIYONI yayi da gudu na arce ina dariya.
Karin ango Akazo yi da shike maman su uncle ABBA ne shuwa shiyasa uncle Ali ya Dan dauki
haskenta yayinda uncle abban yadau duhun mahaifinsu Wanda yake kanuri gaba da baya
hakan yasa ba Karin angon da hausawa keyi akayi ba. Kaulu akayi wato original din na kanurai.
Karkashi ne za'a Dama ka lakata ka taba ma ango a hannu kayi masa addu'a sai ka lika kudi.
Niko abin yanamin dadi lokacin muna shiri Dan ango ya kusa zama. Su nana sonata hura hanci
wai na janyo baza'ayi party ba nace nifa rawa ce banyi gaban maza amma ina zuwa aunty
maryam na samu tana cikin mutane sunanta korafin yadda ka biye min aka ki yin Partyn tana
bada hakuri.
Koda na shigo akan hanci suke kallo na suna bata rai shan kanshi na fara tare da dage kai ina
hura hanci na jujjuya musu mazaunai na da basu zauna ba Dan ni albarka kirji gareni amma
mazaunai na basuda girma na bazo a gani daidai kamar na kowa ne.
Gefe naja aunty maryam nace so Nike a Kira mini ma kadan fada ayi mana ganga kura (ganga
kura shine kidan da kanurai keyi wadda yawanci suke hawa kan layi ko sahu a taka rawa iri
daya bawai a girgije Dan mu a tsarin kanuri babu rawar girgiza. Ada kakannin my kanurai suna
ganin kowa Arne Dan lokacin a borno empire kadai akeda musulunci tun kamin ya shiga su
sokoto. Any way ba historynazo Baku ba wannan ma wani fanni ne na daban)
Tace toh babu matsala komawa mukayi na daura liffaya ta blue wato shudi (ba lafaya ba and
also kurkum not kurkur, Dilke not dilka fatan mun gane?) muka fito anata shan kamshi kamar
iyayen Mata. Fili aka buda mini dan dama nasa an sanar da abokan ango cewa da na fito susa
a bude min fili.
Dangwala nayi amma memakon na shafa masa a hannu sai na muka masa a gemu sannan na
ciro bandir din 50 wato dubu 5 na cire hularsa nasa aciki harara ta yayi nayi masa gwalo
yayinda abokansa suka saki baki suna kallon mu uku Niko kara dage gira nake Dan karma suyi
shawagin cewa suna sona kuma abinda zai baka haushi ko kwalliya bamuyi ba Dan ni ka'idata
ban kwalliya bawai Dan inada kyau yasa nake haka ba sai Dan ba kowa ya dace yaga
kwalliyata ba! Nafi karfin wannan.
Bayan mun dawo cikin gida ne na kyalkyale da dariya Dan nasan yadda uncle aliyu keson
gemunsa Kamar me. Masu ganga ne suka iso aka sanar wa maza suka shigo sannan akyi rawa
ta al'ada karfe biyar ummi tayi mana surprise da masu kidan kwarya Dan haka maza suka fice
waje inda ake Kari tare da me ganga yayinda Mata suka rufe kofa bayan an tabbatar babu
namiji muka girgije nan na naje na karkade jiki su nana sai makemin mazaunai suke wai haka
ne rashin iya rawa. Nide nace kanku. Da daddare ne akace ankai amarya aiko ni da nana da
mama mukace toh muma can zamu kwana aka hanamu.
Mama ce ta samu uncle Samir ta roka mana shi Dan taga alamun sa Santa yake amma bai fadi
ba saboda karantarta shekarunta Goma ne.
Aiko babu wata wata ya yarda ya daukemu mu uku a Motansa ya kaimu muku muka saka
wayar mu a plane mode toh amma ba zuwan ba abinda muka tarar ne yasa zan iya ce muku
ana gwarama ko kuma akwai kura hajiya!
UHM IKO SAI ALLAH KO MECECE KURAR NAN? NIDE BARI NA SAMU BAKIN GADO NAYI
SHIRU SANNAN NAJI DAGA GAREKU!
AFWAN KUN JINI SHIRU WAYATA TA DAN SAMI MATSALA NE AMMA ALHMDLLH KOMAI
YA DAWO NORMAL DAN HAKA ACI GABA DA GASHI KAWAI.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty
18th June,2020.
[6/20, 9:16 PM] My Samsung: *YARINYAR CE TAYI MIN FYADE*
*20%TRUE LIFE,80% FICTIONAL STORY*
by miss untichlobanty
Feel free to contact me on :
WATTPAD miss_untichlobanty
INSTAGRAM miss_untichlobanty
TWITTER, miss_untichlobanty
TELEGRAM miss_untichlobanty
Your little sis loves you and don't forget to follow me!
*Indai sunanki maman wani ko ummu wata toh wannan page din naki ne, da Wanda sunasu ya
fara daga A-Z wannan shafin naku ne kuma* Allah yabar kauna
*CHAPTER 17*
AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....
Not edited
LUBA'S POV
Muna isa muka fara kalle kalle , shikam uncle aliyu baya gajiya duk sanda zai sake aure sai ya
canja pant na gidansa. Kuma cikin matan daya aura wannan yama sunanta? Ladidi tafi sauran
kudi Dan kayanta masu kyau.
Nide had yau bani taba magana ba banda gaisuwa Dan bama haduwa ma bansan ko gudu na
take ba.
Shiga dakin amarya mukayi kamar yadda muka saba direct gado muka nufa matan dake dakin
suna binmu da kallo. Wata me kananun ido tace ku kuma fa? Zaku wani shigo ku ajiye mutane
kazamin ...... a gado? Nana ce tace sai akace naki yafi namu? Nikam gyara zama nayi na ware
su liffaya ta Dan zafi nakeji ashar ta dirma Zara yo kaina ladidi ta fito a nayi ta hura hanci meke
faruwa ake min hargagi a gidan miji nifa kar ku sake kimin fada Dan zanci....... mutum ne.
Wannan me kananun idon ne tace AI da fada muke da sauki.... dubi fa kallona tayi ta danyi
murmushi tace to AI su luba ne yayan shi ne fa.....suma sakin fuska sukayi sukace au AI mun
dauka gaiyar sodi ne.
Mama ce tace ni da nana ne yayan sa amma sis luba matar da zai aura ne.... da sauri ladidi ta
juyo tace ban gane ba. Nace zama ki gane da alamu kece wacce be fadawa ba toh aunty ladidi
tun ina yar karama akayi alkawarin sure tsakanin mu..... wani ashar ta lailayo tace Sam bazai
sabu ba.
Wato abinda yake ta cewa zai fadamin kenan? AI yasin bazan zauna da me kama da ifiritai ba.
Jimin yarinya daga kirji sai hanci kamar tsinke saura jiki kuwa kamar an fere tsabar siriranta ace
inyi kishi da ita? Kallonmu tayi tace ku Dan ...... ku fita min a daki.
Sauka su nana sukayi Niko na koma bangaren dama na gadon na kwanta.. kallona suka tsaya
yi nace gurin mijina na kwanta ba naki ba danko nasan barni dama yakeson kwanciya. Tace toh
sannu shegiya karuwa zanko ci.....
Wata ce ta shigo tana fadin angwaye sun iso Dan haka muka fice muka buya kar uncle aliyu
yasa a mayar damu gida hakan yasa ladidi tasha ban mayar Mata da magana ba. Ni yasin
gashinta nikeji kuma saina fadawa uncle aliyu abinda tayi min.
Munajin shewarsu da alamu kudi aka basu can muka jiyo hayaniya kamin ta lafa da alamu sun
tafi ne mukam muna dayan dakin Dan dakuna 3 ne a gidan sai parlour biyu madaidaita. Neman
liffayata na soma yi lokacin da zamu kwanta akan sai in rufu dashi amma ban Ganshi ba sai
lokacin na tuna da cewa yana dakin ladidi tsaki naja na kwanta abina.
ALIYU'S POV
Kaina a kasa bance komai ba aka gama duk hirar abokan ango da kawaye danni kunya nakeji
kuma idan Baku sani ba ladidi shekarunta 19 ne dukda bannwani girmeta and azo a gani ba
amma ni AI nayi aure dayawa ba wannan ne na fari ba. Sanda suka tashi tafiya tukunna na
rakasu
Koda na dawo liffayar ladidi na gani akan gado yana reto Dan murmushi nayi a raina nace ita
kuma har an shiga kintsawa ba kunya ne? Dagawa nayi Dan na gyara naji kamshi ya daki hanci
na rikewa nayi ina shinshina ina jiran ra fito nima na shiga alwala amma me ? Tana fitowa na
ganta da gyalen ta kanta kuma babu alamun alwala a fuskarta.
Nace a ah hajiyata ashe ba gyalenki bane wannan? To ko wata kawar ki ce tayi mantuwa?
Nadau gyalenki ne ma ashe ga naki... wani harara ta balla min tace dalla malam kamin shiru
idan ba renin hankali ba sarai kana ganin gyalen yar iskar yarinyar nan ce zaka wani ce kawata
tayi mantuwa? Kuma sarai AI kaga gyalen dake kaina sanda akayi sayan baki...
Da yake inada Ilimi nasan yan Mata basu iya magana ba kawai nayi murmushi nace Allah sarki
aiko bakin nan ansiyo mini shi ina Dan dariya... toh ke banda abinki ai kaina na kasa ban lura
da gyalen ba kuma wace yar iska kike nufi?
Tace duba ka gani dakyau... kallon liffayar nayi dakyau sai yanzu na tuna inda na Ganshi nace
au ashe ma na luba AI sai yanzu na tuna dazu na ganta dashi a wajen Kari na.
Tace zama ka karashe sauran zance wato ma matar da zaka aura ce baka sanar dani ba?
Ajiyar zuciya na sauke nace yanzu dai muje muyi alwala muyi sallah zan fada miki komai. Turo
baki tayi kamin de ta juya....
Haka mukayi sallah muna cin abinci ina fada Mata yadda akayi zan auri luba tunda matarka
abokiyarka ai babu aibu idan na fada Mata kuma babu wacce ta taba tambaya ta a mata na
shiyasa ma ban fada musu ba aiko ta nuna fahimta sosai naji dadin haka muka kwanta ban
Mata komai ba banda rungumarta da nayi ina shinshinan kamshinta na tuno na luba murmushi
kawai nayi har bacci ya dauke mu...
LADIDI'S POV
Koda mukayi sallah muna cin abinci ya labarta min yadda yar iskan yarinyar nan ta bi min miji...
aiko nace in tasan wata batasan wata ba a gabansa in nuna komai kalau da ya juya ko inci
ubanta taci sa'a ma bazamu dinga haduwa ba da na gasa yar banza.
Duk rashin mutunci Dana buga masa baya nuna damuwa nasan sarai bai kulani bane Dan
yanason ya shiga kasan Dan kamfai na Niko nace nasan maganinsa ga mamaki na babu
abinda yayi min. Inaji shi daya yana murmushi har ya fara sauke numfashi, nina da tunane
tunane na nayi bacci.
LUBA'S POV
Cikin dare na tashi yunwa na kwakulata na nufi kitchen anan na Sami kirjin kaza da guntun
madara dasu dabino harda fruit na dauko nazo na naje ciki na hanka abina yo zan cucina kaina
ne ince wani wai ni yar Gaye? Ko wanke hannu banyi ba na koma bacci.
Da safe wajen karfe 8 na tashi Dan wata yunwar nakeji wanka nayi banida wani kaya kwai sai
nasa half vest Dina da da leggings Wanda nasa kasan lace Dina na fice Dan ban tsammaci su
fito yanzu ba kitchen na shiga babu abinci na leka store aiko ga su bakilawa,su doughnuts da
cake na dibo Abu na tun a kitchen na fara hankama... da uncle Aliyu nayi karo yana dawowa
daga waje har kunya nadan ji na Dan haka nayi sauri na buya bayan labule.....
Bude labulen yayi ya yaba minnwani Abu a gashi na yana min dariyar mugunta... lakatowa nayi
naga kakashi yamutse fuska nayi nace uncle aliyu ka bata min gashina. Dauke doughnut daya
yayi daga kwano na yana fadin bashi na biya daga yanzu na daina kyaleki kiyimin tsiya son
ranki tunda kin fara girma.
Biyoshi nayi kamar zaki ina kukan ya bani abinci na kawai ladidi ta fito tana hamma tace nawan
wai wake sallama ne. Wasu flask ya nuna Mata yana fadin baki fada min anan su luba suka
kwana kallona tayi da sauri kamin tayi murmushi tace au mancewa nati kwi yadau zafi bari
nakai abincin kitchen ko? Shiga daki yayi yayinda ta kalleni kamar zata gutsireni tace Dan
ubanki wa yace ku kwana mun a gida kuma fa nan ba gidan karuwai bane