Showing 1 words to 3000 words out of 48040 words
Chapter 1 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
AURE KO BOKO?
(Littafi Ga Matasa Maza da Mata)
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
GABATARWA
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai.
Duba da halin da matasa ke shiga a kasarmu Nijeriya a yau, daga mazan har matan, akan
rashin aikin yi ga wadanda suka samu damar yin ilmin zamani mai zurfi da matsalolin da hakan
yake haifarwa, sannan da halin wasu daga cikin manyan 'yan bokon wannan zamani na baiwa
boko fifiko akan addini, yasa na yanke shawarar rubuta littafin AURE KO BOKO? Ba don komai
ba sai domin ya zamo hannun ka mai sanda ga irin wadannan 'yan boko da matasa masu zurfin
ilmi marasa aikin yi. Tasirin furucin iyaye akan 'ya'yan su mai kyau ko maras kyau, hakika shi
bakin iyaye kaifin sa da tasirin sa yafi na reza. Sannan 'ya'ya amana ne a hannun mu,
kasancewar Ubangiji yayi musu umarnin su yi wa iyaye biyayya sai da yayi tagociya ga cewa
banda akan umarnin Ubangiji.
Ina fatan wannan dan littafi ya zamo mai amfani ga al'umma, matasa maza da mata, ya zamo
sadaqatul jariya ga iyaye na ya yafe min kurakuran da ke cikinsa.
- Sumayyah Abdulkadir (Takori)
3rd June, 2021
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowanne gidan radiyo ko kafafen yada labarai ba tare da
izni na ba, ko copying dinsa a kafafen sada zumunta, yin hakan karya doka ne kuma abin
tuhuma daga Lauya na Barr. Sadiq Rufai Wali.
GODIYA
Ga dukkan members na Takori's online Forum, na gode da kaunar ku da goyon bayan ku.
FATAN ALKHAIRI
Ga duk makaranta littatafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ina godiya da
yabo da fatan alkhairin da kuke yi mun, Allah ya barmu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da
muka daina numfashi.
SHIMFIDA
BABI NA DAYA
A cikin babbar hedkwatar hukumar sadarwa ta kasa (Nigerian Communications Commission) da
aka fi sani a takaice da (NCC) da ke kan titin Aguiyi Ironsi Street, Maitama, Abuja, motocin
ma’aikatan su ke ta shigowa daya bayan daya harabar ma'aikatar suna fakawa a faffadar
harabar ma'adanar motoci, wannan motar na wane waccan, duk da cewa ba ranar aiki ba ce,
amma alamu sun nuna wani muhimmin taro ne za su yi na iya ma’aikatansu tare da (Board of
Commissioners) din su a babban dakin taron su wanda ya fi kowanne girma cikin ma’aikatar.
Duba da yadda suke ta shige da fice don ganin komai ya kammala ya yi yadda ake so kafin
isowar Executive Chairman.
Kowannensu tsuke cikin suit mai kalar fari daga ciki, baki daga waje, wuyan ya sha tsuka da
tie din bature, da takalma bakake sau ciki a kafafun su. Sai da duk suka gama hallara a dakin
taron, suka nutsu wajen zaman su, kwamishinoni suka iso suka zazzauna, sannan suka ji daga
wajen hall din dirin isowar jibgegiyar motar Executive Chairman wato PROF. ZUBAIR MOHD.
NUMAN.
Farin dattijo mai kyakkyawar suffar fulanin usli da tsantsar ilmin boko. Inda ace ana kure
boko to da mun ce Prof. Numan ya kure shi. Shi din fitacce ne, kuma sananne a kasarmu
Najeriya akan harkar sadarwa, domin ya dade yana rike da manyan mukamai daban-daban a
gwamanatin tarayyah tun kafin ya karbi ragamar (NCC), sannan tsohon malamin jami’ar
Igbinedeon ne.
Prof. Zubair Muhammad bafullatanin garin Numan ne, don haka kallo daya za ka yi masa ka
tabbatar an zuba kyau a zamanin kuruciya. An sha gwagwarmaya a ilmin boko da ma’aikatun
gwamnati, sannan ana kan damawa da shi a shekarun girman sa, domin kuwa na hannun
daman shugaban kasa ne, duk da ba ya siyasa, shi ne ya dora shi matsayin da yake kai a
yanzu, wato Executive Chairman na Nigerian Communication Commission (NCC).
Prof. Zubair ya shigo hall din cikin kakkarfan takunsa, da ganin sa ka ga bakin bature, a
gefensa hagu da dama wasu santala-santalan ‘yammata ne guda biyu; a ido daya ta girmi daya,
sun yi shiga irin ta ‘yammatan zamani gogaggu, ‘ya’yan gata irin su, wato ‘ya’yan kusoshin
gwamnatin Najeriya. Tafiyar su kadai abar kallo ce, yayin da suka maka bakin glass (prada)
wanda ya cinye kusan rabin fuskar su. Mayafin jikinsu shi da babu duk daya. Har gara na
babbar. Kallo daya za ka yi musu ka tabbatar ‘ya’yansa ne na cikinsa, sabida tsananin
kamanninsu da mahaifin nasu, duk da cewa sun fi shi hasken fata kasancewar su mata.
Shigowar su hall din ke da wuya gabadaya ma’aikatan suka mike domin girmamawa ga
shugabansu. Har sai da ya zauna a kujerar sa tare da ‘ya’yansa a dama da hagunsa a kujerar
musamman da aka tanadar musu, sannan gabadaya ma’aikatan suka zauna a mazaunin su.
Bayan addu’ar bude taro daga limamin ma'aikatar mai gabatarwa ya yi bayanin makasudin
taron, wato taron ba na komai ba ne, na taya murna ne ga ‘ya’yan shi Prof. Zubair ga kammala
karatunsu daga jami'ar National Autonomous University, Mexico. Sannan Prof. Zubair ya mike
ya yi jawabin godiya ga ma’aikatansa da kwamishinonin sa a kan hadin kan da suke ba shi
wajen gudanar da ayyukan su na sadarwar Najeriya.
A karshen bayaninsa kuma ya ce, daga yau ya dora babbar ‘yar sa Engnr. Halimah Zubair
Numan matsayin mataimakiyar sa wato (Executive Vice Chairman), ya kuma dora kanwar ta
Hanan Zubair Numan a matsayin (Human Resource Manager), za su shiga ofis daga wannan
satin mai kamawa. Yana fatan za su ba su hadin kai wajen gudanar da ayyukan su tare da su, kamar yadda suka
saba bashi. Su sani cewa ba ya hada komai da wadannan ‘ya’yan nasa guda biyu, dalilin sa ke
nan na kawo su kusa da shi su yi aiki don ba zai iya barinsu su yi aiki a karkashin wani ba, balle
a taka mishi su, shi ya sa ya kawo su karkashin sa. Hanan sai gyada kai ta ke kamar jangwalagwada, tana taunar cingam kas-kas-kas, cikin jin
dadin bayanan da mahaifinta ke yi. Ai gara duk su san matsayin su a gun Daddy tun yanzu,
kada ma su kawo musu raini don sun gan su yara. Yayin da Haleemah ta sunkuyar da kai cike
da jin kunyar wannan rashin kawaici na mahaifin ta. Me ya hada harkar ofis da kaunar da yake
musu saboda Allah? (This is personal).
Daga nan shugaban bangaren daukar ma’aikata na baya (former Human Resource Manager)
wanda yanzu ya koma karkashin Hanan ya mike cikin rashin jin dadi ya yi wa ‘ya’yan Prof.
Zubair barka da zuwa ma'aikatar NCC, tare da alkawarta musu cewa, za su samu duk hadin
kan da suke bukata tare da su. Ya yi bayanin ne cikin cijewa a madadin sauran ma’aikata, duk
da kokarinsa na boye damuwar wannan ragin mukami da aka yi mishi da ‘yar cikin sa rana
daya.
Daga nan aka fara ciye-ciye da shaye-shaye na alfarma, zukatan ma’aikata cike fal da
magana wadda ba wanda ya isa ya furta. Don haka kowa ya hadiye abarsa. Taron da ya dauke
su awanni biyu cif! Kafin a watse direba ya kwaso su Halima da Prof. Zubair zuwa gida.
Gidan Prof. Zubair na nan a unguwar Asokoro, wani tankareren gida mai ginin sama-da-kasa.
Gabadaya ginin gidan an dauko samfur dinsa ne daga kasar Brunei. Sai dai abin da zai ba ka
mamaki shi ne; daga shi sai ‘ya’yansa biyu suke rayuwa cikin wannan tafkeken tankareren
gidan, sai tarin ma’aikata rututu maza da mata. Babu matar aure a cikin sa.
Asalin Prof. Zubair ya fito daga karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa, ya auri matarsa
uwar ‘ya’yansa Safeeyyah, aure na saurayi da budurwa wadda ita kuma Kanuri ce da ya auro
daga Maiduguri, don haka Halima da kanwar ta Hanan kyawunsu na tudu biyu ne, wani irin
sassanyan kyau da ya maida su tamkar ruwa biyu (fulani/kanuri). Ya basu wata irin kala mai
kyau da daukar ido. Halima ce babba, sannan kanwarta Hanan, shekaru biyar kwarara Halima
ta baiwa Hanan.
Hanan na da watanni tara mahaifiyarsu Safeyyah ta rasu a dalilin cutar (blood-cancer), wato
kansar cikin jini. Daga dangin Halima har na Prof. Zubair sun yi kokarin karbar yaran su rike
masa abin ya faskara, domin gabadaya soyayyar da yake yi wa mahaifiyar su ce ta dawo kan
su. Ya dauki soyayya da kulawar duniya ya dora musu har fiye da kima, musamman Hanan
wadda aka mayarwa sunan Safeeyyah.
Prof. Zubair shi ya ci gaba da rainon Hanan da madarar (NAN) har Allah ya raya ta, da
taimakon dattijuwa (Nanny) da ya daukar musu daga Numan, amma fa aikin Asabe kawai in
Zubair ba ya gida ne, da ya dawo zai janye ‘ya’yansa bangarensa ya ci gaba da kula da su da
kansa baya taba gajiya da hidimar su. Sai da Halima ta yi shekaru goma sha biyu ne Babanta
ya daina kwana kusa da ita, ya ware musu daki kusa da nashi.
Allah ya baiwa Halima wata irin kwakwalwa kamar kwamfutar na'ura mai kwakwalwa tun tana
karama, wannan yana da alaka da tsadaddun makarantun da suke yi daga firamare har
sakandire. Don haka ne ake ta yi mata promotion kan promotion ta gama sakandire a kananan
shekaru tana da shekaru goma sha biyar. Manyan darussan da Halima ta kware a kai sune lissafi da kimiyya, don haka tana gama
sakandire Prof. Zubair ya kai ta kasar Mexico ta yi digiri na farko da na biyu cikin kankanin
lokaci a fannin injiniyancin na’ura mai kwakwalwa (software engineering). Yayin da Hanan ta
karanci digiri a kan (human resource management). A shekarar da Halima ta gama masters
dinta, Hanan ma ta kammala digirinta.
Ko da suka dawo gida bayan kammala karatu Prof. Zubair ba tunanin da ya yi ban da ya
zuba su a ma’aikatar sa karkashin kulawar sa, yadda babu wanda ya isa ya taka masa su. Ko
su sha wahala yana raye.
Ba tare da la’akari da kankantar shekarunsu ba, ai dai suna da kwalayen da suka cancanta,
domin Halima komai nata (first class) ne mai daraja ta farko, Hanan ce mai digiri mai daraja ta
biyu. A hankali zai sa tsofaffin ma’aikata su wayar musu da kai a kan komai na NCC.
Haka nan yake zaune gwauro tun mutuwar Safiyyah bai kara aure ba, domin yana da labarin
yadda matan uba ke wahalar da ‘ya’yan miji wadanda babu uwarsu a gidan, amma fa yana da
dalilin da ke hana shi aure da ‘ya’yansa ba su taba sani ba, sabida yana matukar
taka-tsan-tsan. Daga shi sai Ubangijin sa suka san yana dan taba neman mata. Ba ‘ya’yansa kadai ba, babu wanda ya san da wannan bangaren nasa, sabida ba ya jan
kowa a jiki, dangin sa gudun su yake sabida basu da shi, tsakanin sa da kowa harkar aiki ce
kawai. Sannan bai amincewa su Halima yin kawaye ba bayan dawowar su karatu daga Mexico,
kada a lalata masa su (wanzami baya son jarfa).
Kawar Halima ta jiki daya ce a duniya, wato Zarah Datti. Tare suka yi karatu a Autonomous,
ita Zarah diya ce ga tsohon gwamnan Bauchi, har gobe suna tare da Halimah kusan kullum a
waya.
Wadannan ‘ya’ya biyu na Prof. Zubair halayensu sun matukar bambanta. Duk da cewa kamar
su daya a fuska da zubin halitta. Halima duk wani hali na mahaifiyarsu ta kwashe shi kaf, na
gudun duniya da Yakanah. Yarinya ce mai hankali da sanin yakamata, sannan ba ta dauki
duniya a bakin komai ba, mahaifinsu ya kware su ta fannin addini, domin bai ba su ilmin addini
yadda ya kamata ba, ya fi bada karfi ga ba su tsadadden ilmin boko.
A tarayyarta da Zarah Datti, Halima ta koyi muhimman abubuwa na addini, wankan janaba,
alwallah, hatta sallarta sai da ta gyara. Tana kuma ci gaba da neman sani a kan addini daga
yanar gizo da kasasuwan wa’azin Malamai iri-iri data ke saya domin inganta addininta.
Yayin da Hanan duk wani halin mahaifinsu ta kwashe shi tsaf har da kari; fadin rai, son
duniya da gudun talauci. Duk wata harka in dai da talaka za a yi ta, to Hanan ba ta cikinta.
Shekarun Halima ashirin da hudu da haihuwa, yayin da Hanan ke da sha tara.
*****
Bayan sun dawo gida a ranar, da daddare suka hadu da mahaifinsu a babban falonsa, "Daddy",
kamar yadda suke kiran Baban nasu Prof. Zubair, ya dubi kowacce yana murmushi da kofin
tataccen inibi a hannunsa.
“Duk gajiyar taron ne Halima tun dawowar mu ban ji motsin ki ba?”
Halima ta yamutsa fuska, sannan ta jingina kai a kafadun sa. “Actually Daddy ina cikin wani
tunani ne, sai na ga kamar matsayin da ka ba ni ya fi karfi na, Executive Vice Chairman ta NCC
gabadaya fa! Ni ce mataimakiyar ka, kai kadai ne a sama na, ai ma’aikatan ba za su ga girmana
yadda ka ke tsammani ba tunda sun san experience dina bai kai in karbi wannan babban
matsayin ba”.
Prof. Zubair ya ajiye kofin hannunsa, ya maida hankalin sa ga Halima, ya ce, “Halima ki
fahimci wani abu, Nigeria ta riga ta yi lalacewar da kowa nasa kadai yake ginawa, ba ki da
matsalar komai zan daukar miki P.A (Personal Assistant), sannan tsohon mataimaki na ba
korarshi na yi ba, na hada shi da wani mukamin ne daban da bai kai naki ba. Cikin ma’aikata
kuwa duk wanda ba zai darajja ku ba ko ya girmama ku, wallahi korarsa zan yi, zan kara hada
su in jaddada musu wannan”.
Halimah ta kama kai, “Daddy Please.... don’t, ka barsu haka, na tabbata za su bi umarnin ka
kada ka yi musu tsauri da yawa a kan mu za su tsane mu. Na san yadda zan tafiyar da komai,
amma kamar yadda ka ce din ne ina bukatar personal mataimaki kwakkwara, wanda ilminsa ya
kai ya zama P.A dina”. Ya ce, “Muna da applicants (masu neman aiki) da muka yi (shortlisting) din su ba da jimawa
ba. Zan duba daya a ciki wanda na tabbatar bai taba aiki da kowa ba, kuma bai taba aiki da
kowacce ma'aikata ba. Hikimar a nan shi ne, ina so ya zama abokin shawarar ki, kuma
mataimaki wanda ba zai yarda da munafurcin ofis ba, don na ga duk sun shaqa da mukamin da
na ba ku. To sai dai su mutu, amma kun shigo NCC ke nan in ga wanda ya isa ya taka min ku”.
Halima kasa cewa komai ta yi, sai Hanan ce ke dariya, ta ce,
“Shi ya sa nake son Daddyna, aikin ka yana kyau, Allah ya bar min kai Daddy”.
Ta fada tana mai kwanciya a gefen kafadarsa.
Prof. ya yi murmushi ya ce, “Anything for you my lovely daughters. Ni dai burina ku kula da
kan ku, ku fita harkar maza, ba ku babu samari, don ba zan iya aura wa kowa ku ba, don ba na
jin a wannan zamanin zan samu mijin da zai iya rike min ku yadda nake so ku samu a gidan
aure. Don haka da muguwar rawa gwamma kin tashi, don zan iya daure duk wanda ya bata muku
rai, ko ya muzguna muku har sai igiya ta yi rara. Koda kuwa mijin auren ku ne. So, hakura da
auren shi ya fi alkhairi. Ba abinda ba zan yi muku ba, ko me kuke so, ina kara jaddada muku da
ku fita harkar maza duk mayaudara ne. Sannan idan namiji ya wulakanta ku ni ba zan iya dauka ba, ba zan iya yafewa ba. In kuka
maida hankali bisa ayyukanku, ba irin arzikin da ba za ku tara ba, ba abinda ba zan yi ba don
ganin kun dore cikin kwanciyar hankali da jin dadi. Ina fatan kun fahimce ni?”
A sanyaye Halimah ta gyada kai, Hanan kuwa da karsashi ta amsa,