Showing 21001 words to 24000 words out of 48040 words
Chapter 8 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
ya shiga nashi dakin don ya watsa
ruwa, bayan ya gaya wa Halimah in tana bukatar toilet ga shi nan a cikin dakinta.
Bayan ya rufe komai ya dawo gaban Halimah ya zo ya durkusa ya dora hannayensa biyu a
kan gwiwoyinta. Cikin muryar nan tasa mai kidimata, ta gigitata.... a yau ya qawatata ya
sirantata ya kyautata ta fiye da kullum. Ya yi kasa da ita in a very low tone. Ya ce,
“Among all the beautiful names of the world, that husbands calls their wives, I chose to call
you; Ma’am, because you earn my respect, I respect you Halimah and will forever remember
this respect… I promise you a respect till my last breadth… now, I want to see your beautiful
face. Yanzu ina son ganin kyakkyawar fuskar ki.....) Ko da kuwa a jike ta ke da hawaye… Hawayen da na san ni ne silar fitarsu kuma da yardar Allah zan zama silar komawarsu
murmushi…"
Ya fada yana bude mayafin fuskarta, wannan karon ba ta hana shi ba, sabida yadda
kalamansa suka sanyaya mata zuciya.
(A cikin duka sunaye masu dadi na duniya, da maza ke kiran matansu da su na zabi in kira ki
Ma’am”. Sabida kin samu girmamawata, ina girmamaki Halimah. Kuma har abada zan dinga
tuna wannan girman… na yi miki alkawarin girmamawa har zuwa karshen numfashina)”.
Ta bar shi ya bude fuskar, amma duk kokarinta ta kasa yin murmushi. Ta dago hannayen
Hashim daga durkuson da ya yi a gabanta, wata soyayyarsa na kara mamayarta. Ko da irin
wadannan kalaman na bakinsa sun ishe ta rayuwar farin ciki.
“Ka daina durkusa min, you are my husband, and there is no NCC now, not even the throne,
we are now equal, sai ma kai da Allah ya bai wa fifikon daraja mai girma a kaina, darajar mijin
aure (ka daina durkusa min kai mijina ne, kuma babu NCC yanzu ka sani, balle kujerar ofishin.
Don haka daidai muke ni da kai (ba oga ba subordinate). Karo na farko da ya rungume Halimah cikin jikinsa, da ata irin azama, ya sumbaci goshinta,
karan hancinta sannan bakinta. Bai zurfafa sumbar ba sabida yadda jikin Halimah ya soma
kyarma. Bai san kyarmar ta mece ce ba, he just kissed her lightly idan hakan ne ya ba ta tsoro,
shi da ma bai shirya hakan tsakanin su yanzu ba. Daga haduwar su har zuwa aurensu abu ne
da ya faru cikin dan kankanin lokaci kamar kiftawar ido cikin kudura da iradar Ubangiji, shi da
Halima suna bukatar karin fahimtar juna, shakuwa da sakin jiki da juna kafin mu’amalar aure ta
gifta a tsakaninsu.
Duk da ya dauke bakinsa daga fuskarta jikinta bai bar kyarmar da yake yi ba. Ya rike ta sosai
cikin jikinsa, ya ce, “Why are you shivering?”
Daga Halimah babu amsa, sai runtse idanunta da ta yi. Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciya
da gangar jikinta. Amma ba za ta iya fada masa cewa ya ci gaba da kissing dinta ba. Kada ya yi
mata daukan abin da ba haka yake ba. Ta dade da fahimtar nature dinta, ta dade tana kula da
kanta don ganin ba ta yi zina ba, ko wani abu mai kama da ita. Tun daga lokacin da ta fahimci
ita din na da halittar nymphomaniac, ba don ba ta da damar yin zinar a Mexico ba ko an tsoratar
da ita a kan illarta a addini ko ala’ada, sai don ta dade da burin son yin aure, duk kuwa da ta
san shi ne abu na karshe da mahaifinsu ba ya so su yi.
Now that Hashim is passionately kissing her as her choosen husband, gaba daya sha’awar
duniya ce ta sauko ta rufto mata. Suddenly he stopped, asking her why she's shivering, wanda
hakan ya sanya ta cikin mawuyacin hali. That’s why she is shivering. Amma ta san dole ta rike
kanta don tsira da mutunci da martabarta a idon mijinta kada ya dauka ko dama ta saba ne.
Hashim ya umarce ta da su yi alwallah su yi sallar nafila don nuna godiya ga Ubangiji, wanda
ya maida impossiple-possible ba tare da tsimi ko dabararsu ba. Ita dai binsa ta ke da yadda ya
ce, amma idanunta kusan a runtse suke. A haka aka yi sallar, ya yi addu’o’in da manzon rahma
ya umarta. Sannan ya daga ta zuwa gadonta, ita dai ji ta ke kamar ta rike shi lokacin da ya rufa
mata bargo mai santsi (quilt) ya sake russunawa ya sumbaci kuncinta da idanunta. Ya mika
hannu ya yi mata light-off, da muryar nan tasa mai shiga har cikin jinin jikinta ya ce,
“Sleep well Ma’am, goodnight’.
Ya sake sumbato bakinta a hankali. Sannan ya bar dakin zuwa nasa tare da rufo mata kofa.
So yake ta samu hutu da nutsuwar fuskantar sabuwar rayuwarta. Tabbatar da auratayyarsu a
yau is not a good decision (ba hukunci ne mai kyau ba). Amma ga Halimah abin ba haka yake
ba, ko kadan bai yi mata gwaninta ba. *****
BABI NA BAKWAI
Da asubahi Halimah ta ji husky muryar Hashim na rera karatun Alkur’ani cikin suratul Baqara.
Wani abu da ba ta taba ji ana yi a gidansu ba. Sosai karatun ya yi mata dadi, ta nutsu daga
kwance tana sauraro. Kai ka ce Balaraben Madina ke rera karatun sabida yadda yake baiwa
kowanne harafi hakkinsa da izhari, idghami da iklabi. A can Mexico Zarah na koya mata karatu,
amma ko kusa karatun nata bai yi iri daya da na Hashim ba wanda ke yi da cikakken tajweedi.
Har lumshe ido ta yi tana sauraronsa. Ta mance da lokacin sallah, sai da ya dasa aya, ta
kuma ji shi yana murda kofar dakinta. Ita da fushinsa ta kwana, ya lasa mata zuma kuma ya
janye kayar sa, don haka ta yi maza ta shige cikin quilt ta kudundune ita a dole barci ta ke.
Hashim ya ga lokacin da ta yi wuf! Ta shige bargon. Murmushi ya yi ya karaso gaban gadon,
wasu tausasan kayan barci ne a jikinsa da ya sayo a Malta samfurin (Ralph Lauren). Yana zuwa
ya janye bargon gabadaya tana rikewa yana ja har ya yi nasarar dauke shi tsaf! Gabadayanta
ya dauke ta tana wutsil-wutsil da kyawawan kafafunta ita ya sauke ta ba ta so, bai dire ta a
ko’ina ba sai a toilet.
Ya ce, “Now, make your ablution (yi alwalarki) lokacin sallah na fita”.
Ta wani zumburo baki tare da juya masa baya, “Ka fita na ji”.
Kin fita ya yi, ya ce, “Are you pouting at me? (ni ki ke zumburo wa baki)”.
Tana so ta yi fitsari kuma ya ki fita. Ya dauko sabon brush ya matsa mata maclean din
Sensodyne a jiki.
“Brush your teethes”.
“Na ji, ka fita dai”.
“Mene ne in na ga fitsarinki?”
Halimah ta sa hannu tana tura shi waje yana dariya har ya fice, ta rufe kofar tare da murza
mata key.
Cikin nutsuwa ta yi brush din, ta kama ruwa da alwala. Ta fito don ta tada sallah, sai ta samu
Hashim kwance tsakiyar gadonta. Dauke kai ta yi kamar ba ta ganshi ba, amma wani irin sanyi
ta ji a zuciyarta. The pleasant feeling din da mace ke ji in ta ga mijinta kwance a gadonta. Ta
nufi wajen da suka yi sallah jiya, ta yafa mayafi ta tada sallah. Hashim na observing sallahr Halimah sosai, a take ya gano gyararraki masu yawa a cikinta,
kuma tana idarwa ya gaya mata (in a very polite way) ta yadda ba ta ji ta tozarta ba. Kuma nan
da nan ta dauke gyaran cikin kanta.
Lokacin har alfijir ya keto, ya tashi ya fita ya barta tana shirin wanka. Kafin ta fito ta ji gida ya
dume da kamshin suyar kwai da dankali. Ta fito daure da towel santala-santalan kafafunta na
digar ruwa, ta bude jakar kayanta na gida ta zari marasa nauyi ta saka. Ta koma gaban madubi
ta shafa mai, hoda, lip-gloss, ta yi dauri sassauka da dankwalin material din wanda kalarsa ja
ne da ratsin baki. Kin san irin wannan colour a jikin farar mace, nan da nan ta dauki walkiya ga
natural fatar jikinta mai wani irin glowing na ‘ya’yan hutu.
Hashim da ya shigo ya kusa sakin tray din hannunsa wanda ya jero musu abin karin kumallo
sabida kyan da Halima ta yi. Ya ajiye tray din a gefe ya karasa ga Halimah, hannayensa biyu ya
sa ya zagaye ta cikinsu daga waist dinta. Kallon da ya ke mata duk sai ya sa ta jin kunya, ta
boye kanta a kafadunsa. Ya rankwafa kasancewar ya kere ta a tsawo ya hada bakinsu wuri
guda ya soma wani irin kissing dinta with extreme passion, very deep kisses wanda ya zauta
Halimah ya fitar da ita a hayyacinta nan da nan, ba ta san lokacin da ta riko Hashim a cikin
jikinta ba, kyakkyawan riko mai tsanani kamar za ta balla shi.
Sun dauki lokaci a haka. Hashim na shawagi da ita a duniyar sumba har sai da Halimah ta
kasa daurewa ta kankame shi sosai. Is a great new experience wanda bata san da me zata
kwatanta shi ba.
Ya zame da kyar daga tsatstsauran rikon da ta yi masa, ya ja hannunta zuwa inda ya ajiye
musu karin kumallo. Kunya kamar ta kashe Halimah in ta tuno abin da ta yi. Wanda ta tabbata
Hashim ya gane basarwa yayi. So Hashim is not that Ustaz she is looking him as! Murmushi ta
yi mai fidda sauti a lokacin da Hashim ya dauko dankali a fork ya nufo bakinta. “Oya take your breakfast first, sai ki ji dadin sumbatar miji yadda ki ke so".
Zaro ido Halimah ta yi har sai da ta ba shi dariya. Ture hannunsa ta yi, ta ce, ba za ta ci ba.
Ya ce, “Saboda sumba ki ke so ba shi ba ko?”
Ta narke fuska kamar za ta yi kuka, ta ce, “Haaasheeem…!”
Murmushi ya yi, ya ce, “More kisses are coming, only if you take your breakfast…”.
Tashi ta yi a fusace za ta shige toilet ya yi maza ya riko hannunta.
“Sorry Ma’am, na ga you like it ne”.
Ta soma kokawar kwace hannunta, ba ta san lokacin da ya mike ba sai ganinta ta yi dauke a
hannunsa, yana juyi da ita a tsakiyar dakin. Kafin ya dire ta tsakiyar gadonta ya rungume ta
tsam ya soma yi mata abin da ya fahimci ta fi so. Na yanzu yana wane na dazu. Sai kawai
Halimah ta fara hawaye, bi ya yi da harshensa yana side hawayen bai bar ko daya ya diga a
kasa ba. Hawayen da ta ke yi ba na komai ba ne na farin ciki ne da Allah ya mallaka mata
Hashim. Ta san ta gama yin sa’a in dai a fannin soyayya ne sai ko a sauran fannonin da dan
Adam ba ya rasa ajizanci. Ita kuma in dai da irin wannan soyayyar ko Hashim yankar naman
jikinta zai dinga yi ta alkawarta wa kanta ci gaba da zama da shi har zuwa karshen numfashinta.
*****
Wannan abinci dai, sai da ya sandare sannan aka ci shi. Da rana ma shi ya dafa musu jallof din
sphaghetti da kifin gwangwani suka ci. Ba zai manta ba, ya iya girkin ceton kai ne a zamansa
na dalibtaka a ABU Zaria. Wunin ranar zungur bai je ko’ina ba sai masallaci, yana like da
Halimah tana zuba masa shawagaba son ranta kan jiya ya barta ta kwana ita kadai. Sallah in
zai yi sai ya ce su yi jam’i tare, kasancewar babu masallaci a kusa da su.
Da daddare ya ce ta shirya su fita eatry su samu abin da za su ci. Ko da suka dawo gida,
Halimah ta tsaya tana kare wa gidanta kallo, tana kiyasta ‘yan kayan dakin da Daddy ya yi
mata, duk da kayan masu quality ne odar waje, amma a matsayin Daddy da arzikin da Allah ya
yi masa ‘yar aikinsa zai yi wa wannan kayan a matsayin sadaka ba ‘yar cikinsa ba. Ba ta damu
ba ko kadan don da ma ita ba ta son tarkace, she lives a moderate and simple life, ko a gidansu
dakin Hanan ya fi nata kyale-kyale.
A lokacin ne Hanan ta fado mata a rai ta karbi wayar Hashim ta saka lambarta a ciki ta kira
ta.
“Wato kin samu miji kin manta da ni ko?”
Hanan ta yi wata irin dariya ta ce, “Sis, ashe haka auren yake? Gaskiya Daddy ya kware mu
da yawa, da na san haka auren yake ai da tun gama sakandire na yi PROTEST na yi aure”.
Halimah ta ce, “Sannu maras kunya, ni kawarki ce da ki ke min wannan maganar?”
Hanan ta ce, “Fisabilillahi wa zan yi wa in ba ke ba? We have missed a lot. Yanzu haka ni da
Saleem muna kan hanyarmu ta komawa PortHearcourt, can inda yake aiki. Hope we will keep
in touch”.
Halima ta yi musu fatan sauka lafiya, ta bai wa Hashim wayarsa.
Ya yi dan murmushi jin abin da Hanan ke cewa, a zuciyarsa kuma ya ji yana tausaya musu.
Ba su da kowa da za su kira nasu sai junansu, sai mahaifin da ya juya musu baya.
Halimah ta yi shirin kwanciya kenan cikin wata sassaukar rigar barci, Hashim ya shigo
hannunsa da glass cup mai cike da tatacciyar madarar shanu mai sanyi (fresh milk), ya mika wa
Halimah, ta karba tana masa godiya don dazu ne ta gaya masa sai ta sha fresh milk ta ke iya
barci, don haka a hanyarsu ta dawowa ya tsaya ya saya mata katon din madarar oldenburger
suka dawo da ita. Ya sanya su a firjinta na kitchen.
Ta shanye tare da mika masa kofin, ya karba ya aje gefe, sannan ya matsa gareta yace, “I
want be your masseur (ina so in zama professional mai yi miki tausa)”.
Murmushi Halimah ta yi, ta mika masa santala-santalan kafafunta. A hankali ya soma yi mata
wata irin tausa da ba ta taba ji a rayuwarta ba. Kafin ya saki kafar ya kanainaye ta, tausar da ta
rikide ta koma wani babban al’amari wanda ya rikita duniyar Halimah.
Hashim bai yi niyyar tabbatar da aurensa a daren yau ba, amma halin da Halimah ta samu
kanta ya tabbatar in ya kyale ta, za ta cutu, cutuwa ba ‘yar kadan ba, don haka da amincewarta
komai ya faru, domin lokacin da ta mika wuya ba ta sani ba.
Amma lokacin da Halimah ta bi sahun sauran mata Hashim ya sha duka, cizo, har da
yakushi. Ta gane ashe shayi, ruwa ne, hangen kitse ta ke wa rogo. Ta jinjinawa kowace mace
da ke gidan aure ta kuma gode wa Allah da ta killace kanta wa mijin aurenta kadai, yau da ba ta
san da wane bayani za ta wanke kanta a idon Hashim ba. Wanda farin cikin hakan ya gaza boyuwa daga emotions dinsa. Irin tight rungumar da ya yi
mata, da irin deep kisses din da yake blowing mata lungu-lungu, sako-sako, kusfa-kusfa ya
nuna how surprise and excited he was... da samunta da cikakkiyar daraja da martabarta, a
matsayinta na wadda ta yi karatu mai zurfi a Turai. Take kuma yin rayuwa ta walwala da ‘yanci
ta ‘ya’yan da ake yi wa kallon rashin cikakkiyar tarbiyya.
A tsayin daren bakidayansa daga Hashim har Halimah babu wanda ya runtsa. Sun kira daren
night of majesty a rayuwar aurensu. Hashim bai karanci aikin likita ba, amma taimakon da ya
bai wa Halimah ko likita sai haka.
Kuka kam da shagwaba ya sha su, sai dai ya yi murmushi ya shafa kai ya bada hakuri.
Ma’am ta tashi daga Ma’am ta koma sweetheart a cikin bakinsa ba tare da ya san lokacin da
yake fada ba.
*****
Kwana uku ana shan amarci mai suna amarci. A duka kwanakin nan Hashim ke girka musu dan
abin da za su ci.