Showing 18001 words to 21000 words out of 48040 words
Chapter 7 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
ba karamin tsorata yayi ba, ya yarda da gaske take soyayyar, Hanan ce mai
jinya, duk sanda Halima ta farka sunan Hashim take ambato tana rokon Hanan ta kira mata shi
su yi sallama mutuwa zata yi. Bazata iya cigaba da rayuwa ba shi ba. Hanan sai kuka. Don ita
bata son zancen Hashim dinnan itama, ta kuma yarda da gaske Halima take zata iya rasa
arayuwar ta a kan sa.
Don haka ta dau wayar Halima ta kira Hashim da sunan da Halima tayi saving din lambarsa
"Cheriè". Hashim na dagawa yace "Sweatheart, kina so ki kashe ni ne? Ba kira ba messege? Ni
in na kira bata shiga, saura kadan ki ganni a kofar dakin ki, hutun nan ya isa ki dawo haka! I
can't afford missing you....i love you....". Hanan tayi maza ta cire wayar daga kunnen ta, he's so
caring dole ya tafi da rayuwar diya mace. Sai ta ji bazata iya karya zuciyar sa ba, don ko ya zo
Daddy ba bari zai yi ya shigo ba, ya kafa ya tsare da kujera a gaban gadon Halima kullum.
Shima bai zuwa ofis, komai akan sakatare da Hashim yake.
Jinyar Halima ta ki ci ta ki cinyewa. Daddy bai da niyyar janye ra'ayin sa itama bata da niyyar
janye nata. A binciken likitoci kuma sun ga cewa jinin Halimah ya yi mugun hawa, zuciyarta
kuma ta tabu. Suka yi wa Daddy nasiha a kan ya yi hakuri ya yi mata abin da ta ke so don
tserar da lafiyarta. Yaran yanzu ne ka haife su, amma sai dai ka bi su ba dai su bi ka ba. Daddy
don bakin ciki kasa kallon Halimah ya yi lokacin da ta sake farfadowa, wannan karon ta dan
jima bata kara suma ba, don haka aka kai ta aminity room.
Daddy ya tura kofa ya shiga dakin da Halima ke kwance. Tsayawa ya yi a kanta yana kallon
irin zabgewar data yi, gabadaya ta lalace ta fice hayyacinta. Babban takaicin sa wai akan Da
namiji. Da namijin ma wanda bai isa ya mallake ta ba, mai ci a karkashin ta, yayi kwafa ya dube
ta cikin ido ya ce. “To Halimah, zan miki abin da ki ke so, wato auren dan talakawa, dan aikinki, boyi-boyin ki.
Amma bisa sharudda uku kwarara in kin amince”.
Halimah ta daga kumburarrun idanunta tana sauraron Daddynta.
A yadda yanayin fuskar Daddy ya nuna ba ta hango tausayinta ba, ba ta hango jin kai da
rahmar nan da kullum ke cikin idanunsa in zai dube su ba. Sai dai duk da haka zuciyarta na
karfafarta da cewa, ta amince da ko me zai ce in dai zai yarda ta auri Hashim. A yanzun yana
cikin fushi ne, da ya huce zai koma Daddy dinta da ta sani a baya.
Kuma ba ta jin za ta kasa daukar komai in dai za ta tsira da Hashim.
Prof. Zubair ya ce, “Na amince ki auri zabin ki, a bisa sharudda guda uku; na farko daga ke
har shi kun bar aiki da NCC, ku je can ku nemi aikin da za ku yi ko ma a ina ne ba ruwa na.
Na biyu ba yaji, ba saki babu kawo kara.
Na uku kin daina amfana da dukiyata da komai ya fito daga aljihuna. Zan yi miki kayan aure
kamar yadda kowanne uba ke yi wa ‘yar da ya haifa. Bayan wannan kin gama rabar arziki na
Halimah, ki je can ki yi mummunar rayuwar da ki ka zaba wa kanki”.
Halimah na kuka ta ke neman sassauci daga wadannan tsauraran sharudda na Prof. amma
bai saurare ta ba, cewa ya yi tana bata masa lokaci, ta ba shi amsa kawai, yes or no, don yana
da abin yi a gabansa.
Halimah cikin shesshekar kuka, ta ce, “Daddy aure fa na zabi in yi, sunnar ma’aiki, ba yawon
dandi za ni ba, don Allah Daddy ka sassauta min…...”.
Juyawa ya yi ya ba ta baya jin kukanta na neman karya masa zuciya, ya san dalilin sa na
kafa wadannan sharuddan, dole ta hakura da yaron don ba shi da arzikin da zai iya rike ta, ita
kuma ba za ta iya rayuwar wahala ba, shi ya sa ya yanke wadannan sharuddan. Amma ga
dimbin mamakinsa sai ya ji Halimah ta ce cikin shesshekar kuka, “Na amince Daddy, innallaha yarzuqu man ya sha’u bigairi hisab”.
Prof. ya juyo ya yi mata kallon sannu tantabara sarkin soyayyah, sannan ya yi murmushi
mischievous smile (murmushin keta), ya ce,
“Na ba shi dama ya aiko magabatansa”.
Zai fita daga dakin Halimah ta toshe kukan bakinta, ta ce, “Daddy, ba ka sanya mana albarka
ba!.
Ya sa kai zai fita, jin abin da ta fada sai ya dakata, ya juyo sosai.
“Albarkata ku ke nema ku ka kasa yi min biyayya? Ku je mazanku su sa muku albarka”.
Ya fice daga dakin kamar ya kifa don sauri da bacin rai.
Halimah ta sa kanta a tsakankanin cinyoyinta ta fashe da kuka. Ya’ilahi! Wane irin hukunci ta
yanke wa rayuwarta haka? Shin tsakanin ita da Daddy wane ne mai gaskiya a addini da al’ada?
Shin Hashim zai yi mata halacci irin wanda ta yi masa? How sure is she danginsa za su zamo
mata makwafin Daddy? Arziki wannan na Allah ne, don haka ba ta nadamar wannan sharadin
na daddy, ta fi damuwa da wanda ya ce, babu yaji, babu kawo kara. Ta sani a karkashin kowace
soyayya akwai yau da gobe, akwai sabawa irin ta harshe da hakori, to ranar da Hashim ya bata
mata ko ya bakanta mata wajen wa za ta kai kukanta? Ita da bata da Uwa bata da dangi? Anya
ba ta yi kuskure ba?
Da wadannan tunane-tunanen Halima ta kwana ta wuni. Kafin a sallame ta daga gadon
asibiti.
Ta kira lambar Hashim, yana dagawa bata tsaya sauraron komai ba ta ce, “Daddy accepted
the proposal, kana iya turowa daga yanzu zuwa kowanne lokaci”.
Ba ta saurari cewarsa ba ta kashe wayarta. Domin ji ta yi duk ta daina dokin abun, soyayyar
ta ragu, ba ta ma marmarin ganin Hashim din, something like hatred (wani abu kamar tsana)
take ji a ranta, tunda shi ne ya shiga tsakaninta da Daddynta mai sonta.
Tana kallon kiransa na ta shigowa ta ki dagawa, ya koma turo text su ma ta ki karantawa. Sai
da ta dauki wayar domin ta kashe ne ta ga text dinsa na karshe.
Sweatheart
This is the beginning of our blessings insha Allah… na san yakin da ki ka yi kafin ki samo min
wannan damar mai girma ne. Ni kuma na yi miki alkawarin I will never ever let you down… I will
not disappoint you!!!
Much love, Hashim.
A hankali ta runtse idonta rike da wayar a hannunta, zuciyarta ta dan samu sassauci. Ba ta
da haufi daman a kansa, sannan ta sani he is a man of his word. Ga iya kalamai masu wanke
zuciya. Tana son komai nasa, tana sonsa tana mugun kaunarsa. Amma yau yadda ranta ke
jagule din nan Engnr. Hashim Yakasai, bai da kalaman da za su yi tasirin wanke zuciyarta.
*****
BABI NA SHIDDA
Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. An zo an yi tambayar su duka biyun a rana
daya. Daddy ya ce ba ya so a bata masa lokaci, in sun shirya sati mai zuwa su kawo sadaki,
sannan shi ba zai yi wa ‘ya’yansa biki ba domin ba farin ciki yake da auren ba, aure kawai za a
daura da safe, da daddare kowanne ango ya zo ya dauki matarsa. In za su yi bikin can a
gidansu su suka sani, amma shi ba a gabansa ba, zai yiwa kamfanin shirya gidaje magana ya
je ya yi musu jere, ba ya bukatar wasu taron mata.
Ba abin da ke dugunzuma zuciyar Prof. irin rabuwa da zai yi da ‘ya’yan nan nasa dare daya,
it’s not easy for him, yana dai daurewa ne.
Sati na zagayowa aka kawo sadaki, sadakin Hanan ya fi na halima nesa ba kusa ba. Wannan
ya kara dugunzuma ran Prof. amma bai ce komai ba.
Ranar asabar ‘yan kalilan mutanen da Prof. ya gayyato wadanda duk ‘yan uwansa ne kawai
daga Numan babu abokansa kusoshin gwamnati ko guda daya, ta fannin angwayen ma ba a ba
su isasshen lokacin da za su yi gayyata yadda ya kamata ba, don haka su ma ba su yi gayyata
sosai ba. Karfe goma sha daya na safe aka daura auren ENGNR. HASHIM ISMA’EEL YAKASAI da
ENGNR. HALIMAH ZUBAIR MUHAMMAD NUMAN, HANAN da angonta SALEEM USMAN.
Dan reception din nan da ake yi bayan daurin aure Prof. ya ce ba za a yi ba, kowa ya kama
gabansa, da daddare su zo su dauki amaren su.
Sai lokacin da ya shiga dakinsa ya kulle ya samu kansa da zama yana hawaye. Hawayen sa
ba na komai ba ne na bakin cikin ‘ya’yansa sun zabi aure a kan zama da shi, duk kokarinsa na
inganta rayuwarsu. Duk kokarinsa na ganin cewa ba su nemi komai sun rasa ba. Duk kokarinsa
na ganin cewa sun yi zarra a ilmi da career mafi tsada. Duk rainon da ya yi musu ba tare da
taimakon kowa ba, ya kasa yi musu uzuri, yana ganin sun zabi soyayyah ne a kansa, da yake
shi ma ba wai ya yi zurfi ba ne a karatun addini yana ganin tunda ya rayu shekaru ashirin da
uku ba tare da mace ba, su me zai hana su iyawa?
Yau ne Hanan da Halimah suka yi kukan rashin mahaifiya, zahiri wanda ya rasa UWA a
ganinsu shi ne maraya ba wanda ya rasa uba ba.
Ko ‘yar nasihar nan da ake yi wa amare su ba su samu ba. Ko dan lallen amarci ba su samu
ba balle uwa-uba gyaran da ake yi wa mata a yayin aurensu. Sun yi kuka sosai suna rungume
da juna, angwayen sun iso kusan a lokaci daya, inda Daddy ya sa aka yi musu jagora zuwa
falonsa, ya kuma je da kansa ya taho da Hanan da Halimah. Sai da suka zauna daga gefen mazan nasu, sannan daddy ya fiddo fararen ambulan guda
uku, ya mika wa Hashim, Haleemah da Hanan, sannan ya dora bayani.
“Takardar sallama (dissmissal) daga ma’aikatar NCC. Ba lallai ne sun yi muku bayanin yadda
muka yi da su ba, amma na amince da aurenku ne based on sharudda guda uku, kuma suka
amince.
Babu career dinku na NCC.
Babu yaji, babu kawo kara.
Babu kwabona da zai kara ciwon kai wajen hidimarsu.
Sai ku je ku nemi arzikin ku da gumin ku, domin wannan gumi na ne. ranar da ku ka gaji da
daukan nauyin rayuwar su sai ku dawo min da su, ni bazan taba gajiya dasu ba”.
Ya mike ya bi wani corridor a falon zuwa dakinsa yana share hawayen idonsa.
Halimah ta fashe da kuka, amma Hanan idanunta mirsisi. Ita ba ta ga abin damuwa ba a nan.
Account dinta shake yake da kudi, har doller account gare su. Tana da kwalin digirin jami’ar
National Autonomous University of Mexico, wanda duk inda ta nemi aiki da shi a Abuja da gudu
za a ba ta. Ga mijinta mai babban aiki, dan minister. Sister Halimah ita ce cikin matsala tunda
Hashim bai ajiye ba, bai kuma ba wani ajiya ba. Ita ko ba sa aiki daga ita har mijinta ba za su
tagayyara ba, maganin Halimah kenan tantabara uwar soyayya.
To amma me? Da Hanan ta shiga daki don dauko ATM Cards dinsu da files din credentials
dinsu suka ce dauke mu inda ki ka ajiye mu. Tana tsaye baki a bude, alert ya shigo wayarta,
inda ta ga an zuke duk wasu kudi da ke cikin asusunta. Infact ta san ba aikin kowa ba ne, face
Daddy.
Ashe dai da gasken yake ba za su kara rabar arzikinsa ba?
Hankali tashe ta koma falo tana gaya wa Halimah, a lokacin ne hawaye ya balle daga idanun
Hanan.
Hashim ya sanya tafin hannunsa cikin na Halimah ya mikar da ita, tare da sakalo ta a jikinsa,
a haka suka fita a falon yana jin wata sabuwar soyayyarta na kara mamaye shi. Abin da Prof. ya
yi wa ‘ya’yansa akan sa maimakon ya bata ran Hashim, sai ya dasa wata katuwar bishiya mai
korran yabanya ta soyayyar Halimah koriya sharr a zuciyarsa..... Ta sadaukar da komai saboda
shi… soyayyar mahaifinta, kujerarta ta aiki… dukiyarta… qualifications dinta…...
Sai ya ji filin zuciyarsa ya yi wa soyayyar Halimah kadan, ya aro wani katoton filin ya kara
shimfida mata. Zai tsaya mata a rayuwa irin tsayawar da babu wani namiji da ya taba yi wa
matarsa… zai ba ta soyayya da kauna irin wanda ko a fim da litattafan hikaya na soyayya babu
kamarsu… zai himmatu wajen neman arziki ta kowacce hanyar halali don ganin Halimah ba ta
sha wahalar da babanta ke burin ta sha ba, zai zame mata namiji dan goyo har sai ta rasa
katoton zanin da za ta goya shi… zai zame mata uwa, uba, miji, aboki, dan uwa wanda a
kowane lokaci kirjinsa zai zame mata wajen yin kuka don ta ji sanyi, ko dariya don ta yi nishadi.
Yana rokon Allah ya cika masa wadannan burika nashi don jin dadin masoyiyar da bai taba
gani ko jin labarin irinta ba.
*****
Wani taimako da Allah ya yi wa Hashim shi ne, ya sayi mota Henessy bayan dawowarsu daga
Holland da kudin sallamar da aka yi musu a ofis, kamar ya san hakan zai faru. A cikinta ya tuko
su zuwa apartment din da ya kama musu a Maitama, sabida yadda auren ya zo afujajan bai kai
ga sayen gida ba kamar yadda ya yi niyya, don haka yanzu suna tafe a kan titi yake tunanin ya
fasa sayen gida a Abuja tunda zamanshi a garin ya kare, babu aiki. Gara ya koma mahaifarsa
da matarsa ya saya a can, tunda na can Kano ma zai fi arha har zai samu rarar kudi ya yi musu
wasu muhimman bukatun kafin su ga abin da Allah zai yi.
Tun jiya ya kwashe komai nasa daga estate ya maida gidan da ya kama a Maitama a bisa
tunanin da ya yi na bai kamata ya aure ta a gidan ubanta ba. Sai ga shi kuma tunaninsa ya yi
masa rana.
Tukin motar kawai yake yi zuciyarsa a cunkushe. Ya rasa da kalmar da zai rarrashi Halimah,
wadda ke ta kuka tun fitowarsu. Ta rasa me Daddy yake nufi da ita. Wannan wace irin mugunta
ce bayan ya kore su aiki ya kwace asusun bankunansu, hatta takardun karatun su ma ba za su
tsira da su ba? Idan wani ne ya ce mata Daddy zai yi wa wani haka ba za ta taba yarda ba balle
su ‘ya’yan cikinsa, abin sonsa.
Shin me ye laifinsu don sun yi aure raya sunar ma’aiki? So yake su dauwama a gida tare da
shi har su tsufa su rasa mai aurensu? Hujjarsa daya ce, Hashim bai fito daga irin gidan da yake
so ba, kuma a karkashinsu yake, to ita Hanan in haka ne me ya hana ya kaunaci nata auren?
Da ta hada komai waje daya, sai ta ga cewa, auren ne kawai ba ya so su yi ba tare da wata
hujja kwakkwara ba. Sai bokon sa da yayi masa katutu.
Tana wadannan tunane-tunanen suka isa gidan Hashim, flat house ne karami mai karamin
get, da space na adana mota guda daya. Gaba daya girman gidan bai fi girman bangaren
maigadin gidan Prof. ba, amma Halimah ji ta yi wata irin nutsuwa ta shige ta, wani irin
contentment ya lullube zuciyarta, irin wanda ni’imar aure ke haifarwa ga mace, a lokacin da ta
mallaki gidanta ita kadai.
Da kansa ya je ya rufe get din ya dawo ya rungumi Halimah zuwa ciki. Sai da ya kai ta har
gefen kyakkyawan gadonta, ya yi kokarin bude mayafin kanta, amma ta ki saki. Duk da cewa
zuwa yanzu ta hakura ta daina kukan.
Ya koma ya shigo da akwatunan kayanta, ya rufe ko’ina