Showing 36001 words to 39000 words out of 48040 words
Chapter 13 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
abu na karshe da ba zai
taba yarda ya faru ba a rayuwarsa, shi ne Halimah ta haihu bai yanka wa dansa ragon suna ba.
Lokacin da ya ba wa maigidan notice din su tashi, cewa ya yi ai kudin shekara suka biya,
kuma yanzu watanni biyar ke nan, sai dai in ya maido musu rabin kudinsu ko ya bari zuwa
karshen shekara su tashi.
Hashim kamar ya yi hauka, ya ce su tashi ya sayar da gidan, zai cira a ciki ya ba su.
Dillalin gidaje na unguwar Janbulo ganin yadda Hashim ya ke a uzurce da son saida gidan da
gaggawa lokacin da ya je ya same shi, sai ya yi wa gidan tayin wulakanci, kashi talatin cikin dari
na kudinsa na zahiri. Without a second thought Hashim ya ce ya sayar da gidan da ya zubar da
guminsa da lokacinsa ya mallaka a kudade naira miliyan biyu kacal.
Makotan Hashim sune shaidun sa, suka sa hannu shima yasa, cinikin gida ya tabbata, gidan
Janbulo ya tashi daga mallakar Hashim.
Hannu da hannu suka ba shi kudinsa, don Hashim ko account ba shi da shi yanzu, banki sun
rufe shi, jimawa da ya yi ba ya amfani da shi.
Ya zubo kudinsa a babbar leda ya yana tafiya da sassarfa a gefen titi cike da farin ciki yana
kiyasi, kiyasin abubuwan da zai saya wa Halimah da babynsu; Katon ragon sunan da zai saya;
dandasheshen leshin da zai saya mata ta daura ranar suna; da kiwonta da zai dawo mata da
shi ta yi ta cin kwai da nama ta samu jini a jikinta ta maida wannan komadar. Da shagon kayan
masurufin da zai sake bude…....... sai ji ya yi da mugun karfi an warce ledar hannunsa, daya ya
cilla wa daya sun haye lifan sun bace a titin kamar kiftawar ido.
Saboda gigicewa Hashim takawa ya yi da gudu iya karfinsa a kan titi ko zai cimma wadan
nan marasa imani, amma yana hawa tsakiyar kwalta ya ji an yi sama da shi an wulwula shi,
sannan ya fado tim! Tsakiyar titi jina-jina.
Duk da muguwar buguwar da ya yi ta ko’ina, amma bai fita a hayyacinsa ba, fadi yake,
“Matata tana asibiti, don Allah ku taimake ni ku kai ni Aminu Kano”.
Wanda ya buge shi din ya ce, “Kai ma ai asibitin ka ke bukata, na yi zaton ba ka da hankali
da ka hawo tsakiyar motoci kana gudu, ashe da hankalinka, tunda har kana sane da matarka da
ke asibiti”.
Suka kakkama shi suka sanya shi a motar mutumin suka nufi Aminu Kano da shi.
A A&E aka karbe shi inda suka yi masa treating ciwuwwukan da ya ji, suka yi masa dorin
karaya a kafa, wanda ya kade shi duk shi ya biya komai. Har ya gaji da surutun Hashim a kan
matarsa da ke asibiti rai a hannun Allah, ya taimaka masa ya kai shi wajenta.
Da zai tafi ne ya ji tausayin Hashim ya kama shi, da ma har yanzu akwai mazan da ke son
matansu haka cikin al’ummar Hausawa? Ya ce da shi,
“Gaya min dakin da matar taka ta ke, in je in gaya musu, ni zan wuce gida, ka yi hakuri ba ni
da laifi domin kuwa gabana ka sha ina kwarara gudu”.
Hashim ya gaya msa tana gynae emergency ya tambayi nurses din Halimah Zubair da aka
kawo dazu, tunda suna da sunan kowace patient tare da su, tana tare da kanwarta Sa’adatu da
mijinta Lawal
Ba jimawa sai ga mutumin tare da Lawal da Sa’adatu hankali tashe. Sa’adatu ta fashe da
kuka ganin mummunan yanayin da yake ciki, har da karaya. Lawal yana ta tambayarsa garin ya
ya? Ya kau da kai ya labarta musu komai har mutumin da ya kade shi yana jin su.
Sa’adatu ta ce, “Yaya me ya kai ka? Wa ya aike ka ka sayar da kadarar da ta rage maka? Ka
ke samun sanyi daga karkashinta?”
“Kaddara Sa’adatu, kaddara!” Ya fada yana lumshe idonsa.
“Ya ya jikin Halimah? Ta ci abinci?”
Lawal ya gaya masa tun kawo ta barci ta ke yi, amma an sa mata ruwa da jini, kuma likitoci
na ta kokari a kanta. Sun ce babyn ma ba ya motsi yadda ya kamata sabida ba ta cin abinci.
Hawaye suka zubo daga idon Hashim, ya ce,
“Sa’adatu ba ni da sa’a a rayuwa ta!”.
Ta kama hannunsa ta rike cikin nata, “Kada ka ce haka Yaya, ka ce, alhamdulillah cikin
kowanne hali, domin kuwa ka fi dubu. Ni zan je gida yanzu in samo muku abin da za ku ci, na yi
waya da Yaya Rabi’a ta ce tana zuwa yanzu”.
Bai ce komai ba, ya maida idanunsa ya runtse. Mutumin ya fice ba tare da sun lura da shi ba.
Sa’adatu da Lawal ma suka fita, shi Lawal sallah zai yi ya dawo, ita kuma adaidaita ta hau zuwa
unguwarsu Dorayi.
Ba ta fi awanni biyu ba ta dawo da filas din shayi da na abinci, ta yi musu tuwon dawa miyar
busasshiyar kubewa, Lawal ya zuba masa, ita kuma ta dau na Halima ta tafi.
Kwanansu biyar ke nan suna jinyar Hashim da Halimah. Halimah ta fara jin karfin jikinta, da
ta tambayi Hashim, Sa’adatu ta gaya mata komai.
Halimah ta wani irin lumshe idonta..… gidan da ya rage musu ma ya sayar, barayi sun
kwace kudin, mota ta buge shi...… duk a dalilinta. Ko dai gaskiya Yaya Rabi’a ta fada, farar
kafar ce da ita?
Yaya Rabi’a tun zuwanta na farko da Sa’adatu ta gaya mata duk abin da ya faru, takaici bai
barta ta kara dawowa ba. Ko duba Halimah ba ta shiga ba, sai abinci ta ke aiko musu kullum
sau uku a rana, don haka Sa’adatu ta huta komawa gida yin girki.
An riga sallamar Halimah bayan likitoci sun tabbatar da koshin lafiyarta da ta abin da ke
cikinta. An dade da maida Hashim male ward bangaren wadanda aka yi wa aikin kashi. Ana
i-gobe za a sallame shi mutumin da ya kade shi ya zo don su yi sallama ta karshe.
Bayan sun gaisa ya ce da shi, “Sunana Alhaji Aminu Kwangila, ni dan Kano ne gaba da baya,
sana’ata ita ce kwangila. Na tausaya maka kan abin da ya same ka, Allah ya yi maka sakayyah
ta alkhairi.
Ga wannan na ba ka kyauta fisabilillahi, amma ka tabbata ka je banki ka bude account ka
zuba su a ciki. Yanzu Najeriya ba irin ta baya ba ce, ba tsaro ba gaskiya, babu tausayi a
zukatan bata-gari. Kada ka kara yawo da kudi masu kauri a jikin ka’.
Ya ajiye masa cheque na kudi na gugar wuri har naira miliyan uku. Hashim ya kasa gasgata
abin da yake gani, don haka he is speechless, wordless, motionless har sai da ya ji Alhaji
Aminu yana yi masa sallama zai wuce, ya sauko daga gadon ya ba shi hannu idanunsa taf!
Hawaye, “Allah ya yi maka sakayya da mafificin alherinSa”.
“Ameen kanina, Allah ya ba ka lafiya”.
Daga haka ya fice, sallamarsu da Alhaji Aminu kenan.
Washegari aka sallame shi, bai zarce ko ina ba daga asibiti sai bankin Zenith, ya bude
account ya karbi kudinsa ya alkinta su. Aka ba shi ATM card, ya ciri wasu masu dama ya nufo
gida.
Halima zaune ita da zungureren cikinta, daga ita har jaririnta kugi cikinsu yake yi, rabonta da
abinci tun kokon safe da makwabciyarsu ke sayarwa da ta sayi na naira talatin ta sha. Jiran
dawowar Hashim ta ke yi don yau za a sallame shi, ba ta da kudin mota da ta je sun taho tare.
Kafafunta mike kan yagalgalalliyar kujerar falon ta tun ta aure. Ta tsufa, yadin ya faffarke ta
burma ciki. Tunani ta ke kafin ta haihu za ta kwashe su ta sayar wa Lawan da yake kafinta ne
inyaso ko riga ce ta saya wa babynta da kudin.
Hashim ya shigo da sallama, hannunsa rike da ledoji manya-manya, rabon da ta ji muryar
Hashim da wannan karsashin ba za ta iya tunawa ba. A hankali ya zauna saboda kafarsa ba
duka ta warke ba. Wani kasalallen murmushi ya kashe Halimah da shi.
“Sannu da gida Maman Innata”.
Murmushi ta yi masa, “Sannu da dawowa, ya ya jikin?”
“Alhamdu lillah, kafa ta yi kyau, sai dai a can ciki ina jin ciwo sosai”.
Ledar farko ya janyo ya bude ya fiddo kwalin danyar madarar oldenburger sai rabar sanyi ke
fita a jikinta. Yawun Halimah ya yi bala’in tsinkewa.
“Yaushe rabon duniya da ayyaraye!?”
Halima ta ce a zuciyarta kafin ta gama hadiye miyau, Hashim ya fiddo wata zazzafar
gasassar kaza gashin Yahuza Suya, an yayyanka ta an zuba mata vegetables yankakku a
kanta.
Tura su ya yi duka gaban Halimah.
“Ci ki koshi Sweetheart”.
Abinki da mai tsohon ciki, tana aika madarar nan a cikinta dan cikinta wani irin juyi ya hau yi,
tabbacin bai taba cin abu mai dadin wannan ba. Saboda dokantuwa da cin naman ba ta samu
zarafin yi wa Hashim tambayoyi ba sai da ta ci ta koshi, a lokacin shi kuma Hashim ya tafi don
ya yi wanka. Da ta bude sauran ledodin hawayen dadi ne suka zubo mata, shawul din daukar jariri guda
uku, kayan sanyi saiti uku, dirkekiyar diaper da kayan baby (overall) wajen kala ashirin. Ga wani
tsadadden leshi ruwan zuma mai duwatsu da ratsin choculate colour, atamfa Holland, Super da
shadda, mayafai da suka shiga da kayan da takalma da jaka (flat) samfurin vincci Hashim ya fito ya taddata tana duba kayan, da suka hada ido tambayoyi da tuhuma ne fal
idanunta. Murmushi ya yi ya wuce yana saka kaya. Sai da ya shirya ya yi fresh abinsa, sannan
ya zauna ya fayyace mata komai.
Farin ciki ya nuna a kan fuskarta, amma sai ta ce, “This is too much Cherie. Ya ba ka ne don
ka yi wani muhimmin abun da su. Bai kamata mu yi bushasha ba, kada ka manta ba mu da
sauran kadara yanzu”.
“Na sani Sweetheart, amma ban ga amfanin arzikin da ba za ki ci shi ba. Bai fi 150k na kashe
ba, na kuma ware na ragon suna. Sa’adatu zan saya mata firji ta fara sana’a, ke ma haka in
kina so, sannan poultry dinki zan mayar miki. Duka-duka za a kashe atleast 500k, saura 2m+
mu yi shawarar geniune business din da za mu yi”. Halimah ta yi dan tunani, ta ce, “Duniyar bakidaya yanzu ta information technology ce. Ina
ganin ka kama babban shago a bakin titi a yi business center and internet café, a kuma dinga
sayar da assessories na waya a shagon, a sayi injin photocopy da duk abin da ya shafi
computer na tabbata zai samu karbuwa. Ga ka guru a kan computer”. Murmushi ya yi ya kwanto da barin jikinta a jikin sa.
“My wife is forever clever. She always thinks rationally. Wannan shawara ce mai kyau, kuma
da ita zan yi amfani insha Allah”.
*****
Kafin Halimah ta shiga EDD dinta duk abin da suka shawarta ya kammala. Tare suka zauna
suka tsara komai suka lissafa. Kyakkyawan business center and internet café ya kammala a
kan titin tsohuwar jami’ar Bayero.
Yanzu sun maida hankalinsu ne kan jiran haihuwar Halimah.
Sa’adatu ta yi matukar murna da katoton freezer dinta, iri daya da na Halimah, ga kajinta sun
dawo. Rayuwa ta fara yi musu gardi.
Hashim kullum ya tafi shago hankalinsa yana kan Halimah, don haka ya saya musu sababbin
kananan wayoyi shi da ita. Akai-akai yake kiranta yana jin halin da ta ke ciki, sannan karfe biyar
ya rufe shago ya dawo gida.
Sai yanzu da ta yi waya, ya tuno da lambar wayar Hanan da Seun ya taba bata, ta yi mata
kyakkyawan boyo a cikin filonta.
Yau da Hashim ya fita ne ta tuno da lambar. Ta taka tinkis-tinkis da zungureren cikinta ta
dauko takardar. Bugun farko layin ya shiga, amma har ta tsinke ba a daga ba. Haka ta yi ta
gwadawa har Allah ya taimake ta mai wayar ta daga.
“Hello”. Hanan ta fada da muryar gayunta da ba ta taba canzawa.
Halimah ta lumshe idonta, wani irin farin ciki ya ratsa ta. For the first time da ta ji muryar
Hanan bayan rabuwarsu shekaru kusan biyar.
“Sunana Halimah Zubair Numan”.
Hanan a kwance ta ke, ba ta san lokacin da ta mike tsaye ba. Ta kankame wayar hannunta.
Da karfi ta ce, “Sis LEEMAH! Ke ce?
Where have you been all these while sis Leemah?
Ki ka bar ‘yar uwarki cikin wahala da qaqa-ni-kayi da rayuwar kaico! Babu kowa a tare da ita”.
“Ke ce ki ka bar ni Hanan, bayan tafiyarki PortHercourt ba ki kara kirana ba. Ni in na kira ba
ta shiga. Muka zo muka bar Abuja zuwa Kano, tun daga nan life was not as it was before, things
have changed abruptly. So many bitter experiences… months back, I came to Abuja just to
reconcile with Daddy… A karshe ya kore ni Hanan, ya kuma bini da muguwar addu'a. Seun, ya ba ni lambarki. I’m
about to become a mother now Hanan, how was life there with you? Domin na ji wani abu mara
dadi a bakin Daddy… concerning you!”
Tunda ta fara bayani ko sau daya ba ta tsaya ta sha numfashi ba don tsoron kada Hanan ta
sake kubuce mata. Hawaye sai ambaliya suke a fuskarta.
“Salim ya sake ni Sis”.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. In ji Halimah.
Hanan ta kankame wayar hannunta sosai don kada Halimah ta kara kubuce mata. A gurguje
ta shiga ba ta labari.
“Bayan mun rabu, PortHearcourt muka koma, zamana da Salim zama ne na soyayya zallah.
Yana sona, yana kula da ni shekara biyu babu haihuwa, sai bari (miscarriage) da nake ta yi.
Daddy bai taba nemana ba ko sau daya, danginsa ko na Mama ban san inda zan gansu ba.
Aka zo aka yi ma Dad din Salim sarauta muka dawo Arewa, nan Maman Salim ta ce sai dai
ya bar ni wajensu ya koma shi kadai in ya so ya dinga zuwa duk karshen wata.
A wannan zaman da na yi tare da su ne suka gane komai da ya shafe ni, ba ni da dangi,
ubana ya sallama ni. As a royal family as they are… wannan abun kunya ne a gare su, su hada
iri da ni, jikokinsu za su tashi babu dangin uwa, wanda su kuma hakan abin kunya ne a gidan
sarautarsu. Suka yi wa Salim umarni ya sake ni, suka aura masa mai asali da gatan iyaye. An raini family dinsu da bin umarnin na gaba, don haka Salim ya rufe ido ya ba ni takardar
saki har guda biyu.
Ba irin neman da ban yi miki a Abuja ba, har gidan da ku ka zauna na bincika na je, na tadda
wasu a gidan suka ce kun dade da tashi, basu san inda ku ka koma ba, za ki ce waya, bayan
mun koma PortHearcourt na canza layi to get rid of my boy friends don kare darajar aurena, na
manta cewa lambarki na ciki, kuma na yi destroying layin. Dole kan ba yadda zan yi na dawo gida kamar yadda ya kore ki ni ma korata ya yi, amma
ban yarda na tafi ba, a wajen ajiye motoci nake shimfida dankwalina na kwanta, har tsayin
kwana uku, duk yana kallona ta CCTV.
A rana ta hudu ne ban sani ba ko tausayina ya ji, sakamakon ruwan sama mai thunder daya
kare a kaina, ya sa Seun ya kirawo ni, ya tambaye ni me ya dawo da ni? Na gaya masa komai.
Ya ce, "Yanzu kin yarda wannan shi ne abin da nake gudar muku… wulakanci da tozarcin
maza? A raina na ce, kai ka jawo aka wulakanta nin ai, tunda kai ka maida ni mara gata don
kawai na zabi AURE...sunar Anabi SAW......to such an extent