Showing 6001 words to 9000 words out of 48040 words
Chapter 3 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
jibanci ilminsa da shi kansa. Kwarai
hazakarsa ta yi matukar impressing dinta. Sannan kamannin sa, kwarjinin sa da haibar sa sun
tsaya mata a rai. A hankali ta maida takardun cikin jakar, sannu a hankali ta ja motar ta fita daga harabar
gidansu zuwa asibitin Nizamiye.
Yana zaune a gefen gadon kafafunsa a kasa, baki, dogo, siriri wanda kai tsaye za ka kira shi
da handsome, gantleman. Ga Halima ba wannan ne a ranta ba; kimarsa ta karu a idanunta ne
bayan takardunsa da ta gani. Ta kuma tabbata neman aiki ya kawo shi NCC don tana sane da
zuwan applicants din da aka yi shortlisting dinsu, wadanda aka yi wa aptitude test tun kafin
kama aikinsu ita da Hanan. Wanda muhimmin abin da ya sa Daddy bankado takardunsu don ya
nema mata P.A ne a cikinsu.
Da sallama ta shiga, ya dago manyan idanunsa ya dube ta. Ba su da maraba ita da yarinyar
dazu, abin da ya sa ya gane ba ita ba ce shi ne, wannan ba ta kai ta haske ba, sannan ta fi ta
kaurin jiki, kuma tana da tauwadar Allah a gefen dogon hancinta. Sai ya kasa amsa sallamarta.
Ta ja farar kujerar da ke gabansa ta zauna.
“I’m sorry, ni ce na buge ka dazun accidently kana tafiya bisa titi, na yi horn, na yi horn ba ka
matsa ba. Ina kokarin kauce maka wata motar ta fuskanto ni dole motata ta shafe ka ka yi
hakuri please, tsautsayi ne”.
Ta fada cikin tattausar muryarta wadda ta kara tabbatar masa ba yarinyar dazu ba ce.
Wannan ta san mutuncin mutane kuma tana da hankali. Amma duk yadda aka yi suna da
kakkarfar alaka.
“I’m Halimah Numan”.
Ta fada in subdued (cikin yin kasa da murya).
“I’m Hashim Yakasai”. Ya bata amsa a takaice.
“Na gode Mr. Hashim, takardunka suna wajena, in ka amince zan yi amfani da su, daga nan
zuwa jibi da za a sallame ka”.
“Babu komai”. Ya fada yana kara mamakin ma’aikatar da ya kawo kansa, ma'aikatar da tayi
ficce da kaurin suna a Najeriya, highly compepetitive, ashe NCC din duka ma’aikatar kananan
yara ce?
“Ga abinci Mr. Hashim, let me serve you”. Ta fada tana mai janyo kwandon da ta shigo da shi.
Ta zuba lafiyayyen abincin da farfesun kayan ciki a dan karamin bowl ta mika masa. Karba ya yi
don cikinsa rabonsa da abinci tun daren jiya. Ba bata lokaci ya soma ci yayin da Halima ta
maida hankali ga danna wayar hannunta. Da ya gama cin abincin ne ta soma yi masa tambayoyi, daga wane gari yake? Me ya zo yi
NCC har ta buge shi? Me ya kautar da hankalinsa haka?
A takaice ya ce, ya zo intabiyu ne, unfortunately bai samu ya yi ba. Hawan shi kan titi kuwa
ya yi nisa a tunani ne, daga Kano yake.
Daidai lokacin aka kira sallar magriba, don haka Halima ta yi masa sallama da alkawarin
gobe kafin ta shiga wajen aikinta za ta zo ta ga lafiyarsa.
Halima ta koma gida ta tarar Daddy da Hanan sun dawo. Sallah ta yi, sannan ta fadi abin da
mai girkinsu za ta kawo mata. Sai da ta gama cin abinci sannan ta sanya takalminta na zaman
gida ta nufi falon Daddy.
Prof. Zubair ya kura mata ido. Tana karasowa zuwa kujerar da yake zaune, ta zauna gefensa
tare da dafa kafarsa ta dama.
“Daddy sannu da gida”.
“Yau ina ki ka je Halima throughout ban ganki a ofis ba?”
“Tsautsayi ne ya same ni Daddy, wani bawan Allah na buge da mota, yanzu haka na kai shi
asibiti yana karbar treatment, ina wajensa tun dazu”.
Hanan ta ce, “To tunda kin kai shi asibiti kin biya kudin magani zaman me za ki je ki yi a
wajensa?”
Harararta Halima ta yi, “Ki daina sa min baki in ina magana tunda ba da ke nake magana ba”.
Hanan ta zumburo baki, ta kauda kai.
Halima ta dubi Daddy tana murmushi, “Daddy I have found my P.A (na samu P.A dina)”.
Prof. Zubair ya kalle ta yana dan cakuda fuska, “Bayan ma’aikatan da Hanan ta dauka yau?
Na zata a cikinsu za a zabi daya?”
Girgiza kai Halima ta yi, “No Daddy, na zabi Mr. Hashim, bari in kawo maka takardunsa ka
gani. Shi ma ya yi aptitude tuntuni”.
Ta mike zuwa dakinta ta dauko takardun daga inda ta adana su. Ta kawo wa mahaifinta.
“Hashim Isma’eel Yakasai”. Prof. Zubair ya fada a fili, “Takardunsa are excellent. Tunda kuma
ya yi miki shi ke nan, gobe Hanan sai ku ba shi offer”.
Hanan ta sake zumburo baki.
Halima ta yi wa mahaifin nasu godiya, ta ce za ta je ta kwanta don gobe sammako za ta yi
tunda yau ba ta je ofis ba.
Washegari ma haka Halima ta karbi breakfast ta tafi da shi asibiti.
Yana kwance idanunsa a lumshe. Tsammani za ka yi barci yake yi, nan kuwa zugin dinkin da
ke goshinsa ne ya dame shi. Halima ta yi sallama ta shigo biye da ita nurse ce dauke da
kwandon abinci. Ya bude idanunsa da ke lumshe sun canza launi sabida rashin barcin da bai
samu ba jiya. Ya amsa sallamarta, Nurse din ta ba shi magani ta fita bayan ta zuba masa
abincin da Halima ta kawo.
“Ya ya jikin Mr. Hashim?”
“Alhamdu lillah Ma’am”.
Daga haka duk suka ja baki suka yi shiru. Daga bisani Halima ta duba agogon (swatch) da ke
daure a damtsen hannunta. Ta dube shi fuskarta na nuna kulawa.
“Lokacin shiga ofis dina ya yi, idan na tashi zan biyo ta nan in kara ganin jikin naka. Ga karin
kumallon ka, let me serve you…” Ta fada tana janyo kwandon gabanta, ta zuba mishi chips da
egg da plaintain a plate ta hada mishi shayi mai kauri ta ba shi, sannan ta yi masa sallama ta
juya cikin takunta na nutsuwa ta fita. Shi kuma ya bi ta da kallo, kafin ya sauke idanunsa a kan farantin hannunsa, cikin ransa
yana jinjina wannan kirki irin nata, duk da cewa daga ganinta ka ga ‘yar wani kusa a kasarmu ta
Najeriya.
****
BABI NA UKU
Engnr. Halima Zubair Numan, ta shiga ofishinta a kan lokaci yau. Ta daidaita bisa teburinta
yayin da sakatariyarta Rose ta shigo mata da files din da za ta duba. Da adadin mutanen da za
ta gani a yau. Amma ko me take yi tunanin patient dinta na Nizamiye Hospital yana manne cikin
ranta. Waya ta dauka ta buga ofishin Hanan suka yi magana, sannan ta kira sakataren Hanan ya
karbi umarnin da ta ba shi. Kafin lokacin tashinta ya yi offer din Mr. Hashim ta shigo hannunta,
don haka tana tashi asibitin Nizamiye ta nufa tana murza sitiyarin motarta cikin gwaninta.
Ta same shi yana sallar la’asar, za ka iya gane daga wanka ya fito, domin sumar kansa a jike
ta ke, sai dai kayan jikinsa su ya mayar, wadanda har da digon jini a jikinsu. Halima ta ji ba dadi,
me ya sa ba ta yi tunanin sayo masa ko da jallabiyya ba ne? Ko ta karbo masa kayan Daddy?
Da ya idar da sallah ne suka hada ido a lokaci guda, Halima ta yi masa murmushi. Sannan ta
ja kujera ta zauna, shi ma ya koma gefen gadon ya zauna. Magana ta ke a waya inda ya
fahimci tana kwatanta wa wani dakin da suke ne. Ba jimawa sai ga wata budurwa kabila ta
shigo dauke kwandon abinci. Tana gaishe su ba ta tsaya ba ta fita. “Ka yi hakuri Mr. Hashim, I was too occupied at office ban samu kawo abincin rananka a kan
lokaci ba. Ga wannan please ka duba”. Ta mika masa takardar da ke kalmashe cikin ambulan
sannan ta maida hankali ga zuba masa abinci.
Hashim Yakasai ya dauka mafarki yake yi, ko ko cikin zautuwa yake ganin abin da yake gani
rubuce a kan takardar. Doguwar takardar daukar aiki ce (offer letter) da NCC dauke da matsayin
Technical Assistant ga mataimakiyar shugaba. Sai ka’idojin daukar aiki. Ya tambayi kansa, “Ba
dai wannan yarinyar da ke gabansa ce mataimakiyar shugaban NCC ba? He can’t believe it”.
Ya kasa gaskata idanunsa.
“Ina fatan Mr. Hashim zai yi farin cikin yin aiki tare da ni, matsayin personal assistant dina?”
Ta fada tana mika masa plate din abinci.
Hashim ya kasa magana don har yanzu bai fita daga shock din da yake ciki ba. Amma a
karshe sai ya ga bai kamata ya yi mamaki ba, don da ganin Halima ka ga mai dimbin ilmi a
kananan shekaru, sannan bai san matsayin ubanta ba. Don haka daukansa aiki da ta yi a dare
daya bai kamata ya mamakantar da shi har haka ba. Ya karbi plate din da ta ke mika masa, sannan bakinsa ya motsa wajen yin godiya. Godiyar
da bai san iyakar wadda zai yi ba. Halima ba ta bi ta kan godiyarsa ba ta mike tana rataya
jakarta.
“Zan wuce gida Mr. Hashim, sai gobe kuma, direba zai zo ya tafi da kai ka dauko kayanka
daga inda ka sauka. Muna da estate na ma’aikatan mu, za a ware maka gida a yau in ya dauko
ka zai wuce da kai can. Sannan akwai motar office da za ka rika amfani da ita, gobe zai damka
maka mukullin in ya kai ka”. Tana fadin haka ta juya a kan duga-duganta tana fadin,
“Na barka lafiya Mr. Hashim”.
Hashim saukowa ya yi daga gadon ya yi sujudush-shukr, ya dauko wayarsa da ya jona a caji
ya kira Inna Hajara da yayarsa Dr. Rabi’a duk ya gaya musu wannan nasibi da ya same shi
rana daya. Kusan sun fi shi farin ciki, Inna nata zabgawa Halima addu’a.
Wannan shi ne mafari, tushen duka kaddarorin Halima da Hashim. Wanda yake a rubuce
tamkar zanen dutse a allon kaddarar su. Kaddarorin da da a ce sun san za su faru, da tun daga
asibiti kowanne ya kama gabansa. To amma ita kaddara rubutacciya ce da ba abin da ya isa ya
kankare ta.
****
Hashim Yakasai, zaune a kan kafafunsa ya sunkuyar da kai yana sauraron Prof. Zubair, a
lokacin da Halima ta gabatar da shi gare shi. Prof. Zubair ya dube shi ya dinga zubo masa
tambayoyi kamar ma’aikacin BBC. Hatta tushen uwarsa da ubansa sai da ya tambaya, da
sana’ar mahaifinsa kafin ya rasu, tunda Hashim yake bai taba haduwa da murdadden dan boko
irin Prof. Zubair ba. Daga karshe Prof. ya ce,
“Ka yi hakuri tambayoyina sun yi yawa, wasu kuma za ka ga ba su da alaka da aikinka.
And you may find my questions too strict (za ka iya jin tambayoyina sun yi tsauri), hakan ya faru
ne saboda da gudan jinina za ka yi aiki, yaran da bana hada su da komai, don haka duk wanda
zai yi alaka da su dole in sanshi ciki-da-bai. Sannan in ja masa kunne… my two daughters are
precious than diamond!. Ko da wasa kada ka yi abin da zai bata wa Halimatu rai, ka yi duk abin
da ta umarce ka ba tare da musu ba. Ka yi mata biyayya kamar yadda za ka yi mini muddin
kana so aikinka ya dore.
Idan ta kawo min complain ko guda daya a kanka, ka sani ka bar NCC kenan. Ina karbar
excuse a kan komai amma ban da akan my daughters. Sannan duk abin da ka gaya min ba wai
na hau kai na zauna ba ne, a’ah, ina da mutane a Kano da zan sa su binciko min komai a
kanka. Idan na samu karya ko daya cikin abin da ka fada a kanka ko iyayenka da muhallin ku,
ka bar NCC. Ina fatan Mr. Hashim ya fahimce ni?”
Hashim kansa na duke, yana mamakin wanna dattijo ya amsa da cewa,
“Na fahimta ranka ya dade, kuma insha Allahu zan kiyaye”.
Halima ta lumshe idonta cikin takaicin Daddyn nata, ba ta san yaushe zai daina wannan halin
nasa na rashin kawaici a kansu ba.
Hanan kuwa ba abin da ta ke so a duniya irin ya dinga wannan gargadin a kansu, wannan ne
ke ba ta damar taka su yadda ta ke so, yake kuma kara mata fadin rai da ji da kai.
Daga wannan ranar Engnr. Hashim Yakasai ya kama aiki a NCC karkashin ofishin Executive
Vice Chairman wato Engnr. Halimah Numan. Ofishinsa na manne da nata kamar ciki da falo ne,
sannan a tadda ofishin sakatariya inda ake karbar baki. Cikin dan lokaci suka gane cewa,
kowannensu mai kwazo ne har fiye da dan uwasa. Tun Hashim na mamaki idan Halima tana
initiating abubuwa tana fadin yadda za su tsara su cikin ilmi da sanin makamar aiki, da yadda
shi kansa mahaifinta ta ke cin sa gyara a wasu abubuwan, Hashim har ya zo ya daina mamaki.
Ya yarda yarinyar gifted ce. Babanta ya san haka, shi ya sa ya ba ta matsayin da ya san za ta
iya rikewa.
Shi yake handling duka al’amuranta, kama daga shirya mata appointments, seminers,
workshop na ma’aikata da kula da bayanan sirrinta.
Cikin wata guda kacal wani irin sabo da aminci mai karfi ya shiga tsakaninsu, wanda kowa da
ke aiki karkashin Halima ya san Mr. Hashim yana da wani special reception fiye da na kowa a
gare ta.
Hanan ba zuwa ofishin Halima ta ke ba, sai da babban dalili. Duk wata magana da ta shafi
aiki a ofis ta waya suke yinta ko Hanan din ta aiko sakatariyarta. Sai a gida suke haduwa. Ta
san Halima ta dau P.A, amma ba su taba katarin haduwa ba, don Mr. Hashim ba ya zuwa gidan
Prof, sabgar aiki ce kadai ke hada su, in sun tashi kowa ya nufi gida shi ke nan, inda wani abun
kuma sai dai su tattauna shi ta waya.
Yau litinin Mr. Hashim ya tashi da zazzabin cizon sauro (malaria) duk karfin halinsa ya kasa
fita aiki, ya kira sakatariyar Halima ya fada mata. Ko da Halima ta iso ofis ta ga kujerarsa
wayam, kasancewar sai an wuce ta ofishinsa za a isa nata ofishin. Ta tambayi Rose ko ina
yake? Nan ta ke gaya mata wayar da suka yi na rashin lafiyarsa ba zai iya driving zuwa ofis ba. Halima na aiki, amma sai ta samu kanta da shiga damuwa. Damuwar da ta rasa dalilinta.
Amma da ta yi tsam da ranta, sai ta fahimci rashin lafiyar Hashim ne ya tsaya mata a zuciya, ya
hana ta walwala. Ta san duk ciwon da zai kwantar da hashim ya kasa fitowa aiki, to ya isa a kira
shi ciwo. Domin kuwa Mr. Hashim jarumi ne ba a fannin aiki kadai ba, har ma a koshin lafiya. He
is always healthy and energetic.
Don haka da ta tashi aiki sai ta samu kanta da karya kan motarta Toyota Avensis ta nufi
unguwar Colorado Close inda estate din ma’aikatan NCC yake.
Gidaje ne (flat) duk iri daya. Akwai parking space wanda akalla zai ci motoci biyu a gaban
kowanne gida. Da shuke-shuken korran furanni. Dakunan barci biyu da falo, sai wadataccen
kitchen da toilet manne da kowanne bedroom. Akwai faffadan terrace a gaban gidan wadda ke
dauke da kujerun shan iska. A hankali Halima ta yi parking motarta kusa da ta Hashim ta dauko jakarta ta fito. Sau biyu ta
danna kararrawa kafin Hashim ya iya fitowa ya bude, wanda ke dukunkune cikin blanket,
idanunsa sun kada sabida zafin zazzabi. Yana sanye da sweater mai kauri (V-neck) ruwan toka
da bakin trouser. Yana bude kofar idanun ta suka sauka cikin nasa. Hashim da Halimah, a tare
suka ji wani abu mai mai karfi ya fizgi zukatansu a lokaci guda. Ba karamin kyau ya yi mata ba
duk da kadawar da idanunsa suka yi, sai hakan ya ba su