Showing 42001 words to 45000 words out of 48040 words
Chapter 15 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
ta ce da Halima da ke shimfida mata sabon
wankakken zanin gadonta.
“Sis, ni fa guest house zan je na kwana, gobe da safe in zo, I can’t sleep here…” Ta fada
tana nuna mataccen gadon Halimah.
Halimah ta ji ba dadi, amma ta san da gaske ta ke, ba za ta iya kwana a kai ba. Ta yi magana
da direbanta ta waya sai ga jakunkuna bi-da-bi yana shigowa da su, sai da suka cike filin dakin
Halimah, set ne kamar na lefe har dozen guda.
Ta jawo ta farko ta bude, suttura ce damkam tun daga kan laces, atamfa, voile, materials,
shadda babu irin wadda babu, ta ce, “Ga shi nan ki yi fitar suna”.
Ta biyu mayafai ne da slepping dresses, ta uku inner wears, ta hudu kayan kwalliya da
tsadaddun kayan shafa. Ta biyar duk takalma da jaka ne. ragowar kuwa kayan baby ne lodi-lodi
da pampers katon uku da duk abin da jariri zai bukata daga shekarar farko zuwa shekaru biyar.
Halimah ta manta da irin wannan rayuwar, don haka ban da na baby ba abin da ya burge ta a
ciki.
Ta ce, “Hanan, why? Na gaya miki Cherie ya mana komai, kuma ba zan yi amfani da kudin
jikin Daddy ba balle na ma’aikatar sa. Ko da zan yi yawo tsirara.... fatara za ta yi karshen
numfashina”.
Hanan ta runtse ido, “Ki sassauta kalamanki, na san ya bata miki rai, kuma yana kan bata
miki, but that will not change the fact that he is your father. Komai ki ka fada a kansa Mala’iku na
rubutawa.
Sannan wannan kudin ba na aikin NCC ba ne, kada ki manta dan minista na aura, kuma
nake tare da shi har gobe. Ba abin da bana samu a jikinsa, kuma ina da business bayan aikina.
Ina shigo da electronincs daga kasar Japan. So ni ba da Daddy na dogara ba, ba da
ma’aikatarsa ba”. Dole ta kashe bakin Halimah, ta yi ta mata godiya. Tana jinta tana ta kiraye-kirayen waya
tana bada order. Ba ta dai san me ta ke saya ba don a hankali ta ke magana. Wajejen karfe tara
na dare bayan sun gama cin abinci ta bar kayanta a nan, handbag dinta kawai ta dauka suka
wuce Tahir Guest palace. Washegari ya kama sunan Baby Safiyyah, Hashim ya yanka katoton ragon da ya tanada aka
yi radin suna a masallaci. Wajejen karfe goma na safe Halimah ta yi wanka ta dandasa kwalliya
da leshin da Hashim ya dinka mata, ta gyare Safiyya cikin kayan da babanta ya saya mata.
Hashim ma ya yi ado da farar shadda kaftan sai walainiya suke. Hanan ta iso, ta fiddo wayarta ta yi ta yi musu hoto su da babynsu. Sannan ta ce da Hashim
tana neman izni za a yi gyara a dakin Halima.
Ai kuwa Hashim ya kankance ido ya ce ba ya so, ta yi abin da ya kawo ta (zumunci) ta koma
gida, wadancan lodin akwatunan ma da ta tsibe musu ta kwashe abunta. Shi bai gaza da
iyalinsa ba, kuma ba zai taba gazawa ba. Ran Hanan ya yi mummunan baci, ta ce, “You cannot
stop me daga yi wa ‘yar uwata alheri, just don kana aurenta ba za ka raba mu ba. Ai a
al’adance idan mace ta haihu ‘yan uwanta su na sayen kayan jariri da atamfofi su kawo mata”.
Da ya ji ta fi shi gaskiya sai ya sa kai ya fita kawai. Yana fita ta sa kamfanin furnitures din da
ta zo tare da su su fidda komai na dakin Halima su kafa sababbin furnitures din da ta saya
mata, farare sol, gogaggu ‘yan kasar italiya. Ga wasu luntsuma-luntsuman kujeru masu tsadar
gaske, sannan aka kafa labulaye launin kujerun aka yada center carpet a kasa. Nan da nan
dakin Halima ya dau walainiya.
Sallamar Sa’adatu da Dr. Rabi’a Hanan ce ta amsa, suka shigo suna ta mamakin abin da
suka gani. Halimah ta gaya musu Hanan kanwarta ce uwa daya uba daya. Nan Dr. Rabi’a ta
fara zare ido cikin borin kunya, don ita har ranta ta bayar Halimah ba ta da kowa, a bariki
Hashim ya auro ta a Abuja. Allah ya so ta ta yo musu girki cooler-cooler nan ta gabatar da shi gare su tana ta borin
kunya. Hanan da ba ta san komai ba sai yaba mata ta ke, don Halimah ta gaya mata yayar su
Hashim ce.
Makota sun shisshigo haka abokan arzikin Inna da ‘yan uwan mijin Sa’adatu, kowa ya ci
abinci mai kyau ya yi guzurinsa. Sai kallon Hanan ake ana karawa, domin ta zamo kamar wata
Zarah a cikin matan da suka halarci sunan, sutturarta da apperance dinta.
Sai bayan isha kowa ya watse aka bar Halimah da Hanan. Hashim saboda Hanan yana café
dinsa bai dawo da wuri ba. Don ya bar su su yi sallama sosai kasancewar gobe Hanan za ta
koma gida.
Hanan da ke rike da baby tana kallonta ta lura da wani abu. Tunda ta zo ba ta ga kwayar
idanunta ba. Ta dubi Halimah tana murmushi, ta ce, “Sleeping beauty, ita ba ta gajiya da barci,
da safe barci da dare ma bacci?”
Halimah ta dubi kanwarta, ta ce, “Umh”. Kawai in ta girma kowa ya sani, ba sa son baki ya
kama ‘yarsu.
Sai karfe goma suka yi sallama kamar ba za su rabu ba, domin gobe da asubah za su dauki
hanya don ta samu ofis a kan lokaci.
*****
Suka ci gaba da rainon diyarsu Safiyya tare da ba ta kulawa ta musamman, bayan soyayyar
iyaye ita wannan ‘yar suna jinta sosai a ransu, saboda rauninta.
Watannin Safiyyah hudu, duk wanda ke tare da su ya san cewa ba ta gani. Ga wani irin kyau
da Allah ya ba ta. Tausayi da kyawunta shi ne ke sayo mata soyayya a zukatan al’ummah.
Hanan ta gaya mata cewa, tun bayan haihuwar Safiyyah Daddy ya sanya ta a ma’aikatan
NCC da aka tura karo kwas a kan harkar Telecommunication kasar Manrovia, ba ta so tafiyar
ba, amma Salim ya karfafe ta da cewa, ta je, wannan zai ba ta damar rainon cikinta cikin
kwanciyar hankali har sai ta haihu. Don kuwa ya shirya karbar dansa, in ya so iyayensa su zabi
abin da ya fi musu amfani tsakanin barinsa da matarsa ko su raini abin da ta haifa masa. Kwas
din zai dauke su watanni shidda.
Bayan tafiyar Hanan suna waya akai-akai, kuma ta gaya mata ta shiga EDD dinta.
Yau Hanan ta kira ta ne da kyakkyawan albishir na ta sauka lafiya, ta haifi diya mace mai
tsananin kama da mahaifinta. Nan da watanni biyu za ta kammala kwas dinta ta dawo gida ta
fuskanci Daddy.
An ce dai ba'a murna da haihuwar dan gaba da fatiha, amma Halimah sosai ta ke murna. Jin
‘yar ta ke kamar Safiyyah a zuciyarta musamman da Hanan ta turo mata hotunanta. Kyau har
zuba yake, da ma an ce shegun ‘ya’ya kyawu ne da su. Ta gaya mata Salim ya je Manrovia ya
ga babynsa ya ba ta kudi masu yawa don ta shayar masa da baby. Ba dai haka aka so ba wai kanin miji ya fi miji kyau. Halimah ta kara tunatar da ita yawaita
istigfari, hailala da salatin Annabi, to calm Allah’s anger against them. Ita ma tana taya su da
roka musu gafarar Ubangiji.
****
BAYAN WATANNI BIYU
Gidan Proffessor Numan.
Asokoro, Abuja, Nigeria.
Direban da ya dauko Hanan da ‘yarta daga filin jirgi ya yi horn a tankareren get din gidan Prof.
Numan, Seun ya zo ya fara shaida motar sannan ya bude suka shiga. Duk da cewa gabanta
mugun faduwa yake yi, amma tana ta jan addu’a wadda Halimah ta koya mata. Ta ce, ita za ta
yi ta karantawa a lokacin da za ta fuskanci Daddy. Direban ya bi bayanta da jakunkunanta. A kasaitaccen falonsa ta fara yin tozali da shi. Dauke ta ke da yarinyar a kafadunta wadda ta
radawa suna Yusra. Barcinta ta ke hankali kwance, ta zuge sliding door din da ta raba falon
farko da falon da Daddy ke ciki.
Zaune yake yana ta aiki kamar yadda ya saba; bisa computer ne, bisa takardu ne, bisa
macbook ne duk dai babu wanda ba ya yi. Yana yi yana duba agogo don jiran isowar ‘yar sa
Hanan.
Da sallama ta shigo, ya daga kai ya dube ta da murmushi.
“Welcome back daughter…....”
Ta karaso ta rungume shi da hannu daya yayin da dayan ke dauke da baby.
“I missed you Daddy…”
“Missed you too daughter, how is Manrovia…?”
Sauran maganar ta makale a makoshin sa, sakamakon kuka da yarinyar hannun Hanan ta
canyara. Cikin mamaki da al’ajabi ya dubi Hanan sosai wadda ta zauna gefe ta fiddo nono ta sa
wa ‘yar a baki.
A firgice Prof. ya mike tsaye, “Me zan gani haka? ‘Yar wa ki ka dauko? Na ce daga ina ki ka
dauko ta?”
Hanan ta sunkuyar da kai ta soma hawaye, ba ta ce komai ba. Ya sake maimaita tambayar
sa, wannan karon a matukar fusace, Hanan ta soma shivering (karkarwa) kamin ta tattaro
courage ta ce, “I’m sorry Daddy, ‘ya ta ce, ni na haife ta!”
Wani gigitaccen mari ya dauke ta da shi, ya sake dauke daya kuncin nata da wanda ya fi na
farko, sannan ya nuna ta da dan yatsa.
“Karya ki ke ki tozarta ni. Ashe karuwanci ki ka tafi ba inda na tura ki ba? Fitar min da ita
daga gida kafin na kashe ta, hukunci ya hau kaina”.
Kuka sosai Hanan ta saki, “Daddy ni ce ‘yarka Hanan, ‘yar da ka raina ba tare da taimakon
uwa ba. Ka tuna girman amanarmu da Allah ya dora maka. Wannan yarinya da ka yi aiki da
fadar Allah da ManzonSa da ba ta zo a haka ba. Ni ban yi karuwanci ba, ban taba sanin Da
namiji ba bayan tsohon mijina, Salim. Kuma shi ne uban ‘yar sa, ka yi min alfarma ka bar ni in
shayar da ita. Ranar da na yaye ta zan ba shi ‘yarsa in ci gaba da zama karkashin biyayyar ka”.
Tun daga yatsar kafarsa har gashin kansa gumi yake. Ji ya yi jikinsa ya yi bala’in sanyi. Wani
abu mai kama da nadama na son ziyartarsa. Zama ya yi a kujera ya dafe kansa da hannu
bibbiyu. Yayin da Hanan ta sauko daga kujera ta zube gwiwoyinta a gabansa tana hawaye
dauke da ‘yarta. “Daddy, ka hana mu aure, ka hana mu zaman gidan miji saboda boko. Mu din kuma ba
waliyyai ba ne ‘yan Adam ne ajizai, wadanda shaidan ya yi alkawarin ja ga halaka muddin ba
mu bi fadar Allah ba. Ubangiji ya yi maka umarnin ka yi mana aure daga shekarun fara balaga,
amma Daddy ka ki hakan. Na zo na yi aure ba bisa yarda da amincewarka ba, ka bar ni babu
kulawa a gidan aure kamar ba ni da kowa. Dangin mijina suka kasa karbata sabida rashin gatan
iyaye. Mijina ya sake ni a kan dole, ba don yana so ba sai don bin iyayensa.
Daddy ka san bond din da ke tsakanin mata da mijinta? Musamman wadanda suka rabu ba
bisa wata kwakkwarar hujja ba? A lokacin ne Ubangiji ke sanya musu kaunar juna wadda in ba
a yi sa’a ba, sai ta kai su ga tabewa da halaka, wanda wannan shi ne hakikanin abin da ya faru
da ni. Daddy mu marayu ne, amana a hannunka ka yi tunani da mahaifiyarmu na raye, za ta
amince da rayuwar da ka sanya mu a ciki?
Kudi dai Daddy na duniya ban san wane iri ka ke so ka yi ba. Ilmin boko na duniya ban san
wane iri ka ke so mu yi ba. Ba ka bai wa masu bukata aiki sai mu da ba ma bukata. Ba ka
tunanin lahirar mu, kullum cikin rayuwar duniya da neman kudi kawai ka ke cusa ni. Ba ka
la’akari da kasancewata diya mace mai rauni, wadda halittar ta ta karfinta da juriyarta ba kamar
namiji ba ne. Na samu komai da dan Adam ke bukata a rayuwa ban da aure. Ka gaya min in
ban yi zina ba me ya rage min a duniya?
Sis Leemah. Ka yanke ta daga jikinka kawai saboda ta zabi ta raya sunnar Annabi, ba don ta
kasance mai tsoron Allah ba babu shakka abin da ya same ni shi zai same ta. Ta jure duk wasu
azabobinka shekara da shekaru, amma wallahi ta fi ni kwanciyar hankali a halin yanzu, tunda
tana cikin rahmar aure tare da mijinta da ke sonta saboda Allah, da tsarkakkiyar zuri’a wadanda
a ko’ina za ta yi alfahari da tutiya da cewa, ta hanyar sunna ta same su…” Ta kama kafafunsa jikinta na karkarwa.
“Ka bar min ‘yata ina sonta. Ita ce sanyin idaniya ta. Na yi maka alkawarin zan ci gaba da yi
maka biyayya har PhD zan dora in dawo in ci gaba da aiki har iya inda ka ke so. Amma don
Allah ka yi min alfarma ka bar min ‘yata in raine ta in ta kai munzali ita in yi mata aure ta haifa
min tsarkakkiyar zuri’a. Ka yafe min, ka sa min albarka. Na tuba na bi Allah na bi ka… ba zan
kara yin zina ba!”
Ta hade hannayenta biyu cikin roko, fuskarta sharkaf da hawaye.
Prof. Bai ce mata komai ba ya juya cikin wani hali zuwa dakin sa.
Daga ranar bata kara ganin shi ba, ya shige daki ya rufe kamar wanda ya shiga halwa, bata
san me yake ci a dakin ba ofis ma baya zuwa. Tun tana zuba idon zai kwace mata 'ya har ta
saki jikin ta ta cigaba da hidimar 'yar ta cikin gidan.
A kwana na biyar ne rannan ta shiga wanka ta bar Yusra kwance akan gado tana ta tsala
kuka. Prof. Yayi shirin ofis zai wuce ta gaban dakin Hanan amma kukan Yusra yasa dole ya
dakata, yana jin wani iri a zuciyar sa. Hakika a kwanakinnan biyar ba abinda yake a daki sai
neman gafarar Allah, ya yarda duk abinda Hanan ta fada gaskiya ne, kuma rashin mai gaya
masa gaskiya akan iyalinsa shine babban abinda yayi tasiri a kansa.
Abin da ba ta taba zato ba, abin da ba ta taba tsammana ba. Daddy ya shigo dakin ta. Hannu
biyu ya sa ya dauki 'yar. Idanunsa cike taf da hawaye, kamar ta daya da Safeeyah. Ya rungume
ta a jikinsa tsawon lokaci bai ce komai ba. Hanan dake tsaye bakin kofar toilet daure da tawul
don farin ciki ko motsi ta kasa yi. Sannan ya ajiyeta a kan kujera yana kallonta, ya juya ga Hanan dake tsaye yace.
“Ki ba ta nono ta sha, tun daga daki na nake jiyo kukan ta”.
Hanan gigicewa ta yi don murna, ta kasa ba wa ‘yar nono sai jijjiga ta ta ke tana fadin,
“Daddy, ka yafe mana? Za ka dawo da Sis Leemah? Za ka bar ni in koma gidan mijina? Za ka
bayyana kanka a matsayin ubana ga dangin mijina?”
Tambayoyin ta ke jejjerowa a jere, ko numfashi ba ta shaka. Prof. bai ce mata komai ba, ‘yar
cikinsa da ya haifa ta shayar da shi ilmi, ilmin rayuwa wanda bai taba zama ya ankara da shi ba.
Da gaske akwai mutane irinsa da yawa a wannan zamanin, wadanda suka riki boko da
career da muhimmanci fiye da bautar Ubangijinsu, fiye da feelings din ‘ya’yansu. Neman duniya
ya danne na lahira, burinsu kawai ‘ya’yansu su fi na kowa. Ba ruwansu da halin da ‘ya’yan
talakawa ke ciki. Duk wani vacancy mai maiko na ‘ya’yansu ne, dan talaka ya mutu don rashin
aikin yi ba damuwarsu ba ne.
Ga result (sakamako) na fifita duniya kan umarnin Ubangiji yau ‘yarsa ta kawo masa har gida,
wanda ba zai taba kankaruwa daga jikinsa ba, jikar sa… 'yar gaba da fatiha…. Wai don ma
Allah ya takaita korar da ya yi mata lokacin da mijinta ya sake ta, bai sa ta shiga duniya ba.
Tunani na karshe da ya kutso cikin kwakwalwarsa shi ne, HALEEMAH… his innocent
daughter Haleemah!!! How cruelly he treated her… how he abandoned her… how he scolded
her… how he sent her away, da zaluncin da ya yi mata kawai don ta zabi AURE