Showing 15001 words to 18000 words out of 48040 words
Chapter 6 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
ne shaida, ina tsananin sonki Halimahhh”.
Duk wata soyayya sun gama kullo ta daga Malta sun yo gammon ta sun taho Abuja da ita.
Dauke da alkawurra masu karfi a tsakanin su. Ko da suka dawo, Halima ta dauki hutun sati
guda, don ta samu ta warware gajiyar tafiya, inda ta damka komai a hannun Hashim her
Technical Asistant sannan P.A dinta, da sakatariyarta, Rose.
Hashim ya je gida Kano washegarin dawowarsu ya kwana daya, ya gaya wa Inna da Yaya
Rabi’a cewa ya samu mata a can Abuja. Daga Inna har Rabi’a ba su ji dadi ba, don ba irin
auren da suke so ya yi ba kenan, so su ke ya zo ya nemi yarinya a Kano daidai karfinsa. A
hakan ma don ma ba su ji wace ce ya kinkimo ba.
Ita Dr. Rabi’a ma har ta yi masa kamun wata dalibarta a Legal da ta yaba da hankalinta. Ba
za ta fice sa’ar Sa’adatu ba. Amma sun kwana da sanin halin Hashim in ya sa kai a abu sai ya
ga abin da ya ture wa buzu nadi, kuma dai yana da foresight (tsinkaye) ba zai dauko matar da
za ta cutar da shi ba, ko wadda ba za ta girmama su ba. Don haka suka ba shi kyawawan
addu’o’i daga bakunansu.
Inna ta ce, in sun tsaida lokacin zuwa gaisuwa ya yi magana ta yi wa Yayanta da ke Sudan
waya, da ‘yan uwan mahaifinsa.
A washegari Hashim ya dawo Abuja, ya rungumi ofishin Halimah. Don ta samu ta huta sosai.
Prof. yana yabawa da yadda yake gudanar da komai, ya gayawa Halimah nan da dan lokaci,..
her P.A deserves promotion. (Mataimakin ta ya cancanci karin girma). Wannan abu da Daddy
ya fada ba karamin faranta ran Halimah ya yi ba, har ta ke hango alamun nasara cikin rigimar
da ta ke shirin gabatarwa.
A daren yau misalin karfe tara na dare ta zuge labulayen dakin ta don ta samu ta shaki fresh
air. Wani abu ne guda daya ya dauki hankalin ta, a cikin wata bakuwar mota ta hangi Hanan
tare da wani kyakkyawan saurayi, abinda idanunta suka gane mata ba karamin kidimata ya yi
ba. Hanan ta bude kofa kafarta daya na waje, yayin da jikinta ke cikin motar suna sumbatar juna
ita da saurayin. Sun jima a haka kafin Hanan din ta fito tana daga masa hannu, yana daga mata
ya ja motar ya bar gidan.
Da sauri ta saki labulen gabanta na wani irin bugu na tashin hankali. Hanan ta murda kofar
dakin ta shigo tana cilla jakarta tana cafewa, da gani cikin nishadi ta ke. Amma kallon fuskar
Halimah kawai ta yi ta shiga taitayinta. Halimah ta hadiyi miyau da kyar, ta ce.
“Hanan, waye ya sauke ki a mota yanzun nan?”
Hanan ta yi shiru, Halimah ba ta jira amsarta ba, ta kwashe ta da mari, tace,
“Me na ga kuna yi cikin mota haka?”
Da farko Hanan ta nuna firgici, don ba ta taba zaton Halimah ta gansu ba. Sai kuma ta fuske
ta dubi cikin idon Halima tana hawaye ta ce.
“Saurayi na ne… an ce ba za mu yi aure ba… bautar ofis kawai za mu yi muna tarawa Daddy
kudi… bayan ni kuma mutum ce ba mutum-mutumi ba. In ba mu yi romancing a mota don rage
wa kanmu zafi ba so ake mu je mu kama daki a hotel ko me? Mts!”
Ta yi tsaki tare da ficewa daga dakin, ta banko wa Halimah kofarta.
Da kyar Halimah ta lalubi gefen gado ta zauna. Ga wadda ta fi ta iya protest, sai dai nata
akwai tarin kuruciya a ciki da karancin ilmin addini. Amma sai ta ga cewa tunda har Hanan ta
bude baki ta fadi haka, ya tabbata aure ta ke so itama, ba ta da yadda za ta yi. Sai ta ga cewa
kamar wata sassaukar hanya ce Allah ya kawo mata wajen gabatar da bukatarta ga Daddy,
idan har Hanan za ta ba ta hadin kai su duka su taru su ce aure suke so.
Fita ta yi zuwa dakin Hanan, don sauri har tana tuntube. Ta same ta tana canza kayan jikinta,
ga yatsun Halima sun kwanta lambam a farar fuskarta, ta tausasa murya ta ce,
“Ki yi hakuri Hanan!”
Jin da sulhu ta zo ba da wa’azi ba, ya sa Hanan ta dakata da abin da ta ke yi, ta dan ba ta
hankalinta. Halimah ta yi mata murmushi ta ce, “Wajen ki na zo, magana za mu yi ta fahimta”.
Hanan ta koma bakin gado ta zauna, Halimah ta zauna a kusa da ita, ta dubi Hanan ta ce,
“Na samu miji, aure zan yi Hanan”.
Hanan ta bude baki tana kallonta, da kyar ta iya cewa, “With Daddy’s consent (da amincewar
Daddy)?”
Halima ta ce, “Har yanzu ban samu guts din gaya masa ba, amma tabbas aure zan yi”.
Hanan ta motsa baki a hankali kamar mai ciwon hakori ta ce,
“Ni sau nawa ina samun mijin yana korar su? Amma wallahi wannan karon ba zan iya rabuwa
da Saleem ba”.
Halimah ta sanya hannunta cikin na Hanan ta ratsa yatsun su (fingers cross) Sannan ta ce,
“Then we have to unite and protest!”
Hanan ta dan fiddo ido cikin tsoro ta ce, “Ina tsoron Daddy, kin san dai tunda muka taso
maganarsa daya ce ba zai aurar da mu ba, saboda baza'a iya rike masa mu ba, amma zai yi
mana komai a rayuwa…”.
“Kina tsoron Daddy, amma ba kya tsoron Mahaliccinki? Wannan abin da ki ke aikatawa is an
act of fornication (nau’in zina ne) wanda ba komai ya janyo miki ba sai rashin aure. Hanan, mu
karfafi kanmu mu fuskanci Daddy, ni na gaya miki a karshe zai hakura ko da da farko ya nuna
rashin amincewar sa, kada ki manta shi ya haife mu, ba shi da abin da ya wuce mu. Duk hukuncin da zai mana a kan hakan ba zai yanke mu daga jikinsa ba. Iyaka ya yi fushi na
dan lokaci ya huce. Idan ba za ki ba ni goyon baya ba mu kwaci ‘yancin mu da addini ya ba mu
ba, ni zan yi aure na in tafi in barki a gidan nan ke kadai. Ya rage naki”.
Tana gama fadin haka ta mike za ta bar dakin. Har ta kai bakin kofa hanan ta kira sunanta.
Dakatawa ta yi ba tare da ta juyo ba.
Hanan ta tako a hankali ta zagayo gabanta, idanunta fal hawaye ta ce,
“Ba zan iya zama a gidan nan babu ke ba. I’m with you sis Leemah”.
Sai hawaye ya gangaro daga idonta.
Halimah ta kai hannu tana share mata.
“In dai Saleem da gaske yake ki gaya masa ya fito. A goben nan za mu tunkari Daddy a yi ta
ta kare. Amma sai kin cire tsoron Daddy a ranki Hanan za mu yi nasara”.
Hanan ta gyada kai, ta ce, “Insha Allah”.
*****
BABI NA SHIDDA
Prof. Zubair Muhammad Numan, yana zaune a balcony din shan iskarsa kan wasu kujeru sakar
kaba, yana sauraron radiyon da ke gefenshi, inda ake labaran VOA na harshen hausa, misalin
karfe goma na safe, kasancewar ranar asabar ce babu aiki. Halima da Hanan suka shigo a tare,
kowacce sanye da bakar jallabiya kamar wasu takarun Makkah, kai a kasa salalaf-salalaf suka
shigo inda yake, kowacce ta je gefen kafarsa daya ta zauna.
Ya rage sautin radiyon ya ba su hankalin sa.
“What happened my daughters?” Saboda bai saba su zo su zauna a kasa don yana kan
kujera ba, sai dai su zauna a hagu da daman sa.
Halimah ta ambaci sunan Allah Al-Hakeem gwanin hikima, don ya bata hikimar zance, Zarah
ta taba koya mata wasu ayoyi daga Suratul-Daha in kana so a fahimce ka, tace a hankali;
"Rabbi sharahli sadry, wayassirly amri, wahlul uqdatan min lisany, yafqahu qauly...... sannan
ta kwarara zuciyarta, ta soma magana cikin sanyin murya.
“I’m sorry Dad, I’m very sorry Daddy, idan abinda zan fada bai maka dadi ba. Na zo yau in
gaya maka cewa, na tsayar da miji. Suna so a ba su lokaci su zo tambaya”.
Tana rufe baki, Hanan ta dora nata.
“Daddy, ni ma na samu miji, dan gidan Minister Usman ne, sun ce suna so su zo tambaya in
an ba su appointment”.
Kowacce ta sunkuyar da kai kasa, gabanta na dukan tara-tara ba uku-uku ba. Don ba
karamin practice da rehearsal suka sha a daki ba kafin su shirya wadannan gajerun kalaman.
Prof. ya yi musu kallon tsaf, sannan yayi dan murmushi, ya ce,
“Wato kun je mazan banza sun hure muku kunne ku yi min rashin biyayya ko? Sau nawa zan
gaya muku ba zan iya aurar da ku ba? Yanzu har kun yi girman da za ku dubi tsabar idona ku
ce min aure ku ke so Halima da Hanan? Me ku ke so? Me za ku samo a gidan auren wanda
babu shi a gidanku? Ku tashi ku ba ni waje tun ban sa kafar wando daya da ku ba”. Halima ta hadiyi miyau da kyar tace "Dad! Na gaya maka aure nake so, shekaruna 24, sai na
tsufa na rasa mashinshini saboda biyayyar ka? Kace karatu, mun yi kowanne irin karatu, kace
aiki, gashi muna ta yi maka, mun tara maka kudi wadanda zasu isheka har karshen rayuwar ka,
a yanzu hakkin mu na 'yan adam muke bukata, 'yancin da Allah ya baiwa kowa na raya sunnar
Manzo, ko don mu bamu da UWA? Bamu da wani majibinci da zamu kaiwa bukatar mu bayan
kai?" Ta fashe da kuka.
Hanan ma ta zaburo "Daddy na yi hakurin Allah na yi na manzo, ka yi min aure ina son Salim
bazan iya hakura da shi ba".
Don bakin ciki ya rasa me zai ce musu, anya 'ya'yan sa da ya sani ne wadannan? Hanan da
Halimah masu kunya da kawaici? Wace irin fitsara suka koyo haka? Aure wane iri? Ba dai a
gidan sa ba! Shi da girman sa bai damu kan sa da wani aure ba sai su? Da me ya rage su?
Sai kawai ya tashi ya bar su a wurin, don ya tabbata in ya cigaba da kallon su a gaban sa zai
iya illata su. Auren banza auren wofi me zasu je su samo a gidan auren wanda baya basu? Su
yara ne basu san wani me auren ya kunsa ba (a tunanin sa fa).
Tun daga ranar Hanan da Halima suka hada baki suka daina cin abinci, suka daina zuwa
ofis, ko falo sun daina fitowa, kullum suna kwance a gadon dakunansu kamar ruwa. Shi ma
Daddyn ya yi fushi mai tsanani ba ya neman su. Damuwarsa daya ce, ofis da suka daina zuwa.
Ba ya son ya bai wa bare ko ‘ya’yan talakawa wadannan guraben aikin a NCC, ya fi so daga shi
sai ‘ya’yan cikinsa su ci gaba da cin gajiyar NCC su kadai, ga ‘ya’yan sun yi masa murabus za
su bula masa kasa a ido.
Kwarai yake cikin damuwa, musamman da kukunsu Helen ta same shi har falonsa ta gaya
masa yau kwana uku tana kai abincin Halimah da Hanan dining amma yadda ta kai haka ta ke
daukowa, ba sa tabawa. Ba ta san me suke ci ba, tana tsoron kada ulcer ta kama su. A kwance
suke wuni, a kwance suke kwana, in ta musu magana ba sa amsa mata. Hankalin Prof. ya fara tashi, zai iya jure komai, amma ban da zamansu cikin yunwa. Shi kuma
har gobe bai shirya rabuwa da ‘ya'yan nan nasa ba. Ya damka su ga wani banzan namiji da bai
san darajar su ba. Me zai gaya musu su gane bayan wanda ya yi shekara da shekau yana gaya
musu, amma rana daya suka sa kafa suka yi fatali da shi? Haka ya danne bacin ransa yau da ya dawo ya shiga dakin nasu. Halin da ya riske su a ciki
ya yi matukar daga masa hankali.
Kwanaki uku kacal bai gansu ba, amma har kasusuwan wuya sun yi. Sannan kwanaki uku
kenan da fatar jikinsu ba ta ga ruwa ba balle sabulu. Idanunsu sun yi zuru-zuru sun zurma ciki
da yunwar da suka sanya kansu. Ruwan lipton kawai suke sha, wanda suke jonawa a kettle a
dakunansu. Shi kuma lipton ma’abota shanshi sun sani ba ya maganin yunwa, sai ma ya rarake
ciki.
Ya ce, “Is that serious to this extent? Ku same ni a falo mu yanke magana ta karshe”.
Suna tangadi da dafa bango kamar wadanda suka sha kayan maye suka bi bayan Daddy
falon sa kamar yadda ya bukata.
Sai da suka zauna a gefen kafafunsa sannan ya fara da tambayar Hanan wane ne mijin da ta
samo, kuma a ina suka hadu? Kada ta boye masa komai, ta gaya masa gaskiya.
Hanan ba ta boye ba, ta gaya masa haduwarta da Saleem a wajen dinner din kawarta, da
inda yake aiki, wato shell company da kuma ko wane ne mahaifinsa. Ta kare zancenta da cewa,
kuma shi da gaske aurenta zai yi, idan har Daddyn ya ba shi dama.
Ko babu komai Prof. Zubair ya dan ji sanyi a kan zabin nata, jin cewa ba karamin gida ta
samo mijin ba. Domin Minister Usman sananne ne a Nigeria. Halimah ma ya yi mata tambaya
irin yadda ya yi wa Hanan.
Halimah ta sunkuyar da kanta, kirjinta na bugawa. She is not sure… ko Daddy zai yi farin ciki
da zabinta. Ga alama ya karbi na Hanan. A hankali cikin sanyin muryarta ta ce,
“Daddy, Hashim ne!”.
Kwata-kwata hankalinsa bai kawo masa wanda ta ke nufi ba. Ya ce, “Wane ne ubansa?”
Wannan tambaya ta yi wa Halimah rashin dadi. A raunane ta ce, “Mahaifinsa ya rasu”.
Ya yi dan jim, sannan ya ce, "Waye mahaifin nasa nake tambayarki?”
Halimah ta karfafi zuciyarta ta fito fili ta gaya wa mahaifinta ko wane Hashim ta ke nufi, ba
wani ba ne sai Personal Assistant din ta Engnr. Hashim Yakasai.
Wani ashar Prof. ya saki, ya kara da cewa, “Ban san ba ki da hankali ba sai yau, domin a da
kallon wadda ta fi kowa hankali da tsinkaye nake miki".
Halimah ta soma kuka tana rokon mahaifinta, ta kama kafarsa ya fizge ya tashi ya barta a
wurin tana gursheken kuka.
Hanan ce ta kamata zuwa daki, kafin azahar sai ga Halima tana suma idanunta na
kakkafewa. Hanan ta firgita, a guje ta fita falo tana kuka tana rokon Daddy ya zo ya ga Halimah.
Da farko ya ki ko kallon inda ta ke, sai ga kukunsu a guje tana gaya musu Halimah rai ya yi
halinsa… she is no more… tana cilla hannuwa tana kiran Jesus ya taimake ta.
Zuciyar UBA… Jin cewa Halimah ta mutu bai sa shi yin nadamar hukuncin da ya yi mata ba,
don da ya hada jini da talaka mai ci a karkashinsa gara komai zai faru da ita ya faru. Zuciyar sa
ta yi laushi ne da ya tuno ko wace ce Halimah a gare shi. Ta rayu cikin biyayyarsa da kaunarsa
a kulliyar rayuwarta. Ta fi Hanan yi masa biyayya… hatta aikin nan ba so ta ke yi ba, tana yi ne
don amfaninsa. Albashinta bata taba komi a banki take barin sa....tace shi take taramawa. A
hankali ya mike ya bi bayan Hanan wadda ta rufa a guje (helter-skelter) zuwa dakin Halimah.
Tsintsiyar hannunta ya kama ya saurara, sai ya fahimci da sauran numfashinta, watakila dai
doguwar suma ta yi, da kansa ya dauke ta zuwa mota, ya yi asibitin da suke zuwa da ita.
Suna zuwalikitoci suka karbi Halimah, aka rufu a kan ta. Kwana uku ana abu daya, Halima ko
ta farfado sai ta kara sumewa, Hashim bai san abindaake yi ba don a zaton sa har lokacin
Halima na hutu ne.
Ba karamar jinya Halima tayi ba, kafin ta soma shaida wadanda ke kanta, gabadaya ta fita
hayyacin ta, kwana bakwai cur tana kwance gadon asibiti sai ruwa da ake kara mata akai-akai
da allurai. Daddy