Showing 39001 words to 42000 words out of 48040 words
Chapter 14 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
that kowa zai iya taka ni. Da ka
kare min alfarmata ta uba babu wanda zai wulakanta ni’. Ya ce bisa sharadi uku za ki zauna tare da ni, in kin amince to, in ba ki amince ba ki manta
kin taba sanina a rayuwarki.
-Ba za ki kara yin aure ba.
-Ba za ki yi alaka da Haleemah ba.
-Za ki koma karatu ki karo masters dinki ki dawo ki koma aikinki a NCC.
Duk na amince, as I have no alternative. Na koma Mexico tsayin shekara guda na hado
masters dina na dawo. Ya dora ni a kan kujerar ki”.
Hanan ta dan yi shiru, sannan ta ci gaba.
“Sai ga Salim ya dawo yana so ya maida ni dakina mu zauna a PortHearcourt ba da sanin
iyayensa ba. Na gaya miki muna son juna ni da Salim, iyaye ne suka raba mu ta karfin gaske.
Na duba na ga babu mafita, komen nawa ba zai yiwu ba ba tare da Daddy ya sani ba, kuma ba
tare da ya sake kora ta ba. Ga shi ina son Salim, so mai tsanani ba dan kadan ba. I’m sorry sis Leemah, because I know I disappoint you, and I’m going to break your heart, sai
muka ga tunda aure ya gagara bari muci gaba da rayuwarmu out of wedlock. Kullum Daddy ya
fita, ko ya yi tafiya to ni da Salim muna tare a hotels. Zancen nan da nake miki ciki ne a jikina na
wata biyar, mun yi mun yi ya fita ya qi. Idan na haife cikin nan this will tarnish the image of their
royal house, abin kunyar da ya fi musu rashin asali na da rashin mahaifana. Shi kuma Daddy
zai yi rainon dan shege a gidansa, tunda ya ki karbar na sunnah…”.
Hanan ta karasa cikin matsanancin kuka.
Halimah ta ce, “Hasbunallahu wani’imal wakeel”.
Bayan wannan ta kasa cewa komai, sai sauraron kukan Hanan mai keta zuciya. Daga baya
bayan ambaton sunayen Allah da ta ke ta yi ta samu kwarin gwiwar cewa Hanan.
“Kada ki kara kokarin zubar da cikin wata biyar, you wll lose your precious life for nothing (za
ki yi asarar rayuwaki a banza). Idan sun ki karbar dan, ni ki ba ni zan hada da nawa in rike
mana Hanan. Ki barsu su girbi abin da suka shuka. Lallai tsakanin iyaye da ‘ya’ya ma akwai
hisabi. Wata shari’ar sai a lahira”. Tun daga ranar kullum sai daya ta kira daya, ta ji halin da ‘yar uwarta ke ciki. Hatta motsin
jariran da ke kwance karkashin mararsu sai sun gaya wa juna. Rannan Hanan ta ce ta tura
mata account number dinta za ta turo mata kudi ta yi sayayyar haihuwa.
Halimah ta girgiza kai, “Na haramta wa kaina kudin jikin Daddy har abada! Daga ranar da
yace "kada Allah yasa na haihu lafiya". Kada ki damu, ba abin da Cherie bai saya mana ba,
imagine har dinkin fitar suna ya karbo duk da ya ce ba taro za mu yi ba”.
Hanan ta ce, “Amma ai gumina ne, tuda aiki nake suna biyana”.
Halimah ta ce, “Ki bar zancen nan don Allah. Ba zan karbi kudin NCC ba ko da zan yi yawo
tsirara”.
A daren ranar nakuda ta kama Halimah, ta kwana cikin gumurzu, sai da gari ya waye suka
wuce asibiti. Tana shiga labour room ta sunkuto kyakkyawar ‘yarta mai tsananin kama da ita.
Just as Hashim dreamt of (kamar yadda Hashim yake mafarki).
Duk addu’o’in da suka kamata Hashim ya yi wa ‘yarsa. Ya daga rigarta wajen al'aurarta ya
karanta mata (Wa Maryama ibnat Imranallaty ahsanat farjaha fanafakhna fihi min ruhi na wa
sadaqat bi kalimati rabbiha wa kutubihi wa kanat minal qaaniteen). Da Halimah ta dawo
hayyacinta ya dauko ‘yar ya dora mata a kan ruwan cikinta. Tana murmushi ta yunkura ta rike babyn sosai a kirjinta. Sannan ta sa ta a gaba da kallo.
Har cute face irin tata. Amma hatta yatsun hannunta da na kafa irin na Hashim ne. Ta sumbaci
‘yar, Hashim kuma ya sumbace su tare, ya saita wayarsa ya yi musu hoto su ukun.
“Don Allah ka tura wa Hanan”.
Halimah ta fada wa Hashim.
“Cherie you know she don’t like me (kin san ba ta shiri da ni) ta ya ya zan tura mata hoton ‘ya
ta?)”
Halimah ta yi murmushi, “Hanan din da ka sani a baya ba ita ce yanzu ba, she is now a
changed person. Har cewa ta ke na gaishe ka.
Ta karanto masa lambar Hanan ya yi saving ya tura mata hoton.
Sai ga wayar Hanan nan da nan ta wayar Hashim.
Hashim ya mika wa Halimah, muryarta a hankali ta ke fita, ta ce, “Hanan kin ga ‘yarki ko?
Labour akwai wahala, Allah ya jikan Mamanmu, ya haskaka kabarinta”.
“Ban taba ganin abin da ya shiga raina, nake so irin jaririyar mu ba”.
Hanan ta fada da murmushi mai sauti.
“Dole Aunty ta zo ganin diyarta. In na zo Kano wace unguwa zan ce a kai ni?”
Halimah ta zaro ido, “kada ki yi abin da zai ja miki matsala da Daddy, besides bai kamata ki
kamo hanya ba a cikin condition din da ki ke ba, Allah ya gani cikinki ba na halal ba ne, ba
kuma murna nake da faruwar hakan ba, amma so nake ki haife shi lafiya. Domin ya zamo ayar
Ubangiji ga Daddy, in an hana aure ba za a hana afkuwar zina ba, sai wadanda Ubangiji ya
tsallakar. Hanan duk abin da za ki haifa Dana ne, ni za ki haifawa. Ki yi zamanki ba sai kin zo
ba, addu’arki za ta riske mu har inda muke.
Hanan na dade da gane ba tarin arziki da dukiya shi ne jin dadi ga diya mace ba, a’a samun
miji na gari mai sonta da tausaya mata, wanda zai tsare mata lalurorinta iya karfinsa, ya kuma
ba ta soyayyah da kauna da gangar jiki da zuciyarsa. Shi ne babbar sa’ar da mace za ta yi a
rayuwar duniya. Daga hakan ba abin da ya rage mata sai zaman neman cikawa da imani”.
Hanan ta share hawayen da maganganun Halimah suka sa ta, ta ce, “Sis Leemah, I’m
regretting, na biyewa son zuciya cikin bacin ran Daddy na aikata kuskuren da har abada ba zai
goge daga tarihin rayuwar zuri’armu ba. Sis Leemah, na yi duk iya kokarina in zauna under
marital rope (karkashin igiyar aure) Daddy bai ba ni dama ba, ya ki amincewa, yau ni ce zan
haife dan shege a gidanmu ina ji ina gani? Don Allah me zan yi Allah ya yafe mini?” Ta fashe da
kuka.
“Istigfari Hanan. Ki lazimci istigfari tun daga yanzu. Yunkurin cire wannan cikin babban hatsari
ne ga rayuwarki, kuma kisan kai ne, wanda girman laifinsa ya fi na abin da ki ka aikata. Don
haka ki ci gaba da istigfari ki bar wa Allah ikonSa. Tunda dai Salim din ya amince cikinsa ne”.
Ta ci gaba da lallashin Hanan wadda haihuwar Halimah ta hanyar halali ta bi ta birkitata,
nadamarta ta karu. Da tasani ta yarda da shawarar Salim sun koma secret marriage din da ya fi
alfanu fiye da wannan son zuciya da suka aikata.
Da kyar Halima ta samu ta yi shiru. Ta kanga mata kukan baby a kunne. Dariya ta hau yi, ga
hawaye shabe-shabe a kan fuskarta. Da haka suka yi sallama.
Kwanan Halimah biyu likita ya ki sallamarta, sabida a bincikensu kan baby sun ga akwai
matsala. Kuma sun gaya wa Hashim cewa akwai matsalar, amma suna kan yin test za su gaya
masa washegari. Wannan duk ya bi ya damu Hashim, tun lokacin yake wani irin sukuku.
Sa’adatu ke ta jigilar abincinsu ita da mijinta Lawal. Dr. Rabi’a ta zo sau daya, ko daga yadda ta
ga baby dinsu a shirye cikin tsadaddun kayan sanyi ta fahimci akwai sauyi a tare da su, sannan
cike suke da walwala ba kamar da ba.
Hashim ya lura da wani abu, babynsu ba ta bude idanun ta. Sau daya ya ga kwayar idon ta.
Lokacin da ta zo duniya kawai. Daga wannan lokacin, tunda ta rufe ido ba ta sake budewa ba,
amma tana ta wutsil-wutsil din ta na alamun koshin lafiya, kuma ta kama nono tana sha sosai.
Sai da suka yi kwanaki hudu sannan likita ya kira su shi da Halimahn, tana rungume da
babyn a jikin ta. Ita sam ba ta lura da abin da Hashim ya lura da shi ba. Ta dauka babyn mai
yawan barci ce kawai. Sai da suka nutsu a gabansa sannan ya duba _file_ dinsu da ke
gabansa, ya gyara zaman farin gilashin idonsa. Ya dube su cike da alhinin abinda zai fada, kafin
yayi ta maza ya ce.
“I’m sorry Mr&Mrs, your baby was born BLIND!”.
Numfashin Halimah ya dauke na wucin gadi. La-shakka da tana da B.P babu abin da zai
hana hauhawar shi a nan take. Da sauri ta dubi babyn wadda ke rungume a kirjin ta. Hashim ya
lumshe idanun sa, babu abin da ya zo masa a rai a wannan lokacin sai maganar mahaifin
Halima Prof. Zubair Muhammad Numan. A ranar da suka je Abuja neman gafarar sa.
“Allah ya sa kada ki haifi duk abin da yake cikin ki lafiya!”.
Yayi nisa a wannan tunanin ya tsinkayi muryar likita can saman kansa.
“Za mu iya yi mata surgery, a samu ko remnant vision dinta a ceta, ta yadda ko haske ne zai
iya ratsa idanunta. Amma wannan total blindness ne, babu likitan duniya da zai ce maka idanun
nan za su bude. Surgery din kuma abu ne da zai ci kudi, saboda haka a shawarce; hakura da
karbar kaddarar shi ya fi.
Saboda ko an kashe kudin an yi, dan abin da za a ceto ba zai sa idanun su bude ba. Haske
ne kawai zai dinga ratsa idanunta. Wannan shi ne abin da consultant dinmu na Ophthalmology
ya tabbatar, Dr. Abubakar Turaki Abdullahi GAYA. Kuma duk fadin asibitin nan babu na biyun
sa”.
Hashim ya zuki numfashi da kyar ya fesar. Muryarsa ta dashe amma a haka ya yi wa likitan
godiya, ya kuma tabbatar masa sun karbi kaddarar Ubangiji. Za su raini ‘yarsu yadda Ubangiji
yake son ganin ta.
Halimah da ke hawaye tana ta kallon yarinyar da wata irin kauna, ta ce,
“A’a Cherie, a yi mata surgery din, ko Allah zai sa a dace”.
Hashim ya kama ta ya mikar da ita, ya karbi babyn daga hannunta.
“Ko za a yi ba yanzu ba Sweetheart, ba zan iya bari a kwantar da kankanuwar halittar
Ubangiji irin wannan a gadon tiyata ba. Ki bari sai Allah ya raya ta ta fara girma.
We will raise our daughter with so much affection… ba abinda nakasarta zai taba daga
soyayyar da za mu yi mata".
A haka suka bar ofishin, Halimah na kuka wurjanjan. Ba kukan kasancewar ‘yar ta da Hashim
makauniya ta ke ba, kukan tausaya mata ta ke, tana hango mata rayuwa cikin wannan situation
din musamman wajen neman ilmi, rainon 'ya'ya da rayuwar aure.
“Allah ya raya min ke *SAFEEYAH* ya albarkaci rayuwarki, Ya daukaka ki daukaka ta
buwayarsa, a nakashen da ki ke”.
Ta fada a hankali, a lokacin da suka shiga adaidaita sahu don komawa gida.
****
BABI NA GOMA SHA BIYU
Suka ja bakinsu suka yi shiru ba su gaya wa kowa ba. Hatta Sa’adatu wadda ke taimaka wa
Halimah da komai, ita ke wanke baby safe da yamma. Makota na ta shigowa suna musu barka
da abokan arzikin Inna.
Hashim ya bar wa ‘yarsa suna Safiyyah kamar yadda Halimah ta roki alfarma. Ana i-gobe
suna Hanan ta kira ta a waya, “Sis, ga ni cikin Kano, wace unguwa ku ke?”
Cikin matsanancin mamaki Halimah ta ce, “Kina Kano fa ki ka ce Hanan? Bana ce ki yi
zamanki kada ki zo ba? Kina son jawo wa kanki matsala da Daddy? And our unborn baby”.
“Na yi kokarin hakan amma na kasa. I want to see my little Princess. Tunda na riga na zo
magana ta kare, ki gaya min unguwar da kike zan zo”.
“Yakasai”. In ji Halimah. “Idan kin shigo Yakasai ki kira Cherie zai zo ya shigo da ku har
gidanmu. Ga shi a gida ya hana Safiyyah sakat, wai wasa yake yi mata”.
Hanan ta lumshe ido, “So is our little Princess our dear mother! Allah ya tsawaita rayuwarta ta
ba mu kulawar uwa da ba mu samu ba”.
Halimah ta yi murmushi.
Tun daga soron kofar gida Hanan ta soma shiga tashin hankali, ba dai a wannan gidan ‘yar
uwarta ke rayuwa ba?
Hanan ba ta gama tsinkewa ba, tsoron Ubangiji bai gama ratsa ta ba, sai da ta tsinci kanta a
dakin Halima.
Babu komai sai ledar tsakar daki, wasu rubabbun kujeru, wani tsohon gado karyayye, da
wata wardrove duk kofofinta sun fita. Babu madubi balle kayan kwalliya, sai dai kuma dakin a
tsaftace yake a share tas, a goge. Ga turaren wuta mai dadin kamshi Halimah ta kunna don
kashe karnin jego. Da ta yi tozali da Halimah kuma, sai hawaye ya tsinke a idanunta.
She is as old as 40 year old lady, unattractive, sai dai babu kazanta a jikinta. Wannan
Halimahr mai gayu da kwalisa, wadda a kullum ta ke sparkling kamar wata dan daren goma sha
hudu, fatar jikinta ta ke glowing kamar ana yi mata wankan inji. Amma a hakan tana jin dadin
rayuwarta da mijinta. Abin da ba ta sani ba shi ne, yadda ka dauki rayuwa a haka ta ke zuwa
maka, in ka dauke ta da sauki komai na duniya ba zai dame ka ba, idan ka cika zuciyarka da
wadatar zuci, ka gama hutawa a rayuwarka.
“LEEMAH!”
Hanan ta fada muryarta na karkarwa.
Halimah ta ajiye Safiyyah a kan ‘yar katifarta ta mike ta rungume kanwarta Hanan suka fashe
da kuka mai ban tausayi.
“I missed you Leemah…”
“I missed you Hanan, na yi kewar rigimarki da fitinarki”.
Hanan ta ture ta ta dunkule hannu tana bugunta a kirji. “Ni kuma na yi kewar discipline da
authoritativeness din Yayata”.
Daga haka suka koma dariya ga hawaye shabe-shabe a kan fuskokinsu. Gyaran muryar
Hashim ne ya ankarar da su shigowarsa, ya shigo da leda a hannunsa ya ajiye wa Hanan
Maltina da ruwan roba masu sanyi, sannan da snacks din Oasis Bakery cikin farar ledar
shagon. “Na gode Mr. Hashim”. Hanan ta fada tana murmushi, karon farko da suka taba yin maganar
arziki ita da shi. “But ni da driver na ne, please ka diba ka kai masa”.
“Already an ba shi. Barka da zuwa, ya ya hanya?”
“Alhamsu lillah, it was a nice experience, sabida ban taba tafiyar mota mai nisa haka ba. Na
so in biyo jirgi aka ce ba jirgi yau sai gobe, ni kuma a matse nake da in dauki Mamana”.
Hashim ya yi murmushi, ya dauko babyn daga katifarta ya ba ta.
“Wow! Masha Allah, wannan hancin da bakin duk irin nawa ne”.
Hashim ya ce, “Allah ya sa kada ta yo halin, nason girma da fadin rai”. Amma a zuciyarsa. Ya
fice ya barsu.
Kaji uku Halimah ta sa aka kamo aka gyare mata, ta soya su ta yi miyar dage-dage da su mai
rai da lafiya, sannan ta yi hadin salad da dafaffen kwai, ta dafa farar shinkafa da macaroni duk
don kanwarta Hanan, wadda ta zo kwanciya ta rasa inda za ta kwanta a dakin Halimah, don ba
za ta iya kwanciya a wannan shamulalliyar katifar tata ba. Balle ta hau wadannan burmammun
kujerun nata. Don haka bayan ta ci abinci ta huta,