Showing 30001 words to 33000 words out of 48040 words
Chapter 11 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
azaba. Daga asibiti gidan
Inna ya wuce da ita, don ya san wannan jinyar ta fi karfinsa.
Inna ta yi salati ta sanar da Ubangiji da ta ji abin da ya faru, ta yi addu’ar Allah ya mayar da
alkhairi. Ta shiga kula da Halimah bilhakki. Rabi’a ta zo ta yi masa jaje, ta kuma duba Halima,
duk da dai ba wai tana sonta ba ne har yanzu. Ta ba ta hakkinta ne da ya rataya a kanta.
Watan Halimah biyu a gidan Inna tana jinya kafin ta samu lafiyar kafarta, amma tabo ya
kwanta lambam. Suka koma Janbulo inda aka koma ‘yar gidan jiya.
Sai kuma laulayin ciki ya sako Halima a gaba. Ba ta iya cin komai sai yalo data. Duk ta rame
ta yankwane, a karshe likita ya rike ta a asibiti ake ta sa mata ruwa.
Kwanansu hudu aka sallame su. Hashim ya ga cewa, ba zai iya da Halimah ba don ko kudin
yalo datan watarana rasawa yake yi, don haka ya kara maida ita gidan Inna.
Inna da yake babba ce ta san abin da za ta iya ci, kuma shi ta ke mata, kunun tsamiya, tuwon
laushi miyar kalkashi da miyar zogale, sosai Halimah ke bude ciki ta ci, tuni ta kara murmurewa.
Sa’adatu ta samu miji wani malaminsu na sakandire, amma sai daga auren suke sabida ba
su shirya ba. A karshe Inna ta sa ragunanta da ta ke kiwo manya-manya a kasuwa ta sayar, Dr.
Rabi’a ta kawo nata gudunmawar, Hashim babu ko sisi, aka tsaida lokacin auren watanni uku
masu zuwa. Ta dade rabon da ta yi magana da Hanan, ko ta kira layin ba ya shiga. Ko dai Hanan ta daina
amfani da layin, ko kuma ba ta kasar Nigeria. Ta taba gaya mata sun dawo Kano, amma ba ta
gaya mata wani address ba. Ta so ta gaya mata maganar samun cikinta da konewarta. Sosai ta
ke kewar Hanan duk da cewa in suna tare din fada suke yi irin na sako da sako. Daddy fa?
Ta yi ajiyar zuciya tana lalubar zuciyarta, did she really missed him? A take amsa ta zo mata,
“No, she didn’t. He is, but a cruel father (shi ba komai ba ne sai mugun uba a gare su), wanda
ya zama silar duk wannan wahalalliyar rayuwar da suke ciki.
Ta kai hannu ta shafe hawayen idanunta. A fili ta ke addu’a ba ta san cewa a filin ta ke yi ba.
“Ya Allah ka ga zuciyata, Ka ga niyyata ta alkhairi ce, ta raya sunnar manzonKa. Ban yi aure
don in zamo mara biyayya ga mahaifina ba, sai don kare kaina daga dattin ZINA. Allah ga
HASHEEM! Ka dubi lamarinsa Ka tausaya masa. Ka sa sai dai ya zamo mai bayarwa ba mai
karba ba. Allah ka yalwata masa, Ka azurta shi ta inda bai tsammani ba…’ Ji ta yi Hasheem ya kwantar da kai a gadon bayanta, ya lumshe ido yana jin addu’o’inta.
Tana rufe baki ya dora tasa.
“Allah ga Halimatu-Sa’adiyyah, Ka ba ta aljannah albarkacin aure. Idan har miji ke daga wa
mace kafa ta shiga aljannah, na daga, na kara dagawa. Ina rokonKa Ka ba ta mafi darajar
aljannah (Firdaus). Ka sa ta zamo uwargidana a gidan aljannah ba tare da hurul-eeni ba”.
Da sauri ta juya ta rungume shi. Ya yi azama wajen ba ta masauki a katafaren kirjinsa. Sosai
yake sumbatarta kamar zai cinye ta. Ba ta yi nawa ba wajen maida martani. Wani yanayi suka
tsinci kansu wanda ya zarta na amarcinsu. Har suka manta cewa a gidan inna suke.
*****
Duk wani tattali na duniya Hashim ya dauka ya dora a kan cikin Halimah. Ba shi da zabi a kan
jinsin da za ta haifa, kowanne ne ya san zai so, matukar zai yi kama da Halimarsa.
Sabida halin babu, a asibitin Murtala Halima ke bin layin awo, in ka ganta ba za ka taba
tsammanin Engnr. Halimah Zubair ce ba, wadda manyan kasashen duniya daidaya ne ba ta
taka kafarta ba. Wadda ba ta taba sanin wani abu wai shi BABU a rayuwarta tun haihuwarta ba.
Haliman da ke jan motoci irin su Toyota Avensis, Discussion Continues da Rolls-Royces a
titunan Abuja. Haliman da kafin ka samu appointment din ganinta sai ka isa wane a manyan
kusoshin Nigeria. Ta dauki rayuwarta bakidaya a matsayin bautar Allah, bautar aure bautar
Allah ne. Allah shi ne mai bayarwa kuma mai karba.
A wannan lokacin imaninta ya karu, ta kara dagewa da ibadah tana rokon Allah ya sauke ta
lafiya, ta samu sanyin idaniya, wanda shi kadai za ta kalla a matsayin jininta a halin yanzu, don
alkawarin da Hashim ya yi mata na kaita ga dangin mahaifiyarta har yau bai samu cika shi ba
sabida yanayin da suke ciki. Hashim ba shi da kowacce sana’a sai lesson da yake yi wa ‘ya’yan wani maikudi a nan
unguwarsu ana biyanshi dubu goma a wata. Da wannan dubu goman da kuma taimakon Inna
suke gangandawa suke cin abinci. Ya dade da daina smoking tun suna Abuja, sabida son da
yake yi wa matarsa Halimah. Cikin Halimah na da wata bakwai, ta fito toilet da daddare za ta kama ruwa ta ci uban tuntube
da bokiti ta fada da baka a kan cikinta. Wata razananniyar kara ta saki, wadda ta taso Hashim a
gigice, yana zuwa toilet din ya kunna fitila abin da ya gani ya razana shi, jini ne ke malala daga
kasan kafafunta. Ya rasa me zai yi? Ya rasa taimakon da zai ba ta. Ga shi cikin sulusin dare. Ya sunkutota ya
fito da ita tsakiyar dakin ya shimfide. Tana ta murkususu shi kuma yana kiran sunanta yana
rokonta ta yafe masa shi ya janyo mata duk wahalar da ta ke ciki.
Wani uban nishi da Halimah ta yi sai ga Da ya fado, ba jimawa mabiya ta biyo baya.
Hannunsa na karkarwa ya dauki dan cikin kazantar haihuwa ya rungume a jikinsa. Sai dai
tsawon lokaci bai ji ya yi kukan da ake cewa jarirai na yi in sun iso duniya ba. Bai ga yana
wutsil-wutsil da kafafu da hannayensa ba. Kada dai hakan na nufin… there baby is no more? Hashim ba ya son yarda da tunaninsa.
Halimah don wahala bingirewa ta yi a wajen tana barcin wahala. Har aka yi kiran assalatu bai
ga alamun babyn nan ya motsa ba. Gari ya soma haske dole ya ajiye jaririn a gefen Halimah ya
fita ya buga wa makwabtansa kofa, ya ce su zo su taimaka masa, Halima ta haihu cikin dare. Matar gidan suna mutunci da Halimah sosai, duk da ta girme ta nesa ba kusa ba. Ta dauko
mayafi ta bi bayansa. Ta dauki jaririn nan ta bubbuga shi, amma babu motsi. Yaro babba da shi
kamar ba bakwaini ba an gama yi masa cikakkiyar halittarsa.
“Ku yi hakuri Hashim, bai zo da rai ba, ko kuma bayan haihuwar ya koma”.
Hashim ya rike kansa yana fadin, “Ya Allah I seek your forgiveness, idan wani laifi na yi maka
ka ke hukunta ni nau’i-nau’i”.
Hajiya Mukarrama ta ce, “Kul! Hashim, maza yi istigfari ga sabonka ka gaggauta cewa
astagfirullah- alhamdu lillah…”
A hankali yake maimaitawa, kamar mara lafiyan da ya zo gargara ake lakanta masa kalmar
shahada. Ya daga Halimah daga kasa jina-jina cikin kazantar haihuwa ya rungume ta a jikinsa.
Ba ta san yana yi ba sai barci ta ke yi, wani wahalallen barci da ba ta taba yin irinsa a rayuwarta
ba. Hajiya mukarrama ta dauko kwalin indomie a kicin dinsu ta sanya jaririn a ciki ta rufe. Ta ce
ya ba ta waje ta gyara Haliman, dole ta tashi daga barcin nata. Juyawar nan da za ta yi ta ji ta
sakayau babu nauyin cikinta.
Ido ta bude a kan Hashim, shi kuma ya girgiza mata kai, sannan ya lumshe idonsa. Ta kai
hannu ta shafo cikin ba ta san lokacin da ta mike zaune ba.
“Ina babyna Hashim?”
Ya kama ta ya rike yana magana cikin taushin murya.
“Allah da ya ba mu Ya fi mu sonsa, don haka kada ki yi bakin ciki don Ya karbi abinsa”.
Halima ji ta yi duniyar na juya mata, wani duhu ya mamayi idonta. Sai bude ido ta yi ta ganta
a gadon asibiti, Hajiya Mukarrama a gabanta. Kanta bisa cinyar Hashim ko kunyar Hajiya
Mukarrama bai ji ba.
Kwanan Halimah biyu a asibitin Murtala sannan aka sallame ta. Inna ta ce Yakasai za ta
wuce da ita. Jego zata yi mata sosai domin kuwa ita da mai haihuwar wata tara ba su da
maraba. Hashim bai ja ba, ko shi ya so hakan.
Sa’adatu ita ta dinga taimaka wa Inna wajen jegon Halimah, amma Dr. Rabi’a tunda ta zo sau
daya ta jajanta ba ta kara zuwa ba. A ranta ta ce, Hashim ya je bariki ya auro mai farar kafa, ya
kasa mallakar kwandalar kansa, dan da ya haifa ma a duniya kansa bai tsira ba.
(Hasbunallahu wani’imal wakeel. Wani babban kuskure da mata ke yi ke nan, kiran ‘yar
uwarsu musulma da mai farar kafa in mijinta does not succeed in life. Sun manta an ce rabon
bawa da arziki sai mutuwa. Sannan RAI DAI… ba ya rabuwa da rabo… sai dai idan ya kare.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba. Idan kuma Ubangiji ya riga ya rubuta
wa bawa kaddarorinsa na rayuwa ciki har da arziki da talauci, babu dan Adam din da ya isa ya
kankare. Allah ka hani harshenmu yi wa ‘yan uwanmu musulmi mugun alkaba’i, ameen).
Ranar da Halimah ta yi kwanaki talatin tana jego, wani mummunan tashin hankali wanda ya fi
na rasa baby ya same su.
Ya tsayar da komai na rayuwarsu dungurugum!
Inna Haajara ce ta shiga bandaki da buta a hannunta za ta yi alwalar magriba, sai ta zame ta
fadi, shiru-shiru Halimah da Sa’a ba su ganta ta fito ba, sai zuwa suka yi suka tadda ta ba rai a
jikinta.
Halimah na ganin cewa, mutuwar Inna Haajara, ita aka yi wa mutuwa ba kowa ba, don ita ce
ba ta da kowa da za ta kira uwarta bayan Innar.
Ta rike ta da amana da kyautatawa kamar uwar da ta haife ta. Ta zauna da ita da zuciya
daya. Zuwa yanzu ta gama fahimtar Dr. Rabi’a ba ta sonta a kan dalilin da ba ta sani ba.
A wajen makokin Inna ta wulakantata a cikin mutane ya fi a kirga, sai dai ta shiga daki ta ci
kukanta ta more. Har tana cewa tunda ta shigo gidan su masifa ke bibiyar Hashim. Sa’adatu ce
ta samu Yayanta a boye wanda mutuwar mahaifiyarsa ya fyadar da shi a lokaci guda, don
mutuwa ce kamar ta fuju’a, Inna lafiyarta kalau ko ciwon kai ba ta yi ba. Tana tsaka da hidimta
wa rayuwarsu Allah ya amshi ranta.
Ta gaya masa duk abin da Dr. Rabi’a ke fada a kan Halima, kuma a gaban idon Haliman.
Hatta gashin jikin Hashim gabadaya sai da ya mimmike, idanunsa suka kada suka yi jajir,
bakinsa har rawa yake kamar yadda ilahirin jikinsa ke kyarma kamar ana kada masa gangi. Bai
tsinci kansa a ko’ina ba, sai a gaban Yayarsa Rabi’a. “Adda Rabi’a, ki sani daga yau babu ni babu ke. Ko a hanya muka gamu kada ki nuna kin
taba sanina. Da ma Inna da Baba ne suka hada kuma babu su, me rabawa ta raba.
Wadda ki ke kira ‘yar barikin mai farar kafar ta fiye min ke sau shurin masaki. Sannan babu
wanda ya isa ya taba mutuncin ta in kyale shi. Ko wane ne, idan na ce kowa… ina nufin ko KE!”
Rabi’a ta bude baki tana kallonsa.
“Hashim ni ka ke yi wa diban albarka a kan mace? Macen ma wadda ta zabi namiji a kan
iyayenta? Tunda ka aure ta mun taba ganin wani nata? In ba daga barikin ta fito ba, daga ina ta
ke?
Hannunsa ne ya fita daga jikinsa zai mari Rabi’a, ya tuna yawan shekarunta a kan nasa.
Hankali tashe ya juya don barin wajen ya yi ido hudu da Halimah da ke rakube a bayan kofa.
Yawan hawayen da ta ke bulbularwa su suka tabbatar masa ta gama jin maganganun Yayarsa
Rabi’a. Hannunta kawai ya ja, suka bar dakin Inna zuwa nasu dakin. “Hada kayanki tsaf mu koma gida”.
Ba ta iya ta ce komai ba ban da bin umarninsa. Ta gaban Adda Rabi’a da sauran ‘yan zaman
makoki da ba su kai ga watsewa ba Hashim ya wuce rike da Halimah. Daya hannun nasa kuma
jakar kayanta ne. Adda Rabi’a ta yi tsaki ta ce,
“Idan ka ga dama ku bar kasar kai da mai farar kafarka”.
A wannan daren, duk iya rarrashi irin na Hashim, duk kwarewarsa wajen sarrafa harshe, ya
kasa rarrashin Halimah. Wadda ta hada kai da gwiwa tana rero kuka mai tsuma rai da keta
zuciya. Tambayar kanta ta ke, to ko abin da ta yi don tserar da kanta daga zina wato AURE
kuskure ne? Ko dai Daddy ne a kan daidai? Ya san haka auren yake shi ya sa ya ce ba za su yi
ba, don ba zai iya jurar wani ya wulakanta masa su ba? Yau abin da ya fi wulakanci ta gani a
gidan aure a bainar jama’a.
Shin mene ne laifi a cikin soyayyar da ta ke wa Hashim? Ta baro gatanta, pride dinta,
duniyarta, kwalayen ilminta, reputation dinta, career dinta duk don ta rayu da Hashim, yau
abokiyar haihuwarsa na neman kala mata witchraft (maita) tunda a fakaice so ta ke ta ce Inna
ma ta rasu ne saboda ta rabe ta, kalmar farar kafa ta kasa bacewa daga zuciyarta. Yau ita ake
yi wa gorin rashin yin arziki, bayan wanda ta tsallake saboda HASHIM!!!
****
BABI NA GOMA
Ba ta rarrasu ba sai da ta ga Hashim yana hawaye shi ma, abin da bai taba yi a gabanta ba. Ya
tabbatar mata ba shi ba yaya Rabi’a, ya yanke duk wata ‘yan uwantaka da ke tsakaninsu. Ba ita
ta ci wa mutunci ba shi ta ci wa. Tunda shi ne fakiri ba ita ba, shi ne mai farar kafar da ya raba
ta da duniyarta, ya tsumbula ta a tasa duniyar ta talauci da wahala…”
Da sauri Halimah ta toshe masa baki, “In kana so in hakura sai ka janye kalaminka na cewa
ka yanke zumunci da ‘yar uwarka. Kai fa ka ce min akwai wutar da Allah ya tanada saboda
masu yanke zumunci. Ta kira ni duk abin da ta ga dama, BA ZAN DAINA SONKA BA!!!
Wata irin runguma Hashim ya yi mata, tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanya ta.
“Halimah you are indeed a virtous wife, who her price is far above rubies”. (Zaynab Alkali).
Soyayya nau’i-nau’i ya shiga nuna mata duk da ba ta responding amma ta yi accepting. Har
sai da ya tabbatar ya mantar da ita Yaya Rabi’a and her hayaniya. Ya mantar da ita kalmar
‘Farar Kafa’ da ta ke ta yi mata yawo a kwanya. Bai bar komai cikin kwanyar tata ba, sai tunanin
ci gaba da rayuwa da shi har zuwa karshen numfashinta.
*****
Lokacin da aka raba gadon Inna, wanda ba komai ba ne kajin gidan gona ne da wasu
dabbobinta, kasancewarsa namiji ya samu rabin dabbobin yayin da Rabi’a da Sa’adatu suka
samu kaso hamsin cikin dari su biyu.
Sa’adatu ta koma gidan Rabi’ah kafin lokacin bikinta ya cika, amma tana yawan kawowa
Halima ziyara. Wani lokacin ma har ta kwana, duk da zagin da Dr. Rabi’a ke mata kan sai ta
kwaso wa kanta wata masifar. Gidansu na gado ne, mallakinsu duka ukun don haka suka barshi
ba tare da sun sayar ba. Halima ta zauna ta yi tunani, ta ga cewa za ta iya zama a gidan Inna, ko don ta ci gaba da yin
sana’ar Inna su kara samun rufin asiri. Don haka ta bai wa Hashim shawarar su koma Yakasai,
gidansu su bayar da shi haya, tunda yana da kyau, kuma yana da yalwa. Sannan yana
fitacciyar unguwa kamar