Showing 27001 words to 30000 words out of 48040 words

Chapter 10 - AURE KO BOKO PART 1&2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

dawo? Da fatan
kin samu su Inna lafiya?”
Filo ta dauka ta hau buga masa shi kuma ya rike yana mata dariyar keta. Ya ce, “Ita Inna ai
so ta ke a yi maza a dire mata jika tunda haka ne kuwa dole ta dawo da ke ki kwana bisa
hakarkarin mijinki”.

Washegari Inna ta hada musu breakfast mai kyau, kunun gyada fari tas ya ji madarar ruwa ta
peak da wani lafiyayyen kosai mai dadi wanda aka fasa kwai a cikinsa. Sa’adatu ce ta kawo
musu, suna ci tana ta santi. What a simple life! Wato a rayuwa ko kwalin PhD gare ka ba za ka
daina daukar ilmi ba. Yau ta shigo wata rayuwa da ba ta san da ita ba. Amma sai ta samu ta fi
tata dadi da armashi. Tabbas dumbin arziki ba shi ne jin dadin rayuwa ba.
A ganin Halimah ka samu mijin da ke sonka, uwa mai sonka a gefe da rufin asirin Allah ba
tare da ka ci hakkin kowa ba shi ne jin dadin rayuwa. Tana missing Daddy, amma ta fi maraba
da sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta.

Washegari Inna sai fitowa ta yi ta ga Halimah na yi mata wanke-wanke. Ta share tsakar gidan
tsaf! Inna ta runtse idonta tana fadin,
“Me ya sa Halimah? Don me za ki wahalar da kanki daga zuwanki jiya-jiya? In kin bari ai
Sa’adatu na gida za ta yi in gari ya gama haske. Don Allah kada ki kara tunda kanwarku tana
nan”.
Maganganun Inna ne suka taso Hashim daga barcin da ya koma bayan ya dawo masallaci.
Ya shafa gefensa babu Halimah. Mikewa ya yi ya zura jallabiyyarsa kan wandon jikinsa wanda
bai karasa idon sawunsa ba ya fita.
Nan ya same su ita da Inna, Innar na ta yi mata fadan wanke-wanke da shara. Murmushi ya
yi ya koma daki, Halimah ta kara shigewa sukuf! Cikin ransa ta yi wa kowacce mace fintinkau a
zuciyarsa.
Kullum kafin a dora abincin rana sai Inna ta tambayi Halima abin da ta ke so shi za a girka,
haka duk dare. Halimah ta fi ambatar abincin gargajiya wanda ba ta saba da shi ba. Ga Inna
gwanar girkin gargajiya, Halimah kan zauna gefe ita da Sa’adatu suna taya ta ayyuka tana nuna
musu yadda za su yi, tana kuma yi wa Halima bayanin komai don ta iya a karan-kanta. Da ma
kuma kwakwalwar Halima ba irin ta kowa ba ce tsaf! Ta ke dauke komai, har ana i-gobe za su
koma Abuja Inna ta sakar musu girki ita da Sa’adatu, suka yi sinasir da miyar ganye. Kuma
sinasir din ya yi kyau sosai. Dare ya yi su shige daki mijinta ya shayar da ita soyayya mai zakin
da ta fi ruwan zuma, wanda bukatar Halimah a rayuwa ke nan. Ba ta fito fili ta fada ba, amma
Hashim a matsayinsa na mai ilmi ya gama gane she’s a nymphomaniac. Yana rokon Allah ya
tsawaita ransa, ya ci gaba da ba shi lafiyar da zai ci gaba da iya wa Halimah da dukkan bukatun
rayuwarta.
Sun je gidan Dr. Rabi’a sun wuni, sai dai ko kadan Halimah ba ta ji dadin tarbar da ta samu
daga Rabi’a ba, kamar ba ta farin ciki da ita matsayin matar kaninta, kuma ba ta san me ya sa
ba. Ita kuwa Rabi’a a bangarenta gani ta ke Halimah ta fi karfinsu, za ta mallake musu dan uwa
ko da wannan fitinannen kyawun nata. Bayan wannan ba ta da wani dalili na not welcoming
Haleemah.
Da za su tafi Halimah ta kawo tsarabar swiss-lace mai kalar ruwan zuma ta ba ta. Dr. Rabi’a
ba ta taba haihuwa ba.
Kafin su bar Kano sai da aka aza harsashin ginin Hashim a matsakaicin filin da ya saya a
unguwar Janbulo, karamin gida ya sa aka zana masa wanda ba zai ci kudi ba. Amma ya samu
tsari mai kyau. Only three bedrooms da falo mai yalwa, kitchen wadatacce da toilets guda biyu,
get din gidan karami ne, parking space mai cin mota daya. Sun je shi da Halimah sun ga yadda ake aikin. Sosai Halimah ta yaba kai ka ce wani
hadadden gida ake mata a G.R.A, Allah Ubangiji da ya halicce ta sai ya sako ta cikin masu
wadatar zuci, masu yakanah, masu godiya ga duk ni’imar da ya yi musu komai kankantarta.
Kwanakinsu bakwai cif! Suka kamo hanyar Abuja, bayan motarsu dankare da tsarabobin da
Inna Haajara ta hada musu. Halimah ta yi kewar dattijuwar har ta ke rokon Hashim ya dauko
musu ita ta kwana biyu tare da su a Abuja. Hashim ya ce, Inna ba za ta yarda ba.
Bayan dawowarsu daga Kano, Hashim ya soma buga-bugar neman aiki a ma’aikatu ko Allah
zai sa ya dace, Halimah da babu takardu a hannu sai zaman gida, da girka wa maigida abinci.
Haka bai hakura da cike vacancies ta online ba. Wasu za su kira shi aptitude daga nan ba ya
kara ji daga gare su.

Dan kudin hannunsa gabadaya gini ya lamushe, inda Allah ya taimake su ma kudin hayar na
shekara suka biya, kuma sun shake store da freezer da abinci, abin da suke saya ba shi da
yawa. Haka zai fita tun safe goye da jakar takardunsa sai magriba zai dawo a yunwace babu ko
sisi. Halimah ta koyi wani abu wai shi tattali na kayan abinci da kayan sanyawa, wanda a
rayuwarta ba ta taba zaton watarana irin wannan za ta zo mata ba. Da za ta yi wa kaya
sanyawa har uku kafin ta wanke su.
Inda Allah ya kara taimakonta cikin kayan da Daddy ya yi mata har da karamin injin wanki, da
shi suke wanki, ta zauna ta goge musu kayan da kanta da iron, wanda shi kansa amfani da iron
din Hashim ne ya koya mata.
Sabida zurfin ciki irin na Halimah, suna yawan waya da Hanan amma ko da subutar baki ba
ta taba gaya wa Hanan suna cikin wani hali ba, balle ta nemi taimako daga gare ta. Abin da ta
sa wa ranta shi ne, Allah na tare da su, kuma bai manta da su ba.
Shekara ta zagayo Halimah ko batan wata ba ta taba yi ba, babu aiki ga Hashim babu
alamarsa. Allah kadai ya san da yadda suka cimma shekarar nan a cikin garin Abuja. Kudin
haya ya kare aka ba su notice, dole suka tattaro komai nasu da ke cikin gidan cikin akori-kura,
kudin akori-kurar ma Landlord (mai gidan da suke haya) shi ya biya musu (full tank) sabida sun
yi zaman mutunci tare da shi.

Gidan nasu an gama ginin, an yi plasta, amma ba a samu zarafin yi masa fenti ba. A haka
suka shiga abinsu, Sa’adatu da Dr. Rabia suka zo suka taimaka musu suka jera kayan Halimah,
sabida kayan masu quality ne ba abin da suka yi. Dr. Rabi’a ta tambaye shi ya ba a yi fenti ba?
Shiru ya yi yana sosa kai, ta san halin Hashim sarai, ba ya bayyana babunsa sai samunsa. Idan
ya samu kowa da ke jikinsa sai ya shaida ta hanyar kasonsa da zai ware masa.
Dan aikin da ya yi a Abuja na shekara guda ba karamar hidima ya yi musu ba, don haka
washegari sai ga masu yin fenti ta turo su yi duk gidan, ba tare da ta yi shawara da Hashim ba.
Kwarai ya ji dadin wannan karamci na ‘yar uwarsa. Har gida ya je ya yi mata godiya. Halimah
gwanar iya tsari, sosai ta tsara gidanta, ya yi kyau sosai kamar gidan wani ma’aikacin banki.

*****

A yayin da rayuwa ta juya wa dan Adam, abin da ake so shi ne, ya karfafa imaninsa, ya sa a
ransa Allah na sane da shi. Yana jarraba imaninsa ne. To hakan ce ta faru da Halima, ranar da
ta budi ido a gidan mijinta ko kwayar shinkafar da za su dafa ba su da ita. Ba irin buga-bugar
neman aikin da Hashim ba ya yi har kuwa da koyarwa a sakandire, amma condition na kasarmu
da komai sai kana da kafa ya hana Hashim samun aiki. Har tsohuwar makarantar da ya yi
koyarwa wato ‘Yan Dutse ya je ya roki su maida shi, inda suka sanar da shi ai tuni suka maye
gurbinsa da wani. For now ba sa bukatar sabbin malamai.
Don haka wuni guda sur! Yau Hashim ya kasa fita ko’ina, babbar damuwarsa ita ce ya bar
Halimah da yunwa. Wasu hawaye masu zafi ke taruwar masa a ido yana maida su. Ba ya
nadamar auran Halimah, kuma har abada ba zai yi ba. Ya yi alkawarin rike Halimah da kula da
ita, amma in bai da abin yi da me zai kula da itan? Da me zai ciyar da ita? Ba ya son ya gaya
wa Inna halin da suke ciki, don kuwa yanzu za ta maida ciyarwarsu a kanta, dan jarin kiwon kaji

da ragunanta ya kare a kansa. A wannan matakin na rayuwa kam, in bai ciyar da Inna ba, ai ba
zai bari ta ciyar mishi da mata da shi kanshi ba.
Wani tunani ne ya zo masa, zumbur ya mike ya dau mukullin motarsa ya fita. Halimah na
kallon talabijin shirin Arewa24 cikinta yana ta damka, yunwa kamar ta mutu, rabonta da abinci
tun daren jiya da suka ci gurasar teburin mai tsire. Tana ta cijewa tana daurewa, tare da kurbar
ruwan bunun da ke cikin kofi a gefenta, wanda ko sukari babu a cikinsa. Ta gabanta ya zo ya wuce da sauri, tana tambayarsa inda za shi, yana tafiya yana ce mata,
“I’m coming…”
Wajen sayar da motocin hannu ya nufa, aka yi cinikin henessy dinsa, kashi uku cikin goman
kudin da ya siye ta. Ya bada takardu aka dunkulo kudinsa aka ba shi.
Bai zame ko’ina ba sai super market ya dankaro wa Halimah shopping ya sayo kayan abinci,
aka cika masa dan sahu taf! Ya nufo gida. Halimah sai gani ta yi ana ta sauke mata kaya,
mamaki ya hana ta cewa komai, har yaran suka gama Hashim ya sallame su.
Zama ya yi rigijib a kan kujera cike da gajiya. Halimah ta zauna kusa da shi a sanyaye.
“Cherie, ina ka samo kudi haka? I hope it’s by halal means?”
Rungumota ya yi barin jikinsa na dama, “Ki min zaton alkhairi Sweetheart, ba zan taba ciyar
da ke da haraam ba”.
Tana wasa da botirin rigarshi ta yi murmushi, ta ce, “I trust my husband, but I need an
explanation”.
Ya ce, “Sai kin ci abinci ga kaji nan a ciki ki gyara ki yi mana farfesu. Tashi mu je in taimaka
miki”.
Tare suka yi girkinsu mai rai da motsi, wanda suka dade ba su ci irinshi ba, suka ci cikin
marmari. Sai lokacin kwanciya barcinsu yake sanar da ita motarsu ya siyar, ba zai iya jure
ganinta tana jin yunwa ba, in Allah bai kama shi da laifin hakan ba, shi ba zai taba yafe wa
kansa ba. Ko kadan Halimah ba ta ji dadi ba, domin ta saba da motar, amma ta yarda ba su da wani
option na samun kudi masu kauri ban da hakan.
Ta ce, “Sauran kudin me za ka yi da su?”
Ya jingina a jikinta, ya ce, “Karamin provision shop zan bude a dan shagon jikin gidan nan”.
Halimah ta amince da shawararsa, ta kuma ce ya debi kayan abincin ya kai wa Inna ko don
ta sa musu albarka.
Cikin sati daya provision shop ya budu, Hashim na zama a ciki daga karfe tara na safe zuwa
azahar, ya shigo ya ci abinci ya koma, la’asar ya shigo ya yi sallah ya kuma zuwa magriba ya
rufe shagon sai kuma gobe. Dr. Rabi’a ma na kokarin nema masa lecturing a Legal, amma abu
ya faskara sabida ba sa karantar da field dinsa. ****




BABI NA TARA
Halimah na suyar manja da za su ci wake da shinkafa da shi, ta ji kauri wanda ba ta san daga
ina yake fitowa ba. Ta dudduba dakunansu ta tabbatar ba daga nan ba ne, sai kawai ta koma

kicin ta ci gaba da aikinta.
Hashim ya tafi kasuwa zai saro kayayyakin da suka kare a shago. Bude wannan shago ba
karamin taimako ya yi musu ba, ba sa samun wata riba ta a zo a gani, amma suna daukar
komai su yi amfani da shi kenan ribar a cikinsu suke cinye ta.
Ba su da matsalar abinci, omon wanki, sabulun wanka ko sauran kananun abubuwan
amfanin yau da kullum. Sannan suna diba su kai wa Inna na neman albarka. Ita kuma
lokaci-lokaci tana aiko musu da cret din kwai da kajin gidan gona biyu ko uku.
Ta gama suyar manjanta wanda ya ji albasa, sai tashin kamshi yake yi, ta ji hayaniya daga
waje ana fadin, “A kawo taimako… gobara! Gobara a shagon Hashim!!!”
Saboda kidimewa ba ta san sanda ta saki soyayyen manjan hannunta ba ya kware a kan
kafafunta.
Wani ihu hade da salati Halimah ta saki, duk da azabar da ta ke ji, amma hankalinta na kan
gobarar da ake fadi a shagon Hashim. Kafin ka ce me ye wannan fatar farar kyakkyawar kafarta
ta tashi ta kukkumbura. Amma a haka ta yo waje da gudu ko mayafi ba ta tsaya dauka ba,
domin ta manta da shi. Wuta ce ganga-ganga mutane nata watsa mata ruwan omo, amma sabida kayan da ke ciki
masu cin wuta ne sai kara habaka ta ke yi, Halima ta koma gefe tana hawaye tana kallon yadda
gabadaya abin da suka dogara da shi yake konewa kurmus! Shago kam ya kone, ba abin da ya
yi saura sai gawayi. Sai da ya gama konewa aka samu wutar ta tsaya, already ba abin da aka iya cirewa sai
gawayi. Har ta soma lasar wani bangare na bangon gidan ya yi bakikirin. Babu wanda ya lura
da Halimah ta durkushe ta ci kukanta ta koshi, sai da mutane suka watse ana ta cigiyar Hashim,
sannan ta lallaba ta koma gida.
Sai yamma lis Hashim ya dawo cikin adaidaita sahun da aka dankaro wa kayan provision.
Tun daga nesa ya hango bangon gidansa ya yi bakikkirin.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Kawai yake ambata, har mai adaidaita ya juyo yana
tambayarsa, “Malam lafiya?”
Motar na tafiya haka Hashim ya dirgo ya yanka a guje, ba abin da yake masa amsa-kuwwa a
kunne irin HALIMAH!!!
Ga babban kwanciyar hankalinsa da ita ya fara tozali yana shiga harabar gidan, tana zaune a
kan kujerar roba da suke zama da yamma su sha iska ta kada kanwa tana ta kwara wa kafarta
bayan tuni ta riga ta tashi. Da sauri ya duka ya rungume ta yana fadin,
“Halima, are you alright?”
Har wani irin girgiza ta yake yi. Da ganinta ta ci kuka ta koshi.
“Tell me Halimah, are you okey?”
Ta sanya fuskarsa cikin tafukanta ta ce, “I’m okey Hashim. But shagon mu ya kone kurmus,
shi ne garin kidima na kone kafafuna da manja”.
Ya kai idonsa ga kafafun nata, tsigar jikinsa ta yi wani irin tashi. Ga shi ba shi da motar da zai
saka ta a ciki ya kai ta asibiti, kada kuma ya goya ta a bayansa a ce ya haukace. Amma tabbas
ba shi da maraba da zautaccen a wannan lokacin. Ba shago ne damuwarsa ba, lafiyar Halimah
ce. “Bari in samo adaidaita sai mu tafi asibiti kin ji? Sorry sweetheart”.

Ko ta kan zancen shago bai bi ba, ya juya ya fita jikinsa na kyarma, mutanen unguwa nata yi
masa jaje, amma ko amsawa ba ya iya yi, ya tare dan sahu ya shige ba bayani, da kyar ya ce
da shi matarsa za su kai asibiti.
Har cikin get suka shiga da adaidaitan, ya dauko mata hijabin sallarta. Bai ji kunyar mutumin
ba ya sunkuce ta ya sa ta a motar tana fadin, ya kyale ta za ta iya takawa, amma ina!
Asibitin malam Aminu Kano suka je, bangaren accident & emergency, da kyar suka samu aka
karbe su. Aka yi mata treatment sosai tana ta kuka da hawayenta don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login